7&8
J I K A R B A U S H E
©️®️ MEENAT A. YANDOMA
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
HARAMUN NE SARRAFAMIN LABARI TA KO WACE SIGA BA TARE DA IZININA BA. 'YAN YOUTUBE MA HAKA
*GARABASA =* GARABASA =
Ina yan sari da masu siyen dai-dai ga dama gareku
MUNADA PAD SOFTCARE MAI MATUQAR KYAU DA BIYAN BUQATA LONG CE SANNAN GUM DINTA MAI MATUQAR DANQO
KAN FARASHIN SARI 50 PIECES #2500
100 PIECES #5K
PADS DINMU SABBINE FIL EXPIRE 2028
LOCATION KATSINA TITIN QOFAR GUGA
CALL OR CHAT ***
🅿️ 7&8
...Kai tsaye Bukkar Baushe ta nufa sai dai iskan da ya watsata gefe ne ya sakata saurin mikewa ta na gyara shiri.
"Ya asirce wurin, in dai har ba a cire wannan layar ba tabbas ba zan iya shiga cikin gidan ba"
Tsaye tsohuwa ta yi tana tunanin mafita domin muddun ta bari gari ya waye Baushe ya farka to fa kashinta ya bushe.
Sunan Samu ta kira. Da sauri ta fito tare da rusunawa gabanshi.
"Kaf layoyin da ke jikin Bukkar can a tabbatar an ciresu" rufe bakinta ke da wuya samu ta aiwatar da haka.
Dariyar mugunta ta yi tare da shigewa cikin. Ba karamin mamaki tasha ba domin ko mai na Bukkar Baushe ya tsarefe su.
Ya zamar mata dole ko me zata yi ta yi shi kafin gari ya karasa waye wa. Kai tsaye dakin Mahaifiyar Samu ta dosa babu bata lokaci ta watsa mata wani magani a fuska.
Tamkar yadda gunki ke daskarewa haka gangar jikinta ta daskare. Ihu Samu ke son yi amma ina ji ta yi tamkar an wani abu an dade mata baki.
Kecewa da dariya Baushe yayi. "Kina Mamakin abin da na aikawa Mahaifiyarki ko? To ki daina mamaki domin zata dawwama a wannan halin har zuwa karshen rayuwarta. Ke ce kadai kike da halin fitar da ita in kinso."
Tsana da kiyayyar Baushe CE ta mamaye zuciyar Samu. "Kai Kaka na ne tun tashina kai nake kallo a matsayin gatana, ji nake tamkar mafarki na ke a ko wane lokaci zan iya farkawa. Rayuwar Mahaifiyata a gaba ta ke da komai ka fadamin koma meye zan aikata ko da zai zama ajalina"
Dariyar ƙeta tsohuwar ta kuma ke ce wa da ita a karo na barkatai.
"Kin gane Macijin da ke shigowa cikin garin nan? Shi nake da bukata a ko wane hali. Za ki bar nahiyar nan tare da shiga duniya nemansa"
Shuru Samu ta yi. Lokaci daya Mugayen mafarkan da ta jima ta na yi suka dawo mata daya bayan daya.
Maganar Baushe ce ta katse mata tunanin.
"Ki tabbatar kin dawo min da shi domin ce ton rayuwar mahaifiyarki"
"Zan dawo da shi duk rintsi. Kai ko don in GA bayanka ya zame min wajibi in dawo s tare da Shi. Ni ce nan wadda zata zama ajalinka ka rubuta ka aje"
Wata yar karamar laya ya sake mata a cikin gashin kai tare da dafe goshinta ya karanta wasu ɗalasimai.
Jajur idanuwanta suka yi tamkar zasu fitar da wuta. A cikin ficewar hayyaci ta fita ba tare da sanin in da kafarta ke sauka ba.
"Baushe na Kunno maka wutar da ita ce zata mana ajalinka. Ka rasa soyayyar Samu har abada ko da ta dawo ina da tabbacin ita zata zama ajalinka." Ta na karasa maganar ta bace.
Sanyin safiya shi ya yi sanadin farkarwar Baushe ya mike a kidime ya na jin kanshi na rasawa. Tunawa da yayi da tsohuwa a kidime ya yi hanyar gida ya na fatan abinda ya ke tunani bai faru ba.
Samu kuwa tun bayan baro gidan tafiya take ba tare da sanin in da ta ke saka kafa ba. Ta yi nisa da jejin da suke rayuwa sosai ta yadda in ta na cikin hayyacinta ba zata iya tafiyar da ƙafafunta ba...
