Chapter 23&24
by @nanameera08
*IMARA 💋💋*
Chapter 23-24
Mikiya writers asso...
A ƙofar gidansu ya yi parking, ya kashe motar ya juyo yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi. Haɗe gifts ɗinta tayi tana ƙoƙarin buɗe motar ya ce"a'a, ko sallama babu zaki tafi?" hannunta akan handle ɗin ƙofar ta ce"Nagode Sosai Allah ya saka da Alkhairi" ɗan murmushi ya yi ya ce"shikenan, tunda naga gidan zan zo" da sauri ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta. Fahima dake kallonsu tun ɗazu ta ce"tom friend, bye, Allah ya ƙaddara saduwarmu" murmushi Imara tayi tana kallonta ta ce"Nagode sosai Fahima sai anjima" murmushi suka yi a tare ta buɗe motar ta sauka. Sauka shima yayi ya ciro mata trolley ɗinta yana murmushi ya ce"sai na zo" ɗan murmushi tayi baya bata ce komai ba ta juya ta shige gida.
Da É—an saurinta ta shiga gidan tana murmushi ta ce"Granny! Granny! Granny!, ki fito na dawo, I'm back" shiru Imara taji hakan yasa ta É—an haÉ—e rai ta ce"grannyyy! kina ina?" Ajiye kayan hannunta tayi akan tabarma sannan ta shige É—akin da sauri
"Granny ina ta kiranki kina bacci, ko zuwa ki ɗaukeni ba kiyi ba" tafada tana faɗawa kan katifar, murmushi tayi ta shiga janye bargon data rufa tana cewa "a wannan zafin kike rufa granny, gaskiya..." Kasa ƙarasa maganar tayi saboda ganin yanda Granny ke rawar sanyi, a firgice ta ce"subhanallahi, bakida lafiya ne Granny, zazzaɓi kike ne?" hannunta Granny ta kama jikinta na rawa ta ce"Fatima" kallonta Imara tayi tana hawaye ta ce"na'am Granny, sannu, bari na kira likita ya duba ki, ko muje asibiti ne?" ɗan murmushi tayi ta ce"ai ciwona bana asibiti bane Imara, kedai ki dinga yimin addu'a kinji, ki daina wannan kukan" tafada tana share mata hawaye, riƙe hannunta Imara tayi tana girgiza kai ta ce"a'a Granny, wlh bansani ba ma dana nemi excuse a school nazo, ki tashi muje asibiti dan Allah, ni banason naga mutum bashida lafiya, barin ma kuma ke, ki tashi Granny" ta miƙe daga kan katifar ta buɗe kayansu ta ɗauko mata hijabi, kallonta kawai granny take tana murmushi mai haɗe da hawaye, dawowa Imara tayi ta saka mata ta ɗagota ta ce"Granny tashi mu tafi, daure kinji" girgiza kanta tayi idanunta na neman rufewa ta ce"a'a Imara, daina taɓa ni, ciwon dake jikina baya son a taɓa shi, akwai wasu maganganu da nakeson faɗa miki.
