Chapter 41&42
by @nanameera08
*IMARA 💋💋*
41&42.
***
Mikiya writers asso...
Girgiza kanta ta yi, sai kuma ta janye fuskarta a hankali ta ce"sai da safe" hannunta ya kama ya ɗora mata robar naman ya ce"Allah ya tashemu lafiya, karki manta ki yi addu'a" gyaɗa masa kai Imara ta yi sannan ta fice daga ɗakin. Ajiyar zuciya Abaan ya sauke ya koma ya cigaba da aikin gabansa. Ko kaɗan ba ta lura da Khalil ba ta tura ƙofar ɗakinta ta shiga tana wasa da robar hannunta. A gefen gado ta ajiye robar sannan ta shige toilet dan watsa ruwa, tana fitowa ta sanya sleeping dress ta ɗaure gashin kanta sannan ta kwanta akan gadon ta lumshe idanunta.
***A hankali ta juya da niyyar komawa ɗaya ɓangaren, rufar da ta gani ya sanya ta s buɗe idanunta, a firgice ta tashi zaune tana kallon mutumin dake tsaye a kanta. Baya ta fara yi tana girgiza kanta gabaɗaya jikinta rawa yake, ganin yanda ta tsora ta ya sanya Khalil kunna hasken ɗakin, kallonsa ta yi sai kuma ta saki ajiyar zuciya ta dafe ƙirjinta. Sai da ya ga ta nutsu sosai sannan ya ce"ki yi haƙuri na tsorata ki" Imara ba ta ce masa komai ba ta sauka daga kan gadon ta ɗauko ruwa a fridge ta ɓalle murfin, sai da ta kusa shanyewa sannan ta ajiye ta dawo ta zauna can nesa dashi. Sun ɗauki mintuna babu wanda ya ce wani abu, Khalil na son aiwatar da abin da ya kawo shi sai dai yana fargabar yanda Imara za ta karɓi al'amarin. Turo baki ta yi dan bacci ta ke ji gashi ba za ta iya ce masa ya bar ɗakin ba, can ƙasa da murya ta ce
"Yaya Khalil dare ya yi sosai fa, kuma gobe da safe ina da makaranta"
Zazzafan numfashi Khalil ya sauke kafin ya juyo ya kalleta ya ce"Na sani Imara, yanzu ne lokacin da ya fi dacewa na zo inda ki ke shiyasa" ƙura masa idanu Imara ta yi tana mamakin furucin bakinsa. Numfasawa ya yi sai kuma ya ce
"Imara tun ranar da idanuna suka yi tozali dake ki ka shiga raina, ki yi haƙuri da abin da zan faɗa amma har cikin zuciyata ina ƙaunarki, nasan ba lallai ne na zama wanda ya fara faɗa miki haka ba, amma ina da tabbacin zan yi nasara akan su duka. Ina da niyyar mallakar ki matsayin matata ta sunna, ina fatan ba za ki juyamin baya ba Imara"
Ras! Haka Imara ta ji gabanta ya faɗi, tashin hankali ƙarara ya bayyana akan fuskarta, cikin rawar murya ta fara cewa
"Yaya amma ni ai kamar ƙanwarka nake, kuma ma kaga kai saurayi ne, ni kuma na taɓa aure. Ina jin tsoro, dan Allah a bar maganar nan"
Ɗan murmushi Khalil ya yi ya miƙe tsaye ya ce"sanin haka yasa na fallasa miki asirin zuciyata, nasan ba za ki ƙini ba, ina da wannan tabbacin Imara. Zan baki lokaci ki yi tunani, amma ina fatan samun babban matsayi cikin zuciyarki." Da idanu kawai Imara ta bi shi har ya fice daga ɗakin, wani irin gumi ta ji yana tsatstsafo mata, duk da Ac dake kunne a ɗakin, me Khalil ya ke nufi?, idan har ya furta yana son ta a gaban mutane ba za ta iya bijirewa ba kodan hallacin da mutane gidan suka yi mata, haka kuma ba za ta iya haƙura da soyyayar Abaan ba!. Da wannan tunanin ta koma ta kwanta, sai dai duk yanda ta yi da bacci ya ƙi zuwar mata, daga ƙarshe kawai ta tashi ta shige toilet ta ɗauro alwala, sallar nafila ta hau yi, kafin daga bisani ta zauna tana roƙon Allah ya zaɓa mata abin da ya fi Alkhairi a rayuwarta.
