ƊAYA CIKIN BIYU

ƊAYA CIKIN BIYU

by @mrsisham12

7--8⚔️👑👑 ƊAYA CIKIN BIYU 👑👑⚔️

🔥A story of love,hatred and violence ⚔️🔥

🤍*Story and written*🤍

~By~

Aisha Abbas (*MRS 🌹 ISHAM 🌹*)

(*Yar lelen jarumai writers*).

Jarumai writers association 📚📚📚🖋️🤩

❤️🔥Page 7____8

Galadima Abdul Aleem ne haɗe da waziri Abdul Qadeer,se kuma wa'yanda suka kasance manyan faɗa zaune a fada suna magana, Sheikh Abu Dhabi da be jima da shigowa ba ne ya yi murmushi bayan ya ji duk jawabin da galadima Abdul Aleem ya yi.

" Ya kai Abdul Aleem yau sati biyu kenan da mutuwar sarki Taifur Rahman,kuma a wannan lokacin ne ya kamata a karanta sakon da ya barwa ya'yan sa,domin mu ji menene zamuyi saboda tantance Shugabar mu a cikin su,kar ka manta kana matsayin ubane a wajen su, tsoro ko kuma fargaba, babu bukatar ya samu gurbi a cikin zuciyarka, ka sani a bari ya huce shi ke kawo rabon wani ".

Cikin sanyi jiki galadima Abdul Aleem ya zauna akan kujerar sa,yana me riƙe habarsa domin shi gani yake abubuwan da zasu biyo baya babu wanda ze kauna ci hakan.

" Babu tsoro a raina se de akwai fargaba, wallahi ɗaukan mulki a bawa mutum daya a hana daya shine babban tashin hankali da kuma barazana da zamu fuskanta . idan kuma muka bawa daya wacce ba ita bace asalin shugabar to tabbas mun siyawa kan mu masifa ne haɗe da jalala ".

" Babu wani jalala da ku ka siyawa kan ku,har se bakuyi abinda ya dace a lokacin da ya dace ba. nan ne za ku san kun tafka babban kuskure wanda, samuwar mafita ze matukar tsanani a gare mu baki ɗaya ".Muryar wannan tsoho ya dira musu a cikin dodunan kunnuwan su kamar a mafarki

Duk juyawa suka yi domin kallon ta inda maganar ya fito. a gefe da su suka hango mai girma Sheikhy yana sanye da fararen kaya har suna ɗaukan ido,komai na jikinsa fari ne kama daga sumar kansa kasumban sa,gashin ido,gashin gira da komai fari ne tas haka zalika sandar hannun sa.

Cikin girmamawa duk suka miƙe domin basu tsamci ziyartar sa a wannan rana ba,amma dake ze iya zuwa a ko wani lokaci da ko wani rana, se hakan be basu mamaki ba,domin shi me tafiya ne akan iska,se de ku gansa kawai a cikin ku.

Yana dogara sandar sa me ɗauke da wani irin abu kamar kwalba a saman sandar yana fito da wuta kaɗan-kaɗan .ya soma takowa zuwa cikin su,se da ya samu guri a kusa da kujerar da na galadima yake ya zauna yana me daga musu hannu alamar su zauna,zama duk suka yi kafin ya soma ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya.

Sheikh Abu Dhabi ne ya furta " ya shugabana ba mu yi tsammanin zaka kawo mana ziyara a wannan lokaci ba ".

Yar dariya yay kafin ya ce " bana buƙatar izini domin shigowa masarautar Bayaan,domin yau shekaru sama da dari da saba'in ban taɓa tambayar izinin ko wani mahaluki domin shigowa masarautar da ta kasance ni ne nake bata kariya ba ".

" Wannan haka yake ya kai mai girma Sheikhy,shin akwai wani haske ne da zaka ƙara mana dangane da babban al amarin da muke ciki!? ".

Waziri Abdul Qadeer ya tambaya cikin girmamawa.domin kuwa babu wanda ya isa ya yiwa mai girma Sheikhy magana cikin gadara ko kuma gatsali domin shi ba ko wani irin gama garin mutane bane ya kasance farin rauhanin aljani da ya yi sama da shekara ɗari biyu a doron duniya, sannan kuma shi ne ya kasance yana bawa masarautar Bayaan kariya,sannan shine wanda ya bada umarnin da a mayar da Muzna da Muzaina zuwa wata ƙasa daban.

" Abdul Aleem,kar ka bari abubuwan da kake mafarkin su,su yi galaba akan ka,ko Masarautar Bayaan ya samu adalin shugaba ko akasin haka to tabbas zata shiga cikin gagarumin mawuyacin halin da ko wani ɗan adam din dake cikin masarautar se ya roki mutuwa da bakinsa, hakan yana cikin ƙaddarar wannan masarauta . se de abinda nasani shine me bawa wannan masarautar kariya an haifeta kuma ta shigo duk halin gwagwarmayar da za'a shiga ita ce nan zata gyara komai zata mayar da komai iya zuwa mazaunin sa ".

" Amma in hakan be faru ba fa ya Sheikhy!?". Wani daga cikin amintaccen bafade ya yi wannan tambayar cikin tsoro.

Kallon sa Sheikhy ya yi na wasu yan lokuta kana ya ce

" Kowa ze mutu,kasar Kuwait gaba daya zata koma kamar babban filin da ba'a taɓa halittar wasu yan adam ba,zata bushe, bishiyoyi zasu bushe su sandare

,haka zalika ganyaye da ciyayi zasu bushe su dinga tsinkewa da kansu daga zaran iska ya kada domin rashin samun ruwa,a yayinda ruwan kuwa ze ƙame kamas tamkar ba'a taɓa samun ko da digar ruwa a wannan nahiyar ba,tsananin yunwa da zafin rana ne ze sa dabbobin da suka yi ragowa su dinga fadowa ƙasa a mace babu rai a jikinsu, aljanu masu ƙanana hali zasu shiga masifa, bala'i muddin hakan ya kasance,bazasu samu inda zasu kebe ko kuma yin hidimomin rayuwar su na yau da kullum ba ".

Ya gama faɗa yana bin ko wannensu da kallo, shurun da cikin fada ya ɗauka kaɗai ya isa ya fayyace Irin tsoro da firgicin da ko wannensu ya shiga.

