ƊAYA CIKIN BIYU

ƊAYA CIKIN BIYU

by @mrsisham12

13-15⚔️👑👑 ƊAYA CIKIN BIYU 👑👑⚔️

🔥A story of love,hatred and violence ⚔️🔥

🤍*Story and written*🤍

~By~

Aisha Abbas (*MRS 🌹 ISHAM 🌹*)

(*Yar lelen jarumai writers*).

Jarumai writers association 📚📚📚🖋️🤩

❤️🔥Page 13--14--15

" why ain’t you saying anything?”.

“ I don’t like that man at all wallahi” ta fada hankali kwance. Zaro ido wake Muzna tayi jin abinda Muzaina ta fada wai bata son Galadima Abdul aleem.

Zama ta yi Akan bed din ta “ wai Beb ke kowa bakya so,mutane fa rahama ne. In fact Abu Aleem is our uncle. Bayan Aba bamu da kowa bayan su”.

Mikewa ta yi ta nufi gadon ta zauna bisa gefenta.

“ Muzna!. Kin San meye?, bana son ki dinga yawan tuna min abinda nake da masaniya akai,yeah of course nasan Abu Aleem uncle na mu ne amma hakan baze sa in so shi ba. Yanzu bari in sa kaya se mu tafi dinning din duk da ma ke naga alamar bakya Jin yunwa.Aina ki ka ci abinci!? dan yau ba ki yini a palace ba!”.

Girgiza Kai kawai ta yi tana me rolling eyes din ta hade da aza su bisa na Muzaina da ta gama magana yanzu

“. Well shikenan na fahimta amma ko me za ki yi I must tell you the truth,abinci kuma a wajen masaurata naci gurin wata dattijuwa me kirki sosai “.

Gaba daya idanunta ta ware Tana bin Muzna da kallon al ajabi “ Muzna kina da hankali kuwa?,do you want to kill your self?,a gurin wayanda ba ki yarda da lafiyar su ba ki ka ci abinci “.

“ to meye a ciki?”.

Galla mata harara ta yi “ you’re so careless with your life”.

Girgiza Kai ta yi kana ta shige ta saka kaya da mamakinta bata iske Muzna a bedroom din ba,se da taji Karan ruwa ne ta fahimci tana toilet zama tayi tana jiran fitowarta.

Gaba daya sun hallara a dinning suna cin abinci babu abinda ka ke ji se Karan spoons.

Bayan sun kammala ne masu aiki suka kwashe hade da gyara ko’ina. Galadima Abdul aleem ya bukaci da su basa aron hankalinsu.

" Abinda yasa na tara gaba dayan ku a nan shine Gobe in sha Allah zaa yi taron gabatar da Muzna da Muzaina wa masarauta domin da yawa mutane basu San su ba. Kuma yakamata a ce sun san su. Allah ya jikan marigayiya sarauniya da kuma marigayi sarki”.

“ Ameen “ duka suka amsa,

Kallon juna jadwah da Muzna suka yi domin tunanin da suke yi ya zo daya.ganin alamun damuwa dauke akan fuskarta ne yasa Jadwah ta mata alama da ta kwantar da hankalinta.

Bayan kowa ya watse ne suka zo har bangarenta babu abinda suka sameta Tana yi face safa da marwa domin wannan gabatar dasu da zaa yi gobe tona mata asiri ne a gurin sadauki Zubair.

“ oh my god Jadwah shin dole ne yin wannan taro for goddess sake,yanzu shikenan Sadauki Zubair ze dauke ni a matsayin makaryaciya. Ya Allah gaba daya kaina ya daure “.

Itama Jadwah ta shiga rudu domin wannan taro da aka shiryasa bakaramin girgiza su ya yi ba domin ko ta halin qaqa tabbas Sadauki Zubair se ya ganta.

Jan hannunta ta yi suka zauna sannan ta kwantar mata da hankali kana ta ce

“ Gimbiya abinda ze faru shine ki je ki samu sadauki zubair ki sanar masa da ko ke wacece ze iya yafe miki,amma muddin kika kuskura ya gan ki Gobe wallahi ransa ze baci ze dauke ki maci amana. Da ya ji a gurin wani gwara ya ji a bakin ki,Sadauki Zubair yana matukar kaunar ze fahimce ki “. Tabbas tq yarda da shawaran da Jadwah ta bata domin shine kadai mafita a gareta.

