TAREEQ IMAM BOOK 2

Chapter 003

by @jeeddah3256

TAREEQ IMAM

Na

Jeeddah Aliyu

Arewabook@Jeeddah3256

003.

Tun daga yanayi da fizgota ta tabbatar yau duka da zai mata bana wasa bane. Tsanani firgita da tai ga kuma zafin da ke ratsa damtse hannunta sakamakon mugun riƙo da ya mata, yasa tayin wuƙi-wuƙi da idanuwa tsoro ya bayyana ƙarara akan kyakkyawar farar fuskarta. Idanuwanta ta sauke akan murtuƙaƙƙiyar fuskarsa cikin sarƙewar harshe ta furta. "Da...All...ah..Ya...Tashh....

Tun kafin ta ƙarasa magana ta ji saukar rikitattacen mari, sai da ji da ganinta suka ɗauke na ɗan wani lokaci, bayan wuyanta ya riƙe ya dinga sakar mata naushi kamar yana dukan sa'ansa kafin ya ture ta da ƙarfin gaske gefen goshinta ya bugi glass door.

Ta fasa ihu da dukkan ƙarfinta cikin sauti mai ƙarar gaske gaba ɗaya illahirin gidan ya cika da amon sautin muryarta, duhu ya fara mamayewa ganinta tun tana gani dishi-dishi har ta ji diff komai ya tsaya mata cakk! numfashinta ya ɗauke tamkar ɗaukewar wutar lantarki kana ta zube ƙasa dai-dai securities ɗin gidan suna ƙarasowa da gudunsu da sauri Tareeq ya cire agogonshi da ke maƙale cikin tafin hannunta, sai da ya watsa musu mugun kallo tare da nuna su da yatsa yana cizan lips ɗinshi na ƙasa, ya yi ƙwafa alamar da ke nuna gargaɗi kana ya nufi gate cikin tafiyarshi ta ƙasaita, sai kace wanda ya aikata abin arziki da gudu ɗan Bala ya zo ya buɗe mishi gate ya fice abinsa hankalinshi kwace zuciyarshi zaune.

Ummi tana fitowa daga bathroom ta ji ihun Tahreem nan take gabanta yai mummunan faɗuwa, da gudunta ta fito daga ɗakinta dai-dai Aayya, Fadila da Baby su ma suna fitowa a guje yadda ihunta ya karaɗe gidan za ka zaci a main parlour take.

Har ture juna suke wajen fita Ummi ce a gaba sai Fadila da ke take mata baya, ɗaya daga cikin securities ɗin ne ya ɗago ta gaba ɗaya jini ya wanke mata fuska.

"Innalillahi wa'inna illaihim raji'un....Bello me ya same ta?"

Ummi ta faɗa sa'ili da ta durƙusa gaban Tahreem tana tattaɓa ta.

"Hajiya nima ban sani ba muna bakin Gate ne muka jiyo ihunta."

Bello ya faɗa domin yana gudun aji mutuwar sarki daga bakinshi.

Cike da zallar masifa Aayya ta ce.

"Amma kuwa Bello ba ku da amfani a gidanan taya yarinya za ta ji mummunan rauni irin wannan tsabar lalacewa ace ba ku san dalili ba. Bari Imamu ya dawo daga kai har tawagarka sai kun bar gidanan katti banza kattin wofi kuna cinye mana abinci a banza bakwa kula da aikinku yadda ya dace."

Kuka Ummi ta fashe dashi lokaci da ta fahimci babu numfashi a jikin Tahreem.

"To ko dai zamewa tai ta faɗi ne?"

Baby ta tambaya fuskarta shimfiɗe da mamaki.

"Kai Bello ɗauke ta kasa ta mota mu kai ta hospital kuna kallo ko numfashi ba ta yi kun tsaya ɓata lokaci."

Fadila ta faɗa a ɗan fusace domin ba ƙaramin haushi securities ɗin suka ɓata ba.