" Uhummmmmmmmmm" galadima Abdul Aleem ya sauke wani Gwauron numfashi kafin ya ce

" Shin ta ya'ya ne za mu gane wacece asalin shugabar mu a cikin su !?".

" Ta yin gwajin tantancewa,wanda ake yi tun zamanin kaka da kakanni,sede na wannan lokaci ze fi ko wanne tsauri da zafi.domin a gabaki daya tarihin Bayaan ba'a taɓa shiga tsaka me wuya wajen tantance shugaba ba se wannan lokaci.

Aby na biyu kuma shine, yin aiki da abinda sarki Taifur Rahman ya rubuta a wasikar sa da ya bari ".

" In sha Allah,shin yaushe ne za'a yi sadaukarwar!?".

Galadima Abdul Aleem ya yi tambayar.

Sheikh Abu Dhabi ya basa amsa

" Ranar da za'a naɗa sabuwar shugaba,daren da wata ze faɗa".

Yau ma kamar yadda ta saba ta gama duk wani shirin ta cikin wandon jeans se doguwar riga da tsayin sa ya wuce guiwa yanada faɗi,gashin kanta ta mayar da shi asalin natural din sa baki ne wuluk me tsantsi da sheki, fuskar ta babu wani yalwantaccen kwalliya.kafarta na sanye da takalmi flat shoe ta yi masifar kyau,komai dinta yana da kyau kamar wacce ta zauna ta zana kanta. Murmushi take yi haɗe da sauri domin ta gama,fita ne kawai ta rage mata dan zuwa ganin sa,tsayawa tayi tana kallon kan ta a mudubi tana murmushi.

Shigowa dakin Haseena ta yi ta gama ƙarewa kawarta ta kallo, ta ga yanda take ta sakin murmushi,ita yanda ta sauya ne abin ke bata mamaki domin yawanci da rana bazaka taɓa samun Muzna ba ka gama nemanta amma ba zaka sameta ba.

" Muzna why are you acting so strange nowadays!?".

Ta cikin mudubin ta kalle ta hallau tana murmushin ta ce

" Kamar ya bangane ba,acting strange like how!?". Itama ta mayar mata da tambaya. Karasowa gabanta ta yi,ta soma binta da kallo daga ƙasa har sama kana ta harɗe hannu a kirji,ta kuma furta

" Ehh mana gaba daya kin sauya,bana taɓa samun ki se dare lokacin kuma kinyi bacci,ina ki ke zuwa ne!?, yanzu haka na haɗu da Muzaina a falo tana neman ki".

Duk maganar da Haseena take mata ita de murmushi kawai take yi tana me ɗaukan turare tana fesawa jikinta, batare da ta kula ta ba.

Da mamaki Haseena take kallon Muzna ganin a maimakon ta bata amsa amma ta tsaya batacewa komai se murmushin da take sakar mata.

Cikin dogon nazari da kuma son gaskata abinda zuciyarta ke ayyana mata,da matuƙar al'ajabi ta ce

" Wait!,wait!, dakata, Muzna shin kin faɗa soyayya ne!?".

Dakatawa da fesa turaren da take yi ta yi,batare da ta kalleta ba ya ce

" Meyasa ki ka faɗi haka Haseena".

" Saboda wannan sauyawar ta ki yafi kama da wanda ya faɗa soyayya sabon shiga,ki duba yanda ki kayi light make up mara hayaniya ga kuma yanda ki ka yi dressing and abu mafi la'akari shine yanda ki ke ta wani sakin murmushi ba kaukautawa".

" Hhhhhhhhhh lallai Haseena,to ni babu wani soyayya da na faɗa kwantar da hankali".

Ta gama magana tana fesa mata turare.sannan ta damƙa mata kwalban ta nufi hanyar barin dakin tana ce mata

" Bari in dan zaga in dawo ".

Ko da Muzna ta fice a dakin murmushi itama Haseena ta yi a zuciyarta tace

" Tabbas kin faɗa soyayya ƙawata,ina fatan za ki samu farin ciki a rayuwar ki ".

Tsaye take a jikin bishiyar darbebejiya me girma,wanda ke kusa da filin daga,ta labe a bayan bishiyar tana leken yanda suke gabatar da motsa jiki. Yanda yake gabatar da komai cikin nutsuwa da jarumta hakan na matukar burgeta a yayinda take jin son sa na sake dankaruwa a birnin zuciyarta.

A karo na sau babu a dadi ta kuma leƙo kanta domin ta gansa,yana tsaye yana daga wani nannauyan karfe,juyowa yayi ta bangaren da take dasauri ta boye a jikin bishiyar tana sauke numfashi tare da godewa Allah da yasa be ganta ba,se da ta nutsu sosai wanda a ƙalla ta kai kusan minti biyar kafin a hankali ta kuma lekawa sede cikin rashin sa'a bata ganshi a filin dagan ba. iya wa'yanda suke tare ne ta ga ni amma babu shi, yanayin fuskarta ne ya sauya alamar rashin jin dadi.

" Shin ina ne kuma inda yaje shi " ta faɗi haka a zuciyarta.

Taɓa kafadar ta aka yi ta baya, juyowa tayi dan ganin waye, suman tsaye tayi lokacin da ta haɗa ido da wanda ke tsaye a gabanta.

" Wacece ke,kuma daga ina ki ke!?" Wannan sune abinda ta ji ya furta da muryar sa me dadin sauraro,satan kallon sa tayi taga yanda ya zuba mata ido hannun sa na zube cikin aljihun wandon sa.Jikinsa babu riga se lafiyayyar karfaffan jikinsa da yaci karfe,idonta ya sauka.

Sosa wuyanta tayi dan ji tayi wani irin kunya ya lullube ta,bata taɓa tunanin wannan ranan ze zo ba, ga shi yau ya kamata dumu-dumu tana lekensa.

" Bazakiyi magana ba?,ko de kurma ce ke?, ɓalle ma na san ke din ba kurma bace".

Ya faɗa yana kuma kafeta da idanunsa da suke da masifar haske.