Shuru ta yi Tana me daura hannunta a habarta,Tana tunanin yanda ze yi react.Kara mata kwarin guiwa sosai ta yi.

Yarima Ishaq kuwa ya baro bangarensa ya zo na Muzna domin so ya ke yi su yi magana ko da ya rike handle din bedroom dinta ze shiga maganar da ya ji suke yi na zuwa tunkarar Sadauki Zubair shi ya dakatar dashi wannan Abu ba karamin dadi ya masa ba. Wata makirar murmushi ya saki domin kuwa ya samu hanya mafi sauki da ze shiga tsakanin su batare da ya wahalar da kan sa ba,be ko shiga dakin ba ya juya izuwa bangarensa yana me murmushi lokaci zuwa lokaci.

Waya ya dauka ya yi magana dan gajere sannan ya ajiye yana me harde hannu a kirji.

Muzaina tana zaune a bedroom dinta ga system a gabanta tana video call da business partners din ta da suke kasan canada. Shigo wa dakin Aliyah ta yi da wasu bayi guda biyu a bayanta rike da kwalaye fashion.

“ barka da wannan lokaci gimbiya Muzaina “.

Batare da ta samu damar dago da kanta ba ta furta “ barka”.

“ Ummu Zaheenat ce ta aikoni da Kayan da zakiyi amfani dash na taron Gobe”.

Hallau bata dago ba ta nuna mata gefen gadonta alamun su ajiye agun .

Tabe Baki tayi ganin yanda take nuna mata Izza alama ta musu da su ajiye,. Koda suka baro bangaren Muzaina na Muzna suka nufa domin ajiye mata nata.

Basu tarar da ita a bangaren nata ba se Jadwah dake zaune bisa kujera tana chatting.

“ madam ke kuma Ina nema ki Ashe kina nan”.

“ kuma fa nacewa Hamra in de kin nemeni to Ina nan”.

“ to ai shikenan Ina gimbiya?”.

Mikewa ta yi ta nufi wajen bayin dake tsaye kan su a kasa ta karbi kwalayen Tana me fadin

“ kun yi sabani ta je a domin ta warwarewa Sadauki gaskiyar ita wacece “.

Ta fada Tana zama ta soma bude su ya hayyu ya qayyum wato iya saman su kadai da jikin Kayan ne ya samu bayyana,wasu irin arnayen daukar ido yake yi saboda tsnananin duwatsu da suka yi wa kayan yawa ga sheki da walwal da suke.

“ ya Allah gaskiya kayan nan sun masifar yin kyau fiyeda yanda Baki tunani”. Cewar Jadwah da ta bude Kayan ba Karamin tafiya da hankalinta suka yi ba se Shafa su take.

“ tun farko da na ce muku yakamata ta samu Sadauki ta fada masa komai ai kin saurarata ku Kai se yanzu da ku ka ga gobe ze gano gaskiya shine ku ka saduda “. Fadar Aliyah.

“ za ku iya tafiya”. Jadwah ta fadawa bayin,se da suka fita ne ta dawo da kallon ta kan Aliyah

“ yanzu se mu zauna mu jira dawuwarta “.

Suna zaune suna hira suka ga ta shigo jiki amace kamar wacce Kwai ya fashewa a ciki.

Duk mikewa su ka yi suka tsaya ganin yanayin da ta shigo dashi hakan yasa suka ji jikinsu ya mutu sosai domin sun san yanda suka gano tan nan sun samu sabani da Sadauki ne.

Riko hannunta suka yi hade da zama akan kujera.

Cikin jimami Aliyah ta furta “ Kiyi hakuri na San nan da zuwa wani lokaci kalilan ze sauko,yanzu ki basa lokaci ya gama fushin sa”.

“ Wallahi gaba daya jikina ya yi sanyi. Amma ga shawara me ze hana ki je ki samu Yumma ki fada mata abinda ke wakana nasan tunda ita mahaifiyarsa ce dole in ta masa magana ya saurareta “. Jadwah ta fada fuska dauke da damuwa.