IMARA ki kula da rayuwa ki yarda da duk ƙaddarar data zo miki ba lallai yanzu ki fahimci abinda yake akwai ba amma tabbas watarana zaki gane abinda nake yawan gaya miki idan kinada rabo zaki iya haɗuwa da iyayenki idan kuma ubangiji bai ƙadarta ba to shikenan ke dasu har abada, hannunta ta sanya cikin samirar dake gefenta ta xaro wata kyakkyawar sarƙa sai kyalli take cikin kakkarwar hannu ta danƙa mata cikin nata siririn hannun tana kallonta da idanunta wanda suka fara rufewa ta ce"wannan ita kaɗai ce ragowar abinda yake mallakinki ki kula da ita karki bari tabar wuyanki IMARA domin ita ɗin ƙaddararki ce ki kul..." Tsit ɗan ƙaramin ɗakin ya ɗauki shiru na wasu sakwanni kafin Imara ta mayar da idanunta kan mahaifiyar tata ta kalleta da son sanin abinda ya sanya tayi shiru saidai yanda taga idanunta sun ƙafe ya sanya ta saki wani razanannen ihu, sakinta Imara tayi ta shiga girgiza kai bakinta na rawa ta ce"granny banason irin wannan wasan, ki bari, ni ki daina yimin, ki tashi kawai wlh" jin tayi shiru bata ce komai ba yasa ta tashi a firgice tayi waje. Makotansu gidan Baba Hansatu ta shiga, zaune ta sameta tana yanka kuɓewa ta ƙarasa cikin tashin hankali ta ce"Baba zo muje ki ganta, granny ce, granny Baba" tashi Baba Hansatu tayi ta ce"mene ya faru?" Waje Imara tayi tana ihu, mayafi ta zara akan igiya tayi waje ƙafarta babu ko takalmi.
Zanin dake gefenta Baba Hansatu ta sanya ta rufe fuskarta, wata zabura Imara tayi ta ƙarasa wajen ta yaye zanin ta rungume granny jikinta sai wata irin kyarma yake, hannunta Baba Hansatu ta kama tana kuka ta ce"kiyi haƙuri Imara, Allah ya yiwa Asiya rasuwa, daman tunda kika tafi makaranta ciwo ya zo ya ci ƙarfinta, gashi kuma yanzu ya yi ajalinta kiyi mata addu'a kawai" girgiza kai Imara ta shiga yi tana sauke ajiyar zuciya dan kuka ma ya gagara ta yisa, tashi Baba Hansatu tayi ta fita dan faɗawa sauran maƙota su shigo ayi mata suttura a kaita gidanta na gaskiya.
*Days later*
Zaune take kan tabarma a tsakar gidan, ta cure jikinta waje guda, tunanine fal zuciyarta, tun ranar da aka kai granny ƙabari bata sake samun nutsuwa ba, shikenan ita yanzu batada kowa, kowa ya tafi ya barta, babu Daddynta babu Umma, babu granny babu Dodo, kowa ya gudu ya barta, ita kaɗai, kuka ne ya ci ƙarfinta ta kifa kanta tana yi babu ƙaƙƙautawa. Sallama aka yi ta ɗago kanta ba tareda ta amsa ba, kwanan abinci ta ajiye mata ta ce"gashi nan in ji baba ta ce a kawo miki" kallon kwanon abincin tayi sai kuma ta kalli yarinyar ta sake sunkuyar da kanta, girgiza kai Asabe tayi ta juya ta fice daga gidan. Haka Imara ta cigaba da rayuwa a cikin gidan ba tareda kowa ba, babu wani mai ɗauke mata kewa ko kuma ya yi hira da ita, gaba ɗaya ta rame saboda damuwa da tayi mata yawa, a haka har akayi arba'in ɗin mutuwar Granny.
