JIKAR BAUSHE

1&2

by @meenatyandoma

JIKAR BAUSHE

©️®️ MEENAT A. YANDOMA

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

HARAMUN NE SARRAFA MIN LABARI TA KO WACE SIGA BA TARE DA IZINI NA BA. 'YAN YOUTUBE MA HAKA

🅿️ 1&2

Farin ciki da murna sune suka wanzu a kan fuskar jama'ar wannan gida. Hannunta riƙe da amarya sai faman rangaɗa guɗa ta ke. Momy da Dada kuwa Kallo daya zaka yi masu ka hango zallar firgice da tashin hankali a tattare da su.

Ƙanwar Momy ce ta zungurota da sauri ta yi firgigit! Tare da nuna masu dakin da zasu shiga. Tamkar jira ta ke tsalle ta yi a kan gadon tare da tuntsurewa da dariya. "A samu wani ta taɓa ni. Don Allah ku tabbatar min da gaske yau ni ce a ɗakin Asiim. Matsayin matarsa." Ilahirin jama'ar da ke cikin ɗakin Dariya suka kwashe da ita, ganin Farida duk ta rude.

Ƙanwar Mahaifiyarta ce ta Umurce a ba su wuri. Mutanen ɗakin ficewa suka yi tare da ja masu ƙofa.

Hankalinta ta mayar a kan Farida. "Ba sai na yi dogon turanci ba. Kin dai san fama da baƙar wahalar da muka sha kafin a karkato da hankalinsa a kanki. Kada kiyi wasa da duk magungunan da Gobe da nisa ya bada, kinga wannan uwar mijin ta shi da waccan Kakar ta sa! Sai kin iya takunki. Abu na farko da za ki yi shi ne ki raba shi da Uwarshi. Ke ba ma uwar kadai ba Kowa ma ki raba su ya zama na ki ke daya."

"Umma ni fa ce! Ki zuba ido daya bayan daya duk sai na yi maganin kowa"

"Yawwa 'yar albarka! Nasan jininmu ba za su bani kunya ba. Yanzu bari In baki wuri ki kimtsa Kinsan yanzu za a mayar da mu."

Ɗakin da ya gaji da haduwa ta ƙarewa kallo tare da dauko jikkarta. Gabanta ne ya yanke ya faɗi. Zuciyarta ta yi tsalle tamkar zata faso ƙirji ta fado.

Murza idanuwanta ta hauyi ko sune suke mata gizo. Ganin ba zai fisshe ta ba ya dakata zazzage jikkata a saman gado.

Sai dai bata rina ba. Domin magunguna dai sunyi ɓatan dabo, a firgice ta nufi ƙofa sai dai kafin ta ƙarara ƙofar ce ta kulle kanta da ƙarfin tsiya.

Cike da mamaki ta ke tsaye kwakkwaran motsi ma ta kasa. Motsin da ta ji a ƙarƙashin gadon ne ya kara hauhawar tashin hankalinta. Wutar ɗakin ce ta fara fafarniya fankokin suka kunna kansu tare da falfala azababben gudu.

Ihu ta ke son yi amma ina! Bakinta ji ta yi tamkar an saka Gum an datse Shi. Lafawa da fafarniyar wutar tayi, sai dai ji tayi ana fizagarta da ƙarfin tsiya.

Bugata aka yi kanta ya haɗu da gefen bedside. Da ƙyar ta miƙe dafe da goshi lokaci daya komai na ɗankin ta fara ganin ya na koma mata bibbiyu.

Kuka take amma sam baka jiyo sauki domin bakinta a daɗe ya ke sai hawaye da ke tsere a kan kumatunta.

Hirɗeɗen Macijin da ya fito daga ƙarƙashin gadonta ne ya sakata daskarewa a inda ta ke.

Harshe ya fiddo tare da tunkaro inda ta ke gadan-gadan. Jajayen idanunshi ya kafeta da su, tare da saka jelarshi ya shaƙar mata wuya.

Azabar da ta ke ji ce ta dakatar fara shure-shure da ƙafafuwan. Ihun da ta yi sa'ar saki shi ya yi daidai da kafa mata haƙora da Macijin ya yi.

Jinin jikinta ya ke zuga ba tare da imani ba sai da jikinta ya koma fari sol. Ƙanwar Mahaifiyarta ce ta ji gabanta ya tsinke ya faɗi.

"Kamar fa ihun Farida" ta fada cike da tashin hankali. Rige-rigen shiga dakin suke, ganin ƙaton maciji suka ga ya fita ta tagar (Window) ihu ta saki tare da girgiza ta "Faridaaa"

Mahaifiyar Asiim kuwa ganin Farida yashe a ƙasa jikinta fari fat! Yanke jiki ta yi ta faɗi.

Kuka Dada Ke yi tana faɗar "shi kenan! Ita ma wannan mun rasata. Wannan wane irin bala'i ne ke bibiyarmu."

Nan fa gida ya rikice da iface iface wasu kuma suka hau yanke jiki suna faduwa...

Ƙasurgumin jeji ne wanda ihunka banza kururuwarka a wofi. Sanye ya ke cikin kaya.

Wanda aka hada da fatar damusa. Dattijo ne wanda shekarunsa zasu haura tamanin, kallo daya za kayi masa gabanka ya yanke ya fadi sakamakon uwayen layoyin da ke sakale a kowace kusurwa a jikinshi.

Ganyayen magunguna ya rika Sara tare da haƙo wasu.

Gefenshi matashiyar budurwa ce sanye cikin kayan saki, kalar fatarta baka ce sai dai Allah ya yi halitta a wurin. "Kaka " ta kira sunan shi cikin girmamawa.

"Akwai matsala" ta furta tare da dafe kanta da take jin tamkar zai tarwatse, ga wani irin jiri da ke ɗibarta.

Da sauri Baushe ya tarbe Samu da ke kokarin faɗuwa. "Tabbas ya shigo garin. Me yasa a ko da yaushe muke samun sabani." Maganarsa ce ta makale sakamakon idanun Samu da ya ga sun fara rikiɗa.

A gaggauce ya buɗe jikkarshi tare da shaƙa mata wani magani a hanci.

Jikinta ne ya fara karkarwa idanunsa suka ƙara fitowa waje, a hankali ciwon ya lafa sai dai jiri da ta ke gani.

Riko hannunta ya yi suka miƙe tare da taimaka mata suka fara tafiya. Wulgawar inuwar da ya ga ta wuce su tamkar walkiya ita ta ƙara tayar masa da hankali.

Samu kuwa ilahirin jikinta ciwo kara dawowa yayi gurnanin da ya ji ta fara ne ya saka shi karanto wasu ɗalasiman tsafi. Idanunsu ya rufe sai gasu a cikin garin.

Da kuka mahaifiyarta ta tarbesu domin tasan ciwon Samu ne ya tashi.

Iface-ifacen da Baushe ya ji ne suka ƙara tabbatar ma shi da abinda ya ke zargi.

Kofar gida ya fito sai dai gawarwakin da ya ga an jera ma shi reras ya saka gabanshi yankewa ya fadi.

Lokaci daya abinda ya faru ya dawo masa tamkar yadda madubi ke dawo ma mutum da suffarshi.

Ihu da ya ji an kurma a cikin gidan ne ya saka shi saurin shigewa mutane suka take ma shi baya...