***Haka Imara ta cigaba da rayuwa a cikin gidan, duk yanda Khalil yake son magana da ita haka take avoiding É—insa, domin bata fatan abin da zai haÉ—a su. A haka har suka fara exams ta first semester a makaranta.
Zaune suke cikin wani ɗan ƙaramin restaurant dake cikin makarantar, da idanu Nana ta bi Imara wadda ta zuba tagumi tun shigowar su. Har aka kawo musu abin da suka yi order Imara ba ta sani ba, tsaki Nana ta yi sannan ta ɗan daki table ɗin gabansu, a ɗan firgice Imara ta kalleta sai kuma ta shiga murje idanunta. Harararta Nana ta yi ta ce
"Wannan tunanin babu abin da zai haifar miki sai wahala Malama, it's better for you to stop it"
Numfasawa Imara ta yi ta ja lemonta ta sha sannan ta ce"ni ce miki na yi tunani nake?" taɓe baki Nana ta yi ta ce"a'a ban sani ba!" Murmushi Imara ta yi ta dafata ta ce"haba ƙawar I'm sorry, zan daina in sha Allah" murmushin ita ma Nana ta yi ta ce"ohyaa mu yi saboda akwai paper a gabanmu" gyaɗa kai Imara ta yi sannan ta cigaba da shan lemonta.
Ƙarfe 4:20pm suka fito daga paper, dafe kai Imara ta yi ta ce"wayyo uwata, nagaji wlh" dariya Nana ta yi ta ce"za ma ki yi bayani ne Hajiya, gobe ma akwai paper" zaro idanu Imara ta yi ta ce"Allah gamu gareka"
Taɓo ta Nana ta yi da hannu, maida idanunta ta yi ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta, ƙarasowa gabansu ya yi ya kalleta ya ce"Imara ya exams ɗin?" cikin sakin fuska ta ce"wlh sir exams Alhamdulillah, kuna bamu wuta" dariya Ya yi ya ce"ku yi haƙuri, a ƙarasa a haka" girgiza kai Nana ta yi ta ce"kai sir, ai shikenan, da dai an tausaya mana" dariya ya ce "Khadijah rigima, kawai ku yi karatu, nasan bamu da matsala daku" murmushi su ka yi ya ce"tafiya za ku yi?" gyaɗa masa kai Imara ta yi ya ce"to mu je na sauke ku?" Girgiza kai ta yi ta ce" ai za'a zo a ɗaukemu, ka ga idan muka tafi za'a neme mu a gida" jinjina kai ya yi ya ce"haka ne kuma, to sai goben ku" ɗaga masa hannu su kayi ya juya ya bar wajen. Jan hannun Nana ta yi ta ce" mu je ni nagaji"
Waro idanu Nana ta yi ta ce"kai, kinga Yaya Khalil ne ya zo ɗaukar mu fa" da sauri Imara ta kalli motar, shiru ta yi suka ƙarasa, fitowa ya yi yana kallonsu ya ce"yan makaranta" dariya Nana ta yi ta ce"kai yaya, akwai wahala school wlh" dariya ya yi yana kallon Imara ya ce"beauty wai haka?" gyaɗa masa kai ta yi tana murmushi, Khalil ya ce"to ai sai ku dage ku yi passing, idan kun gama exams za mu je yawo" tsalle Nana tayi ta ce"shiyasa nake mugun son ka Yaya" dariya kawai ya yi sannan suka shiga mota suka tafi. Sai da ya biya dasu mall ya siya musu chocolate sannan suka tafi gida. Yana gama parking Imara ta sauka da sauri ta shige gida gudun ka da ya yi kiranta, da idanu kawai Khalil ya bita sai kuma ya yi murmushi. Turus ta yi ganin akwatina na kaya a zube a parlon, Jadda da wasu tsofaffi sai buɗe kayan suke.
