ROYAL POLITICS 2

Matawalle

by @maidambu41

ROYAL POLITICS 🔥
_An yanka ta tashi_
    Ramlat A Manga
       Mai_Dambu
TOP-NOTCH SEASON 4
  Sadaukarwa ga Auntyna RUKAYYA GOMBE 🥰 🤩 😍

Follow this link to join my WhatsApp group: ***

Hajiata indai kinsan kina Neman jaka da takalmi na fita kunya na alfarma na shiga taro na zuwa villa,to gaskiya kawata karki wuce group dinnan domin kuwa akwai luxury bag's unique shoe's jewelries iya ganinki,hmm baa cewa komai dai ki shiga idonki ya gane Miki yar uwa

11
Dole ya fito daga asibiti bai da yadda ya iya da Nady, Faruq na ganinshi ya mike suka nufin wurin motarshi, ya bude mishi ya shiga sannan ya suka bar asibitin.
---
Ita Nady koda Faruq ya ajiye ta a gida, zirga-zirga take kamar zata yi hauka ita da tasan yarinyar da ta mara ba ita ba d tayi mata rashin mutunci ba, ai da bata fara marinta ba, kallon kyakkyawar fuskarta tayi tana ji kamar zata mutu.  Shigowa yayi ta juya tana kallonshi idanunta yayi jajjur, "Prince!" D'aga mata hannu yayi yana me wucewa ta, bin bayansa tayi sai ta juya tana kallon Faruq. "Munafuki mai ka gaya mishi? Gaya min me ka gaya mishi? Zaka gaya min ko sai na saka an b'atar min da ka...!"
         A fusace ya tawo ya riko hannunta suka wuce cikin parlourn ya turata. Idanunsa yayi jajjur kamar zai fado kasa ya ce mata. "Ki kiyaye ni wallahi!" Ya nuna mata yatsa,yadda yayi maganar idanunshi a warwaje yasa ta ja da baya saboda ba matukar tsoro ya bata ba, rufe bakinta tayi ta fashe da wani irin kuka, tana kallonshi da idanunta masu zubin na mage.  "You hate me?" Ta tambaye shi tana wani irin sheshakar kuka, zubewa tai a wurin tana wani irin kuka ita kaɗai tasan yadda take ji yadda ya daka mata tsawa. Wucewa yayi ya barta a parlourn ta cigaba da wani irin kuka.
***
His Excellency.
Musharraf.
       Kallon Jagaba yayi kafin ya mai da hankalinshi kan Goga da yake zaune ya hade hannunsa dukka biyu. "Nace wannan rikicin ya kare anan!" D'ago kai Goga yayi yana kallon Mai Girma Gwamna. "Taya zai kare anan kashe min dan uwa yayi fa?" "Amma ai kai ma ka kashe mishi dan uwa dai ko? Dukkanku akan daukar fansa suke kashe kanku baku da buri ne? Baku da gobe ne? Ina bukatarku ko don amfanin zaben gobe."  Juya kai Jagaba yayi ya ce . "Ai ni na yafe mishi, yanzu ma abinda ya faru bana ce daga daba ta ce domin abin bai bada ma'ana ba, duk Yaran dabana na kori kowa ni daya nake rayuwa." Dukar table din Goga yayi ya ce mishi. "Na rantse da Sarkin da yake busa numfashi, bai kare ba zan farauci Yaron dare da rana, zan tabbatar na kawo shi har nan, Yara biyu ka kashe min sannan ka nuna ba kome."  "Wai kai Goga Jagaba ba shugabanka bane? Ba shi ya kawo ka cikin wannan harkan ba?" Dariyar renin hankali ya musu kafin ya ce mishi. "Ya kawo ni? Hmm kai ma kayi hankali kada ka yi renon dan kishiya!" Ya saka kai zai fita Musharraf ya ce mishi. "Dakata kada ka sake ka fita!" "Akan me ba zan fita ba? Kasan ko rufe ni ka saka ayi za a fitar da ni kafin faduwar rana, don haka zan fita amma ya sani yayi ta gudu sannan kada yayi sake ranshi yayi barci domin kuwa barci bana shi bane, ina gaya maka kowa ya hadiye tabarya lallai zai yi kwanan tsaye!"
"Kai Goga dakata a wurin!" Juyawa yayi ya kalli Mai girma Gwamna ya ce mishi. "Ba naki jin maganarka bane amma matukar ina tare da wannan mutumin a wuri guda zan aikata kome, don haka ka kyale ni na tafi." Ya fada yana me barin parlourn domin guest house dinsa ya gayyace su.

