Chapter 47&48
by @nanameera08
*IMARA 💋💋*
47&48.
***
Mikiya writers asso...
Ƙarfe 5:20pm Umaima ta fito cikin wata Abaya black colour, sosai rigar ta haskata ta yi kyau duk da ba wata kwalliya ta yi ba, ɗakin Nana ta shiga ta sameta tana ƙoƙarin saka agogo, irin rigar Umaima ce a jikinta da alama ita ce kalar kayan cocktail ɗin. Kallon agogo ta yi sai kuma ta ce"Imara ba ta fito ba ko?" gyaɗa mata kai Nana ta yi tana cigaba da shirinta, girgiza kai Umaima ta yi sannan ta fice daga ɗakin. Kwance ta hangi Imara ta yi ruf da ciki babu ko alamun tana shirin fita, ƙarasawa Umaima ta yi ta daketa, tashi zaune ta yi tana murza idanunta, Umaima kamar za ta yi kuka ta ce"yanzu Imara ba ki ma shirya ba?, lokaci fa na tafiya, so ki ke mu makara?" da mamaki Imara ke kallonta sai kuma ta ce "shirin me zan yi?" ɗan tsaki Umaima ta yi ta ce"shirin cocktail mana" taɓe baki Imara ta yi ta ce"ni ba zan je ba" zaro idanu Umaima ta yi kafin ta ce"look Imara dan Allah kar ki ɓata mana lokaci, ki tashi mana, kinsan dai babu yanda za'a yi ki ce ba za ki je ba ko?" Tashi tsaye ta yi tana kallon Umaima ta ce"to ni babu in da zan je wlh, ni bana son zuwa, kawai ku tafi mana. Kuma dan Allah karki cewa Mamah komai, Allah ya tsare" tana gama faɗin haka ta shige toilet abin ta. Da idanu kawai Umaima ta bita sai kuma ta juya ta fice daga ɗakin. A corridor suka haɗu da Nana, ganin yanda ranta yake a haɗe yasa Nana ta ce"cewa ta yi ba zata je ba hala?" Gyaɗa mata kai Umaima tayi. Murmushi kawai Nana ta yi ta ce"karki sake ce mata komai, ki zo mu tafi dan Allah"
"Amma Nana ya za'a yi a ce bata je ba?, akan wane dalili?" jan hannunta Nana ta yi ta ce"kin ga fa, ba dole ne sai mutum ya je ba, maybe bata ra'ayin zuwa irin waÉ—annan tarukan tunda kinga bata da shiga mutane, just leave her"
"Wa za'a bari?"
Suka tsinkayi muryar Mamah a bayansu. Girgiza kai Nana ta yi ta ce" ba kowa, wai daman Imara ce ta ce ba zata je partyn yau ba, shine na ce a ƙyaleta, maybe bata saba bane" shiru Mamah ta yi na ɗan wasu sakkani sai kuma ta ce"ku je kawai, bari na yiwa Abaan magana maybe shi ta ji maganarsa. Idan bata je ba ai sai ya zama abin magana" murmushi Umaima ta yi dan har ga Allah tafi son ace Imara taje wajen.
****Zaune ta sameshi kan kujera ya tankwashe ƙafafunsa idanun zube bisa system ɗin dake gabansa, zama ta yi kusa da shi tana murmushi ta ce"amma dai kasan yanzu ba lokacin wannan aikin bane ko?" ɗago kansa ya yi ya zuba mata idanu, murmushi ta yi ganin yanda idanunsa suka faɗa yasa ta ce"ba ka cin abinci ko?, sai yaushe zaka daina irin wannan abun ne Abaan?" langwaɓar da kansa ya yi kamar wanda aka yiwa dole ya ce"Mamah nagaji" dafa kansa ta yi ta ji zafi, girgiza kai ta yi cike da tausayinsa ta ce"sannu, kaga har zazzaɓi zai kamaka, ka tashi ka yi wanka, lokaci na tafiya, kar azo ana jiran ango bai zo ba" kamar zai yi kuka ya ce"Mamah ni fa nagaji wlh" dungure masa kai ta yi ta ce"banason shashanci, maza ka tashi, zan aiko Imara ta kawo maka ruwan tea kasha sai ka zo ka tafi. And kuma ka yi mata magana ance ta shirya taƙi wai ba zata je ba" bai ce komai ba ya rufe system ɗin ya tashi ya shige bedroom ɗinsa, da idanu kawai Mamah ta bishi sai kuma ta fice daga ɗakin.
