ƊAYA CIKIN BIYU
by @mrsisham12
9–10⚔️👑👑 ƊAYA CIKIN BIYU 👑👑⚔️
🔥A story of love,hatred and violence ⚔️🔥
🤍*Story and written*🤍
~By~
Aisha Abbas (*MRS 🌹 ISHAM 🌹*)
(*Yar lelen jarumai writers*).
Jarumai writers association 📚📚📚🖋️🤩
❤️🔥Page 9____10
" Ina ki ka je na ga su Jadwah sun dawo ba tare da ke ba gimbiya Muzna!!?".
Tana cikin tafiya ta jiyo Muryar Ummu zaheenat na yi mata magana.
Tsayawa ta yi ta amsa mata " Ummu zaheenat na tsaya a lambu ne na ɗan sha iska, shin bayan haka akwai wani abu ne!?".
" Babu komai dama yar uwar ki ce ke tambayar ki domin ba ta ga dawuwar ki ba".
" Nagode da kulawa ".
Ta faɗa tana shigewa ciki tare da nufar bangaren Muzaina.
Babu zato babu tsammani ta ji an fisgota ta faɗa jikin mutum,a gigice cike da tsoro ta kalli fuskar sa,wani wawan tsaki ta ja tana me hankade sa a jikinta.
" Wannan wani irin hauka ne!?,wai tukuna Yarima Ishaq ka manta nidin wacece!?, gimbiya ce, amma hakan be hana ka dinga min wannan abun ba,ko kana tunanin ni din nan yar iska ce?,to ba haka nake ba,kayi gaggawar fita a rayuwata. ko kuma wallahi ina iya samun Abu Aleem in sanar masa".
Narkar da muryar sa ya yi ya koma kalar tausayi " but Muzna I love you,ina kaunar ki tun ranar da na a za idona akan ki Allah ya sa min soyayyar ki a raina".
Wani kallon takwas saura kwata ta masa ta ture sa haɗe da yin gaba ta barosa a baya yana me bin ta da kallo.
" My Muzaina ga ni naji labarin kan cewa kina nemana".
Tana daga kwance ta jiyo Muryar Muzna din hakan ya sa ta miƙa mata hannu alamar ta zo,zama tayi a kan gadon kafin itama tayi irin kwanciyar da Muzaina tayi dukkanin su kan su na kallon sama.
" Ina son zan yi tafiya ".
" Zuwa ina kenan?,amma de kin san de Abu Aleem baze yarda ba ko !?".
Miƙewa zaune tayi tana yatsina fuska " excuse me,waye shi da ze hana ni zuwa duk inda na gadama!?,he has no right".
Muzna da dama ta san za'a yi haka,domin Muzaina bata bin ta kan abinda mutane zasu ce, tana rayuwar ta ne with freedom.
" Shikenan to Allah ya kai mu " ta faɗa tana kallon ta.
Suna a kwance wata baiwa dake yi wa Muzaina hidima ta shigo ɗauke da babban tray na alfarma dake ɗauke da nau'in abinci kala-kala a cikin kuloli,durkusawa ta yi ta ajiye, sannan ta soma kokarin zuba musu.
" Dakata ban sa ki ba tashi ki fice min da gani". Jiki na kerma wannan baiwa ta fice tun kafin ta amshi hukunci.
Girgiza kai kawai Muzna ta yi ta miƙe ta zuba musu abincin suka fara ci.
Haka suka ci gaba da rayuwa a cikin masauratar,ana nuna musu gata iya gata da kulawa, soyayya me karfi ya sa'ke kulluwa a tsakanin Muzna da Sadauki Zubair wanda kusan a ko yaushe suna tare,kuma har wannan lokacin be gane cewa ita din yar sarki ce ba.duk wata hanya da ze bada kofa da ze gane hakan ta toshe sa,duk yanda ta so ta boyewa su Jadwah se da suka bi kwakwafi suka gane,haka Muzaina da yarima Farasat suna ɗan taɓa soyayya ba laifi duk da ma shi ya bawa abin karfi,ita maganar sarauta shine a gabanta.
Duk suna zaune a babban falo har tsawon karfe sha daya na dare suna hira.ban da sarauniya dake can sashen ta, lokaci zuwa lokaci galadima Abdul Aleem yana duban agogo.
" Shin dama Ishaq na kaiwa dare har haka babu wanda ya sanar mini" ya faɗa yana kallon yarima Farasat da Yarima Haysam.
Sunkuyar da kai sukayi domin wannan ba sabon abu ne, kullum in ya fita se tsakar dare yake dawuwa.
" Kun mini shuru ko ba da ku nake magana ba!?".
Ya faɗa a faɗace.
" Afuwan ya Abu Aleem,ka yi masa gafara".
Cewar yarima Haysam.
Haka da ya faɗa ne ya sa'ke tabbatarwa galadima Abdul Aleem wannan ba shine karo na farko da yarima Ishaq ke kai wa dare ba.
Masifa ya fara yi musu gaba daya domin a cewar sa ai suna da masaniya amma babu wanda ya sanar masa ya dau mataki,duk se da suka sha jinin jikin su,suka yi Shuru.
" Ka yi hakuri nima ban san da wannan zancen kaiwa daren da yake yi ba da na sanar dakai ". Cewar mahaifiyar Yarima Ishaq wato Ummu Xulaihah..
Waziri kam shuru ya yi ya ma rasa abin faɗa domin a cikin ya'yan sa yarima Ishaq yana basa ciwon kai.
Muzna, Hamra, Aliyah, Jadwah duk suna zaune a guri guda sun nutsu suna jin yanda galadima Abdul Aleem ke ta ruwan masifa,ita kuwa Muzaina tabe baki tayi tana ci gaba da danna wayar ta.da taga ma hayaniyar tasa zata dameta hakan yasa ta bar falon ta wuce sashen ta.
Har sha biyu suna zaune kuma har lokacin be dawo ba,.
Da fito ya shigo a bakin sa a maimakon sallama,yana tafiya yana ɗan layi kana ganin sa kasan a make yake,fito yake yi yana tafiya hannun sa riƙe da car key din sa ko kaɗan be lura da mutanen dake cikin falon ba . se ma waka da ya soma rerawa.