Da sauri Ummi ta koma ciki ta dauƙo hijab haɗi da ATM card ɗinta.

Tana dawowa ta ci karo da Baby ta dauƙowa Aayya nata hijab ga baki ɗaya suka ɗuguma zuwa asibiti.

Kasancewar asibitin da suke zuwa ce shiyasa aka karɓe su da gaggawa nan take aka shiga treatment ɗinta, dukkansu tsa-tsaye suka yi a bakin ƙofar ɗakin da aka shigar da ita.

Har zuwa lokaci Aayya tana kumfar baki.

"Wannan lalacewar ta Tahreem tayi yawa duk girmanta ace batasan yadda ake tafiya ba, gashinan garin shan-shancinta ta jawo mana zuwa asibiti da magaribar fari."

A fusace Baby ta maida wa Aayya magana cikin ɓacin rai take cewa.

"Dan girman ALLAH Aayya ki barmu mu ji da abin da ke damun mu ko ke kin wuce ALLAH ya kawo miki tsau-tsayi ki zame ki karya hannu ko ƙafa?"

"La'ilaha'illahu......Maryama ni kike yi wa mummunan fatan In-sha-ALLAH akan ɗaya daga cikin ubanai ki karaya za ta ƙare ba dai ni Aayya ba, ƴar banza yarinya mai kambun baka.

Fitowar doctor Hafiz yasa ba wanda yasake bin ta kan Aayya balle ta sami mai bata amsa.

"Dr Hafiz ya jikin nata?"

Ummi ta faɗa muryarta na rawa.

"Al-hamdulillah! Ta farfaɗo ta ɗan bugu a gefen kanta har mun mata ɗimki nayi mata allurar bacci saboda tana buƙatar hutu, da zarar ta farka za a yi discharge ɗinku.

"Al-hamdulillah!

Kusan a tare suka faɗa kafin Fadila tai karaf ta ce "doctor za mu iya shiga mu ganta?"

"Kwarai kuwa amma Dan ALLAH banda hayaniya."

Cikin yatsine fuska Baby ta nuna Aayya da baki tare da furta

"Ita za ka faɗawa Dr domin tun ɗazu kwakwazonta ka ke ji, gara ka kashe mata gargaɗi tun wuri ta gane akwai bambanci tsakanin asibiti da gidan Imamu."

Baby ta ƙarasa magana cikin gatse.

"Na shiga uku ni Aayya Maryama ni kike faɗawa magana Kamar wata sa'arki, Amina a gaban ki ƴarki ke kwashe min albarka tsabar lalacewa kin zuba mata idanu taci karenta babu babbaka ko? To bari Imamu ya dawo wallahi daga ke har ita sai nasa yaci min mutumcin ku mutanen banza da wofi."

Ajiyar zuciya Ummi tayi tare da goge zufan goshinta da gefen hijabinta, kafin ta dallawa Baby harara rai ɓaci ta ce.

"Bana cike da iskanci Baby Aayya sa'arki ce da za ki dinga faɗa mata magana son ranki, maza bata haƙuri kafin na rufe ki da duka."

Turo baki Baby tayi cikin yatsina ta dubi Aayya.

"Yi haƙuri Aayyarmu."

Ta faɗa a takaice kana ta tura ƙofar ɗakin da Tahreem take wanda tuni Fadila ta tsofa ciki.

"Aikin banza can ki nemo Aayyarku wannan Aayya ta Tareeq ce domin shi kaɗai ne duk a cikin ƴaƴa da Imamu ya haifa da ba ya min ɗibar albarka."

"Dan ALLAH Aayya ki daina biyewa yaranan su na saka ki kumfar baki."

Ummi ta faɗa tana mai tura ƙofar ɗakin ta shiga, mugun kallo Ayya ta bi ta dashi kafin tai ƙwafa ta bi bayanta.

A kwance suka tarar da Tahreem an yi mata fixing ɗin drip sai sharar bacci take kusa da ƙafafuwanta Ummi ta zauna, cike da alhini take kallon gefen goshinta da ke lulluɓe da bandeji.