****Zaune suke gidan makeup ɗin bayan an gama yi mata, sosai ta yi kyau dan daman da kyanta Masha Allah. Murmushi Amrish ta yi ta ce"ke matar nan kin yi wani irin kyau wlh" dariya Jidda ta yi ta ce"da gaske?, ki ce zan tashi kan mijina" tuntsirewa da dariya Raheena ta yi ta ce"ba dole ba, ai kedai ki bar komai a hannuna, wlh sai kin mallakeshi a tafin hannunki, babu boka babu malam" numfasawa Jidda ta yi sai kuma ta ce"nikam ina tsoro wlh, saboda malamin da muke zuwa wajensa ya ce yanada riƙon addini kuma asiri zai wahala ya ci shi" taɓe baki Xahra ta yi ta ce"ni banga wanda asiri ba ya ci ba, kawai dai ba zai iya bane, ki bari sai bayan auren akwai wajen wanda zamu je wlh duk taurin kan namiji sai ya dawo ɗan boyi-boyin ki. Ke duk rashin mutunci irin na Abbas sai da aka ladabtar min dashi, yanzu ko tsinke na ajiye na ce kar ya tsallake wlh ba zai iya tsallakawa ba, kuma ni ke juya dukiyarsa" ajiyar zuciya Jidda ta sauke kafin ta kalleta ta ce"ni fa ba wai inason na dinga juya dukiyarsa ba ne ko wani abun, kawai ni ya so ni, ya fifitani akan komai nasa, mu yi zama na lafiya da soyyaya wlh ni shine kaɗai burina"
Tsaki Xahra ta yi ta ce"ke banza ce ai shiyasa, to ai muddin yana sonki dole ya yi miki biyayya, mazan wannan zamanin idan ba da haka ba babu inda zamu kai labari, musamman miji irin naki mai kyau da kuÉ—i wlh idan ki ka yi sake kina zaune za'a kawo wata cikin gidan"
Saurin dafe ƙirjinta ta yi, lokaci ɗaya Imara ta faɗo mata arai, girgiza kanta ta yi tana kallon Xahra ta ce"Allah ya kiyaye, ni wai ina Munceey ta shiga ne?" tsaki Amrish ta yi ta ce"daga cewa fa gatanan kinga har mun gama abin da muke bata dawo ba, kawai mu tafi wlh"
"To mu je ina?, ai sai ango ya zo da motoci ya É—auki amarya ko?" Girgiza kai Jidda ta yi ta ce"a'a bari dai mu jira su, ai kinga bai san mun gama ba inaga"
****Fitowa ta yi daga kitchen hannunta riƙe da ɗan ƙaramin tea flask wanda Mamah ta bata, Jadda dake zaune kan kujera ta shiga bin ta da kallo kafin ta ce"ni ko wa nake gani haka kamar Imara?" a sanyaye ta ce"ni ce Jadda"
"Muhammadu Rasulullahi, ina wajen bikin?, ko ke ba ki je ba?, nima kinga jira nake angon ya fito mu tafi tare" girgiza kai Imara ta yi ta ce"ban shirya bane Jadda"
"Akan me?, je ki shirya na yi dropping ɗinki" Khalil dake tsaye a bayanta ya yi maganar, kamar za tayi kuka ta ce"ai yaya Khalil kaina ciwo yake shiyasa" girgiza kai ya yi ya ce"ayyah, sannu to, idan muka tafi a hanya sai na siya miki magani ko?" shiru ta yi ba ta sake cewa komai ba. Taɓe baki Jadda ta yi ta ce"yawwa, ni idan za ku tafin ma sai mu tafi tare, tun da na fuskanci shi wancan yaron ba shida niyyar sakkowa mu shige" murmushi kawai Khalil ya yi sai kuma ya ce"Tom Jadda bari na shirya, na kira Adeel ma ya cemin wai yana wajen"
"Sallamammen yaro mai halin uwarsa, nan fa na zauna ina jiran yaron nan sai cemin ya yi wai mota zai kai a sakowa fetur, shine ya yimin zamba cikin aminci ya gudu" ba Khalil ba hatta Imara dake tsaye sai da ta yi dariya, ya kalleta ya ce"Tom Jadda ni zan kai ki karki damu, Imara je ki shirya" da idamu kawai Imara ta bishi dan tama rasa abin da za ta ce masa dan kuwa ba zuwa za tayi ba.
****Tura kofar ɗakin tayi a hankali, babu kowa a parlon hakan yasa ta shiga ta ajiye flask ɗin, tana shirin fita ta ji wayarsa tana ƙara, kallon ƙofar bedroom ɗin ta yi sai kuma ta kalli screen ɗin wayar, babu suna hakan yasa ta ɗauki wayar ta ɗaga ta kai kunne.
"Hello Yaya, mun gama fa, kai muke jira kawai"
Saurin ajiye wayar ta yi ba tare da kashe ba, da idanu kawai Abaan ya bita ya ƙaraso wajen, ɗaukar wayar ya yi ya kai kunnensa, bai sake kallonta ba ya shige kitchen. Da idanu kawai Imara ta bi shi sai kuma ta tashi tsaye tana shirin fita.
"And who give u the permission?"