" Ehhhhh zuciyata tana bugawa ne a gare ki, kyakyawa ce ke surar ki ma abin kallo ne,zo ki ja ni muje duniyar wata, ki nu na min salon soyayyar ki,ya ke masoyiya ta zo ki janiiiiiii". Ya na wakar haɗe da nooding head din sa.
( Tom wannan wakar wata waka ce ta larabci na fassara muku domin kuma ku ji me yake fadi😂😂😂😂😂😂).
They are all shocked ganin yanda ya shigo a maye yana abu kamar ba musulmi ba,.
Dakatawa yayi sakamakon sauka da kyakyawan idanunsa suka yi a kan muzna dake tsaye tana masa kallon tsana,tsabar sharri na maye ita kadai ya gani a kaf cikin falon.
Da hannu ya nuna ta yana " kai shin ke din ce ko gizo nake gani?,kai Ishaq me yasa zaka mata magana ko ka manta kana fushi da ita ne !?". Ya tambayi kan sa yana rufe bakinsa da hannu kamar wani ƙaramin yaro.
" Shin meyasa ki ka tsane ni gimbiya, saboda na ce ina son ki!?,please ki bani dama in gwada miki kalar tawa soyayyar a gareki zan kauna ce ki fiye da komai, please ki aure ni gimbiya" ya kareshe maganar murya a karye kamar me shirin yin kuka ga idanunsa da suka yi jawur,ya taka ya isa kusa da ita yana kokarin rungumar ta baya ta ja,ya rungumi iska,cikin jin kunyar abinda yake aikatawa waziri ya nufesa a fusace ya wanke sa da mari.
" Ishaq ni zaka zubar wa da mutunci?, Allah ya sa ni ban taɓa aikata irin wannan munanan dabi'un ba lokacin da nake kuruciyata,amma na haifi mashayin giya ya subhanallah ".
Yana magana ne a yayinda idanun sa ke cike tab da kwalla shi kaɗai yasan baƙin cikin da ya kunsa.
Galadima Abdul Aleem bakin ciki da takaici ne suka haɗu suka tokare masa zuciya se kallon yarima Ishaq din kawai yake yi,haka Ummu Xulaihah kuka take yi kasa-kasa.
Yana riƙe da kuncin sa ya kalli wazirin ya furta " papa laifin me na aikata da zaka mare ni?, duba de ka gani yanda take bina da kallon tsana.. ka kalli yanda labbanta suke masu gwanin sha'awa,idanu kuwa kamar na aljana barbie".
Yunkuri waziri yay ze kuma kai masa wani marin galadima Abdul Aleem ya dakatar da shi ta hanyar faɗin
" Ba'a cikin hankalin sa yake ba a yanzu duk abinda zaka masa ko zaka faɗa masa bayida Amfani kabarsa zuwa safiya".
A fusace waziri ya bar falon ya nufi sashen sa,.
" Haysam, Farasat ku kai sa bangaren sa ".
Rirrike sa suka yi yana turjewa a haka suka shigar da shi ciki.
Dawo da kallon sa kan Muzna da take a tsorace ya yi ya taka izuwa gabanta.
" Tsoro?,kina goben wannan masarautar ko yar uwar ki,me ze sa ki cikin tsoro,duk wani abinda ki ka san ze sa miki rauni ki ajiye sa, yanzu je ki kwanta". Galadima Abdul Aleem ya faɗa mata haka.da sauri ta bar falon duk suka bi ta da kallo,cikin bada umarni ya cewa kowa ya tafi makwancin sa.
Gari na wayewa ko sallah batayi ba tayi wanka ta shirya cikin tsukekken wandon jeans da polo shirt white color, fuskarta fayau se ta ƙara kyau, takalmi ramboot ta saka se facing cap da ta sa a kanta ta fito da doguwar gashinta ta ramin igiyar hular ya zubo ta baya, headphone ta saka wa kunnenta ta kalli kanta a madubi ta fice,dama yau tunda ta farka take son motsa jiki ta hanyar yin sukuwa akan doki.
Wani bafade ne ya mata jagora har zuwa murin dawakai,dake ɗauke da dawakai kosassu na masarauta daga ido ma ka gansu se ka ji sha'awar hawa.
Wani haɗaɗɗen doki aka fito mata dashi ta hau,filin sakuwa ta shiga dake shimfide da grass carpet,ta fara tafiya akai cike da kwarewa.ta zagaya filin yafi sau biyar.
Dawakai suka fito dashi guda uku wanda zasu hau suna goge jikin su.
" Kai Sadauki wancan kamar budurwar ka,amma me take yi akan doki ita da take baiwa kaganta kamar ita ce sarauniyar masarautar". Arman ya faɗa yana kallon sauran abokan nasa.suma maida kallon su izuwa filin sukayi da mamaki suke binta da kallo.
" Shin amma me Muzna take yi anan ko de tare suka zo da gimbiya!?". Sadauki Zubair ya tambayi kan sa.
" Jeka mata magana mu na jiranka anan jeka ɗan yi zancen da masoyiyar ka" cewar Hashim yana tsokanar sa.
Murmushi ya yi ya tafi filin da take,ta cire hular kanta da headphone din,gashinta ya bazu a gadon bayanta hannunta na riƙe da goran ruwa ta buɗe murfin tana zubawa kanta da fuskarta, ruwan yana malaluwa har cikin rigarta.
Tsayawa ya yi a gefenta yana kallon ta cikin so da kauna ganin yanda take abu cikin salo da ɗaukan hankali.
Jikinta ne ya bata ana kallon ta hakan yasa ta jefar da goran ruwan a ƙasa ta soma kokarin saukowa daga kan dokin hannu ya miƙa mata da niyar taimaka mata ta sauko amma me with his surprise se ya ga tana bin sa da kallon kaskanci,kallo irin na kyama.