Da kallo kawai take bin su cike da mamakin Jin abinda ko waccen su take fada batare da sun tsaya sun ji me take tafe dashi ba har sun yanke abinda ya faru tsakaninta da Sadauki Zubair.

“ relax guys,gaba daya kun cikani da surutu”. Nutsuwa duk suka yi suna sauraranta.

Furzar da iska tayi daga dan karamin bakinta cikin sanyi murya ta kuma furta

“ ban same sa ba”.

“ kamar ya baki sa me sa ba to Ina yaje “.Cewar Jadwah da gaba daya ta matsu taji kan zancen.

“ yup ban same sa ba,na je filin daga amma ban same sa ba ban kuma samu Arman ko hashim ba. Ina tsaye a gurin ne naga wani matashi yazo shine nake tambayar sa,nan ya shaidamin dakarun wannan masarauta gaba daya sun fita yaki,kuma Sadauki Zubair shine commander.ita kuma Yumma ta je Libya duba kanwarta babu lafiya”.

“That’s to hear ta wani bangaren abun farin cikine kin ga in ya dawo za ki masa bayani cikin nutsuwa kin fa shi baya nan balle mahaifiyarsa”.Cewar Jadwah.

Jinjina Kai Aliyah tai saying

“ hakane kam amma shawaran da zan ba ki shine muddin ya dawo ki samesa ki fada Mai komai domin boye-boyen bayida amfani “.

Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta ji bayanan su “ shikenan. Meye a cikin wa’yannan kwalayen “. Ta fada Tana bude Kayan da aka kawo mata.

“ wow Masha Allah sun yi kyau sosai”.

ENGLAND 🏴󠁧󠁢󠁥󠁮󠁧󠁿

KINGDOM OF WISDOM

Wata kyakyawar matashiyar budurwace wacce jinin turawa da Mulki ke yawo a jikinta wacce bazata wuce shekara 20 ba a duniya tana tsaye hannunta da doguwar wuka irin ta masarauta da ake yaki da ita se jujjuyasa take yi cikin kwarewa domin kuwa ta horu da irin wa’yannan horon fada hakan yasa ta girma cikin jarumta. Jikinta na sanye da riga da wando fari sun tsuketa se dede cikinta dake dame da belt baki jan gashin kanta ba kwance a gadon bayanta. Se da ta gama tukuna ta mayar da wukar cikin gidanta tana me cusa hannunta cikin jan gashinta tabe fuska ta yi alamar ta dan gaji hannu ta Mika alamar a mika mata abu da sauri wata baiwarta ta so ta mika mata towel da glass of water.

Dan goggoge zufa tayi tasha ruwan kafin ta soma tafiya cike da kasaita bayi kusan goma ne suka bi bayanta Kai tsaye wani hadadden part ta nufa tunda ta shiga bayi suke kwasar gaisuwa,bedroom din ta da ya gaji da haduwa ta shiga cikin nutsuwa ta soma cire rigar jikinta yayi saura bra seda ta cire Kayan jikinta sannan daura towel ta shiga toilet tayi wanka bayan ta fito ne ta samu masu mata hidima suna jiranta zama tayi a kujera suka soma goge mata jiki hade da shafa mata lotions masu tsada bayan sun gama shiryata ne cikin doguwar riga matsatstse brown color sosai ta fito mata da shape dinta takalmin kafarta hill ne sosai Wanda ya Kara mata tsayi,sosai ta yi kyau se baza kamshi take yi.

Take mata baya suka yi izuwa Palace a hanyar ta zuwa ne wani servant ya dakatar dasu ta hanyar sunkuyar da kan sa hade da fadin

“ PRINCESS GABRIEL.,QUEEN na da bukatar ki a church domin gabatar da adduar neman tuba”.

Yar siririn tsaki ta ja cike da shagwaba ta ce “ ita da su waye a church din?.”

Cike da girmamawa ya bata amsa “ tare take da me girma president David Abraham da matar sa excellency Katrina Abraham”.