Cak ta tsaya sai kuma ta juyo ta kalleshi da idanunta wanda ruwa yake kwance a cikinsu. Bai mata magana ba ya zauna kan kujera ya haɗa tea ɗinsa, gajiya ta yi da tsaiwar ta nemi waje ta zauna a ƙasa ta kifa kanta akan gwuiwarta, sai da ya shanye shayin sannan ya ɗago ya kalleta, numfasawa ya yi kafin ya ce"mene dalilin rashin zuwan?" ɗago kanta ta yi a hankali bayan ta goge hawayen da suka zubo mata ta ce"ni kawai bana son zuwa" gyara zamansa ya yi yana kallonta sosai ya ce"saboda akwai abin da ke cikin ranki?, Imara kar ki koyawa kan ki wata ɗabi'a wadda ba taki ba, ki daina wannan abun da ki ke, kar na sake ji ko kuma ganin irin wannan dabi'ar, banason a sake kawomin ƙararki kin ji abin da nace?" Saurin gyaɗa masa kai ta yi tana ƙoƙarin ɓoye kukan dake shirin kwace mata. Tashi tsaye ya yi ya ce"ki tashi ki je ki shirya, Khalil zai tafi ya tafi dake, kuma ina sake faɗa miki kar a sake kawon ƙararki daga yau har ranar da za'a gama bikin nan" daga haka ya fice daga ɗakin ya barta zaune.
Duk wani taku da Abaan ke yi masifa ce a gurin Imara, tana jin kamar yana tafiya da rayuwarta, duk yanda take ƙoƙarin cire son shi daga cikin zuciyarta abun ya gagara, burinta bai shige ta ganta zaune kusa da shi ba, idan dare ya yi har Allah Allah take gari ya waye domin tayi ido biyu da shi, amma da alama duk abubuwan da take a banza suke tafiya, da alama Abaan bai lura da halin da take ciki ba ballantana tayi tunanin samun abin da take so daga gare shi.
****Around 7pm suka yi parking a wajen event ɗin, kallonta Khalil ya yi ganin yanda ta yi shiru ya ce"sannu, kan ne har yanzu?, ko dai mu fara zuwa mu siyo maganin?" girgiza masa kai tayi cikin sanyin murya ta ce"naji sauƙi sosai" girgiza kansa ya yi ya ce"a'a Imara, idan da kin ji sauki ba haka za ki yi ba, bari a tashi sai muje koda su Umaima ne a siya miki magani kinji" gyaɗa masa kai kawai tayi, sannan ta sauka daga motar. Yana sauka ya haɗu da su Kamal hakan yasa ya kalleta ya ce"maza je ki shiga Imara" gyaɗa masa kai ta yi sannan ta fara tafiya. Tana shiga hall ɗin ta hangeta can saman stage sanye da fararen kaya, yayinda duk wata budurwa dake wajen ta saka baƙar riga, hakan yasa suka yi kyau ba ƙarami ba. Kallo ɗaya ta yiwa Abaan dake zaune kusa da ita yana sanye da suit farare gashin kansa wanda ya sha gyara sai sheƙi yake, dafe ƙirjinta ta yi sai kuma ta nemi kujera acan bayan ta yi zamanta. Tana zaune aka dinga tashi ana zuwa rawa da amarya, Jidda ba zaka ce bikinta ake ba dan sakar jikinta ta yi tana rawarta hankali kwance. Tana kallon sanda su Umaima suka je kan stage aka dinga liƙa kuɗi kamar ba'a san zafinsu ba, tashi Imara ta yi ta fita daga hall ɗin ta nemi can wani dandamali ta zauna.
Sai wajen ƙarfe 9pm sannan aka fara fitowa daga wajen, har sannan tana zaune a wajen, ta dunƙule jikinta saboda wani zazzaɓi da ya rufe ta. Har sun shiga mota Khalil ya ƙaraso wajen yana kallonsu ya ce"ina Imara?" Da mamaki Umaima ta ce"Imara kuma?, ai ba ta zo ba" zaro ido Khalil ya yi ya ce"wane irin bata zo ba, ni ne nan na kawota wajen nan, na ce ta shiga ciki, kuma akan ido ta shiga ciki yanzu kuma ku ce bata zo ba" girgiza kai Nana ta yi ta ce"wlh to Yaya bamu ganta ba, mu muna tare da yaya Adeel" jinjina kai Adeel ya yi ya ce"gaskiya bata zo inda suke ba, koma ta shigo ɗin" da sauri Khalil ya bar wajen ya shiga dubata sai dai iya dubansa ban ganta ba. Can ya hangi su Abaan tsaye suna magana da Kamal, ƙarasawa ya yi yana kallonsu, ganin irin yanda yake kallonsu ya sanya Kamal ya ce"Khalil lafiya dai?, meya faru?" girgiza kai ya yi ya ce
"IMARA!"
# *IMARA 💋*
# *Bestnovel*
# *Nanameera*
# *2025*.
*Sauran posting 1 na kammala book one, ƴar uwa har yanzu ba ki yi payment ba??, kina son ganin yanda abun zai kasance kuwa?, da a baki labari ai gara ki bayar saboda haka maza-maza ki yi payment ta wannan account ɗin 7041901078 Hauwa Adamu lawan opay, sai ki turon shaidar biya ta lambata ***, ₦500 kacal, karki bari ayi babu ke, daga gobe ne💃💃, taku har kullum Nanameera*