Tashi tayi babu ruwa a gidan dan famfon nasu ya daina yi, hakan yasa ta ɗauki bokiti dan ta samo wanda zata yi amfani dashi, tafiya kawai take ba tareda tana kallon gabanta ba, tunani ya yi mata yawa, bata banbance a gida take ko kuma a hanya. Duk irin horn ɗin da suke mata bata ji ba, wani wawan burki yaja dan sauran kaɗan ya kaɗeta, sai a sannan ta dawo cikin hankalinta ta kalli motar dake gabanta. Kallonsa ɗaya na cikin motar ya yi cikin harshen larabci ya ce"lafiya dai?" kashe motar ya yi bai ce masa komai ba ya sauka daga motar, ƙarasawa wajenta ya yi ta ɗan kalleshi a rikice ta ce" I'm sorry dan Allah ban ganku ba" shiru taji ya yi yasa ta sunkuyar da kanta, fitowa ɗayan ya yi yana kallonsa ya ce "wai Maheer mene haka ka manta abubuwan dake gabanmu ne?" ko ta kansa Maheer bai bi ba, sai ma sake kallonta da yake yana murmushi, cikin sanyin murya ya ce"sannunki" kallonsa tayi ta ce"yawwa, kuyi haƙuri na ɓata muku lokaci" ta faɗa tana kallonsa, murmushi ya yi ya ce" ba komai yarinya, ina zaki je haka?" kallon bokitin hannunta tayi ta ce"ruwa zan ɗan ɗebo" shiru ya yi sai kuma ya ce"ɗebo ruwa kuma da kanki?" jinjina masa kai tayi dan maganar ta fara damunta. Murmushi ya yi ya ce"anyway, I'm Maheer bin Fahad al-kuwari, mun zo aiki ne daga Qatar kuma naji ina sonki idan babu damuwa zan aureki" da sauri Imara ta kalleshi sai kuma ta ɗauke kanta tana wasada fingers ɗinta, jin bata ce komai ba yasa ya ce"kefa ya sunanki?, ina ne gidanku?, bakiyi kamada yar nan garin ba kodai kin zo hutu ne?" ɗan murmushi tayi ta ce"a'a anan nake, gidanmu yana can baya babu nisa" numfasawa ya yi ya ce"muje naga gidan to, ki bar ɗiban ruwan za'a kawo muku" toh kawai ta ce dashi sannan tayi gaba yana bin ta a baya. Kallonsa Tareeq ya yi sai kuma ya girgiza kai ya biyo su. A ƙofar gidan ta tsaya ta ce"nan ne gidanmu, amma babu kowa a ciki sai ni kaɗai" dan waro idanu ya yi ya ce"meyasa?, ko sunyi tafiya ne?" gyaɗa masa kai tayi saboda kukan daya tawo mata ta shige gidan ba tareda ta sake cewa komai ba. Da idanu ya bita har ta shige sai kuma ya juyo ya kalli Tareeq, harararsa ya yi ya ce"ai sai ka shige mu tafi ko, nasan meyasa ka biyota ai, koni nayi mamaki sosai, kamar Katalina fa" ɗan haɗe rai ya yi ya ce"bansan ana kiran sunanta ka sani, zan samo information ɗin yarinyar nan da ita zan koma Qatar" tuntsirewa da dariya Tareeq ya yi ya ce"idan kaje tanada wanda take so fa?, har zaka wani yi confirming na tafiya da ita?" tsaki ya yi bai ce masa komai ba ya hangi wani yaro, da hannu ya yi masa alamar da ya zo yaron ya zo yana kallonsa ya ce"akwai manya a gidan nan? ya nuna gidan Baba Hansatu, gyaɗa masa kai yaron ya yi ya ce"Eh akwai, gidan Baba Hansatu ne" ajiyar zuciya ya sauke ya ce"yawwa Boy, cene ana sallama da ita kaji" da gudu ya bar wajen ya shige gidan. Kallon Tareeq ya yi ya ɗaga masa gira, dariya kawai ya yi ya cigaba da danna wayarsa.