Fadila da Baby suka jingina da bangon ɗakin zuciyarsu cike take fal da tausayin Tahreem,wata irin ƙauna suke mata kasancewarta marainiya kuma ƙarama a cikinsu shiyasa ko ciwon kai take gaba ɗaya sai sun shiga damuwa. Tareeq ne kaɗai bai damu da ita ba, ba dan baya ƙaunarta ba kawai dai yana cin zalinta ne dan ya fahimci duk gidan ita kaɗai ce zai taɓa ya saka su ɓacin rai shiyasa, duk lokaci da suka haɗu sai ya zalunce ta hanya rankwashi ko ya murɗe mata kunne, ko kuma ya ja mata gashi yana kiranta da mai red hair Kasancewar sumar kanta ba ɓaki bane jajir yake sai tsantsi tsiya don ko kitso ba a mata sai dai ayi mata parking da hairband ko ai mata kalaba.

Tareeq yana fita kai tsaye gidan su Rooney ya nufa yana zuwa gidan ya wuce ɗakin Ronney da ke boys questers, koda ya shiga Ronney yana zaune gefen gado yana ɗaure igiyoyin takalmin shi. Hannu Tareeq ya miƙa mai suka kashe ya nemi doguwar kujera guda ɗaya tal da ke ɗakin ya zauna.

"Dan ALLAH Rooney ka sa wa jikinka gishiri mu bar unguwar nan na rantse maka da ALLAH idan Ummi ta rutsani a gidanan yau kashina ya bushe ko ɗazu ta min duka, don kawai Maman Nana ta kai ƙarana.

Balle yau na ɗebo ta da zafi na kuma tabbata ko yanzu ba tsallake wa dukan nata zan yi ba."

Dariya Ronney yasa har yana dukan gefen gado.

"Wai Slugger sai yaushe za ka wuce duka a wurin Ummi?"

"Ba rana Rooney saboda kullum ni mai laifi ne a wajenta. Musamman yau da na taɓo shalelenta red hair.

Zaro idanuwa Ronney ya yi cikin ƙaduwa ya ce.

"Kutt! lallai yau abokina ka taɓo tsuliyar dodo ALLAH yasa ba dukanta ka yi ba?"

"Sai dai kar a koma abokina don har goshinta na fasa kai a takaice kwance na baro ta cikin jini, dukan da Ummi tai min na huce akanta."

"Saboda Ummi ba ta buguwa shine ka huce akan ƴarta wallahi ka ji tsoron ALLAH kada haƙƙin marainiya ya kama ka."

Ronney ya faɗa yana mai miƙewa tsaye.

"Kai dallah mu tafi ba wani haƙƙi da zai kama ni maraya nawa ne ake zalunta sai ni da na taɓa guda ɗaya shine haƙƙi zai kamani zance banza kawai in fact Ummi ce ta jawo mata ko gobe ta dake ni sai na rama akan red hair ai Rooney Ummi tayi sake da na gano mai jan gashi ita ne weakness ɗinta."

Sosai furucin shi ya ba wa Ronney dariya, cikin dariya ya ce.

"Gaskiya abokina kai taƙadari ne na ƙarshe bangon littafi, na rantse da ALLAH ban taɓa gani tsagera irinka ba."

Tareeq yai murmushi yana shafa sumar kanshi, suna fitowa suka ci ƙaro da Lil-prince ya ɗauko motar Abbanshi saboda yau haka suka tsara da tsalelliya motar Alhaji Sa'id marafa za su fita Da gudu tsiya suka bar unguwar kai tsaye wani wurin hutawa suka nufa dama, anan suke zama a duk lokacin da suka haɗa joint.

Anan suka tarar da raguwar abokan rashin jinsu Hisham Yahaya ɗan kwangila da suke yi wa laƙabi da Dezzy sai Sadeeq A. Salis shi kuma su na kira shi da Sasco sai mace ɗaya kacal da ke team ɗin nasu Rufaida Mustapha sodangi suna kira ta da Roofy Sodangi.

