IMARA

Chapter 25&26

by @nanameera08

***

*IMARA 💋 💋*

25&26

Mikiya writers asso...

***

A hankali ta shiga buɗe idanunta, a ɗan firgice ta tashi zaune tana ƙarewa ɗakin kallo, turo ƙofar ɗakin a kayi, tayi saurin kallon wajen dan ganin wanda zai shigo. Wata irin bugawa zuciyar Imara tayi sanda tayi ido biyu dashi, ya ƙaraso hannunsa riƙe da tray. A kan table ɗin dake gefen gadon ya ajiye sannan ya zauna kusada ita yana kallonta, saurin matsawa tayi muryarta na rawa ta ce"a'a, lafiya?, ina ne nan?, dan Allah ka mayar dani gidanmu" murmushi Maheer ya yi bai ce komai ba ya zaro wayarsa yana dannawa a hankali, kallonsa Imara tayi sai kuma ta sake kallon daƙin, tayi saurin miƙewa tsaye tana kallonsa ta ce"ni ka mayar dani gida, bangane wannan abun ba" wayarsa ya mayar aljihu ya miƙe tsaye yana kallonta ya ce"ya kamata ki kwantar da hankalinki Imara, ki zauna ki ci abinci" wani kallo tayi masa ta ɗauke kanta tana jijjiga ƙafa, murmushi ya yi ya ce "shikenan, zauna ki ci abinci sai muyi maganar" kallonsa tayi sai kuma ta kalii inda ya ajiye tray ɗin abincin, yunwa take ji sosai hakan yasa ta nemi waje can gefe dashi ta zauna. Kallonta Maheer ya yi ya ɗauko tray ɗin ya ajiye mata a gabanta ya juya ya fice daga ɗakin, da idanu ta bishi sai kuma ta gyara zamanta ta buɗe abincin, Irish potato ne aka soya shi da kwai sai plantain da akayi garnishing da ita. Tea ta haɗa sannan ta fara cin abinci. Saida ta cinye komai tas saboda yunwar dake cikinta, ta yi gyatsa. Kamar jira yake ta gama ci ya shigo ɗakin, wannan karan ya sauya kaya, t-shirt ce white colour a jikinsa sai wando jins blue colour, kallo ɗaya tayi masa ta sunkuyar da kanta tana wasa da fingers ɗinta. Ƙarasowa ya yi ya zauna gefenta, ƙamshin turarensa ya daki hancinta tayi saurin lumshe idanunta, a ɗan firgice ta juyo ganin yanda ya riƙe hannunta cikin nasa, kallonsa tayi taga murmushi yake, saurin janye hannun nata tayi tana turo baki ta ce"akan me zaka dinga riƙeni?" Maheer couldn't help it but smile, above 2mins kafin ya ce"tashi mu je" tana kallon wani wajen daban ta ce"ina zaka kaini?, gida?" girgiza kansa ya yi ya ce"idan mun je zaki gani" taɓe baki tayi ta ce"ni to babu inda zanje" ta faɗa tana tura baki gaba. Murmushi ya yi ya ce"idan bazaki iya tafiya ba sai na ɗaukeki" da sauri ta miƙe tsaye tana zaro ido ta ce"Allah ya kiyaye" da hannu ya yi mata da su tafi, ta kalleshi sai kuma ta kalli hanyar, kamar wacce kwai ya fashewa a jiki haka ta fara tafiya.

A bakin shopping mall ɗin ya yi parking, ta kalli wajen, idan bata manta ba sun taɓa zuwa wajen da Daddynta, sunkuyar da kanta tayi tana jin wata irin kewa, Allah sarki rayuwa ta tabbata idan da Daddynta na raye da zuwa yanzu ba wannan ƙaddarar ce ta afka mata ba, Daddynta bazai taɓa aurar da ita a shekarunta ba. Kallonta Maheer ya tsaya yana yi ganin kamar bata jin abin da yake cewa, taɓa ya yi tayi saurin kallonsa sai kuma ta haɗe fuska,

"Meke damunki?"