Cikin inda-inda ta soma cewa " uhm_dama nazo wucewa ne na ganku kuna motsa jiki shine na tsaya ina kallon ku shi-shi-shi-kenan". Ta gama maganar gaba daya a daburce domin bakaramin gwarjini ya mata ba,jinta tayi kamar wacce a kace ta yi wani babban zunubi se ta ji kamar idanunsan suna nukurkusan sassan jikin ta.

Se da ya gama nazartan ta kafin ya ce

" Yau kwana goma sha uku kina zuwa nan wajen, lokacin da ki ka fi zuwa domin kin san kin fi ganina a irin wannan lokacin shine karfe ɗaya na rana,da kuma yammaci idan rana ya ɓace, shin kina da matsala da ni ne !?".

Cike da jin kunya ta ce " ka yi hakuri,nasan na aikata kuskure,ya kasance kana matuƙar burge ni ne yasa ko da yaushe nake kaɗaicewa a wannan karkashin bishiyar domin ganin ka".

Dariya ya yi wanda ya sake bayyana kyawun sa,sosai take kallon chocolate color face din sa yanda yake dariyar bakaramin tafiya da imaninta ya yi ba,a ranta ta furta

" Ya Salam,dama yana dariya haka, tabbas wannan bawa naka yanada tsananin kyawun da ya tafi da zuciyar Muzna Taifur Rahman".

" Shikenan nagode da burgeki da nake yi,ke din wacece domin ban taɓa kallon ki a wannan masarautar ba,sannan kuma abu na gaba ki rufa min asiri ki dena zuwa nan dan kar a ɗinga ganin ki saboda akwai banbanci sosai a tsakanin yar masu hannu da shuni da kuma ya'yan bayi".

" Sunana Muzna ".

" Ni kuma sunana Zubair amma an fi kirana da Sadauki Zubair".

Ya faɗa yana gyara tsayuwar sa.

" Ka cancanci sunan ".

Kawar da zancen nata ya yi ta hanyar faɗin " se de baki faɗa min ke din wacece ba,domin bana son wani abu ya biyo baya,ko da wasa bana son wani alaka ta haɗa ni da ya'yan manya".

" Saboda me yasa hakan!?". Ta tambaye sa cikin rashin jin dadi.

" Saboda a ko da yaushe kan su suka sani,ni kuma na tsani mutum me son kansa,na tsani mutum makaryaci da kuma mayaudari.bugu da ƙari ni din bawa ne, ɗan baiwa,ina iya kokarina wajen ganin na kare mutuncina".

Jikinta ne ya yi sanyi domin tasan muddin yasan ita din wacece tofa dole ze ja baya da ita,hakan yasa ta yanke hukuncin boye masa ko ita din wacece.

" Ni ba yar kowa bace hasalima ma ni baiwa ce a wannan masarauta ".

Cikin tuhuma yake kallon tufafin jikinta da yasan ko rigar da take sanye da shi ze iya ciyar dashi na tsawon shekaru uku saboda tsadar sa, fahimta da ta yi be yarda ba, saboda yanda ya ga tufafin jikinta hakan yasa ta yi saurin faɗin

" Ni na kasance me yiwa gimbiya hidima,shi yasa nake da kaya masu kyau domin tana yawan yi mini kyautar kayayyaki kuma tana da kirki ".

Hallau kallon tuhuma yake bin ta dashi kafin ya buɗe baki haɗe da fadin

" Wata gimbiya kenan!?".

" Gimbiya Muzaina,ita ce nakewa hidima " ta faɗa tana me addu'ar Allah yasa kar ya kuma cillo mata da wata tambayar domin ta lura yana da bin diddigi.

" Tom amma ya na ji sunan na ku na shigen kama da na juna !?".

Lokaci daya ta ji gabanta ya yanke ya tsinke,ta kuma shiga wani rudin domin yana daf da kure ramin karyar ta.

" Ehh,haka ne amma akwai banbanci".

A nutse ya furta " shikenan, Bismillah " ya faɗa yana me zama akan grass carpet din dake gindin bishiyar.

Zama ta yi itama tana sauke ajiyar zuciya a boye batare da ya gani ba.

" Amma shin ku yan ƙasar Kuwait ne "

Murmushi yay " eh kwarai ma kuwa,mu yan ƙasar Kuwait ne, saboda kin gan ni baki a gaban ki shisa ki ka min wannan tambayar ko!? " dariya suka yi a tare domin maganar tasa ya yi barkwanci.

" Ah ah ko kaɗan ba haka bane,na tambaye ka hakan ne saboda naga kaff cikin wannan masarautar ban taɓa ganin me kyawun ka ba kuma kalar fatar ka ya kuma sa ka kwanta min a rai sosai ".

" Hhhhhh Tom na gode " ya faɗa yana yar dariya.

Shuru suka yi babu wanda ya kuma magana a cikin su,.ganin shurun ya yi yawa ne yasa shi faɗin

" Amma a wani bangare na bayi ki ke,bangaren ƙananan bayi ko kuma,bangaren matsagaitan bayi!?,ko bangaren manyan bayi!?,domin ko kaɗan jikin ki be nuna alamar kina aiki sosai ko kuma kina bangaren ƙananun bayi ba".

Cikin gajiya da tambayoyin sa masu kiɗima ta,ta ce

" Manyan bayi ".

" Okay ayyah".

Tun daga nan suka kuma yin shuru babu me magana se satan kallon sa da take yi.

Kiran sallah aka soma yi a babban masallacin dake cikin masarautar hakan yasa cikin sauri ya miƙe haɗe da miƙa mata hannu ta kama ta miƙe itama.

Kallon ta yay sannan ya ce

" Tom ina me godiya Muzna,zan je sallah se wani lokaci kuma".

Yana gama magana ya tafi ya barta tsaye a gun har ya isa cikin filin daga tana kallon sa ya ɗauki goran ruwansa ya tafi. Murmushi tayi lokacin da taga ya ɓacewa ganinta sannan itama ta bar wajen.

Horn take dannawa da ƙarfi wanda a ƙalla yanzu ta kusan mintuna biyu a bakin masarautar tana matsa horn cikin ɓacin rai da hassala amma ba a zo an buɗe ba.

