12
KURURUWA A KUNNEN KURMA🥀 🥀
A 2025NOVEL
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHEEM
(OUM AMEER)
Wattpad:@ Ummu-Amir
Arewabooks: @Aminatuibrahimbawa
From d experience writer of:
Zaytoonah
Abarwa rai
Gudun wuce sa'a
Kibiyar so
Kulsum
Bahiyya
Nuudarr
Littafin kuɗi ne. #500 kacal, zaki iya turawa ta wannan asusun 3132703269 Ibrahim Amina Bawa, sai ki tura shaidar biya ta wannan Layin ***. 🙏🙏
FREE PAGE 12
"Safnah...! Safnah.." A hankali na shiga buɗe idanuwana waɗanda suka yi min mugun nauyi tsabar yanda nasha kuka na kalle shi for some minute, sai kuma na waiga na fara kalle kalle yayin da ƙwaƙwalwata ta shiga tsananin ruɗanin son tuna miye yake faruwa dani...Muryan Naseer na sake tsinta cikin tausasawa yana faɗin. "Ta shi ki yi Sallah ƙarfe bakwai na safe ake magana". Wa su irin hawaye ne masu zafi suka wanke min fuskata jiki sanyaye na ce. "Ƙarfe bakwai na safe ne yanzu Naseer? Miye ya ke faruwa dani? Kai na ya na mini ciwo sosai tamkar zai tsage gida biyu haka ni ke ji...." Rungumo ni yayi murya kamar yayi kuka ya ce. "Babu abinda zai same ki sai alheri Safnah, ta shi kije ki yi sallah ki shirya mu sauka ƙasa ki zauna kafin na je na dawo" Da ƙyar na iya miƙewa tsaye sanadiyyar wani mugun tsami da naji jiki na yayi tamkar an naɗa min duka, da ƙyar na iya ɗaga ƙafata ta dama itama akan bala'in zogin da ta ke min wanda ban san dalili ba,ganin ina tangal-tangal kamar zan faɗi ya sa Naseer yayi saurin riƙa ne muka shiga toilet ɗin a tare, ruwa ya haɗamin masu ɗumi ya ce na shiga nayi wanka ko zan samu jikina ya saki, yana tsaye wurin nayi wanka na kambala sannan na yi alwala muka fito ya bani wata doguwar riga ta roba na saka da hijab na yi sallah, daga nan muka sauka ƙasa kamar yanda ya ce, da kanshi ya je ya haɗo min Tea mai zafi ya bani ya ce in sha. Kallon shi na yi hawaye cike da idanuna na ce. "Naseer wani abu yana faruwa dani ko?" Zaunawa yayi dab da ni ya kalle ni cike da ruɗani ya ce "Ba zaki iya tuna komai ba Safnah" Girgiza kai na nayi tare da runtse idanuna gam da nufin don dole sai na tuno abinda yake faruwa....saukar hannun shi akan babban ɗan yatsan ƙafa ta inda na bugu yasa na yi saurin buɗe ido tare da janye ƙafar tawa da ƙarfi ina mai duba yatsan, akaifar wurin har ta ɗago sosai tsabar yanda na je direwa daga kan gado a daren jiya na faɗo ba daidai ba.... "Sannu kinji" Hawaye na na share ina kallon shi na ce "Miye ya ji mini ciwo a ƙafa na? Nayi iya nazari Naseer but I can't recall anything, kai ma ɗin baka san miye ya faru dani ba? Can ƙasan rai na ina ji bani da lafiya akwai abinda ya ke damuna..." Da sauri ya ƙanƙame ni cikin jikinsa kamar zai yi kuka ya ce " Miye haka wai! Na ce miye haka for goodness sake? We just got married 2days ago, but why did we ended this way?.... Look Safnah! Ɗago Ki kalle ni kinji " Ɗagowa nayi na kalle sa kamar yanda ya ce,tuni idanuwansa suka canja launi, muryar sa na wani irin rawa tsabar ɓacin rai ya ce." Babu abinda zai same ki I promise you this, ki yi haƙuri in sha Allah babu abinda zai same ki, ko ma mutum ne ko aljan ko waye shi ba zai taɓa iya nasara akan mu ba in sha Allah, kiyi haƙuri