Shiru tayi masa, ya ce"mu je ko?" sauka tayi daga motar ta tsaya tana jiransa, kashe motar ya yi ya fito yana kallonta ya ce"muje" tafiya ta fara yi tana kallonsa, suna shiga ya nemi kujera ya zauna, É—aya daga cikin ma'aikatan wajen ce tazo tana kallonsa ta ce"u are welcome sir" jinjina mata kai ya yi ta ce" me ake so?" Imara ya nuna mata ya ce "kaya wanda zai yi mata nakeson ki haÉ—a" cikin girmamawa ta ce"okay sir, ta kalli Imara ta ce"mu je Madam" kallonsa Imara tayi ya gyaÉ—a mata kai sannan tabi bayanta. Kaya sosai aka siya mata masu tsada kafin su bar mall É—in, a wani restaurant ya tsaya ya yi parking yana kallonta ya ce"mu je kici abinci" da sauri ta kalleshi sai kuma ta É—auke kanta tana kallon titi ta ce"bayan wanda naci, ni bana jin yunwa" murmushi Maheer ya yi ya ce"ai tunda rana kika ci abinci, kuma kinga yanzu magrib akayi"

"Nidai a ƙoshe nake, naga ɗazu naci abincin, kawai ka mayar dani gida mana" ta faɗa ba tareda ta kalli inda yake ba. Bai sake magana ba ya sauka daga motar kai tsaye kuma cikin restaurant ɗin ya nufa, binsa tayi da harara a ƙufule ta ce"aikin banza, ko ana dole" .

Bayan minti goma Maheer ya fito hannunsa riƙe da ledoji guda biyu, kallo ɗaya Imara tayi masa ta ɗauke idanunta, har suka je gida babu wanda ya sake magana a cikinsu. Bayan ya yi parking ya kalleta ya ce"ki shiga ciki zan je na dawo" bata ce masa komai ba ta buɗe handle ɗin motar ta sauka, ledojin daya miƙo mata ta kalla sai kuma ta ce"amma nace maka na ƙoshi ko?" murmushi ya yi ya ce"ai ba cewa nayi ki ci ba, ki shiga dashi kawai" ɗan tura baki ta yi sannan ta amsa ta juya ta shige gidan. Da idanu Maheer ya bita sai kuma ya girgiza kansa fuskarsa fal murmushi ya yiwa motar key ya bar gidan.

Imara nashiga ta wuce sama kai tsaye, ɗakin da ta zauna ɗazu nan ta shiga. Ta ajiye veil ɗinta kan gadon sannan ta shige toilet ta ɗauro alwala, tana fitowa ta tsaya jikin mudubi tana kallon veil ɗin data ajiye, ya yi ƙarami da sallah hakan yasa ta buɗe wardrobe ɗin dake ɗakin ko zata samu wani abu, ɗan kwaɓe fuska tayi ganin babu komai a ciki, ta koma ta zauna ta zuba uban tagumi.

Sai bayan sallahr magrib sannan Maheer ya shigo gidan, time ɗin tana zaune bayan ta idar da sallah da veil ɗin nata, sallama ya yi ya turo ƙofar ya shigo, a ciki ta amsa sallamar ya ƙaraso ya zauna gefenta yana kallonta ya ce"tashu muje ƙasa kici abinci" kamar ba zatayi magana ba sai kuma ta ce "sai yaushe zaka mayar dani gidanmu?" numfasawa ya yi ya ce "Imara Inason kibar wannan maganar, idan Allah ya kaimu next week zamu tafi gida, kinsan yanzu ke matata ce, saboda haka ni ne nakeda ikon tafiya dake duk inda zani, kuma bakida wani waje sai inda na ajiye ki, nayi miki alƙawarin zan kula da ke fiye da yanda kike tunani. Zan kai ki cikin ahalina, zan zame miki uwa zan zame miki uba, abinda kawai nakeso shine yardar ki" ya ƙarashe maganar yana dafa hannunta, kallon hannun nata tayi sai kuma ta kalli fuskarsa, haka kawai ta ji ta yarda da Maheer, ta yi shiru na wasu mintuna sannan ta ce"meyasa ka aureni?" murmushi Maheer ya yi ya ce"saboda ina sonki" cikin rawar murya ta ce"zan yarda da kai amma dan Allah karka juyamin baya, karka sakani kuka, ka ɗaukeni matsayin ƙanwarka wacce ba zaka cutar da ita ba, kaji Yaya!"

Da sauri Maheer ya ɗago ya kalleta sai kuma ya yi murmushi ya kamo hannunta ya riƙe cikin nasa ya ce"Thank you" ɗan murmushi tayi har saida beauty point ɗinta ya loma ta ce"nima nagode" hannunta ya kama ya tashi ya ce"muje ki ci abinci" gyaɗa masa kai tayi ya nuna mata hanya, tayi gaba ya bita a baya.