A fusace ta fito a motar da take ta jikin gate ta tura ƙaramar kofar nan ta tadda wasu da basu samu zuwa masallaci ba acikin bayin suna gabatar da sallah, tsayawa ta yi a wajen tana karkada kai domin ranta ya masifar hassala,da sauri bafaden da ya kasance shine me gadin ya miƙe bayan an sallame saboda suna sallah suna jiyo yanda ake matsa horn din.

Yana sussukuyar da kai ya nufo ta alamar bata hakuri,amma kafin ya kai ga buɗe bakinsa ta ɗauke sa da mahaukatan zafafan mari guda biyu hagu da dama. Dattijon mai gadin riƙe kuncinsa ya yi da hannunsa biyu yana zubar da kwalla,hatta su kansu sauran bayin dake wajen se da suka ji saukar marin kamar a kuncinsu,ganin yanda bata lura da girmansa ta dagargare ta dake sa.

Cikin takaici ta nuna sa da yatsa ta soma faɗin

" Har kai waye da zanzo ina horn ka ƙi buɗe min gate banza ƙaskantacen bawa wulakantacce".

Murya na rawa yana zubar da kwalla ya ce

" Kiyi min afuwa gimbiya sallah muke yi wannan ne yasa ban buɗe miki ba ki gafarceni ".

Wani irin wulakantaccen kallo take watsa matsa

" Dallah yi mun shuru,tsohon banza tsohon wofi daga rana irinta yau bazaka sa'ke maimaita dabbanci irin wannan ba ".

Key din motar dake hannun ta wurga masa a jiki ta ja doguwar tsaki ta sa kai ta bar su tsaye kai a ƙasa, ta shige ciki.

Seda suka tabbatar da ta ɓacewa ganin su kafin suka ɗago suna bin bayanta da kallo suna jinjina abinda ya faru.

Yarima Farasat dake tsaye a bayansu basu lura dashi ba duk ya ga kuma ya ji abinda ya faru, karasowa wajen ya yi ya bawa mai gadin da ta mara hakuri sannan ya bi bayanta.

A hanyar ta na shiga sashin ta ya cimma ta.ko da ta juyo taga shine hakan be sa ta tsaya ba ta shiga falonta.

" Muzaina meyasa za ki mari mutumin da ya kasance tsoho,ko bama tsoho ba ya dace ki yi haka!?".

Tana cire jacket din saman kayanta hankali kwance ta ce

" Saboda ya yi rashin biyayya a gare ni kuma dole ya karɓi hukunci".

Iska ya furzar a bakinsa " amma kin ga ai sallah su ke yi ko ba haka ba ?,a duk duniya akwai uzurin da yakai wannan gaida Ubangijin sa yake yi".

" Farasat " ta kira sunan sa.

Ba tare da ya amsa ta ba ya zuba mata manyan idanunsa.

" Shin kazo ne dan ka rama masa marin da na masa ko kuma kazo ne dan ka ci min mutunci!? Wanne daya ka zo yi !?".

Zama ya yi a kusa da ita, tabbas ya lura da Muzaina batada kirki ko kaɗan. ita duk girmanka zata iya maka duk abinda ta gadama,haka zalika bata da kara duk yanda ku ke da ita abu in ya haɗa ku se ta maka rashin mutunci.ya jima da observing nata, amma ya zeyi Allah ya ɗaura masa sonta babu yanda ze yi dole ya ɗinga nuna mata gaskiya.

Cikin dabara da lallami ya samo faɗin

" Babu ko ɗaya,amma abinda ki ka yi be dace ba,eh ya miki laifi be buɗe kofa da wuri ba,amma ki koyi yi wa mutane uzuri,ke kyakyawa kuma nutsatsatsiyar macece,be kamata a ce da girman ki a gan ki kina masifa ba,hakan ze zubar miki da mutunciki. sannan wannan kyakyawar farar hannun naki an yi sa ne domin wanke jikin ki da kuma yiwa hadaddiyar fuskar ki kwalliya, bawai kiyi duka dashi ba ya ke gimbiya ta,shi sa nake ce miki be dace ba,in Allah ya yi kece fa future queen din mu haba my love ".

Murmushi ta soma sakarwa tana shan kamshi cike da ji da kai da jin dadin yanda yarima Farasat ya dinga hura mata kai.

" Shikenan naji amma suma wa'yannan banzayen bayin suna da kayan haushi ".

" Zan faɗa musu su kiyaye,bana son in ga kina ɓata ran ki akan abinda be kai ya kawo ba ".

Murmushi kawai tayi,bata ce masa komai ba,hakan yasa ya miƙe haɗe da faɗin

" Ni zan wuce zan je in ga na da Ummu Xulaihah ".

Tafiya ya yi ya barta ita daya saboda bayin da aka basu ita ta hana masu yi mata hidima shigowa shashenta inde tana nan, a cewar ta kyama suke bata.

" Dazun da ki ka fita Mubeen ya kirawo wayanki domin sanar miki da hutun da aka ba ki ya ƙare,yakamata mu koma dan ki ci gaba da Film din da ku ka fara".

Tana baje zaune a kasan carpet din dakin,gashin kan ta da Haseena ta mayar mata dashi donot ta sa headband,jikinta kuma kayan bacci ne masu laushi, yanda ta kwabe fuska se ta koma kamar wata karamar yarinya. Ta ƙi cewa komai se sake turo baki da take yi domin Muzna duk inda ake neman asalin shagwababbiya ta ta wuce nan.

" Kin yi shuru ba ki ce komai ba ".

Murya a shagwabe ta ce " nayi matukar kewan Aba,da yana raye nasan da shi da kansa ze ce in koma amma yanzu ki ga Abbu Aleem ya ce bazamu ko ina ba ".

Zaro ido Haseena ta yi cike da mamaki " kamarya bazaku koma ba?".

" Haka ya faɗa wai saboda mun dawo gida kenan,dan Allah wannan magana ne!?,ni ina son in yi rayuwa ta cike da yanci,ina son in yi duk abinda nake so,banason dogara da kowa i want to be my own boss, amma suna so su daƙile min mafarki na. Haseena tunda nake ban taɓa sha'awar sarauta ko kuma wani abu na kasuwanci ba ko aikin gwamnati ba,ke kin san wacece ni". Tana magana hawaye na gangarowa daga kwarya idanunta.