Babu yanda ta iya domin ba wani son ziyartar church take ba,daga bakin church din taji pastor nata zuba preaching.

Dago Kai QUEEN JESSICA ta yi ta daura idanunta akan yarta daya tilo wato Princess Gabriel.

“ Ƴata Gabriel “ ta fada tana takawa izuwa gareta rungumeta tayi tana riko hannunta suka karasa gaban pastor. Murmushi President David ya yi yana shafa kanta “ lokaci na gudu sosai kin ga har surkarmu ta girma” ya fada yana kallon matar sa,murmushi tayi hade da rungume Princess Gabriel.

“ barka da warhaka Uncle David nayi kewar ku sosai” Princess Gabriel ta fada a shagwabe

“ hhhhh yata mu ma mun kewar ki sosai shisa muka zo domin cin abincin Safiya tare da ku”.

Queen Jessica dake kallon su ne ta yi murmushi.

Bayan pastor ya gama adduar ne President ya dubesa ya ce “ Pastor Emmanuel Ina so a duba lokaci mafi albarka da zaa yi wa wa’yannan yara namu baiko domin in san yaushe zan fadawa Jay ya dawo gida “.

Cikin gamsuwa Queen Jessica ta jinjina kai. rufe ido pastor ya yi yana kirge da yatsunsa kusan mintuna uku yana a haka kafin ya bude ido.

“ Mai girma president wato lokaci mafi sa albarka shine kwana talatin masu zuwa ranar da zaa samu lumshewar rana,zaka iya cewa Jay ta dawo gida domin su samu fahimta shi da Princess Gabriel “.

Sosai su ka yi farin ciki da Jin abinda pastor ya fada domin sun jima suna jiran wannan rana domin kara zumuncin dake tsakanin su ta hanyar had’a yayansu aure.

Queen Jessica ita ce Sarauniyar England kuma duk duniya Ƴa daya Allah ya bata wato Princess Gabriel. President David Abraham shine shugaban kasar England in da suke da dan su daya ne Suna JAYSON suna mishi lakabi da Jay Wanda yake Karatunsa na masters a kasar Turkey.

Babban liyafa aka tanadar a teburin cin abinci kalolin abinci yafi ashirin Wanda aka tanadar.bayan sun gama breakfast ne Mai girma president suka tafi.

“ Mom ta ya za ki yarda da wannan hadin auren bayan na ce miki banason shi,ni da shi babu jituwa tsakanin mu tun muna yara ya tsaneni kuma ni ma haka. Dan haka ni bazan taba auren Jay ba shine kawai “.

“A saboda hakane Ai yasa muke so mu had’a ku auren ai, tun kuna yara mu ka yi alkawarin had’a ku aure in kun girma , sannan kar ki manta tun kafin a haifi ki nida president David abokai dan haka ki kwantar da hankalinki auren ki da Jayson kamar an yi an gama “.

Cike da sangarci ta hau bubbuga kafarta a kasa tana kwakulo kuka

“ Mom wannan sam ba adalci bane,bazan taba lamunta ba” ta yi maganar tana me barin bedroom din Queen Jessica.

MASARAUTAR BAYAAN

“ my Haseena na yi missing din ki matuka yaushe za ki zo”. Ta cikin wayar ta jiyo sautin dariyar Haseena tana fadin

“ kar ki damu Ina nan zuwa amma ba nan kusa ba gaskiya,ya ki ke ya jarababbiyar twin din ki!?”. Dariya sosai Muzna ta yi Jin Abinda ta ce.

Bude baki tayi zata yi magana Muzaina ta shigo dakin cikin shirinta na bacci kashe wutar dakin tayi ta furta

“ ki ajiye wannan wayar mu kwanta “.

Jin muryarta da Haseena ta yi ne yasa ta fadin

“ speaking of the devil “.

Sake tuntsirewa da dariya tayi a Karo na biyu. Watsa mata Harara Muzaina tayi ba shiri tayiwa Haseena sallama

“ Haseena ta ki yi bacci cikin aminci “.

Ajiye wayar tayi bayan ta sakata a silent ta je jikin Muzaina ta kwanta hade da musu addua.

