5&6
J I K A R B A U S H E
©️®️ MEENAT A. YANDOMA
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
HARAMUN NE SARRAFAMIN LABARI TA KO WACE SIGA BA TARE DA IZININA BA. 'YAN YOUTUBE MA HAKA
🅿️ 5&6
...Momy ce ta yi ƙarfin halin dafe goshinsa ta na karanta ayatul kursiyyo. Ba shiri ta janye hannunta jin azababben zafi ya mata dirar mikiya.
"Yaya akwai matsala. Ko dai a kira Malamin nan?"
Girgiza kai Momy ta yi cikin rashin sanin madafa.
"Malami dai tun ranar da ya bar gidan nan har yau ko ɗuriyarsa ba a ƙara ji ba. Tsoro na ke ji in sake kiran wani ya zo abin da ya faru da na baya shi ma ya faru da shi"
Tarin da Asiim ya fara ne ya saka su fara jeru mashi sannu. Sauyin da ya ji a jikinsa ne ya tabbatar mashi ya na gaf da wuntsiralawa duniyar da ya saba zuwa tun ƙuruciya har kawo yanzu.
"Zan tafi daki kada wanda ya biyo ni"
"Yanzu kana cikin wannan halin za ka ce kada a biyo ka? Ko kowa bai bika ba ni tabbas zanbi" Dada ta ƙarasa maganar tare da kauda kanta.
Ganin ba su da wata mafita ya saka Momy kiran family doctor dinsu. Asiim kuwa da ya fara fita a hayyacinsa dishi-dishi ya hango likitan.
Allurai guda biyu ya fiddo tare da nufar inda Asiim ya ke.
Ɗif! Wutar ɗakin ta ɗauke. Salatin da Dada ke yi shi ya karasa rikita kowa a falon, domin iya saninsu akwai Nepa.
Asiim kuwa da ya ke cikin mawuyacin hali. Wutar ɗakin ce ta dawo nufar Asiim likitan ya yi da allurai na jijiya ya na kokarin saka masa kalulu.
Sai dai duk iyakar kokarinshi ya tashi a banza domin tamkar yana taba dutse haka jikin Asiim ya koma.
"Kadaaa ka huda min jiki. Ciwo duk ƙarantarsa kashe mu ya ke" ce War Asiim cikin wata irin murya me matukar ban tsoro.
Dada ƙafafunta kasa ɗaukar ta suka yi ba arziki ta yi zaman yan bori.
Likitan kuwa bai dauki maganar da yayi a bakin komai ba. A zatonsa zafin ciwo ne ke dawainiya da shi.
Allura ya dauka ya na kokarin juyar da Asiim, sai dai ji yayi allurar ta lankwashe shi kuma hannunsa tamkar an damƙa masa garwashin wuta.
Ba shiri ya sake ta tare da furta "Oh! " Tush! Kake ji, tarwatsewar kwan Nepa.
"Ku kira Mani Malam. Dama ban yarda da yaron nan ba wannan abubuwan da ya ke yi canza miki shi aka yi amma wannan ba ainahin ɗanki ba ne."
Dada ta karasa maganar a hautsine.
Kamar an jefo shi haka ya wuntsilo daga saman kujerar. Kai tsaye dakinshi ya nufa tare da maido Kyaure ya rufe.
Likita kuwa bai bata lokaci ba ya haɗa kayansa ya bar gidan.
"Zinatu canza miki ɗa aka yi. Wannan ba ainahin abin da kika haifa ba ne, ni yanzu babbar damuwata dare yayi a cikin gidan nan yau nasan kowa ba zai rintsa ba. Duk yadda aka yi Mahaifin Asiim ba mutum ba ne, Zinatu aljani ki ka aura"
"Hajiya na roke ki ki daina fadar haka. Wallahi Alhaji mutum ne kaddarar Asiim ce ta zo a haka"
"Ba za ki taba yarda ba, ni kuma bazan daina fada ba. Kinsan danginshi ne yanzu a tsareki ba zaki iya nuna ko da mutum daya ba ne a matsayin tsatsonsa."
"Hajiya! Ki yi shuru yanzu ba lokacin wannan maganar ba ne. Mu fuskanci matsalarmu"
Luba ta kama hannun Yayar Tata suka nufi dakin Asiim. Sai dai ganinshi suka yi a rufe
Asiim da ke kwance saman gado ya rufe ilahirin jikinsa ya na karkarwa. Da kyar ya zaro hannunshi da ke masa azababben zafi.