Ba tare da ta amsa tayin da yake mata ba ta sauko ta soma tafiya tana saka hannunta duka biyu tana kokarin haɗe gashinta,ganin ta ƙi kulasa ne yasa ya yi tunanin ko laifi ya mata da yasa tai fushi dashi.
Bayanta yabi ganin tana kokarin yi masa nisa,.
" Abar kauna ki gafarceni in har laifi na yi miki, amma kar ki min irin wannan horon na ƙin min magana".
Bata ko nuna tasan da ruwan alamar mutum ba taci gaba da tafiyar ta, ganin hallau ta ƙi kulasa ne yasa ya riƙo hannunta,.a fusace ta tsaya daga tafiyar da take yi ta juya ta wanke sa da mari. Tsantsan mamaki ne ya hana Sadauki Zubair motsawa daga tsayen da yake yana kallon ta,Bama shi ɗaya ba su Hashim da Arman da suke kallon su daga nesa kaɗan al amarin ya matukar jijjiga su.
" Kai wulakantaccen bawa idan ka kuskura wannan kazamar hannun naka ya kuma taɓa ni se na sa an wulakantaka kazami kawai mtsssw " ta ƙare magana tana watsa mai harara ta bar sa tsaye kamar wani gunki.
Da sauri su Arman suka iso gare sa suna fadin
" Shin menene yake damunta yau kamar wacce aka sauya ".
Gwauron numfashi Sadauki Zubair ya sauke " ina tunanin wani laifin na yi mata,amma yau gaba daya ta sauya min kamar ba ita ba " ya faɗa hakan dan ya kwantarwa abokan nasa hankali amma shi yasan me yake ji a zuciyar sa.hawa dawakan da basu yi ba kenan suka tafi.
Se karfe goma na safiya Yarima Ishaq ya farka daga bacci yana miƙa ƙarewa dakin nasa kallo ya yi,yana me riƙe kansa dake jujjuya masa toilet ya nufa yayi wanka haɗe da Alwala yazo ya gabatar da sallah asuba,yana zaune akan sallah galadima Abdul Aleem ya shigo cikin dakin nasa ya zauna a kujera yana jiran sa ya idar.
Bayan ya idar ne ya kalli galadima nan take abinda ya faru daren jiya ya soma tariyo masa a kwakwalwarsa.
" Barka da wayewar gari Abu Aleem".
" Barka".
Bayan nan kuma duk suka yi Shuru,yarima Ishaq da se zullumin abinda ze faɗawa galadima yake yi ne ya miƙe ya koma bakin gadon sa ya zauna.
" Ishaq...".
" Na'am Abu Aleem".
" Shin ka yi wa rayuwar ka adalci Kenan,ko kuma mu ka mana adalci?, saboda mun turaka turai kayi karatu a can shine ka kwaso mana dabi'un su kadawo mana dashi,so kake yi duniya ta zage mu ne?,ka duba yan uwanka Haysam da Farasat cikin su waye ka gani yana irin wannan banzan dabi'un!?,to bari in faɗa maka da babban murya mu din jinin larabawa ne masu kyamatar duk wani me mummunar dabi'a fatan ka fahimci hakan?,kar in kuma jin ka bar masarautar nan daga abinda ya kama karfe tara na dare duk yawon ka kayi sa daga safiya zuwa tara in kuma ba haka ba,zan ɗauki mummunar mataki akan ka".
" In sha Allah zan kiyaye ".
" Da ya fi maka alheri ".
Ya faɗa yana miƙewa ze fice.
" Ya Abu Aleem, wallahi ina san ta dan Allah ka yi wani abu ".
Tsayawa ya yi batare da ya juyo ba ya furta masa
" Ita din muna da sa rai akanta babu wanda ya isa ya yiwa shugabar sa ta gobe dole, zaɓin ta shine na mu ko ta aure ka,ko ta zaɓi wani akasin kai,biyayya shine namu". Ya fice abin sa.
Ya mutsa gashin kan sa ya yi saying " you fuck up Ishaq ".
" Jadwah a ganin ki meye ya hana Sadauki Zubair fitowa yau !?".
" Gaskiya gimbiya ban sani ba sede ko in zamu karasa mu tambayi abokan nan sa".
Haka kuwa akayi karasawa wajen su Hashim suka yi, suna musu murmushi cike da mamaki sude suke kallon su.
" Shin ko za mu iya sanin me ya hana Sadauki Zubair fitowa yau ".
Kallon juna suka yi ganin kamar sun rena musu wayo ko kuma ita Muznar ce ta rena musu wayo.
" Yanzu ke bayan abinda ki ka masa be ishe ki ba shine ki ka sa'ke dawuwa hmmm gaskiya mata yan renin hankali ne". Arman ya faɗa yana girgiza kai.
Cikin rashin fahimtar zancen nasa ta ce " meye ta yi masa din ".
" Ohhh bata faɗa miki ba?,yau da safe sun haɗu a murin dawakai ta mare sa dan kawai ya riƙe hannunta".
A tare suka dafa goshi haɗe da faɗin " Muzaina" a hankali.
Tana jin hakan ta gane da Muzaina suka gamu kuma shi ya yi tunanin ita ce shisa ya tunkareta,ko kaɗan hakan be mata dad'i ba.
Cikin sanyi murya ta ce " dan Allah yana ina ne ?".
" Yana bakin tekun lambu ta gabas".
Yana gama sanar da ita ta barsu a gurin.
Hangosa ta yi daga nesa yana zaune a gaban rafin gefen sa ƙananun duwatsu ne yana jefa daddaya a cikin ruwan.
A hankali ta karasa ta zauna a kusa dashi ba tare da ta furta kalma daya ba.hannu ta sa itama ta ɗauki dutsen ta fara jefawa cikin ruwan kamar yanda yake yi.
" Menene ki ka zo yi kuma!?".
" Kayi hakuri da abinda ya faru dazun,ni kaina ban san menene asalin abinda yake damuna ba,jina nake yi kamar wacce ake sauyani dan Allah ka min afuwa nasan ban kyauta ba".