"Jadda wannan kayan fa?"
Nana da ta shigo ta tambaya, washe baki Jadda ta yi ta ce"yawwa yaran kirki ku zo ku ga, irin wannan abun arzikin nakeson kuma a kawo muku" cikin ɗaurewar kai Imara ke kallon Jadda dan kwata-kwata ba ta fahimci abin da take nufi. Shiru Nana ta yi sai kuma ta ce"ko kayan Aunty Jidda ne?" Gyaɗa mata kai Jadda ta yi ta ce"Eh, ɗazu aka shigo dasu, wannan yaron ya yi kaya ba ƙarya"
"Bikin wa za'a yi?"
Imara ta tambaya tana kallon Nana. "Yaya Abaan man, Aunty Jidda zai aura, gashi har an kawo kayan lefe"
Wani irin abu ne ya tokarewa Imara a ƙirji, ta kalli Nana sai kuma ta sake kallon tulin akwatinan, girgiza kanta ta yi muryarta na rawa ta ce"Jad... Jadda wai haka?"
"Eh mana, ashe baki sani ba, Aure zai yi kuma kwa huta, yaro ya girme a gida ya zama magidanci babu aure" tamkar wadda aka zarewa laka haka Imara ta ji jikinta, ba ta sake cewa komai ba ta shige ciki tana tafiya tana haÉ—a hanya. Da idanu Nana ta bi ta sai kuma ta girgiza kai tana tausaya mata domin tasan abin da ke cikin zuciyarta.
***Imara na shiga ɗaki ta nemi waje a ƙasa ta yi zaman dirshin, kuka takeson yi amma ko kaɗan babu wani ruwan hawaye da ya rage a idanunta, gabaɗaya ƙwaƙwalwarta ta tunkushe waje ɗaya, ajiyar zuciya ta shiga saukewa tana maimaita furucin Jadda. Daman aure zai yi ya barta?, ba ta ko samu damar sanar dashi sirrin zuciyarta ba shine zai yi aure ya bar ta?. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke sai kuma hawaye ya biyo kuncinta, ta shiga rera kuka a hankali.
***Da gudu Jidda ta shigo kitchen ɗin ta na zuwa ta rungume Mommy tana dariya ta ce "Mommy gaskiya Nagode sosai, an kawo kayan aurena fa, kuma yaya Adeel ya ce wai sati uku za'a saka. Gaskiya nayi farin ciki, wannan malamin aikinsa yana yi" girgiza kai Mommy ta yi tana dariya ta ce"da ai kina ɗauka ba zan iya ba, sai gashi ta cikin ruwan sanyi mun buraɗa tsohuwar yanda ita kuma za ta tada musu hankali, kinga yanzu kin zama surukar babban gida" tuntsirewa da dariya Jidda ta yi ta ce"wlh kam naga aiki, yanzu dai kina ji Mommy ba wannan ba, ni banason zaman wannan yarinyar a gidan nan please, idan mun koma wajen mutumin nan zan yi masa bayani. Haka kawai na ji hankali bai kwanta da zamanta cikin gidan nan ba wlh" taɓe baki ta yi tana wanke kayan miya ta ce"to ke mene na ki na damuwa da ita?, ke da za ki bar mata gidan?, ai sai ta yi ta zama a cikinsa, ke da za ki tafi gidan aurenki?" Kwaɓe fuska ta yi ta ce"ni a'a wlh Mommy, na riga da nayi alƙawarin sai na fitar da ita daga gidan nan, saboda haka Allah hankalina ba zai taɓa kwanciya ba muddin ina ganinta. Kuma Jadda sai wani jan ta take a jiki" murmushi Mommy ta yi ta ce"shikenan, idan mun koma sai a yi masa maganar ta, ko kuma ki bari mu gama da maganar aurenki, saboda dai kinsan me ya faru, dole ne kiyi abin da ya dace" jinjina kai tayi ta ce" Haka ne Mommy, sannan kuma ni sai an dawo da hankalin Yaya Abaan kai na, dan ko magana fa ba ya wani yimin, idan na kula shi kuma sai ya dinga amsawa sama-sama, inason ya daina yarda da maganar kowa sai ta wa, ya daina ganin ko wace mace a gabansa sai Jidda" murmushi Mommy ta yi ta ce"ke a tunaninki zamu bar shi haka ne?, ai kawai ki zuba min idanu, ni nasan abubuwan da zan aikata" rungumeta ta sake yi tana murmushi ta ce"shiyasa nake ƙara ƙaunar ki Mommy" murmushi ta yi ta ce"nima haka Jiddona, duk wani abu da zai sanyaki farin ciki shine abin da nake mudarin yi, zan yi komai domin farin cikin ki".