Dafe tambarin da ke a wuyanshi yayi idanunsa na rikidewa.
Fadowa yayi daga saman gadon ya na birgima a ƙasa.
Dada kuwa jin shuru ya yi yawa biyo bayan su Momy ta yi.
Gabanta na dukan uku-uku. Mutuwar tsaye tayi tare da kurma ihun da saka su Momy shekowa a guje.
"Macijin wallahi Maciji."
Duk yadda suka so ta dawo cikin hayyacinta abin ya ci tura domin ihu ta ke.
Da kyar suka samu ta nutsu. "Ku mayar da ni gidan Hadi ba zan zauna a nan a kasheni a banza ba, yau ni na ga tashin hankali ganin idona"
"Dada don Allah kiyi mana bayani"
Momy ta fada tare da riko hannunta.
"Wane bayani ya rage maku bayan ku bude dakin can ku ga Asiim ya koma Maciji. Da idona na ga katon Maciji ya fita ta tagar dakinshi"
"Maciji kuma" suka fada a tare.
"Ba fa zan kara kwana a gidan nan ba dole ku mayar da ni gidan Hadi"
Ganin a rikice ta ke ya saka su amincewa za su mayar da ita amma ta bari su buda dakin Asiim.
Da dai ta ga da gaske dakin zasu bude da rarrafe ta bar wurin don ba zata tsaya a bude abinda ta gani ba.
Key din dakin suka dauko sai dai duk yadda suka so ya bude abu ya ci tura. Ga wani irin nishi da suke ji ya na fita a dakin.
Bisimillah ta yi tare da danna key din. Cikin ikon Allah sai ga kofa ta bude
Ƙarar ruwan da ta ji a bayi (toilet) ne ya saka suka zauna a gefen gado.
Tamkar ba shi bane wanda ya gama gumurzu ya fito tsaf abinshi. Mamakin da ya Kamasu bai ɓoyu ba.
"Momy! " Ta tsinkayo muryarshi.
Ruwan da ta zubo a cup ta ke kokarin miko mai
“Waye Husaini?" Cup din dake hannunta ta saki yayi ƙasa ya tarwatse hatta Luba da ke zaune a gefen gadon a gigice ta mike jin abin da Asiim ya faɗa.
Dada kuwa a gigice ta dauke shi da tagwayen maruka tare da shaƙar wuyarshi.
"Sai ka fada mana inda kasan wannan sunan, yau sai na tabbatar ma kowa abin da na jima ina zargi a kanka" Rufe bakinta ya yi daidai da tarwatsewar kwan Nepa lokaci daya iska me karfi ya datse kofar ɗakin. Hudu ne ya yi ma ɗakin ƙawanya ko tafin hannunka ba ka iya gani...
...Tagwaye! Baushe ya furta da ƙarfi tare da yin zaman 'yan bori cikin ƙasa.
Lawisa Mahaifiyar Samu kuwa ƙanƙame ɗiyarta ta yi tare da rushewa da kuka.
"Tarihi zai maimaita kanshi. Na rokeka ka kashe ni tun kafin musibun da suka rage su cimmana."
Tsawar da Baushe ya daka mata ce ta sakata hadiye sauran maganganun jikinta na kyarma.
Fizgo Samu yayi da karfi tare da shaƙa mata garin magani. Lokaci daya idanunta suka kakkafe numfashinta ya tsaya cak!
"Me kayi mata haka? Kasheta kayi."
"Ban kashe ta ba. Amma tabbas ke kwananki ya zo karshe"
Tamkar rugugin aradu haka maganar ta daki kunnuwan Lawisa.
"Tun ba yau ba nasan zan mutu. Amma ko bayan mutuwata ƙullalliyar da ka jima da ƙullewa ka binne ita zata zama ajalinka. Ka ga wannan" ta nuna ma shi Samu da ke ya she cikin ƙasa.
"Ita ce ajalinka, ta zo duniya ne domin daukar fansa ka jira lokaci domin tarihi baya karya. Don mahaifinta ya mutu ba ya na nufin zata wulakanta ba"
Dariyar mugunta Baushe ya kyalkyale da ita.