kinji ko, zan fita yanzu zanje wurin Malam na ji" Gyaɗa kai na nayi na ce "Allah ya tsare, a dawo lafiya" Daga haka ya tashi ya haura sama ya ɗauko wayarsa ya wuce. Ta shi nayi na koma sama zuwa ɗakina domin ji na nike jiki na tamkar ba nawa ba, rigar na cire sannan na matsa gaban madubi ina bin ko ina na jikina da kallo, ta saman ƙirji na ga tsage-tsage kamar yatsun mage sun karce ni, ga wurin gwiwa ta itama ta kumbura wurin yayi ja, sosai ni ke cikin damuwar wai miye ya faru da ni,.... Jiya.. Jiya nike ta ƙoƙarin tuna rayuwar da nayi but babu abinda ta ke hasko min sai ni da Aydah muna fira muna dariya, daga baya kuma Naseer ya dawo... Daga nan kuma ban tuna komai ba.... Wayata da ke kan side bed drawer ce ta hau ɓurari alamar ana neman magana da ni. Rigar na ɗauka na mayar sannan da ƙyar na iya matsawa na ɗauki wayar tare da zaunawa edge ɗin gadon na yi receiving call Wanda yanzu shi ne kira na uku da ya shigo... Murya can ƙasan maƙoshi na ɗaga na ce "Hello Mama" Ranta fes! Cike da arerewa tayi guɗa sannan ta ce " Yanzu dai nasan kin zama Naseer ya zama ke idan da rabo ma an samu er albarka ta, Kinga ana farawa idan an fara da en biyu kuma duka 'ya' ya maza shi ke nan an gama...." "Mama yaushe zaki zo?" daga can tace. "Sai gobe idan Allah ya kai mu Safnah, yau Hajiya Hibba suka ce zasu biyo yanxu suga ɗaki kafin su wuce, shi ne nace su bari na kira naji idan kun tashi bacci" Gyaɗa kaina na yi tamkar ina a gabanta na ce "Eh muntashi har ya fita ma" Cike da mamaki ta ce "Ke har ya fita fa kika ce? Shi ko miye yake nema a duniyar nan da har zai sa yayi asubancin fita haka?" "Wallahi ni ma ban sani ba ya dai ce zai fita ya dawo" Gyaɗa kanta tayi sannan ta ce "To shi kenan, nima dai goben zan shigo domin ranar Talata za'a tafi da Xuhra gidan auren jalli-jogan da suka naniƙa mata, oh mtsw! Wallahi sun dai jazamin salalan tsiya, da so nayi sai na kwana biyu na huta sannan in koma Gusau, to amma ina! Sun ɗauki ɗiya sun baiwa matsiyaci wanda nasan ko wurin kwanan su Hajiya Kakale babu a cikin kurkukun gidan sa dole wahala a kai na da gidana zata ƙare" Gabana ne ya yanke ya faɗi jin ta ambaci sunan Xuhra, sai dai na kasa tuna komai ne hakan yasa na ce "Mama Xuhra da gaske Xunnurain ɗin aka aura mata??" "A'a! Yau na jiki da wani zance,wani abu kika sha ne da har yasa kika manta da rana ɗaya aka ɗaura muku shi.. Ke ni dai sai an jima kada Naseer ɗin ya dawo ya ji ni tun yanxu girma ya faɗi." jin ta tsinke wayar yasa na faɗa kan gado na kwanta shiru tare da runtse idanuwana. Gefen su Ummah kuwa, ƙarfe takwas na safe suka fito daga Gusau zuwa Sokoto, gidan wani cousin brother ɗin Ummar suka wuce suka ci abinci, ko hutawa Umma bata jira sun yi ba ta gargaɗasu zuwa kasuwa wanda ba su dawo ba sai ƙarfe bakwai na yamma. Sun danƙaro kaya daidai ƙarfin kuɗin su, bayan sun gama sallar isha Siddeeq ya kira Xunnurain ya ce ya sanarwa gidan su Xuhra cewa su Hajiya za su je da safe ƙarfe goma idan rai ya kai. Usman ɗin na gama waya da Siddeeq ya yi shiru yana tunanin taya zai iya kiran mutuanen gidan bayan ya wuce ba tare da yayi musu sallama ba. Ganin kiran Ummah yasa yayi saurin