Fitowa Baba Hansatu tayi tana wurga idanu ganin jajayen fata, cikin rawar murya ta ce"sann... sannu yaro, Allah dai yasa ba wani abun nayi ba?" murmushi Maheer ya yi cikin harshen Hausa wanda ba zaka yi tunanin ya iya ba ya fara magana "ko kaɗan bakiyi laifi ba Baba, kawai wasu tambayoyi nake son nayi miki idan babu damuwa" jinjina kai tayi ta ce "to...to.naji Allah ya sa na sani" jingina ya yi da jikin wata bishiya yana kallonta ya ce"wannan yarinyar ta gidan nan, wata fara ta cemin ita kaɗai ce a gidan Inason sanin gaskiya al'amarin" girgiza kai tayi ta ce"Imara kake nufi kenan, Allah sarki, ita da kakarta ne a gidan to kakar ta mutu, kai asalima ba wannan ce kakar tata ba, ƙawar kakarta ce, aka kashe iyayenta kakar ta ɗaukota daga birni to itama aka biyota aka kashe shine ta bawa wannan riƙo kuma yanzu Allah ya yi mata rasuwa. Ita kaɗai take rayuwa a gidan ko ƙawa batada ta kammala makarantar sakandire ma" numfasawa ya yi ya ce"Allah sarki, Allah ya jiƙansu da Rahama, yanzu Baba idan inason aurenta wa zan samu kenan?" Zaro idanu tayi ta ce"aurenta zaka yi?" Gyaɗa mata kai ya yi ta ce"da kuwa ka taimaka mata, akwai mijina sai ya zamar mata waliyyi kai kuma ka kawo naka waliyyin a ɗaura auren" murmushi ya yi ya ce"ai kuwa da na gode sosai in sha Allah zuwa anjima zamu dawo" jinjina masa kai tayi tana murmushi ta ce"To Allah ya kaimu lafiya, an gode sosai" kuɗin Nigeria Tareeq ya zaro ya miƙa mata bandir biyu, a kiɗime ta amshi kuɗin jikinta na ɓari ta ce"kai kai kai, yaro an gode muku ku kam, meyasa sai anjima zaku dawo a ɗaura auren?, ai kawai ayi yanzu, malam yana ciki yanzu a ɗaura ku tafi da ita" murmushi Tareeq ya yi ya ce"tom Baba mun gode Allah ya ƙara girma, kira shi ɗin" komawa tayi da sauri kamar zata tashi sama, da kallo Tareeq ya bita sai kuma yayi murmushi.
"Malam!! Malam!! Malam!!" "Na'am" ya furta yana fitowa daga ɗakin, kallonsa tayi ta ce"malam abun arziki har gida, kalli kaga" ta nuna masa kuɗin dake hannunta, ganinsa tayi a gabanta ya yi saurin karɓar kuɗin yana juyasu ya ce "Hansatu ina kika sami wannan maƙudan kuɗaɗen?" dafe haba tayi tana faɗin "kai dai bari malam, ai arziki Allah ya saukar mana, wannan yarinyar wajen Asiya tazo mana da Alkhairi, aurenta za'a yi shine aka bani wannan, muje yanzu za'a ɗaura auren kai ne waliyyinta" naɗe hannun babbar rigar dake jikinsa ya yi ya ce"Allah mai iko, to muje, kawo a ajiye wannan" ya fita yana tafiya kamar zai fadi.
Anan ƙasan bishiyar aka ɗaura auren Imara da Maheer akan sadaki naira miliyan 1, Tareeq ne ya ce"ya kamata a kira yarinyar dan a bata sadakinta a hannunta" girgiza kai Malam ya yi ya ce"a'a, ba sai an kirata ba kawai a bani zan ajiye mata" murmushi Tareeq ya yi ya ce"ai yanada kyau a sanar da ita sannan ta karɓi haƙƙinta da kanta" ba dan ya so ba aka aika yaro ya yi kiranta. Fitowa tayi tana sanye da hijab onion colour, hangosu da tayi yasa ta ɗan tsaya tana waro idanunta, da hannu Baba y yi mata alama da ta zo ta ƙaraso, cikin sanyin jiki ta ƙarasa wajen murmushi ya yi yana kallonta ya ce"yawwa ƴar albarka daman kiran ki aka yi a nuna miki mijinki a kuma baki sadakin ki" cikin rawar murya ta ce"sa...sadaki kuma Baba?, sadakin wa?, mijin wa?" murmushi ya yi ya ce"wannan bawan Allah ne ya aureki yanzu, arziki ya zo miki har gida Imara, yanzu ma dashi zaku tafi" girgiza kanta ta shiga yi sai kuma ta tafi luuu ta fadi ƙasa a sume.
# *Bestnovel*
# *Heart touching 💔*
# *IMARA 💋*
# *Maheer*
# *Nanameera*
# *2025*
***.