(Ba dai-dai bane a rayuwa uwa ta ce za ta yi wa ɗiyar ta duk wani abu da take so koda kuwa hakan ya saɓawa shari'a ko kuma Addini, Iyaye mata a dinga kiyayewa, farantawa yaro abu ne mai kyau, amma ban da saɓawa mahalicci wajen faranta ran ɗa. Allah ya sa mu dace)
Washegari ko karyawa Imara ba ta yi ba ta fice, dan ko Nana ba ta jira ba. Tana zuwa ta samu waje ta zauna ta zuba uban tagumi, koda Nana ta fito ba ta sameta ba ta yi tunanin ko ta wuce hakan yasa ita ma ta tafi. Zaune ta hangeta ta ɗora hannu akan fuska da alama ta yi nisa a cikin tunanin da ta ke yi, ƙarasawa Nana ta yi ta zauna gefenta ta zuba mata idanu. Above 5mins amma Imara ba ta san Nana ta zauna inda take ba, taɓa ta ta yi, ta ɗago a firgice tana kallonta.
"Imara kinga yanda ki ka rame kuwa?, daga jiya zuwa yau, kar ki saka damuwa a ran ki ki zo ki cuci rayuwarki akan abin da ba za ki samu ba, Yaya Abaan ya riga da ya yi miki nisa Imara. Ka da ki manta Aunty Jidda ita ce wacce zai aura, ina da tabbacin ba za ta taɓa bari ya aure ki ba. Kuma kema kin san da haka, saboda haka ki maida hankalin ki akan karatun ki, shine kawai abin da zai taimaki rayuwar ki, kina da buƙatar ki yi karatu Imara, domin shine kawai gatanki"
Goge hawayen fuskarta Imara ta yi tana kallon Nana ta ce"Nagode Nana, amma ba zan iya cire shi a raina ba. Amma kamar yanda kika faɗa zan maida hankalina akan abin da yake rayuwata, tunanin wani abu bana mara gata irina ba ne, tunanin wani zai so ni ba abu bane mai kyau. In sha Allah zan cire shi daga raina, zan yi ƙoƙarin ganin na gina rayuwata"
Dafa ta Nana ta yi ta ce"ni burina bai shige na ga kin kammala karatun ki lafiya ba" murmushi ta yi ta ce"in sha Allah zan yi haka Nana".
***Tun daga wannan ranar Imara take gujewa kanta duk wani abu da zai haɗata da Abaan, da zarar ta dawo daga makaranta take shigewa ɗaki ba za ta sake fitowa ba sai gobe idan zata tafi makaranta. Ko da Mamah ta yi cigiyarta sai ta ce karatune ya rike ta a haka har suka kammala jarrabawar aka basu hutu, lokacin kuma sauran sati ɗaya bikin Abaan da Jidda. Zaune take kan kujera ta zubawa tv idanu duk da ba fahimtar abin da ake cewa take ba. Ƙamshin turarensa ta ji nan da nan bugun zuciyarta ya sauya, da idanu Mamah ta kalleshi ganin kamar ba shi ba ta ce"Son lafiyarka kuwa?" girgiza kai ya yi ya ce"ki bada abinci a kawomin Mamah" sosai ta yi mamaki ganin yau da bakinsa ya ce a kawo masa abinci, tashi
ta yi ta shiga kitchen ta haÉ—a masa tray na abincin sannan ta fito parlon. Zaune ta iske Imara har sannan bata ko motsa ba
"IMARA"