yankewa cikin hanzari ya kira Umar ya ce mi shi su Hajiya za su shigo gidan gobe. Ni kuma, a hankali na lallaɓa zuwa closet na canza kaya na zuwa wata babbar Atamfa ɗinkin riga da skirt wanda yayi matuƙar karɓar jikina, sai dai da ka kalli fuskata kallo ɗaya zaka fahimci cewa ina cikin damuwa. Ina nan zaune banfi 1 hour ba sai ga baƙin da Mama ta ce an shigo min da su, duk yanda suka saki baki suna ta famar santin gidan kawai biye nike da su tamkar mutum mutumi, domin har suka yi min sallama suka tafi hankali na baya tare da su, na dawo na zauna ban fi 10mnt ba sai ga kiran Aunty Rabi'atou ta ce min suna babban parlorn ƙasa suna jira na, har cikin raina naji daɗin zuwan su shiyasa jiki na rawa na ta shi na sauka zuwa ƙasa. Tsaye na yi na fara bin su da kallo, Yah AbdulMalik, Yah Usman, Deen, Sa'adu, Aunty Rabi'atou da kuma Yah Miƙdad wanda ya ce bikin mu da kwana ɗaya zai juya ya koma.... Sa'ad da Deen ne suka ɗauki ihu lokaci ɗaya suna faɗin. "Iyyeh! Kaga Amaryaaahhh ta ango" Jikin Aunty Rabi'atou na faɗa ina mai fashewa da kuka kawai ba tare da nayi magana ba. Bubbuga bayana ta fara cike da tausayi ta ce "Eyyah sorry kinji! Da haka kowa ya fara wanda a hankali with time in sha Allah ke ma zaki saba" Yah Abdul ne ya ce "Hmm! Wannan kukan gulma ne kawai take yi,a kwana biyun da tayi nan gidan akwai wanda ta ɗauki waya ta kira da sunan tayi missing na shi?" Cike da zolaya Deen ya fashe da dariya ya ce "Ina! Ai wallahi ina kallon ta ranar da za'a fito da ita ko kaɗan ba ta yi kuka ba" Yah Miƙdad ne ya ce "Wannan daban Deen, dole akwai kewa musamman idan kowa ya koma inda ya ke, ga shi za ta je da nisa, tabbas haɗuwa zata yi wuya, muna fata Allah ya bada zaman lafiya da zuria ɗayyaba" sai yanxu Yah Umar ya buɗe bakin sa ya kira sunana ya ce "Safnah!" Ɗagowa nayi na kallesa sannan na ce "Na'am" Cikin nuna kulawa ya ce "Are you alright?" Ido na na sauke ƙasa sannan na gyaɗa kai na ce "I'm fine" kallon yatsan ƙafa na yayi ya ce "To miye ya same ki a ƙafa ga shi har ƙumbar ki ta ɗago" kallon inda yake kallon na yi nima sannan na ce "Datsewa nayi da drawer ban sani ba" Ɗan matsawa baya Aunty Rabi'atou tayi tana mai kafe ni da ido ta ce "Ni duk sai na ganki sukuku kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki, Safnah ko dai akwai wani abu?" Da sauri na girgiza kai na na ce "Ba komai Aunty kawai wannan ciwon ne na ƙafata yake min zogi..." daga haka na miƙe naje na yi magana da ma'aikata na na ce su kawo musu kayan taɓawa na musamman sannan kuma su shirya mana table ɗin lunch. Nan muka zauna muna fira wadda duk rabin firar tsakanin su ne ni dai kawai nayi shiru ina bin su da ido, zuciya ta fal da farin ciki domin take naji duk wani abu mai neman barazana da rayuwa ta ya fice tamkar komai bai faru da ni ba... Muna nan har lokacin sallah yayi suka fita suka yi sallah suka dawo daga nan muka zauna table a tare muka ci abinci gwanin burgewa tamkar kada lokacin ya wuce a gare ni haka nike ji. Suna nan suna batun tafiya Deen duk ya bi ya dameni da tambaya akan ina Naseer kwatsam sai gashi ya shigo. Cikin mutuntawa ya tarbe su ya zauna suka gaisa daga nan ya tashi