" Muzna da a ce ban san ki sosai ba to tabbas zan ce bake bace domin yau naga wani barayi naki da yasa min dasa shakku akan ki, shin kina ganin marin da ki ka min ya dameni ne?, kalaman ne suka min zafi,dan Allah bayan ni kar ki sa'ke faɗawa kowa haka,domin Wannan sune kalmomi mafi tozartarwa".
Maganar sa sosai ya karya mata zuciya se da ta ji tayi nadamar yi masa karya da tayi ga shi ta daure kanta da jijiyoyin ta,batada damar da zata ce masa wacce ya haɗu da ita yau ba ita ba ce yar biyun ta ce amma babu hali.
" Ka yafe min " ta faɗa hawaye na fita a idonta.
" Ai ba zan iya dogon fushi da ke ba ya Nurul qalbi".
Sosai ta basa hakuri haɗe da masa alkawarin hakan baze sa'ke faruwa ba,daga nan suka bage da hirar soyayyar su kusan awan su biyu a bakin rafin kafin suka tafi.
" Amma taya ki ka kasance kawa da baiwar ku kasantuwar ki yar galadima Abdul Aleem amincin Allah ya tabbata a gare sa!?". Arman ya tambaye ta.
" Saboda ta kasance me hankali haɗe da biyayya kuma ai kaga shekarun mu kusan daya ba laifi bane dan mun yi ƙawance ba " ta faɗa musu domin tun dazun suke mata tambayoyi har ta gaji a ranta kuwa tace bazata sa'ke rako Muzna ba.
Karaso su suka yi,ta riƙe hannun Jadwah suka tafi.
" Lallai masu iya magana sun ce so hana ganin laifi, yanzu kasha mari da safiya amma har an maka dadin baki ka hakura".
Kallon Hashim da yay maganar Sadauki yayi yana murmushi " bazaku fahimci komai ba se kun fara soyayya,bari in je gida na bar yumma ita daya".
Ko da shigowar su babban falo suka samu mutane tsaye kowa ya yi carko carko,ga Muzaina dake daga tsaye a bakin kofar mashigar bangaren sarauniya Fatima tana zuba ruwan masifa,kan su ne ya kulle domin basu san menene yake faruwa ba se jin Muzaina da suka yi tana faɗin
" Babu wanda ya isa ya hanani shiga domin kallon mahaifiyata ku gaggauta bani hanya ko kuma kuyi nadama".
Da sauri suka karasa inda take ganin yanda a ƙasa wasu kuyangu guda biyar suka tsare mata hanya.
" My Muzaina menene abinda ya faru! ".
" Wa'yannan banzayen ne suka min shamaki da shiga wajen Ummi,kuma wai Abu Aleem ne ya basu umarni".
Kallon kuyangun Muzna ta yi cikin mutuntawa ta ce " ko zaku iya min karin bayani!?".
" Ran gimbiya ya daɗe, galadima ne ya hane mu da barin kowa ya shiga ciki".
Gyada kai tayi alamar ta fahimta hakan yasa ta riƙo hannun Muzaina din ta jawo ta falo suka zauna amma duk da haka batayi shuru ba se masifa take yi wai an hanasu ganin mahaifiyar su.
Su Ummu zaheenat da Ummu Xulaihah kam sun kasa ko da tashi daga zaunen da suke.
Gefe guda kuma su yarima Haysam ne zaune jikin su a matuƙar mace,.
Fitowa galadima Abdul Aleem suka yi shida wani likita kana ganin fuskokinsu zaka fahimci akwai damuwa a tattare da su,da sauri Muzna ta nufe su.
" Ya Abu Aleem shin menene ya faru da Ummi!?,bacci take yi ne ko kuma batajin dadi !?".ta tambaye sa tana tsare sa da manyan idanunta,cike da tausayin su ya sunkuyar da kai yana me jin nauyin su,ya furta
" Zaku iya shiga ke da Muzaina".
Da sauri ta wuce sa ta shiga ciki Muzaina tana me rufa mata baya.
Koda suka shiga dakin sarauniya Fatima turus suka yi ganin ruwa da aka daura mata ga mashakar iska manne a hancinta ( oxygen).tana kwance.
Kamar wa'yanda kwai ya fashewa a cikin su,suka karaso Muzna ta zauna a gefen damar ta muzaina a gefen hagu.
" Ummi.....".
Muzna ta kirawo sunan ta,a hankali ta buɗe idonta da ya shige ciki tsabar a zabar ciwo ga bakinta da ya bushe,se ta ƙara wani haske.
" Ya..yara na" ta faɗa dakyar murya a dashe.
" Ohh my god Ummi menene Abinda Ya same ki haka jiya fa you're quite well amma yanzu kamar wacce ki ka shekara kina jinya ya Salam " cewar Muzaina dake riƙe da hannun ta a cikin nata.
Murmushin yaƙe ta kwakulo ta yi,ta maida kallonta kan Muzna,ta ga yanda take zubda kwallan ganin ta a cikin wannan halin.
" Ku dena daga hankalinku akan halin da nake ciki,bana son in gan ku cikin wani hali,ko bayan mutuwata ban yafe ku zubar mini da kwalla ko da digo daya bane, addu'ar ku kawai nake buƙata ba kukan ku ba domin kukan ku baze taɓa dawo dani ba. Se kuma ku riƙe min alkawarin da ku ka min duk rintsi duk wuya kar wani abu ya shiga tsakanin ku da ze tarwatsa muku tarayyar ku kunji ko!?".
In banda rawa babu abinda zuciyoyinsu yake yi ga wani tsoro da ya mamaye ransu wani nauyi suka ji kirjin su ya yi kamar an a za musu gungumen dutse.
Dakyar suka iya motsa kan su,suna kallon fuskar ta kamar yau suka soma ganinta a gaba da rayuwar su.
Murmushi ta yi musu me kayatarwa wanda zasu iya cewa tunda suke da ita basu taɓa ganin ta yi irin sa ba,Idonta ne ya soma juyawa ya koma kallon sama.
Da labban bakinta kawai suke iya gane abinda take fadi ba komai bane face kalmatu shahada.