Dalilin shigar Roofy Sodangi gang ɗinsu Tareeq saboda tsananin ƙaunar da take mai duk da kasancewarsu classmate, kuma agemate soyayyar shan mitti suke zubawa abinsu tamkar ba ƴan secondary School ba ko kuma teenagers.

Suna zuwa Roofy ta taso da sauri jikinta har ɓari yake ta rungume Tareeq, ba kunya bare tsoron ALLAH ya ke lalluɓarta a bainar nasi.

Shisha pot aka kawo musu haɗi da champagne bottles, a gefe ɗaya ga ice cubes a cikin wani ɗan ƙaramin bowl, idan suka zuƙi shisha su yi sipping champagne.

Duk yawancin samari da ƴan matan da ke zaune a wuri matasa ne masu ƙaranci shekaru,kallo ɗaya za kai musu ka fahimci cewa ƴaƴa masu hannu da shuni ne wanda suka fi ƙarfin iyayensu, ko kuma wanda ba su da mafaɗi ko ana faɗa ba sa ɗauka.{ALLAH Ubangiji ya shirya mana yaran mu bisa hanya madaidaiciya, dole sai mu ɗage da yiwa ƴaƴanmu addu'a domin muna cikin wani irin zamani da tarbiyya tai ƙaranci, kuma mu dinga lura da irin abokanai da yaran mu ke hulɗa dasu}

A can asibiti kuma sai misali ƙarfe 11:20pm Tahreem ta farka tuni an daɗe da cire mata drip, da sauri Fadila ta fita ta kira doctor da ke on call ya sake duba jikin Tahreem ya ga komai normal ya cike masu discharge papers.

"Baby ki tashe da Aayya mu tafi gida naga kamar bacci ya ɗauke ta."

Ummi tai magana tana ƙoƙarin kama Tahreem ta sakko daga kan gado.

Baby ta nufi gun da Aayya take kwance akan sallaya da tai sallar isha'i.

"Aayya....Aayya! Ki tashi mu tafi gida an sallame mu.

Baby ta faɗa tana ɗan bubbuga kafaɗar Aayya, buɗe idanuwa Aayya tayi tare da jan guntun tsaki.

"Mtsss..!

Kana ta zarce da faɗar.

"Uhmm!... ALLAH shi kyauta yau lalacewa ta cika da mu a asibiti, shi kuma wannan lalatacce likita sai yanzu ya gama, damar sallamar mu, kai Allah dai wadan naka ya lalace."

Ta ƙarasa magana tana warware hijabinta wanda dashi tai matashi.

Fadila ta matso kusa da Ummi ta kama Tahreem suka fice Ummi da Baby suka biyo su a baya yayin da Aayya tana tafe tana mita, duk azababbiyar mita da take yi ba wanda ya ce mata ci kanki.

Sai da suka shiga mota sun ɗau hanyar gida Fadila ta kwantar da kan Tahreem a cibiyoyin ta tana shafa sumar kanta, cike da zallar damuwa tace.

"Gifty garin ya ya kika ji wa kanki mummunan rauni irin wannan?"

Baby da Fadila ke kiranta da suna gifty saboda kyauta ce wacce Allah ya basu, kuma sharp brain gareta bala'in kokari ne da ita gata da ɗan banza surutu.

Sai da Gifty ta lumshe idanuwanta kana ta buɗe su ta ɗago kanta ta yadda za ta iya gani fuskar Fadila da kyau, cikin 'yar muryarta mai cike da yarinta ta ce.

"Lokaci da na dawo daga islamiyya na shigo da gudu, shine muka ci karo da Ya Tareeq by mistake na bangaje shi wristwatch ɗin ya fadi shine ya zabga min mari yana ta dukana ya

kuma ture ni goshina ya bugi glass door.

#Jeeddah Aliyu

#Tareeq

#Tahreem

#Baby

#Fadila