Cike da tausayi Haseena ta sauko daga saman kujerar da take zaune ta zo ta rungume ta,.

" Kiyi hakuri komai ze koma dede,daga zaran sun fahimce ki zasu bar ki kiyi yanda kike fata kinji abar kauna!?".

Gyada mata kai kawai tayi tana share hawayenta.

" Yanzu ni gobe zan koma Russia domin na jima rabona da gida amma na miki alkawarin duk sanda na samu lokaci zan zo domin in gan ki".

Dago kai ta yi ta kalleta haɗe da faɗin " yanzu dagaske tafiya zakiyi Haseena bazaki bari ki ɗan ƙara wani lokaci ba !?".

Shafa kanta tayi " kar ki damu aina miki alkawari zan ɗinga zuwa in sha Allah".

Har cikin ranta bata ji dadin hakan ba,amma ya zatayi?,itama Haseena na da ahali bazata iya dakatar da ita ba.

" Shikenan tom Allah yakaimu,barin in je in ga Ummi,daga nan kuma zan yiwa Yarima Haysam magana a miki booking Flight ".

A haka suka rabu ita ta fice zuwa sashin Ummi ita kuma Haseena ta kwanta.

Ko da ta shiga dakin duhu ya mamaye ciki amma dake farin riga ne da farin hijab a jikin Ummi tana sallah, hakan be hanata ganinta ba kunna switch din ta yi sannan ta zauna tana me jiran ta idar da sallah.

Ta jima tana addu'o i kafin ta sallame,duban ta tayi kallo ɗaya ta mata ta gane wacece,domin ko da duniya ba zasu iya banbance su ba ita zata iya tunda ita ta haife su.

" Muzaina" ta ambaci sunan ta,tana miƙa mata hannu alamar ta zo,tasowa ta yi ta zauna haɗe da kwantar da kanta a jikinta.

" Meya hanaki bacci Muzaina har wannan lokaci!?".

" Ummi haka kawai na ji bana son yin bacci,na kasa yin bacci a can kila zan iya yi a tare da ke".

Duk da tayi mamakin maganar ta,amma se tayi murmushi domin abinda bata taɓa ji daga gare ta ba kenan.

Muzna da ta baro dakinta ne,ta shigo dakin Ummin bakinta ɗauke da sallama,zama tayi a gefen hagun sarauniya Fatima,suka sakata a tsakiya.

" Ummi na,yau anan zan yi bacci na ". Ta faɗa a shagwabe,shafa fuskarta tayi tana murmushi.

" Tom ku tashi muyi addu'a se mu kwanta ko?".

Addu'a suka yi sannan suka hau royal bed din suka kwanta tana tsakiyar su,sun ɗaura kansu a jikin ta tana shafawa.

Shuru ne ya ratsa dakin kamar wa'yanda suke bacci amma dukkanin su idonsu biyu ko wanne da abinda yake tunani.

" Kun san nima marainiyace kamar ku?, lokacin da baban mu ya mutu,bayan shekaru biyu da rashinsa mahaifiyar mu itama ta tafi ta bar mu,amma ban taɓa jina cikin maraici ba,kun san saboda me ?".

Girgiza kai suka yi alamar ah ah.

Ɗorawa ta yi da " saboda ina da yan uwa kuma sun soni sosai mun haɗa kan mu waje daya,bama taɓa yarda wani abu ya shiga tsakanin mu.

Mun rayu ne akan turban da iyayen mu suka daura mu na kaunar juna,dan Allah ku ma ina me rokon ku da ku kasance masu kaunarta juna ko da bayan rai na ne,kar ku sake kyale_kyalen duniya ya farraƙa ku,mulki,kudi,ɗaukaka,duk wanda kaga ya samesa to Allah ne ya riga da ya rubuto masa hakan tun kafin a san ze zo duniya,kun ji ko yarana?"

Tabbas maganganun ta sun yi matukar tasiri a zuciyoyinsu,jikin su ya yi sanyi sosai hakan yasa suka sake mannuwa a jikin ta kana Muzaina ta ce

" Ummi in sha Allah babu abinda ze rabani da Muzna ".

Murmushi tayi hakan ya mata dad'i

" Nasani domin kuna son junan ku sosai ". Ta faɗa tana ci gaba da shafa kan su

" Ummi ni banason yanda ki ke maganar ko bayan ran ki,in sha Allah ba yanzu za ki mutu ba,mu na nan har tsufan mu". Muzna ta faɗi hakan a yayinda siraran hawaye ke kwaranya a idanunta.

" Ya Allah,to meye na kukan Muzna?" Cewar sarauniya Fatima tana miƙewa zaune su ma suka zauna.

Hannu tasa ta goge mata hawayen " be dace ki yi kuka ba ta kan magana irin haka ba,rayukan mu ba'a hannayen mu suke ba,za mu mutu ne a lokacin da ubangijin mu yayi kira a gare mu, kamar yanda Aba din ku ya tafi haka nima wata rana zan tafi, ku ma za ku biyo mu haka kowa ma se ya mutu.

Kar ki zama raguwa mana,ni ban haifi ragwaye ba, ƴa'ƴana basu da rauni dukkanin ku jarumai ne,.ko bayan idona nasan zaku sani alfahari ".

Sunkuyar da kanta ƙasa tayi har lokacin hawaye ya kasa tsayuwa daga Idonta haka kawai take ji a jikinta kamar ta kusa rabuwa da wani gurbi na rayuwar ta.

Ɗan murmushi kan leben baki Muzaina ta yi ta soma faɗin

" Ummi ita fa da ma wannan ƙanwar tawa haka take ko banida lafiya in na ki shan magani se ta fara min kuka har se na sha ".

Ɗago kai tayi tana hararan ta jin abinda ta faɗa

" Ni ba ƙanwar ki bace saboda rana daya a lokaci daya muka zo duniya"

Dariya sarauniya Fatima da Muzaina suka yi mata.

Cikin dariya sarauniya Fatima ta ce

" Eh tabbas rana daya ku ka zo duniya,kuma a lokaci daya. sede saida aka fara fito da Muzaina kafin ke a ka ciroki, to Kinga kuwa ta ri ga ki shan iskar duniya ".