Rintse idanunsu suka yi a tare a lokacin da suka fahimci Allah ya mata cikawa,neman hawaye da kuka suka yi suka rasa zuciyar su ya yi tauri sosai sun alakanta hakan da cewa da tayi bata yafe musu ba in suka yi mata kuka.
A hankali Muzna ta zare mata oxygen din tana me dakatar da ruwan.
Hannu Muzaina tasa ta jawo farar blanket din dake rufe a jikin ta,ta rufe mata fuska.
Barin dakin tayi tana tafiya kamar wacce ta sha abun maye sannu a hankali take tafiya bata ganin kowa a gabanta har ta iso falo,tunda suka ganta a wannan hali suka fahimci me faruwa ya rigada ya faru.
Riƙe hannunta Ummu zaheenat tayi tana hawaye " kar ki faɗa min sarauniya ta tafi ta bar mu".
Gyada mata kai ta yi sannan tace " Ummi ta tafi ta bar marayun ya'yan ta".
Kuka suka fashe dashi banda mazan da idon su ya cika da hawaye karfin hali ne ya hanasu kuka kamar yanda matan suke yi.
Sashen ta ta shiga tana me rufe kofar ta sa key,ta zame a hankali ta zauna a bakin kofar ta haɗe kanta da guiwa,tana tunanin tun da ga farkon rayuwar su har zuwa yanzu tana tuna wai yanzu sune basu da uwa basu da uba. Tunani iri iri haka ya dinga zuwa mata a rai,daga zaran ta yi yunkurin kuka se ta tuna abinda sarauniya ta faɗa musu se ta nemi kukan ta rasa,ta kai kusan awa biyu zaune a bakin kofar dakinta,ta ji ana knocking,dago kanta dake masifan ciwo ta yi ta furta
" Waye ne !?".
" Hamra ce, gimbiya Muzna ana da bukatar ki a fada".
" Okay ina fitowa".
Toilet ta shiga ta sakar wa kanta dake mata ciwo ruwa ba tare da ta cire kayan jikin ta ba se da ta jiƙe sannan ta cire su ta watsar a tsakiyar toilet din ta ɗaura towel ta fito fararen kaya ta saka.
Cikin lokaci kililan mutuwar sarauniya Fatima ya zagaye masarautar Bayaan dama cikin Kuwait da sauran ƙasashen duniya gaba daya.
Ko da Muzna ta fito fuska babu annuri a falo ta iske masu yi mata hidima.bata bi ta kansu ba ta fice suka bi bayanta,duk inda ta wuce bayi take gani zaune jugum-jugum har suka isa fadan da ya cika sosai, Muzaina ta hango cikin fararen kaya irin nata zaune a gaban makaran da sarauniya Fatima ke ciki an shiryata tsaf ga yan uwanta dake gefe suna kuka ƙasa-ƙasa.
Zama dabas tayi a gaban makaran cikin tausayin kansu ta kwantar da kanta a jikin Muzaina,shafa kanta Muzaina tayi itama tana kallon mahaifiyar su dake kwance lifeless.
Sosai suka mata addu'o i na samun rahaman Ubangiji,suna ji suna gani aka ɗauketa aka tafi da ita izuwa gidan ta na gaskiya.rungume junan su suka yi, sosai suka bawa duk wani wanda ke cikin fada tausayi.
Haka aka ci gaba da zaman makoki a fada babu wani abinda yake daga su a gurin se in zasu yi sallah zuwa dare wa'yanda suka zo daga nesa duk sun koma aka bar iya ahalin cikin kewar mutumiyar arziki.
Ko da ta dawo sashen ta ji tayi komai na duniya ya dena mata dadi,jin ta take kamar mara lafiya hakan yasa ta shiga toilet ta murza key ta kunna shower ruwa na zuba a ƙasa, sannan ta shiga cikin jacuzzi da ya kasance cike da ruwa a cikin sa.
Wani Marayan kuka ta saka me taɓa zuciyar duk wani me imani da mara imani tana dukan ruwan da take ciki domin raɗaɗin da zuciyarta yake mata baki baxe taɓa iya furtawa ba.
" Kiyi hakuri ki yafe min Ummi, na kasa cika abinda ki ka faɗa a gare mu. kukan shine kawai ze sanyani samun nutsuwa,ki yafe min Ummi " ta faɗa da wani gunjin kuka me cin rai.
Sosai ta yi kuka na tsawon lokaci wanda ta ji nauyin da take ji a zuciyar ta ya ragu se de ciwon kai da take fama dashi,har karfe tara tana zaune a cikin ruwan bata fita ba.har bacci ya soma ɗaukar ta.
10:00 ta soma jin kukan tsuntsaye wanda hakan yasa ta yi saurin buɗe idonta da suka kasance a lumshe,ga wani masifar sanyi da iska dake kaɗata, hakan yasa ta ɗaga kai, abinda ta gani ya girgiza ruhinta,ganin kan ta tayi a cikin wani ƙasurgumin daji da babu alamar bil adama ko guda daya,ga wasu dogayen bishiyoyi masu tsoratarwa da firgitarwa,babu abinda ka ke iya jiyowa a wannan dajin face kukan namomin daji da tsuntsaye se wasu sauti me firgita zuciya. Cikin ɗari-ɗari ta ziro santaleliyar ƙafafun ta waje ta fito daga cikin jacuzzi da take ciki tana waige-waige, ganin gaba daji baya daji ne tsoronta ya sake ninkuwa,ƙarar zubar ruwa ta ji wanda hakan yasa ta juya baya dan ganin menene jikinta na rawa sosai,wani mummunar halitta ta gani bakinsa na tsilalar da ruwa kamar korama,ga wasu kwarangwal din mutane dake biyo ruwan suna fitowa babu kyan gani hannun su riƙe da takobi,ja da baya ta yi tana jin wani jiri na kokarin zubar da ita,hankalin dodon ne ya dawo kanta bayan ya gaba aman ruwan kwarangwal din cikin murya me firgitarwa ya ce
" Bil adama a sansanin mu!?,ku yi maza ku kamo min ita ku kashe ta ".