ya haura sama, a zuciyar shi ji yake tamkar yayi musu bayanin abinda ya faru da ni kwana biyun nan but kuma kada ya sanya su a damuwa su kasa samun natsuwa a kanta, tunda har ya kira Malam yace mi shi bayanan amma gobe yana dawowa zai zo gwanda ya bari ya dawo su gani. A mota biyu suka zo, munjima gefe ni da Aunty Rabi'atou tana ƙara bani shawarwari akan zamantakewa daga ƙarshe tayi min sallama tace zata dawo sati biyu idan ta samu time, suma haka muka yi sallama da su musamman Deen har da hawayen sa jin cewa zai yi kewata ba kaɗan ba, nima kuka sosai nike tamkar wadda aka ce ba zan sake ganin su ba a rayuwa sai da ƙyar aka samu Naseer ya lallaɓa ni muka koma ciki, suma kuma en uwan nawa ganin yanda Naseer ɗin ya saki jiki da su sannan yana nuna min tsantsar kulawa hakan sai ya sa suka ji hankalin su ya kwanta sosai, duk mai wani tunani sai ya kawar musamman Yah Umar da ya ke ji a ransa cewa bai yarda da amsar da na ba shi ba akan ciwon da naji. Muna shiga ya ja hannuna muka shige ɗakinsa yace min zai yi wanka, ina nan har ya gama ya shiryawa sannan ya sa aka kawo mana abinci nan ya ci don ni ban wani ci sosai ba, bayan ya kambala ya kalleni ya ce "Safnah miye ya ke miki ciwo yanxu?" ƙafana kawai na nuna masa sannan kai na nace "Tun ɗazu kai na yake min ciwo sosai" gyaɗa kansa yayi cike da tausayawa ya ce "Sannu kinji, zai dai na in sha Allah. Batun tafiya ta I decide to go alone with you, so you don't have an option because ba zan iya barin ki yi nisa da ni ba?..." Da sauri na gyaɗa kai na nima nace. "Ni ma na fiso na bika domin ji ni ke kamar wani abu zai faru dani idan baka nan..." Hannaye na ya jimƙe a nasa sosai sannan ya ce "Ba abinda zai faru da ke sai alheri Safnah, yau ma shiyasa na dawo tun yanzu babu inda zan fita muna nan a tare" Ƙoƙarin tuno wani abu ni ke sai na kalle sa na ce "Ka dawo da wuri ne domin wani abu ya faru dani ko? Miye ya ji min ciwo a ƙafana?... Kalli nan" janye wuyan riga ta nayi na nuna masa yaƙushin da na gani sannan na ce "Kaga tsagu a nan ko? Sannan duba Knee ɗina ka gani yana min zafi har ma ya ɗan kumbura,ji ni ke kamar ba ni ba..." Kallo na yake tamkar zai fashe da kuka tsabar yanda abin yake masa ciwo a zuciya,' wannan wane irin abu ne? Duk haukar da yi ta yi jiya tana zuba ihu tana kiran kada na matso kusa da ita bani ba ne ace ta kasa tuna komai' tambayar da yake ta yi wa kansa kenan domin abin yayi matuƙar ɗaure masa kai, mun sha dambe ba ɗan ƙarami ba wurin ganin ya rungumo ni ni kuma sai zillewa nike wanda sai da muka sha matuƙar wuya ni da shi sannan ya samu yayi nasarar kamani ya riƙeni gam a jikin sa ina ihu ina sabbatu har bacci ya ɗaukeni, shi kuma yana nan zaune har asuba bai samu ya runtsa ba ko sallar subhi a nan ɗakin yayi ta tare da ni.... "Naseer baka ga ciwon da nike nuna maka ba ne?" Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya jinjina kansa cikin damuwa ya ce "Kanki ne kika faɗamin cewa yana miki ciwo daga nan kawai sai kika faɗi ƙasa, so may be stressed ne ya miki yawa saboda kinga an daɗe ana ta jiganiyar buki" "To amma miye ya haɗa faɗuwar da nayi da wannan yaƙushin Naseer?" Janyo ni yayi zuwa jikinsa yana faɗin "Nima I don't know about it Safnah, may be kin faɗa ba daidai ba ne wani abu ya karce ki, ki yi shiru muyi bacci kinji, kada ki cika surutu kan ya ƙara miki ciwo" Shirun nayi kamar yanda na ce muka kwanta wanda ban jima ba bacci ya sace ni. Xuhra kuwa,tunda aka shaida ta auren ta da Xunnurain ta kwanta zazzaɓi mai zafi tsabar damuwa, ko baccin kirki ta gagara yi sai yawan tunani, Mummynta sai lallaɓa ta take ƙarin sauƙinta ma ƙanwarta Asma'u ta zo tun ranar ɗaura auren tana tare da ita tana ƙara kwantar mata da hankali. Tana nan zaune akan sallaya bayan ta samu ta rarrafa ta sallaci magrib da isha sai ga Mum Hindou ta shigo ɗakin. Ɗagowa Xuhrah tayi ta kalle ta cikin sanyin ta tace. "mummy ina wuni" gefen Gado ta samu ta zauna tana mai ƙureta da kallo ta ce "Xuhra, Aydah ta sanar min ashe baki ji daɗi ba" ƙara yin ƙasa ta da kanta tayi ta ce "Ɗan zazzaɓi ne but yanzu ya ma sauka" Saukar da murya Mummy Hindou tayi ta ce "Xuhra! Auren nan na san amince masa kawai kika yi domin ba har cikin zuciyar ki ba, to idan kin san cewa zaki cutu ne kawai ki faɗamin ni kuma zan san yanda zanyi dole ya baki takardar ki.... To idan ma ba mugunta ba dan Allah dan annabi ina ke ina wannan matsiyacin? Saboda tsabagen son zuciya irin na ɗan adam kyautar na isa kuma ban isa ba kawai ka aurawa 'ƴarka mai kuɗi ka zo ka ɗauki er wani ka aurawa matsiyaci saboda kawai hassada da baƙin ciki... " A hankali sautin kukanta ya fara tashi jin Mummy Hindou ta sosa ma ta in da yake mata ƙaiƙayi, wallahi tun ranar da aka ɗaura mata aure da shi instead of taji salama sai ma wani ƙara jin sabuwar tsanar sa da ta zo ta tokare mata maƙogoro, tabbas idan har Mummy hindatou zata taimaka mata ta rabu da wannan auren ba zata taɓa daina gode ma ta ba har iya ƙarshen rayuwarta. Ganin cewa kalamanta sun yi tasiri yasa ta ƙara burewa taci gaba da faɗin. "Ai wallahi Hayatu dai an yi azzalumi, idan ba zalunci ba taya zaka nuna fin ƙarfi akan er da ba kai ne ka haife ta ba,...." Shigowar Hajiya Kakale ita ce ta katse mata hanzari lokaci ɗaya tayi tsit! tamkar an anyi ruwa an ɗauke... Ita kuma hajiya Kakale a sheƙe ta shiga kallon ta har ta iso gabanta ta tsaya cikin masifa ta ce." Ke kuma Hindatou sharrin da zaki bi mu da shi kenan? Mun samu Allah ya rufa mana asiri an aurar mana da ita cikin lumana shi ne kike neman tarwatsa mata rayuwa ki sa ta fara tunanin zawarci da ƙaramar ƙurciyar ta..." Cikin neman kare kai Mummy Hindou ta ce." To ni Hajiya miye nawa a ciki? Ganin niyyi ana neman a cutar da ita shiyasa na.... "." Wallahi sai na koɗa miki mari Hindatou! Ke ar xiki ma kika ci darajar Ibrahim ɗin da Umar ne wallahi da sai mun kwashi en kallo da ke. Daman zaman nan da tayi ƙasar waje ba ƙaramin bani baƙin ciki ya ke ba, kullum sai na yi addu'a Allah ya gwadamin auren ta ko hankali na zai kwanta, ga shi kuma Allah mai jin kukan bayinsa ya tausaya min ya amshi roƙo na shi ne zaki zo don rashin tsoron Allah ki na hure mata kunne?... " Ɗagowa Xuhra tayi ta kalle ta murya a ƙasa ta ce" Dan Allah Hajiya ki yi haƙuri.... " harara ta maka mata ta ce " Ke rufa min baki kinji ko? Ai duk