Cuno baki tayi tana " eh de duk da hakan de baran yarda ba".

" To shikenan ".

" Ummi gobe Haseena zata koma ƙasar su Russia gaskiya zan yi kewar ta sosai, yanzu kafin in shigo na samu yarima Haysam na masa magana kan ya mata booking Flight dan cewar ta da wuri take son komawa ".

" Allah sarki, Haseena yarinyar Kirki ce kuma naji dadi sosai da ya kasance kina ƙawance da ita Allah ya nuna mana safiyar ".

Har karfe biyu na dare idanunsu biyu suna hira se da sarauniya taga lokaci ya kure kafin ta basu umarni da su kwanta.

" Dare ya yi duk ku kwanta kar wacce ta kuma magana kun ji ko!?,ku yi bacci cikin aminci".

Washe gari

Miƙewa tayi akan gadon tana hamma haɗe da miƙa,ta kalli Muzaina dake gefenta tana baccinta peacefully.a gefe da gadon ta hango mahaifiyar su sarauniya tana gabatar da sallah asuba hakan yasa ta haɗe gashinta da suka hargitse ta ɗaure sannan ta soma tashin Muzaina ta hanyar bugun fillow da take kwance.

A hankali ta ware idanunta da bacci be ishe su ba ta ɗaura su akan ta tana me faɗin

" Meye kuma !?".

A hankali ta furta " ki tashi kiyi sallah gari ya waye".

A kufule Muzaina ta kuma maida kanta kan fillow tana me rufe Idonta ta ce

" Kar ki kuma tashina tam".

Tunda ta ji hakan tasan ba sallah zatayi ba, hakan yasa ta miƙe ta shiga toilet ta yi wankan safiya haɗe da Ɗaura alwala ta fito, ma'adanar kayan sarauniya taje ta buɗe ta dauko wata dogon rigar me shige da jallabiya ta saka sannan ta saka farar hijabi da tsayinsa ya tsaya mata a cikinta,ta shimfida sallaya a kusa da na sarauniya itama ta tayar da sallah.

Komawa sashen ta tayi bayan ta baro sarauniya Fatima nayiwa Muzaina faɗa akan sallah.

Zaune ta iske Haseena tana zaman jiranta .ta gama duk shiryawan da za ta yi tsaf,zama ta yi a gefenta tana faɗin

" Hasee bari in shirya na rigada na yi wanka ".

" To kiyi sauri Kinga lokaci na kurewa".

Shiryawa tayi cikin bakar dogon riga da jikinsa ya sha tsone, siririn necklace na Gold ta saka a wuyanta da yan ƙananun ɗan kunnen sa, sannan ta gyara gashin ta, tayi light kwalliya,flat shoe baki ta sa kafin ta ce

" Na kammala".

Haseena da tun lokacin da ta fara shiryawan take bin ta da kallo tana murmushi ne ta miƙe ta ce shikenan muje.

Bayi ne suka ɗauki kayanta izuwa motar da ze kai su airport,su kuma suka je wajen galadima domin tayi musu bankwana.sosai suka mata godiya da kuma yi mata alheri,haka suka shiga wajejen Ummu zaheenat da Ummu Xulaihah ta musu bankwana..

Waje na karshe da suka shiga shine wajen sarauniya Fatima, sosai ta yi mata godiya haɗe da mata kyautar zinari masu daraja sosai, Muzaina dake zaune akan kujera tana danna waya ko dagowa batayi ba ɓalle ta kalleta,haka itama ba ta bi ta kanta ba, fitowa suka yi suka iske Hamra da Jadwah suna jiran su a babban falo.

Motoci biyar ne ya musu rakiya izuwa airport,bayan sun isa suka fito riƙe hannun juna suka yi suna me yiwa junansu kallon kewa da zasu yi.

" Zan yi matukar kewar ki Haseena".

" Nima haka,zan zama ni kaɗai yanzu.amma ina addu'ar Allah ya sa'ke haɗa fuskokin mu".

" Ameen ya Allah,ki kula min da kan ki. a duk sanda ki ke da bukatar wani abu, ki min magana ina nan tare dake my Haseena. Sannan kuma ki isar min da sakon gaisuwa ta musamman a wajen kowa na gida".

Gyada mata kai ta yi hawaye na taruwa a Idonta, rungume juna sukayi na ɗan lokaci kafin ta sake ta tana manna mata sumba a goshi, rungume su Hamra ta yi kafin ta tafi ta barsu tsaye suna daga mata hannu.har cikin zuciyar Muzna tana jin babu dadi sun zo a tare sede Allah be yi zasu koma a tare ba.

Motar suka shiga suka ɗauki hanyar komawa masarauta,ko da suka shigo masarautar tun daga nesa ta hango Sadauki Zubair yana tunkaro su hannun sa na riƙe da Kwandon kayan miya.

Ganin yana kokarin ɗago kan sa izuwa ga motar ne yasa gudun kar ya hangota ta yi sauri kwantawa a jikin Jadwah,da kallo suka bita.

" Lafiya gimbiya"? Hamra ta tambaye ta,batace mata komai ba se ɗan dagowan da tayi tana leke ta glass,a jiyar zuciya ta sauke duba da ya ɗan wuce su,.

" Dakata ni zan sauka anan " cikin cika umarni driver da yake jan motar ya dakata.

" Me za ki yi"

Girgiza kai tai tana faɗin " zan ɗan yi abu ne, ku, ku tafi kawai" ta ƙarishe tana buɗe marfin motar ba tare da ta jira an buɗe mata ba,se da ta tabbatar da sun tafi tukuna dan tasan Jadwah zata iya biyo bayanta.

Cikin sauri-sauri ta bi bayan sa har ta cin masa amma bata basa damar fahimtar tana binsa a baya ba.

Tafiya suka yi me nisa tun daga nesa take hango wani gida madaidaici wanda ya kasance a gefen manyan sashen bayi.

A bangaren Sadauki Zubair kuwa tun lokacin da ta soma binsa ya ankara da sautin taku a bayan sa amma se be nuna alamun yasan a na binsa ba har suka yi wannan nisan.