Cikin tafiya irin na horori suka soma binta suna har ba mata takobi,ita kuwa gudu take yi da iya karfin da Allah ya bata tana kuka. Kutsa dajin ta dinga yi ba tare da tasan a inda take a za ƙafafuwan ta ba, ƙafafunta ne taji sun yi mata nauyi ta soma gajiya da gudun da take yi hakan yasa ta faɗi a ƙasa tana ja da baya su kuma suna tunkaro ta, riƙe ƙafafunta suka yi suna janta tana ihu,da iya karfinta ta shure su da ƙafa ta soma rarrafe da gudu wani karkashin bishiya me duhu ta gani cikin hanzari taje ta boye a ciki,tana haki domin ba karamin wahala ta sha ba, ƙafafunta duk sun ji ciwo sun fashe.
Babu abinda takeyi banda sauke numfashi ganin ta samu tsira,inda ta tsuguna ne taji ya soma numfashi yana motsi,wani harbawa kirjinta ya yi ganin masifar a she be ƙare ba,( ni ko nace ai Muzna masifa bata ƙare ba kam). cikin rashin sani ashe akan wata tsohuwar macijiya take zaune batare da ta sani ba,a tsorace ta soma kokarin barin kasan bishiyar se ta ji ana faɗin
" Sarauniyar gobe ina ki ke kokarin tafiya?,shin ba ki san in ki ka fita waje zasu kashe ki bane!?". Ba kowa ne ke magana ba fa ce wannan macijiyar da take zaune akai.
Wani sabon tashin hankali ta kuma shiga,da gudu ta yi yunkurin sauka a jikin ta amma macijiyar ta hanata ta hanyar harɗe ta da bindinta,.
" Ki saurara! ni ba cutar dake zan yi ba,sunana macijiya Markusa,na kasance a wannan dajin kadur din tsawon shekaru dubu biyu ina rayuwa anan,kuma bana taɓa cutar da kowa batare da ya yi yunkurin cutar dani ba,se de ina da matukar hatsari ga duk me muguwar nufi,zan taimaka miki domin zasu iya kashe ki ".
Nutsuwa Muzna ta yi tana sauraran ta jin da tayi ta ce bazata cutar da ita ba amma har yanzu tana ɗari-ɗari dan jikinta se rawa yake . Wani farin haske ne ya mamaye inda take din nan take ta fahimci a cikin kogon dake ƙarƙashin bishiya take.dawo da kallon ta gabanta ta yi ta ci karo da macijiya Markusa da ta kasance rabinta mutum rabinta macijiya gata kyakyawa bazaka ce takai adadin shekaru har dubu biyu ba,daga saman gammon gashinta kuwa wasu macijai ne masu sheki se fitar sa dafi suke yi wanda a ƙalla yawan wannan macizan zai kai hamsin ko fiye da haka.
" Kar ki tsorata da ni, riƙe wannan a hannun ki".ta faɗa tana miƙa mata wani abu kamar kwai.karba tayi tana kallon sa a hannun ta.
" Dole ta inda ki ka fito ta nan ne zaki koma gida ruhinki dole ya koma gangan jikin ki,in ko ba haka ba awanni takwas ki ke dashi,daga zaran kin fita zasu kamaki sukaiwa dodo gartamus shi kuma ze kashe ki ya bawa yaransa su yi farfesun namanki su cinye,amma wannan kwai din shine ze cece ki daga gare su domin sun sani sarai daga zaran wannan kwan ya faɗi a ƙasa ya fashe to duk gabaki dayan su se sun mutu murus.
Zabi biyu gare ki,na farko.. za ki iya neman sulhu da su ta hanyar yi musu daɗaɗan kalamai in sun saurare ki tom in kuma basu saurare ki ba kin zama gawa.
Na biyu... Za ki iya fasa wannan kwan a ƙasa nan take zasu mutu zaki kuma koma gida cikin koshin lafiya da aminci ".
" Nagode sosai macijiya Markusa,bazan taɓa manta halaccin ki a gare ni ba". tana gama faɗin haka suka fara jin takun sawu masu yawa alamun har yanzu ita suke nema,.
Murmushi suka yi wa juna ta fito,tana fitowa kuwa suka ganta suka ɗauke ta sama kamar yar tsana suka fara tafiya da ita,har suka iso ainihin sansanin su,nan taga wasu kwarangwal din masu yawan gaske. Ji ta yi sun direta a ƙasa sun sauke ta gaban dodo gartamus.
Cikin wannan muryar tasa mara dadin sauraro da tsoratarwa ya soma faɗin
" Ke bil adama menene ya kawo ki cikin dajin kadur,ko baki da masaniya kan cewa wannan dajin duk wani bil adama kai bama bil adama ba hatta su kansu aljanun duk wanda ya shigo baya fita da ransa,kin ga wa'yannan duk matattu ne wa'yanda suka mutu na tayar dasu suke min hidima,ke wato gaki tantiriya shine ki ka shigo ko!?".
Muryar ta na ɗan rawa ta ce " wallahi bani na kawo kaina ba ina wanka ne na buɗe ido na nagan ni a nan dan Allah kar ka cutar da ni".
" Hahahahahahahaha,yarinya kin makaro" ku ɗaure min ita ".
Ɗaure ta suka yi a jikin wani bishiya,suna kalllonta suna lashe baki sun ga nama.
Ta jima a wajen daure tana kallon su suna ta harkokin gaban su tayi ihun ta yi maganar har ta gaji babu wanda ya kulata hakan yasa ta soma waka
" Muyiii adalci ga wa'yanda suka kasance marasa laifi......muyi afuwa ga wa'yanda suka kasance masu kyakyawar zuciya.....
Kowa na iya rikidewa ya koma mugu..... Nasan kana da kyakyawar zuciya bazaka cutar da wacce bata son cutar da ku ba,ina ɗauke da muguwar gubaaaaa da ze hallaka kowa......" Haka ta ɗinga maimaita waka tun basu saurareta ba har suka saurareta.
Dodo gartamus ne ya taho gaban bishiyar ya ce
" Kin samu haɗuwa da macijiya Markusa,ta ba ki abinda za ki kashe mu to bazamu baki damar hakan ba ".