Washe gari duk in da ka duba a cikin Bayaan se had’a-hadan had’a taro a ke yi Ana ta preparation a babban filin masarautar me girman ika hamsin.

Karfe 2:30 an gama duk wani shiri kawai Gimbiyo a ke jira,suna can ana shiryasu sun sha light make up.

Hamra dake make up artist ce tana taya masuyiwa Muzna kwalliya gyara mata gashin kanta da aka mayar dashi baya gaba daya ya kwanta se aka dibi gashi kadan daga gefen hagu ta kitsesa haka dama shi ta kitse guda daya ta kwantar dashi aka gashin ta kullesa da sauran. Wani mayen head chain da ya sha stones ta saka mata daga keyar gashin nata se walwali yake.

“ Gimbiya na rantse da Allah ban taba ganin masu kyaun ku ba,an ya zaa samu kuwa?” Dariya tayi jin shirmen Hamra din.

“ you’re so funny Hamra”. ta fada Tana shafa head chain da ta saka mata chains din ta shafa kafin ta cire hannunta tana kallon kanta a mudubi.

Se da aka gama yiwa gashi kwalliya sannan aka miko mata kaya nauyin da ta ji sun yi ne yasa ta ce “ tabb dijam wannan nauyi haka”.

Dan dariya masu kwalliyar suka yi.

Fice wa suka yi a dakin su ka yi domin bata damar saka Kaya.

Warware Kayan ta yi taga abubuwa da yawa cike da rashin fahimta ta tsaya Tana kallon su domin yanda taga abubuwa daya wa yasa ta rude domin tasan babu yanda zaa yi mutum ya shirga wannan Kaya gaba daya a jikinsa.

“ Hamraaaaaaaa”. Ta kwala kiran sunan ta. Shigo wa tai Tana tambayarta meyafaru

“ ke ni ban San ta Ina zan fara saka wannan Kayan ba naga pieces da yawa ga duwatsun da ya Kara musu nauyi na fitina”.

Dariya ta fashe dashi kafin ta ce “ dama na yi tunanin haka in ba an yi guarding din ki ba ba lallai ki iya sawa ba”.

Harara ta watsa mata “ kin San da haka shine zaki tafi ki barni da su”.

“ afuwan “

Daukar wata yar karamar Riga da iyakacinsa cibiya tayi ta mika mata. Bayan ta sane ta juya mata baya ta hade mata botul din rigar.

Wani skirt me tsayi yana nan pencil wanda ya haura saman cikinta ya rufe ciniyarta dake waje ta saka.

A ciki wanda ya kasance yana da tsayi sosai Jadwah ta dauka ta sama nada mata shi Akan skirt din se ya yi fadi sosai da girma Wanda ko kafafunta baa gani.

Da ta gama nada mata shi ne ta dauki wani sarka na zallar zinari Wanda ake ado dashi a ciki Ana daura sa ne a saman Kaya,nan ta daura mata shi,mayafin Kayan da ya gaji da haduwa ne me girman gaske ga kananun stone da manya da aka watsa a jiki yana nan shara-shara ana ganin komai kamar net ta saka mata akai Wanda tsayinsa har yana ja a kasa zat ta fito tamkar Sarauniya. Irin kyawun da Muzna ta yi duk yanda ka so ka fada tofa Baki baze iya zayyanawa ba kamar ba mutum ba tsabar wutar kyau.

“ ya Allah wallahi kin yi masifar kyau”. Cewar Jadwah da ta gama shiryata,murmushi tayi domin ita kanta tasan tayi kyau base an fada mata ba.

High hill ta saka kalar kayan tayi fesa performs masu dadin kamshi. Suna tsaye tana mata hoto wata baiwa ta shigo ta sanar dasu da yanzu zaa tafi

Bayin dake take musu baya ne suka rike mata bindin mayafinta.

A falo suka tarar da Muzaina da ita ma ta shirya cikin kalar kayanta komai sak iri daya babu abinda ya banbanta su se color Kayan na Muzaina orange ne da touches din white and peach,while na Muzna is orange da touches din silver da pink.

Zama ta yi a gefenta tana mata whisper a kunne

“ kin yi kyau sosai my Muzaina “

“ same to you honey”.