Tun daga wannan ranar suke zaune lafiya da Maheer a kullum shaƙuwa ƙara shiga tsakaninsu take, a haka har suka ƙarasa wannan satin, ranar Lahadi tana zaune bakin mirror tana gyara kanta ya shigo, ƙarasowa gabanta ya yi yana murmushi ya tsaya a gefenta yana kallonta ta jikin mudubi, kallonsa itama tayi tana murmushi

"Madam idan kin kammala muna iya tafiya" tashi tsaye tayi bayan ta yi parking gashin nata ta ce"Eh na shirya" gyaÉ—a kai ya yi sannan ya kama hannunta suka fita daga É—akin. A compound É—in gidan suka tsaya, ya buÉ—e mata backseat ta shiga sannan shima ya shiga driver ya ja motar suka tafi, kai tsaye airport suka shige, not too long kuma jirgin su ya tashi i zuwa Qatar.

Around 7pm suka shigo fadar, babu kowa a babban parlon hakan yasa kai tsaye yaja hannunta zuwa ɗakinsa, haɗaɗɗen ɗaki ne wanda yaji kayan more rayuwa, komai na ɗakin blue colour ne, domin shine favourite colour na Maheer, kallonta ya yi yana murmushi ya ce"yawwa Katalina shiga kiyi wanka, akwai kayan ki zan ɗebo miki" da wani irin mamaki Imara ta kalleshi sai kuma tayi murmushi ta ce"yaya manta sunan nawa kayi?, ko kuma tsokanata kake?" girgiza kai ya yi fuskarsa babu alamar murmushi saɓanin ɗazu ya ce"akan me zan manta sunan ki?, sunan da kika ji na ambace ki dashi shine sunan dana zaɓa miki, kuma muddin kina cikin fadar nan shine sunan da zaki dinga amfani dashi"

Tunda ya fara magana Imara ke kallonsa baki buɗe, kwata-kwata bata gane abinda yake faɗa, ƙwaƙwalwarta ta tunkushe tunani ya yi mata yawa, ganin yana shirin fita yasa tayi saurin shan gabansa tana riƙe rigarsa ta ce cikin rawar murya

"Yaya Maheer bangane abinda ka faɗa ba, ka daina yimin irin wannan wasan, tsoro nakeji, zan daina kula ka wlh, banaso, tsoro nakeji...!" Ta ƙarashe maganar tana fashewa da kuka, ta rungumeshi, ɗan tsaki Maheer ya yi kafin ya janyeta daga jikinsa yana kallon fuskarta wacce ta jiƙe da hawaye ya ce"it's better for you to obey my rules or else..." Ya yi mata gargadi da hannunsa sannan ya fice daga ɗakin.

Zubewa Imara tayi akan tiles É—in É—akin, banda tsuma babu abinda jikinta ke yi, wace irin masifa ce ta tunkarota?, wane hannu ta faÉ—a?, wace Katalina?, me Maheer ke nufi?, ko dai mafarki take, tunanin hakan yasa tayi saurin dukan fuskarta idan ma mafarki take ta farka, amma ga mamakin ta sai taga idanunta biyu. Kifa kanta tayi bisa gwuiwoyinta ta fashe da wani sabon kukan.

Ƙarfe takwas da rabi Maheer ya buɗe ɗakin ya shigo, zaune ya sameta kan tiles idanunta sun kumbura, ƙarasawa ya yi ya sanya hannunsa ya ɗagota yana watsa mata wani kallo ya ce"kee!, ina wasa dake ne?, baki ji abin da na ce miki ba?, kina son ranki ya ɓaci right?" girgiza kai Imara ta shiga yi ta ce"a'a wlh, tsoro naji yaya, dan Allah mu koma Jigawa, ka mayar dani gida, tsoro nakeji, bazan iya zama a nan ba" wani tsaki yaja yana kallonta ya ce"karki sake kiramin sunan wani gari anan, ki shirya yanzu ki sakko ƙasa, nasan kin iya yaren su, dan basa jin Hausa" juyawa ya yi ya fita kafin ta buɗe bakinta. Dafe kanta tayi ta jingina da wardrobe cikin wata raunatacciyar murya ta ce"inna lil lahi wa ina ilayhi raji'un, nashiga uku, wayyo Allahna, meke faruwa da rayuwata ne?, wace irin masifa nashiga?" Rashin sanin wanda zai bata waɗannan amsoshin ya sanya ta sake fashewa da wani sabon kukan.