Cikin kwantar da murya Muzna ta ce " ko kaɗan bawai na karɓi wannan guban dan in hallaka ku bane,babu ma manufar hakan a raina, wallahi bazan taɓa iya cutar da abinda be cutar dani ba,ko wanda ya cutar da ni se de in barsa da Allah amma dede da kaxa bazan iya kashewa ba,dodo gartamus nasan Kanada zuciya me kyau,samun dodo irin ka a wannan duniya ze yi wahala sosai,shin meze sani in saka muku guba!?, sulhu kawai nake da bukata,naji na yarda na shigo muku sansani amma kasani namaka imani da mahalicci na bani na kawo kai na ba,ka yi min afuwa".
Shuru dodo gartamus yayi kafin ya fitar da wani huce da ya kusan tayar da guguwa.
" In har kina so in yarda dake ki wurgo min wannan gubar " babu ko shakku ta wurgo masa shi ya cafe.
Tabbas ya yarda da ita,kuma ya ji baze iya cutar da ita ba hakan yasa yai wa kwarangwal din ya'yan gidan sa alamu da ido da sauri suka kunceta haɗe da sauko da ita kasa,.
Hannun sa me tsoratarwa da gashi ya ɗaura akanta yana shafawa " tabbas za ki iya shugaban ci aduk inda ki ka tsinci kan ki,za ki iya kawo gyara a cikin duk jinsin da kika shiga jeki,jeki gangan jikin ki na jiranki ".
" Nagode sosai dodo gartamus,bazan taɓa manta halaccin ka a gare ni ba".
" Kin cancanta".
Rakiya suka yi mata har zuwa wajen da ta fara tsintar kan ta,a wannan karon bata kalli jacuzzi din da ta fito a ciki ba,hakan yasa ta kalle sa
" Dodo gartamus taya zan koma kenan yanzu!?".
" Kar ki daga hankali". Ya faɗa yana busa mata iskar bakinsa me karfi nan take guguwa ya tashi da ita.
" Muzna ki farka menene abinda ya sameta ne!?". Muzaina ta faɗa tare da damuwa akan fuskarta tana riƙe da hannun Muznar gam taki saki.
" Wallahi ke kam nima baiwa ce ta kirawo ni,wai ta shigo dakin ta domin sanar mata da tazo taci abinci shine taga ruwa a malale a tsakar dakin hakan yasa ta dinga bin inda ruwan ke fito nan ta fahimci daga toilet ne,aikuwa tana buɗewa ta ganta kwance cikin jacuzzi ruwa ya cika tabb ita kuma bata numfashi".
Cewar Ummu Zaheenat.
Galadima dake daga tsaye ya ce " kar ku damu za ta farka in sha Allah ".
" Abu Aleem taya zan kwantar da hankali na ina ganin yar uwata kwance kamar wata matacciya?".
Dafa kafaɗar ta Ummu Xulaihah ta yi alamar tayi shuru.
Duk suna tsaye a cikin dakin Muzaina ce kawai zaune a bakin gadon da Muzna ke kwance kamar matacciya.
Firgit ta miƙe tana kokarin saukowa akan gadon riƙe ta tsam Muzaina da Ummu Xulaihah suka yi ganin bata hayyacinta .se da ta gama fisge-fisgen kafin ta yi lakwas ta kwanta jikin Muzaina tana sauke numfashi.
" Muzna shin kina tare da mu !?". Galadima Abdul Aleem ya faɗa yana dafa kanta.
" Abu Aleem shin ya nagan ni anan ni da nake daji ".
Tana magana ne tana kuma kallon dakin ta da kuma kan gadon da take. abun kamar almara tasan de wannan ba mafarki bane haka zalika be yi mata kama da zahiri ba.
" Ki nutsu babu abinda ya same ki mafarki ne kawai ".
Haka suka dinga gamsar da ita kan cewa mafarki ta yi,ita de ko kaɗan ta kasa gaskata hakan jin su kawai take yi.
Abinci Ummu Zaheenat ta bata da kanta domin ko breakfast batayi ba, duk da bataci da yawa ba amma tasa wani abu a cikin ta.
Ko da aka ce ta shiga ta yi wanka ƙin yarda tayi a ganin ta in ta koma toilet din abinda ya faru ze iya maimaita kansa.
Kowa tafiya ya yi izuwa sashen sa aka barta tare da Muzaina da Jadwah,se da ta ga ta samu tayi bacci kafin nan ta kalli Jadwah ta furta
" Bari in je in kwanta seda safe ". Kai ta gyada mata tabi bayanta da kallo.
Wanka Muzaina ta yi ta yi duk wani abinda ta saba yi kafin kwanciya bacci bayan ta shirya cikin kayan bacci ta hau kan makeken royal bed din ta ta kwanta.
2:00Am sanyin da ta ji ya mata yawa ne yasa taja blanket ta dukunkune a ciki,amma se ta ji sanyin kamar sa'ke huro sa ake, cikin bacci ta soma mita.
" Waye kuma ya ƙara AC din mtsssw" ta faɗa cikin bacci tana kuma dunkule kanta waje guda,wani sauti me kuka-kuka ta soma ji yana tashi haɗe da kiran sunanta.
Gaba daya wannan ƙaran ya dameta ya fitine ta, hakan yasa ta zauna tana mutsike ido game da yin hamma.
Ware manyan idanunta tayi waras at The same gurin da Muzna ta tsinci kanta.a hargitse ta mike tsaye tana rarraba ido kamar ta kai ajiya.
Wani gurnani mara dadin ji ta soma ji a bayanta nan take zuciyarta ta soma rawa,a hankali kamar wata mutum mutumi ta soma juyawa har ta juya gaba daya.
Ihu ta fasa sakamakon dodo gartamus da tayi arba dashi a gabanta, ga kwarangwal da yawan su baze taɓa misultuwa ba tsaye bayansa.
" Bil adama a sansanin mu!?,shin ko kin san menene ake yi wa wannan dajin lakabi da shi kuwa?, dajin kadur in de ka shigo tofa babu fita.ku yi maza ku kamo min ita ku kashe ta ".