...Ganin ba su bata iya ganin ko tafin hanunta nan hankalinta ya kara tashi. Kiran Sunan Momy ta ke ko ta na kusa da ita amma shuru kake ji.
Momy kuwa addu'a ce a bakinta ta na ta nanatawa, a hankali duhun ya fara ragewa kofar dakin ce ta fara bude kanta.
Dada da ke riƙe da kwalar Asiim sauri sakinshi tayi jikinta na gyarma. "Sai na fada miki in da nasan sunan nan kike tambaya" suka tsokayo Muryar da ta sha bamban data Asiim na fada.
Ganin ya yi kan Dada gadan gadan da sauri Momy ta sha gabanshi
"Anya kana cikin hayyacinka kuwa, Dada fa ce"
Ganin idanunshi sun rufe fizgoshi ta yi tare da tsinkeshi da mari.
Kallon da ya yima Momy ne ya saka hantar cikinta kadawa. Gefen gadon ya zauna tare da sauke ajiyar zuciya.
Luba kuwa ganin tashin hankalin yau ya zarta na kullum fashewa ta yi da kuka.
"Zinatu yaron nan ba ko ba Aljani ba ne ya zame miki dole a yau ba sai gobe ba mu dinguma mu nufi kauye wurin Hadi"
"Dada na yarda. Amma ina hadaki da girman Allah ki daina kiran Asiim da Aljani, ki duba ki ga abin da ya faru yau. Ni nasan ba zai rasa Jinnu ba "
"Zinatu idanunki sun rufe, kin manta lokacin da za ki auri Ubanshi wace irin fama ce banyi da ke ba ko da ya ke bakin alkalami ya jima da bushewa. Abin da ya ji ma da faruwa yau shi ne ya ke fada sunan da duk in na ji shi sai hantar cikina sai ta kada, sunan da tun kafin ya zo duniya muka yi rami muka binne shin Zeenatu ki fadamin a wurin wa Asiim ya ji wannan sunan?"
Kasa magana Momy ta yi face kukan da ya ci karfinta ta fi ce a dakin da gudu.
Ta ke mata baya suka yi.
Asiim kuwa abubuwan da ya aikata ne suka fara dawo mai daki daki. Kanshi da ke barazanar tarwatsewa ya dafe. Bai jima da kwanci ba bacci ya yi awon gaba da shi.
Tsintar kanshi ya yi a duniyar da ya saba zuwa, sai dai a wannan lokacin tafi muni fiye da ko wane lokaci. Wata jingegiyar Mujiya ya ce ta rika kawo mai hari ya na kokarin guduwa, sai dai kafin ya Ankara Mujiyar ta saka bakinta ta shure shi sunyi sama.
A gigice ya farka daga wannan mummunan mafarkin da ya aure shi. Wanka ya yi tare da haɗa duk wasu abubuwa da ya ke bukata Cikin akwati domin ya san tafiyar ba fashi. Bai jima da gama hada su ba Aunty Luba ta shigo kiranshi.
Kasancewar tun bayan kammala karatun shi kasuwanci ya saka a gaba yaron shago ya kira ya sanar da su zai yi tafiya.
Tunda suka fara tafiya shuru ce ta gifta cikin motar kowa da abin da ya ke saƙawa. Karatun Alkur'ani Momy ta umurta ya kunna sai dai duk yadda ya so kunnawa abin ya ci tura speaker din kawowa ta ke tana daukewa dole suka hakura aka kashe.
Suna Gaf da shiga garin Asiim yana yin da bai taba tsintar kanshi ba ya soma faruwa da shi. Ilahin jikinshi zafi ya fara dauka kanshi ne ya fara matsanancin ciwo lokaci daya wani duhu ya mamaye idanuwashi.
"Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun!" Ita ce ka kalmar da Momy ke ta faman nanatawa tun bayan kwacewar motar a hannun shi.
Wani abu suka daka da karfin tsiya ji kake ƙiiiiiiiii.
A rikice suka fito daga motar tare da yin tozali da matashiyar budurwar da ke kwance rai hannun Allah ta baka da hanci jini ne ke ambaliya.
"Mun shiga uku! Asiim wa ka kashe? Kamar fa bata numfashi" Momy da Luba rige-rigen karasawa wurin budurwar da ke ya she Saman kwalta suka yi.
Kokarin dagota da suke sautin tsuntsaye suka jiyo ya na tunkaro inda suke.
Tsabar firgici Momy mutuwar tsaye ta yi domin tun zuwa ta duniya har kawo yanzu bata taba ganin kalar tsuntsayen ba.
Asiim kuwa harshe ya fara fiddowa ya na kokarin rikiɗa domin a tsakanin shi da tsuntsu yaƙi ne...