Suna cikin tafiya ya ja burki ya tsaya batare da ya juyo ba,itama tsayawa tayi daga bayansa tana runtse ido haɗe da yin murmushi dan ta san yanzu kam ya gane ana binsa.

A hankali ya juyo ya ɗaura idonsa akan ta,ko kaɗan be yi tunanin cewa ita bace,tun daga kasa ya soma ƙare mata kallo ganin tafi ko yaushe kyau,.

Cikin dabur-dabur ta furta

" Uhmm amm barka dai....dama naganka ne shisa nace bari in zo mu gaisa".

Murmushi ya yi " shikenan amma kar ki ƙara irin haka domin wata rana za'a iya kawo miki farmaki,saboda duk wanda ana binsa a baya haka ze yi tunanin abokin gaba ne ".

Gyada kai ta yi cikin jin kunyar sa " in sha Allah".

Har ya juya kuma se idonsa suka sauka akan tsadadden sarkan zinari da dan kunnensa dake manne a dogon wuyanta da kuma kunnuwan ta.

Nu na su ya yi da yatsa ya ce " wannan zinarin fa, wannan zinarin me matuƙar daraja ce taya akai ki ka same sa !?".

Ya tambaye ta yana tsare ta da kallon tuhuma.

Se da gabanta ya fadi jin tambayar da ya watsa mata shi,banda girgiza babu abinda kirjinta yake mata ga ta gagara nemo abinda zata sanar dashi.

Fahimtar da ya yi ta faɗa duniyar tunani yasa ya kyasta mata yatsa a fuska wanda yasa tayi firgit ta dawo hayyacinta.

" Uhmmm wannan sarkan jabun na gimbiya Muzaina ce, lokacin da aka bata sarkan shine ta saka aka min jabunsa.saboda tana ji dani kuma na yabi sarkan sosai" ta karasa maganar tana satan kallon sa ta kasan ido,.

Har yanzu da kallon tuhumar yake binta domin be wani gama yarda da abinda ta faɗa ba, saboda a duk inda kaga jabun abu da na gaskiya seka gane.

Cikin son kawar da maganar ta ce " shin ina zaka je haka naga ka biyo ta nan? ".

Dago mata da Kwandon kayan miya yayi ya nuna mata ya na me cewa

" Yumma ce ta tura ni madafa domin samo mata kayan haɗa miya,nan kuma shine in da muke rayuwa ".

Zaro ido waje tayi da alamun mamaki ta ce " dama ana aikan manya ba ka da kanne ne? ".

Girgiza ya yi " banida su ni daya ne a gun yumma na, Bismillah mu karasa ku gaisa ".

Murmushi tayi suka ci gaba da tafiya suna hira gwanin burgewa har suka iso bakin kofar da ze sada su ciki, dakatawa yay ya kalleta kafin ya ce

" Bari in faɗa mata ina tare da bakuwa ".

Kai kawai ta gyada masa shi kuma ya shiga ciki yana me kiran " ya yumma.gani na dawo gare ki tare da aikan da ki ka min".

Ƙarewa cikin yar filin gidan kallo tayi babu komai se wani yar karamar waje da aka ware alamar shine madafa,nan ma kuma iya kacin tukunya ne,se murhu da su kwanuka yan ƙalilan. A gefe guda kuma wata rubarbiyar carpet ne da yaci kura alamun an jima ba a yi amfani dashi ba,se kuma yar kujeru irin na zaman gida guda biyu a tsakar gidan.

Bakaramin sanyi jikinta ya yi ba ganin yanda suke rayuwa a cikin wannan tsukekken gidan su biyu wanda ta yi imani bazata iya zama a nan ba,.domin ta saba da rayuwar daula.

Tana wannan kalle-kallen suka fito suka tadda ita.

" Marhaban da wannan bakuwar ta mu ". Mahaifiyar Sadauki Zubair ta faɗa tana isowa gaban Muzna.

Kallon dattijuwar ta yi, kyakyawar Balarabiya ce fara sol dan bazama a ce ita ce ta haifi Sadauki Zubair ba sede tsananin kamar da suke yi ne ze shaida maka da hakan.

Haɗe hannunta tayi cikin girmama manya ta furta " ina gaisuwa a gare ki".

" Gaisuwa a gare ki ƴata ". Ta faɗa tana rungumeta haɗe da manna mata kiss a gashin kanta.

Sa'ke ta tayi tana me ɗauko mata yar kujerar ta ajiye mata haɗe da mata alamar ta zauna,zama Muzna ta yi tana kallon Sadauki Zubair dake tsaye yana kallon su yana murmushi.

Zama itama tayi ta riƙe hannun ta tana mata murmushi.

" Masha Allah da wannan kyakyawar halitta,ƴata ke kyakyawa ce tabbas Zubair ya yi dace da samun mace kamar ki" runtse ido Sadauki Zubair ya yi ganin zata masa ɓaran-ɓarama yasa yai saurin faɗin

" Yummaaaaaa, sunanta Muzna".

Fahimtar inda zancen san ya dosa ne yasa Yumma yin murmushi tana sauya magana daban,ita kuma Muzna abin ba karamin sa ta dariya ya yi ba se kawai ta danne tana murmushi.

" Ƴata kyawun ki ya wuce misali,ba ki yi kama da gimbiya ba kin fi kama da sarauniyar Bayaan. Komai na ki abin burgewa ne,shin a wani sashen bayi ki ke!?".

Murmushin yaƙe ta yi " ina sashen manyan bayi,ni ce ke yi wa gimbiya hidima ".

" Na'am na fahimta, Zubair maza kawo mata abincinka wanda baka ci ba ".

Girgiza kai yai yana shigewa ciki bayan mintuna kaɗan ya dawo dauke da plate a rufe da wani plate din ya a jiye a gaban ta.

" Ya Allah.... Zubair haka ka ke so ta ci abincin babu ruwan sha?".

" Ah ah yumma ba damuwa ya barsa kawai". cewar Muzna.

" Shiii, babu kyau mutum yaci abinci ba tare da ya ajiye ruwa a kusa da shi ba, saboda gudun kwarewa".

Komawa cikin ya yi ya dauko mata ruwa a cikin kofin silver ya bata.