A hankali tafara taka stairs É—in benan, sanya take da wata Abaya white colour ta yafa veil É—in Abayar tana tafiya tana kallon fadar. Daga can gefe taji ance

"Tabarakallah"

A ɗan firgice ta juya, sai kuma ta hangi jama'ar gidan zaune akan dinning table. A hankali ta ƙarasa bakinta na rawa ta gaishesu cikin harshen larabci, fuska a sake suka amsa mata musamman Shammah, ta kalleta cikin sakin fuska ta ce"zauna mana" ta faɗa cikin harshen larabci, cikin sanyin jiki Imara ta zauna ta sunkuyar da kanta, a hankali ya tura kujerar ya tashi, da sauri suka kalleshi, Immi ta ce"lafiya?" bai ce mata komai ba ya juya ya bar wajen, da idanu duk suka bi shi, banda Imara wacce har sannan kanta yake a sunkuye. Girgiza kai Shamma tayi ta cigaba da cin abincin ta, dakyar Imara taci abincin bayan takurawar da Shamma tayi mata.

12:30am.

Zaune take gefen gadon ta jingina da jikinsa, tunani ne fal zuciyarta, duk da dare ya yi sosai amma babu alamar bacci a tare da ita, tanada buƙatar ta yi magana da Maheer. Ta kasa gane abin da yake shirin faruwa da rayuwarta. Tana cikin wannan tunanin ya shigo ɗakin yana sanye da wasu pyjames black colour, s hankali ta saki ajiyar zuciya dan har ga Allah taji daɗin shigowar tasa, zama ya yi gefen gadon yana kallonta, gyara zamanta ta yi, tana ƙoƙarin magana ya ɗaga mata hannu.

"Nasan abinda zaki ce, nasan me za ki tambaya, wane ne ni?, meyasa na aureki?, me nake nufi dake?. To bar kiji, ni Maheer ne kamar yanda kika sani, kuma ɗa ga Amir wato Sheikh Fahad bin saleem al-kuwari, na aureki saboda wani dalili, ba lallai bane na sanar dake, the main thing shine ki yi duk wani abu dana umarce ki, daga yau ba irin wannan shigar nakeson kiyi ba, kuma daga yau sunanki Katalina a idona ba IMARA ba, idan har kika kuskura kika ce zaki saɓamin to ba zaki ji daɗin zama cikin fadar nan ba, saboda haka ki kasance yanda nakeso shine kawai abinda zai ceceki.

Kallonsa kawai Imara take tana hawaye, cikin rawar murya ta ce"daman ba saboda Allah ka aureni ba?, daman ƙarya kayimin?, meyasa zaka yaudareni?, meyasa zaka sanya mini soyyarka a zuciya sannan ka cutar dani?, akan me ka rabo ni da dangina?, meyasa! meyasa Maheer!!"

Tashi tsaye ya yi yana kallonta ya ce"ke kika ga zaki iya wahalar da kan ki, kina sona, bakya sona wannan bai dameni ba, abinda nakeso shine kawai abinda nake aiwatarwa, saboda haka zaɓi ya rage naki, kiyi biyayya ki zauna lafiya. Kuma ma da kike magana akan na raboki da kasarku, wa kike dashi a ƙasar?, wane gatanki?, zaman kanki fa kike, ai auranki da nayi taimako ne a gareki, saboda haka ni ba abin rainawar ki bane, fact.

Da idanu Imara ta bishi har ya ɓacewa ganinta, ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, dan kuka ma ya gagareta sai na zuci, komawa tayi ta jingina da gadon tana numfashi sama sama, kafin kuma ta samu ta fashe da wani raunataccen kuka mai shiga zuciyar mae sauraro. Yanda Imara taga rana haka taga dare cikin masarautar Udaid sanda taji anfara kiran sallah asuba ta tashi ta ɗauro alwala ta zauna kan ladduma tana roƙon Allah ya kawo mata mafita.