"Ke sirikata ce sannan har gobe ke yarinya ce. Shin kin manta Samu jikata ce? Duk yadda zanyi sai na yi domin mallake Samu."
Ya karasa maganar tare da ficewa da Samu.
Har gari ya waye Samu na cikin bukkar Baushe ba tare da sanin abinda ke faruwa ba.
Bayan an kauda gawawwakin da wani magani Baushe ya rabawa kowa ya hayaka, in dai Macijin ya ji hayaki zai daskare a wurin har su kama shi.
Cikin daren Samu ta farka ta na neman abinci. Murmushi Baushe ya saki tare da miƙa mata abincin da ya haɗe da magani.
Gama cin abincin ke da wuya ta ji wani irin yanayi ya sauko mata jiri ta fara ji ya na fizgarta.
"Duk abin da na saka kiyi za ki aikata" Baushe ya fada cikin kakkaurar murya.
"Fada taka cikawa tawa" ta fada cikin galabaitacciyar murya.
Miƙewa ya yi tare da mata nuni a kan ta biyo shi. Cikin daren ba tare da sanin kowa ba ya bata suka kara nausawa cikin jeji.
Wata ƙatuwar bishiyar kuka ce ta tsage gida biyu suka shige. Kogon ne mai fadi gani da girma.
Wani Dattijo ne da ya tsufa tukuf zaune bisa fatar damusa idanunshi a rufe.
"Baushe dan kunama, ka ga wanda ba a ganinshi sai ta ɓaci wace bukatar ce ta kawo ka" zubewa yayi saman guiwarshi
Karewa Samu kallo yayi tare da fara magana.
"Matsala ta Farko data kawoka magana ce game da Macijin da ke yiwa al'ummarka dauki daidai. Ka sani duk wani sidda baru ko magani ba zai yi aiki ba, abu daya ne zai iya kawo karshen Macijin nan wato wannan Jikar taka."
A rikice Baushe ya kalli tsohon zuciyarshi a birkice. "Kana mamaki ko? Shin ka manta burinka na son zama boka wanda zai mallake wannan duniyar Samu ita ce wadda zata iya kawo maka Macijin har cikin wannan jejin. Sannan ka sani haduwar Samu da Macijin nan tamkar haduwar Ruwa da wuta ne dole daya zai kashe daya. Muddun ka bari aka ɗauki lokaci baka mallaki su duka biyun ba duk wani sirri daka boye zai bayyana kaf abubuwan da ka boye zasu bayyana. Ka yi maza ka koma gida tun kafin abin da na ke hangowa a cikin daren nan ya cimmaka.
A firgice Baushe ya dauki hanyar gida sai dai kash! Da ya san me zai hadu da shi da bai fito cikin wannan daren ba.
Suna gaf da karasawa ya ji layar da ke wuyanshi ta yi motsi. Sandar da ke a hannunshi ya bugawa Samu ita a take ta koma Mujiya ta yi sama.
"Ki bayyana tun kafin raina ya soma ɓaci"
Kyalkyacewa ta yi da dariya tare da bayyana a cikin mummunar suffarta mai matukar tsoratarwa.
"Baki me bakar aniyar, a tunaninka kai daya ne zaka mallaki duniyar nan? Na dawo ne domin Mallakar Mujiya da kuma Maciji." Rubabbiyar tsohuwar ta fada ciki hautsinanniyar murya.
"Gaban rijiya ba wurin wasan yaro bane sannan ko kura ta rame tafi ƙarfin karnuka su kawo mata raini, kiyi gaggawar komawa duniyar matattu kafin in yi miki mummunan hukunci. Domin tun lokacin Rayuwarki baki iya tsinana komai a kaina ba bare kuma yanzu."
Tuntsirewa ta yi da dariya " A yanzu haka nasan tarihin Maciji kai karshema har ahalinsa na sani. Tabbas na hango maka gobara a kogi wanda Gaf take da yin ambaliya ta cinyeka"
A fusace Baushe ya yi kanta da mugun nufi. Sai dai kafin ya aikata haka tsohuwa ta watsa mai wani ruwa a fuska. Sulalewa yayi a karasa shafar fuskarshi tayi sak ta koma suffar Baushe. Tare da kyalkyacewa da dariya ta nufi cikin garin....