JIKAR BAUSHE

3&4

by @meenatyandoma

J I K A R B A U S H E

©️®️ MEENAT A. YANDOMA

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

HARAMUN NE SARRAFAMIN LABARI TA KO WACE SIGA BA TARE DA IZINI NA BA. 'YAN YOUTUBE MA HAKA

🅿️ 3&4

...'Katuwar Mujiyar da mutane suka hango ta nufo su ne ya saka wasu juyawa a gigice suna ƙoƙarin ficewa daga gidan.

Baushe kuwa ganin bala'in yau ya zarta na kullum wasu ɗalasimai ya riƙa karantawa tare da rufe idanuwansa. Sai dai ba arziki yayi gaggawar buɗe su sakamakon sabuwar kururuwar data daki don kunnenshi.

Duk ƙoƙarin da zai yi ganin Mujiyar ta sauko da ƙaramin yaron da ta shura abu ya ci tura. Sako shi ta yi daga kololuwa fadowar da zaiyi kanshi ya hadu da wani dutse, ko shurawa baiyi ba ya ce ga garinku nan.

Sake rikicewa jama'a suka yi tsawar da Baushe ya daka masu ce ta saka su dawowa cikin hayyacinsu.

Wata ƙatuwar Laya ya fiddo tare da wurgata sama lokaci daya Mujiyar da layar suka yi batan dabo.

"A yau ba zamu bar wurin nan ba sai ka sanar damu halin da wannan nahiya ta mu ta ke ciki. Tun farko mun kasance tamkar bayi a gareka duk wata damuwa ta mu kai ne ke yi mana maganinta, yau mun wayi gari masibu biyu sunyi mana kamun kazar Kuku. Kwakkwaran bayani ka ƙi yi mana game da wannan maciji da ke shigowa ya dauki rayukan danginmu a duk sa'in da ka tafi jeji. Kwatsam yau sai ga Mujiyar da ke firgita dukkan jama'ar mu ita ma yau ta fara mana dauki ɗaiɗai..."

Dukan da Baushe ya kaiwa mutumin da sandar hannunshi ce ta saka shi daskarewa ko mai ya jikinsa ya ƙame.

Shugaban Bokaye da isowarshi kenan da sauri ya riƙe hannun Baushe.

"Wuta ta dafawa shugaban. Ruwa da ƙoramu su sanyaya zuciyarka. Sunyi kurkure tuba suke"

Idanuwansa da suka rikiɗe jajur ya watsama jama'ar da ke wurin. A take suka zube bisa ƙafafunsu su na neman gafarar wautar da ɗaya daga cikinsu ya yi.

"Tsufa ba zai saka in yi sanyi ba, muddun zaku aika abinda wannan ya aikata zaku samu sakamako daidai da na shi." Ya karasa maganar tare da nufar gawawwakin da Macijin ya kashe.

Wani Magani ya debi tare da watsawa sama a take komai ya bayyana a gareshi tamkar ya na wurin.

Doguwar ajiyar zuciya ya sauke domin wannan shi ne karo na farko da ya kasa shawo kan matsala.

Babban abinda ke tayar mai da hankali da ya cika bincike akan sarar Macijin fuskar jikanyarshi ya ke hangowa cikin mawuyacin hali hannun ta riƙe da na wani saurayi da ya juya bayanshi.

"Tarihi zai maimaita kanshi" wata firgitacciyar murya ta daki dodon kunnenshi.

Umurtar mutane yayi a kauda gawawwakin zuwa safiyar gobe, ba tare da bata lokaci ba aka kauda su.

Alama yayima Boka Lammar. Ƙatuwar bukkar da babu mai shigarta sai shi suka nufa. Sandar da ya ke dogarawa ce ya saka tare da bugun Mujiyar da ke kwance tana fizge-fizge.

Lammar kanshi sai da ya firgita tare da ja da baya. "Ya shugabana ka yi min uzuri in hallaka wannan Mujiyar tunda ka kamata"

Kallon ya watsa mai ne ya saka shi hadiye sauran maganar.

"Wannan da kake gani ba Mujiya ba ce Samu ce"

Tsabar gigicewa Boka Lammar ya yi sai da Baushe ya daki kafadarsa kafin ya dawo cikin hayyacinshi.

"Ya shugaba ka gafarce ni akan abinda zan fada."

"Kada ka fadi komai har sai Samu ta koma ainahin Halittar ta"

Sannu a hankali ta fara rikiɗa zuwa suffarta ta asali. Kallonsu take cike da mamakin abinda ya shigo da ita a wannan bukkar da rabonta da ita tun tana yarinya.

"La'ana Mummunan abu ce, wadda komai daren dadewa sai ta zama babbar musibar da zata addabi kowa. Ka gafarce ni da abinda zan fada domin bazai maka dadi ba, jikina ya na bani ruhin tagwaye ne ya dawo wannan duniyar."

Shaƙar da Baushe ya yi mai ce ta saka shi hadiye sauran maganar.

"Ranar da duk ka kara yi min maganar tagwaye ita ce ranar da zaka shaki numfashi na ƙarshe."

"Kaka su waye tagwayen nan da baka so a na tayar da maganarsu" cikin dabara ya shafi goshinta ji lokaci daya ta manta da maganar da ta yi.

Alama ya yi mata ta fita waye. Mugun kallon gargadi na karshe ya watsawa Lammar. Tare da nuna ma shi kofa

Samu kuwa ta na fitowa bukkar da Mahaifiyarta ke ciki ta shige. Da gudu ta rungumeta.