Buɗe mata plate din ta yi dake ɗauke da dum biryani se dabino a gefen sa, tundaga ido taji bazata iya cin wannan abincin ba saboda yanda taga ya yi sanyi.sannan babu wani abin hadi a shinkafar biryanin haka naman ma bashida yawa se kwai guda biyu da dabino a gefe,amma me bazata iya nuna musu ta fi karfin wannan abincin ba,babu yanda ta iya haka ta saka hannu a ciki ta soma tsakura kaɗan a hankali ta kai baki,the test was not bad amma bazata iya ci ba saboda it was low key dish,ɗaurewa ta yi ta haɗiye na bakinta, cikin wayancewa ta ɗauke dabino ta saka a baki tana ci.

A hankali ta ɗago ta kalle ta ta furta " yumma na koshi bana wani jin yunwa".

" Ya Allah,me yasa bazaki karasa ba ke kuwa ".

Yumma ta faɗa tana sa'ke matsar mata da kwanon gabanta.

Sadauki Zubair da ya lura da a koshe take se ya yiwa yumma alama da ido hakan yasa ta cewa

" To shikenan yanzu na miki uzuri, amma karo na gaba in ki ka kuma zuwa to fa bazan bar ki ki tafi ba tare da na cika Miki ciki ba ".

Dariya ita da Sadauki Zubair suka yi tana miƙewa tsaye haɗe da faɗin

" Ya yumma!, nagode sosai da karramawa ".

" Ki ɗauke ni kamar yadda Zubair ya ɗauke ni, Allah ya muku albarka,ki huta gajiya ". ta faɗi hakan a yayinda take shafa mata kanta.

Kallon sa ta yi, ta ce " maza je ka rakata ".

Fita suka yi a gidan suna tafiya cikin nutsuwa babu wanda ya ce wani abu, kowa da abinda yake tunani.

Cikin zazzakar muryarta ya ji ta furta " mahaifiyar ka tana da kirki sosai".

" Kwarai,shisa nake godewa Allah da fitowa dani daga gareta ".

" Tana da kirki sosai kuma tana da kyau ta fika kyau ".

Ta karasa tana murmushi.

" Hhhhhh tafini kyau saboda ni baƙi ne!?" Ya tambaye ta yana dariya.

Dakatawa tayi da tafiyar ganin ta dakata ne yasa shima ya dakata.

" Launin fata ba shine kyau ba,ko ka kasance me hasken fata ko ka kasance me duhun fata, matukar kana da kyakyawar zuciya da kuma yakini me kyau kafi kowa kyau,. sannan kuma ka sani cewa launin Fatar ka shine yaja hankalina a gareka Zubair,INA MATUKAR KAUNAR KA,shin zaka rayu tare da ni!????".

Magana take yi masa a yayinda suke kallon cikin kwayar idon juna.

Be taɓa Sanin ze so wata halittar ya mace da suna soyayya ba seda Allah ya jefo masa da Muzna cikin rayuwar sa,tun rana na farko da ya soma ankara da tana zuwa domin ganinsa ya ji ta burge sa.har ya fara sonta ga shi ita da kanta ta furta masa cewa tana kaunar sa wani sanyi ya ji ya mamaye duk wani magudana dake jikin sa.

Taku biyu ya yi kadan ya matsota cikin tsantsan kaunarta ya furta

" Shin wani mahalukin ɗa namiji ne ze ga wannan kyakyawar halittar ya ce baya son ta!?,ke din ta musamman ce Muzna, tabbas kina ɗauke da abu na musamman a jikin ki,ni a waye da za ki furta min kalmar kauna in ce ah ah,Nima ina kaunar ki ".

Ya faɗa yana murmushi haɗe da riƙe hannayenta duka biyu ya mana musu sumba a ko wannensu.

Cikin farin ciki da ɗaukin jin amsar sa ta kwace hannayenta daga garesa ta rufesu a fuskar ta.

Dariya me sauti ya yi ganin wai kunyar sa take ji ya riƙe hannunta haɗe da cewa

" Muje in raka ki ".

Har sashen manyan bayi ya rakota sannan suka yi sallama se da ta tabbatar da ya ɓacewa ganinta sannan ta bar sashen manyan bayi.

" Wancan kamar ita ce gimbiya Muzna ce ko Muzaina an ce de ba'a gane su,to me take yi a tare da Sadauki Zubair kuma !?".

" Ke bama kama bane kin manta ni ke share bangaren gimbiya Muzaina wallahi wannan duk yanda aka yi gimbiya Muzna ce domin waccan bata dariya".

Cewar wasu bayi mata guda biyu dake labe suna leken su lokacin da suka iso sashen na su.

" Tabb dijam,amma al amarin akwai ban mamaki ".

" Hmmm taya ni dubawa fa wai gimbiya ce ke jera hanya har ma da magana haɗe da murmushi da bawanta".

Haka suka dinga tsegumin su a gurin.

" Hmmm lallai abokina ka yi dace inde wannan kyakyawar yarinyar dake zuwa kallon ka ne,domin Allah ya yi halitta a wajen" cewar Arman daya daga cikin abokan Sadauki Zubair da suke zaune guri daya dashi.

Wani a cikin su ne ya bugi kafaɗar sa haɗe da faɗin

" Arman bashi kaɗai bane ya yi dace itama yarinyar tayi dacen salihin bawa da be taɓa kallon wata mace da sunan soyayya ba".

" Amma Hashim kana ganin auren su za'a yi sa babu wani Matsala?". Shuru suka yi suna kallon sa.

Tunda suka soma zancen sun Sadauki Zubair babu abinda ya ce musu se yanzu da ya ji sun yi batu akan aure hakan yasa ya maida kallon sa shima akan su.

" In sha Allah babu wata matsala,saboda yanda nake bawa a wannan masarautar itama haka kun ga kuwa fada zasu ɗaura mana aure ".

Cikin tayasa murna suka gyada kai cike da gamsuwa da maganar sa.

Yanzu labari ya soma tafiya in har kun bani haɗin kai tofa zamu tafi,in kuma kuka ki bani haɗin kai se mu hakura da wannan daddadar labarin,yawan comment din ku yawan read more din ku.

Comments,like and share fisabilillahi.🥰🥰🥰🫶