           A lokacin da ya fito sai da idanunsa suka cika da kwalla, ya kashe burin Jigal ya janyo shi cikin kazamar rayuwa.  Wayarshi ce tayi ƙara ya saka hannu ya Ciro ya manna a kunne. "Ina hanya!" Ya fada sannan ya kashe wayar kafin ya wuce wurin machine dinsa ya bugata kafin ya bar gidan.  Wurin can solo town ya nufa duk da baya cikin nutsuwa yana isa masu kula da gate din suka bude mishi kofa ya shiga yana kallon kowa.  Can wuri Ahmad Rilwani Yayari ya nufa ya zauna. "Ina jajjanta maka rashin da ka yi." Murmushin gefen baki yayi ya cigaba da kallon yan mata da suke yawo kusan tsirara. "An shigo da kaya, kuma kai nake so ka tsaya akan kayan." "Nawa kasona?" Kallonshi Ahmad yayi ya ce mishi. "Daidai da nauyin kayan." Mikewa yayi zai tafi ya ce mishi. "Me yasa baka son mata?" "Mace da kudi da maciji hatsarinsu yafi na sauran halittun, bar ni da Mandelata!". Ya fada yana barin wurin, sako ne ya shigo mishi yana gani ya juya tare da sara mishi.
***
Zanzabira prison
   Zaune yake a gaban mutumin kamar ya kwanta mishi, don biyayya cikin sanyin murya da lallashi ya ce mishi. "Saura kaɗan ka bar nan gidan, na saka an shirya kome ka kara hakuri." Tunda yake magana bai ce uffan ba, sai da yayi nisa kafin ya ce mishi. "Babban burina naji an saka kukan mutuwar Attahiru Shehu Yayari, kana haka ka biya ni."
"Nayi maka alƙawarin haka! In sha Allah zan gaya maka Zanzabira zata zamo namu."
***
Ikhlas
   Tunda muka dawo saloon na samu Maluma ta gyara min kayana, ganin yadda kaina yake rawa ita kanta bata san me yasa nake zumudin zuwa ba, cikin damuwa wanda nake iya hango shi a cikin idanunta ta ce min. "Zainab!" A duk lokacin da ta min irin wannan kiran don bata cika kiran sunana ba sai babban dalili. "Na'am Maluma!" Na amsa ina kai lomar shinkafa da waken da tayi. "Ki ji tsoron Allah, kada samun damar baki ganin mu yasa ki aikata abinda ranki yake so, yana yana ganinki idan ke baki ganinshi. Na baki shawara ki rike azkar domin shine makamin Muminin, Zainab ni dai babu yadda na iya ne amma da ba zaki bi Turai ba, domin kuwa matar da bata so ki tuntuni ba, har abada ba zata tab'a sonki ba. Amma ki cigaba da addu'a. Allah yana tare da masu addu'a da imani da shi." Nasiha da Malama take min sai nake ganin kamar ko bata son naje ne, domin abin ya min yawa wallahi kawai don zan bisu zuwa Dubai sai ta min takara.

--- Haka Ya Abid da Ya Yunus suka zo suka ta min fada da kwakwazo haka Ya Nawwas da yaji xan tafi sai da ya kirani tayi ya min mita wai na kama kaina. Ban san me yasa suke ganin laifin Mommy Turai ba, kwana biyu kafin Tafiyar Abba da kanshi ya dauke ni muka fita unguwa, fada muka je gidan Alhaji Mamman Abba yayari, lokacin da muka je na gaishe shi cikin nutsuwa ya kalle ni cikin fara'a ya ce min. "Zainab ko?" Gyada kai nayi, "Allah ya miki Albarka." Daga haka ya juya kan Abba ya ce mishi. "Bai zama dole kiwon ya zama daidai ba, amma ni a lissafina akwai shirin da zai iya kai da wani abu, wata sati naji labarin dawowa damina!"  Shiru Abba yayi kafin ya ce mishi. "Idan har an samu mammakon ruwa tow ba mamaki shukar tayi kyau domin ita irin da za a zuba bai zama dole ya wadata ba."

     Dariya irin na manya Alhaji Mamman Abba yayari ya ce mishi. "Ba sai lallai wancan irin ba." Amma maganar gaskiya tun fil azal wancan irin muka tsaya a kai idan kuma aka samu akasi dole mu yi amfani da yan sati bakwai." "Kana tsammanin sai ya zama dole ne za ayi amfani da wancan din?" "Kwarai da gaske."

"Shi kenan Allah yasa mu dace, Y'ata ga wannan." Ya mika min kyauta, girgiza kai nayi Abba ya ce min. "Amsa!" "Allah ya saka da alkhairi."
"Ka mata miji ne?" "Tukuna dai ka ganta nan niman maganarta yayi yawa."
"Allah ya mata albarka, Yaran yanzu baka iya masu da na nimawa Matawalle ita domin rayuwarsa ta gyaru!" "Ikon Allah waye Matawalle?" Murmushi yayi ya ce mishi. "Ba zaka gane ba amma lokaci zai nuna ganar damu." Shiru nayi kaina a kasa wani Matawalle aka samu kowa ye ba zan aure shi ba."
   Sun gama maganarsu sannan muka bar gidan,a hanya Abba yake ce min. "Kina da wanda kike so ne ko babu?" Kaina a kasa nace mishi. "Dama Uwais ne kuma ka ce na daina kula shi." Shiru yayi yana cigaba da tukinsa. "Babu kenan." "Eh shi kenan !" Muna isa gida ya kira Alhaji Mamman Abba yayari ya ce mishi. "Ka shirya idan suka dawo sai ayi bikin!"
"Masha Allah gaskiya na gode, zaka same mu masu rikon amana."

Top_notch season 4 ROYAL POLITICS is not free, pay N500 to get a complete access to the book.

Marubutan TopNotch Writers sun sake zuwa muku da sabon labarai masu ƙayatarwa a tafiyarsu ta Season Four:

MAI_DAMBU kuwa ta faso muku ne da labarin da ya haɗa da Sarauta, Siyasa da kuma Soyayya, duka a littafin ROYAL POLITICS: An yanka ta tashi.

AZIZAT kuma ta tattaro muku rikitacciyar soyayya ne da ya hawo jirgin JayKay ya dira a Kitchen ɗin Ziyada. CHEF ZEEY: Love in the Kitchen

Account Details:
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*

POSTING
*Ɗaya: 500*
*Biyu: 1000*
*Uku: 1500*

DOCUMENT (da zaran an gama posting zai koma)
*Ɗaya: 1k*
*Biyu: 2k*
*Uku: 3k*

domin tura shaidar biya ko Ƙarin bayani, ku tuntuɓi:
*****
Ko
*****
Ko kuma
*****