"Nasha ce miki mu gudu mu bar wannan baƙar nahiyar tun kafin zanen kaddararki ya gama lalacewa. Mujiya fa kika zama yau" ta karasa maganar tare da fashewa da kuka.

Sakinta ta yi tare da dauko wata Kwalba " ki zo mu gudu da wannan kwalbar na tabbatar Baushe ba zai taba ga no inda muke ba. Na shiga tashin hankali mara misali ganin yau ke ce tsaye a gabana kin koma mujiya."

"Na sani domin a zahiri a wata duniya na tsinci kaina, rana ta farko na gamu da wani mai suna Husaini. Wannan tambarin da ki ke gani a wuya na shi ya min shi."

Kwalbar da ke hannunta sakinta ta yi ƙafafunta kasa saukarwa suka yi ba shiri tayi zaman 'yan bori "Shi kenan! Hussaini"

Baushe da tunda suka fara magana ya ke tsaye gaban bukkar karasa shigowa yayi tare da fizgo Samu ya na duba wuyanta. Tambarin da ya yiwa tagwaye da hannun shi yau shi ne ya bayyana a wuyan samu.

Sandar da ke a hannunshi ce ta fadi ƙasa cike da tashin hankali ya fara ja da baya ya na nuna Samu...

...Kuka Dada ke yi tare da riko hannun Momy. A hankali ta fara motsa hannunta da yayi mata nauyi.

"Ita ma Macijin ya kasheta ko? Ta mutu shi kenan! Maganar mutane ta tabbata a kanmu."

Ta karasa maganar tare da fashewa da kuka.

Ita ma Dada Kukan ta ke an rasa mai rarrasar wani. Ƙanwar Momy da ta shigo ce ta saka su lafawa da kukan.

"Yaya mun shiga uku! Da gaske Farida ta mutu, ita ma ta tafi shi kenan Asiim ba zai taba auruwa ba shi kuma ta shi kaddarar kenan "

"Ki daina fadar haka! In shaa Allah zai yi aure ko me tsanani sauki ya na zuwa. Alhaji ka tafi ka barni cikin mawuyacin hali, rana zafi inuwa kuna. Ina ma a ce kafin mutuwarka ka nuna min mutum daya wanda da zan nunawa Asiim a matsayin dangin mahaifinshi"

Shigowar likita ce ta saka su yin shuru. Duba jikinta ya yi tare da sallamarsu.

Yau ma kamar kullum sanye ya ke cikin bakaken kaya wuluk! Dakin ya turo fuskar nan a murtuke idanunshi sun yi jajur tamkar gauta.

Tamkar an saka wuƙa an yanki wuyanshi raɗaɗi gami da azaba suka yi mai dirar mikiya lokaci daya. Lebenshi na kasa ya cije tare da rufe idonshi cike da azaba.

Tausayin shi ne ya ƙara kama Hajiya hawayen da ta ke kokarin boyewa ne suka kubce mata.

Dada kuwa ganin halin da Asiim ke cike da sauri ta riko shi. "Lafiyarka kuwa? Ko dai jikin ne zai tashi"

"Duba min me ya a wuyana" ita ce kalmar da yayi kokarin fizgowa.

"An shiga uku! Wani tambari ne ya bayyana" jin abin da ta fada ya saka shi saurin rufe wuyanshi tare da wurga mata hararar da ta sakata sakin ihu.

"Zinatu kin auro irin masifa, shin kunga abinda na gani a idon Asiim?"

In da sabo sun Saba da halin Asiim da na Dada don tun ya na yaro tana daukarshi zai fara hararata, ita kuma ta ce mai me idanuwan abun kasa.

Wannan Drama tun Mahaifin Asiim na raye ake yinta har kawo yanzu.

Kukan da ya ga mahaifiyarshi na yi ne ya ƙara tayar mai da hankali. Banko ƙofar aka yi da ƙarfin tsiya, ganin ƙanwar Maman farida ce ya saka Momy tashi a zaune.

"Allah ya isa tsakaninmu da ku. Ashe duk abin da ake fada a kanku gaskiya ne, yau ga shi mun rasa diyarmu sanadin hada jini da ku. Allah ya isa tsakaninmu da ku kotu ce zata raba mu."

Cike da ɓacin rai Asiim ya yi kanta tare da nuna mata hanyar fita.

"Bazan fita ba in so kake ka nunamin ka kai dan iska ka fitar da Ni da karfin tsiya"

Dada da ke gefe ganin ciwon Asiim zai iya tashi ya sakata fara bata hakuri ta fita.

Zagin da ta fara dannawa Dada ne ya saka Asiim yin kanta tamkar yunwataccen zaki. Shaketa yayi ya na huci da kyar Security suka banbareta a fusace ya nufi motarshi.

Gudu ya ke tamkar zai tashi sama tsarewar Ubangiji ita ta mayar da shi gida lafiya. Tun a falo ya fara fatali da duk wani abu da ya tari gabanshi.

Jin numfashin shi na kokarin daukewa mikewa ya yi sai dai duhun da ya ga ya gilma ta gabanshi zubewa yayi kasa tamkar matacce.

Momy kuwa daren ranar bata rintsa ba kachokam hankalinta na kan Asiim, jikinta ya na bata a duk in da ya ke ya na cikin mawuyacin hali.

Cikin ikon Allah wayewar gari likita ya sallamesu. Tun daga bakin get take tambayar mai gadi sai dai motarshi da ta hango ta saka ta fadawa fakon da gudu.

Hango shi suka yi a yashe ba a alamun rayuwa a tattare da shi. Ƙanwar Momy ce ta yi saurin riko shi tana girgiza shi tare da kiran sunanshi da karfi....