A haka ta cigaba da rayuwa a cikin gidan cikin takurawar Maheer, ko kaɗan baya barinta ta sake, gabaɗaya ta rame kamar ba ita ba, kullum sai zama a ɗaki tana kuka. Yau ma kamar kullum tana zaune kan kujera cikin ɗakinta ta zuba uban tagumi, akayi sallama aka shigo, a hankali ta ɗaga kanta jin ba muryar Maheer ba, Ameer da ta gani ya sanya tayi saurin miƙewa tana ƙaƙalo murmushin ƙarya ta ce"sannu da zuwa Ameer" lumshe idanunsa ya yi sannan ya buɗe su akanta, cikin rawar baki ta ce"na manta Ameer ka zauna" gyaɗa mata kai ya yi sannan ya zauna gefen gadonta cikin wata kamilalliyar murya ya furta

"Bismillah"

Zama Imara tayi itama tana kallonsa ta ce "Ameer lafiya?" kallonta ya yi da dara-daran idanunsa ya ce"IMARA"

"Na'am Ameer"

Numfasawa ya yi sannan ya ce"nasan zaki yi mamakin abinda zai fito daga bakina, duk da nima abun ya zo mini a bazata, bansan yaushe ba, bansan kuma dalili ba, amma naji na kamu da sonki tun ranar dana fara ɗora idanuna akan ki, inaji kamar ba ranar nafara ganinki ba. Nayi ƙoƙarin ganin na cire tunanin daga raina amma nakasa, inason ki Imara, ina sonki, soyyaya irin wacce bansan iyakarta ba, duk da ke matar ɗana Maheer ce amma ina faɗa miki haka, wlh ina sonki har cikin raina"

A É—imauce Imara ta tashi tsaye tana nuna shi da yatsa amma ta kasa cewa komai, ta shiga girgiza kanta hawaye na zuba akan fuskarta, tayi saurin dafe kanta tana rusa kuka, tashi tsaye Ameer ya yi yana kallonta sai kuma ya girgiza kai ya ce"ban faÉ—a miki sirrin dake zuciyata dan naga hawayen ki ba Lolo, Inason ki zauna kiyi tunani akan magana"

"Tunani?!, tunani fa Ameer?, me zanyi tunani?, ni ce fa IMARA matar Maheer ɗanka, amma ni kake so?, meyasa kuke son ganin ƙarshena ta hanyar irin waɗannan halayen naku, nakasa fahimtar komai, nakasa ganewa, ƙwaƙwalwata tayi ƙarama ba zata iya ɗaukan irin waɗannan tashin hankalin ba, kallon uba mahaifi nake maka nayi tunanin kaima zaka yimin kallon ɗiyarka wacce ka haifa, meyasa kake ƙoƙarin cutar da rayuwarta?, akan me zaka bari sheɗan ya shiga zuciyarka har ya sakaka furta irin waɗannan zantukan. Dan Allah ka tuba tun wuri Ameer, babu wanda zan faɗawa, wlh nayi maka alƙawari, amma karka sake irin wannan maganar. Numfasawa Ameer ya yi idanunsa na kallon ƙasa, s hankali ya ɗago ya kalleta, gabaɗaya launin idanunsa ya koma ja ya girgiza mata kai zai yi magana tayi saurin shigewa toilet saidai kafin ta rufo ƙofar har Ameer ya rigada ya shigo.

Cigaban labari.

Banda kuka babu abinda take yi Mama na taya ta, saida tayi mai isarta sannan ta ɗago kanta tana kukan ta ce "meyasa Mama?, bayan duk wannan wahalar dana sha ya rabu dani, duk wanda ya raɓeni a rayuwa da niyyar naji daɗi sai ya tafi ya barni, kowa baya zama tare dani, nafiso ma na mutu. Ta kalli Mama dake kuka ta ce"dan Allah Mama ki bani abinda zanci ko nasha na mutu, nagaji da rayuwar, banida kowa, banida kowa Mamah! Ni marainiya ce, wacce batada mai sonta, duk sun mutu, meyasa ni nake a raye Mamah?, meyasa!?, dan Allah ki bani abin mutuwa..." Rungumeta Mamah tayi tana shafa kanta ta ce"karki sake cewa haka Imara, kinada kowa, mu zamu zama dangin ki, ba za ki sake maraici ba IMARA, ki daina kuka kinji" ta cigaba da shafa sumar kanta, ajiyar

zuciya Abaan ya sauke kafin ya juya ya bar wajen ba tareda ya shiga É—akin ba.

# *Heart touching 💔*

# *IMARA💋💋*

# *Nanameera*

# *2025*.