Ganin wa'yannan kwarangwal din sun fara matso ta ne yasa ta fara ja da baya. ganin sun kusan cimma ta ne ta ɗiba a casa'in ta fara gudu kamar ƙafafuwan ta zasu bar jikinta,daga zaran ta juya se ta gan su daf da ita,hakan yasa tana hango wani karkashin bishiya me yalwantaccen duhu tayi sauri ta faɗa a ciki,tana sauke ajiyar zuciya.
Ji tayi abinda ta zauna akai ya fara motsawa hakan yasa ta yi kokarin tashi akai amma se macijiya Markusa ta dakatar da ita ta hanyar ce mata
" Sarauniyar gobe ina ki ke kokarin tafiya,shin ba ki san in ki ka fita waje zasu kashe ki bane!?". Nan fa hankalinta ya kuma tashi jin magana kuma Muryar mace.
" Wacece ke dan Allah kar ki cutar da ni" ta fadi hakan cikin tsoro.
" Ki saurara ni ba cutar dake zan yi ba,sunana macijiya markusa,na kasance a wannan dajin kadur din tsawon shekaru dubu biyu ina rayuwa anan,kuma bana taɓa cutar da kowa batare da ya yi yunkurin cutar dani ba,se de ina da matukar hatsari ga duk me muguwar nufi, zan taimaka miki domin zasu iya kashe ki ".
Shuru Muzaina ta yi tana sauraran maganar ta sede har zuwa yanzu a matuƙar tsorace take.
Bayyana mata kanta macijiya Markusa ta yi,se da ta ɗan razana ganin macijiya me Suffar bil adama samanta mutum kasanta macijiya.iya tsorata ta tsorata da macijiya Markusa sede ta yi karfin halin nutsuwa.
" Kar ki tsorata da ni, riƙe wannan a hannun ki".ta faɗa tana miƙa mata wani abu kamar kwai.karba tayi tana kallon sa a hannun ta..
" Shidin menene wannan,nagansa kamar kwai !?".
Murmushi ta yi kafin ta ce
" Dole ta inda ki ka fito ta nan ne zaki koma gida ruhinki dole ya koma gangan jikin ki,in ko ba haka ba awanni biyar ki ke dashi,daga zaran kin fita za su kama ki sukaiwa dodo gartamus shi kuma ze kashe ki ya bawa yaransa su yi farfesun namanki su cinye,amma wannan kwai din shine ze cece ki daga gare su domin sun sani sarai daga zaran wannan kwan ya fadi a ƙasa ya fashe to duk gabaki dayan su se sun mutu murus.
Zabi biyu gare ki,na farko.. za ki iya neman sulhu da su ta hanyar yi musu daɗaɗan kalamai in sun saurare ki tom in kuma basu saurare ki ba kin zama gawa.
Na biyu... Za ki iya fasa wannan kwan a ƙasa nan take zasu mutu zaki kuma koma gida cikin koshin lafiya da aminci ".
" A gaskiya Nagode miki sosai " tana faɗar haka cike da kwarin gwiwa ta fice a kogon ranta fess tunda ta samu abinda zata kare kanta.
Fitowarta ya yi dede da karasowan su,suna zuwa kuwa suka ɗauke ta cak basu tsaya a ko ina ba se a sansanin dodo gartamus.
Ko da isan su suka ajiye ta gaban sa, dubanta yai da firgitattun idanunsa ya daka mata tsawa
" Ke bil adama menene ya shigo dake dajin kadur".
Shuru ta yi tana aiyana wani abu a ranta,baya ta ja kaɗan ta fito da kwan guban da ta boye a bayanta. Suna gani suka fara ihu da kururuwa me matuƙar razana ruhi.
" Kar ki fasa wannan kwan na miki alkawarin zamu mayar da ke har inda ki ka fito,kar ki kashe mu,ina me dukar da wuya a gare ki".
Makirin murmushi Muzaina tayi tana suburbudawa macijiya Markusa albarka da ta ba ta wannan kwan yanda suke kururuwar rokon ta hakan ba karamin dadi ya mata ba.
Sa'ke kwan tayi ya faɗi a ƙasa ya fashe nan take wani koren hayaki ya gauraye wajen gaba daya haka suka dinga zubewa a ƙasa matattu,ita kuwa wani guguwa ne me karfi ya yi wurgi da ita.
Faɗowan da zatayi ta fado a cikin toilet din ta,zama tayi a tsakar toilet din tana karewa ko ina kallo hannunta da ta ɗan buge take mulmulawa kafin ta tashi ta fita,zama tayi a bakin gado tana me duban lokaci nan taga karfe biyar saura minti biyu,ga shi an fara kiraye kirayen sallah asuba. A maimakon ta jira tayi sallah se ta kwanta kawai tana jan bargo tana rufe jikinta harda fuskarta gaba daya.
Mai girma Sheikhy ne tare da Sheikh Abu Dhabi tsaye a gaban mudubin duba suna ganin duk wani abinda ya faru.
Hannu mai girma Sheikhy ya saka ya ja maki a kan sunar ta,.
" Tun daga yanzu mun riga da mun san wacece shugabar mu ta gobe, yanzu gwaji biyu ne ya yi saura ".
" Ya shugabana kawai ban taɓa sanar dakai bane, amma tun ranar farko da na fara ganin wannan yarinyar naji a jikina tana tare da abubuwa na al'ajabi ".
Murmushi irin nasu na manya mai girma Sheikhy yay " lokaci ne ze nu na hakan Abu Dhabi"..
Yau ta makara batayi sallar asuba akan lokaci ba se karfe takwas ta farka da matsanancin ciwon jiki.
To masu karatu anan zan dasa alkalamina se kuma in Allah ya haɗamu monday.
Yanzu labari ya soma tafiya in har kun bani haɗin kai tofa zamu tafi,in kuma kuka ki bani haɗin kai se mu hakura da wannan daddadar labarin,yawan comment din ku yawan read more din ku.
Comments,like and share fisabilillahi.🥰🥰🥰🫶