kece babbar munafukar, miye na zaunawa kina raira mata kuka sai ka ce ita ce zata gafarta miki... " Ita ma dai Aydah da ke tsaye bayan ta tun ɗazu taɓe baki tayi ta ce." Hajiya fa duniyar ta yanxu ta dawo kowa abin ƙwarai ya ke so, kuma idan son samu ne gidan kuɗi shi ne babban gata.... ". Waigowa Hajiya Kakale tayi tana mai yi mata kallon uku saura kwata tace "Lokacin da ubanki ya auri uwarki miliyan nawa ta kuɗi ya ke da ita? Mai kuɗi mai kuɗin banza mai kuɗin wofi! Rufin asiri da kwanciyar hankali shi ne aure matuƙar dai namiji ya tsare miki ci da sha da sutura ya kare miki mutuncinki da na danginki da kuma mutuncin sa shi karan kansa, bayan shi ki faɗa min miye a ciki ake nema?.... Sai kuma ta juya gun Xuhra ta ce "Faɗimatou! Kiji da kyau Wallahi in sha Allahu Usman shi ne mijin ki har mutuwa, ki daina ma ɓatawa kanki lokaci suna tsayawa sauraren shaci faɗi na banza da wofi, kuma duk wanda ba da alheri zai zo wurin ki ba wallahi idan na sake kama mutum yana yi miki huɗubar shaiɗan sai na ci mutuncin sa, duk abinda za su faɗa miki ki ɗauke shi tamkar kururuwa ce su ke yi a kunnen kurma wadda ba ta da amfani. Ta shi mu tafi sashen mahaifinki ina so in yi magana da ke a gabansa" Ba musu Xuhra ta miƙe ta bi ta wuce simi-simi tayi gaba ita kuma ta bi bayan ta, Hajiya Hindou dawowa tayi tamkar an tsoma kaza a ruwan zafi domin hajiya Kakale ba ƙaramin casting ta buga mata ba, daman tun sun san ko wacece Hajiya Kakale, mahaifiyar Mummy Saratu ce wato kakar Xuhra, Bafulatana ce asalin Bafulatana sai dai me Sam bata da kawaici kuma bata da haƙuri, wani lokacin idan abu ya haɗa ta da mutum sai dai ta riƙa faɗa mi shi cewa kunya gareta bata da tsoro, ko yau ne ta fara ganin ki kayi ba daidai ba sai ta faɗa maka gaskiya tun can asali ballantana yanxu ga shi an haɗa da tsufa sai abin ya cakuɗe yayi mata yawa.... Kallon Mummy Hindou Aydah tayi ta ce "To mummy what are we staying for? Tunda har sunga zasu iya haɗiye gatarin sai a sakar musu ɓota, ni dai daga zaran na raka ta gidanta na dawo shi ne dole ina dawowa zan koma school sai lokacin da kuma ta ganni, Allah ya ba su sa'a" ficewa suka yi daga ɗakin wanda har yanxu ita dai Mummy Hindou gaskiya ma ta hana mata yin magana. Ni kuwa, Washe gari lafiya lau na tashi sakamakon baccin da na samu daren jiya wanda na jima banji daɗin bacci irin shi ba wanda ban san miyasa ba, duk tsoron da nike ji da wani yanayi marar daɗi duk na dai na ji kamar ba ni ba, amma kuma abinda na lura da shi gaba ɗaya ƙwaƙwalwata ta kulle bana iya tuna abu mai nisa tamkar wadda ake sarrafawa zuwa wata duniya. Bayan na kambala sallah kwanciya na sake yi akan gado ban farka ba sai da naji Naseer ya shigo yana ta shi na ya ce "Safnah ki tashi baccin nan ya isa haka, ƙarfe goma na safe ake magana, tashi muje ki yi breakfast" miƙewa na yi ina faɗin "Sai na fara yin wanka tukunna domin jiya baki ɗaya banyi wanka ba" Girgiza kai yayi cike da mamaki ya ce "Gaba ɗaya jiya baki yi wanka ba fa kika ce Safnah" Gyaɗa kai na nayi na ce "Eh," Jinjina kai yayi sannan ya ce "OK, to je ki yi ganin ina jiranki, ko na rakaki ne?" girgiza kai na nayi alamar a'a sannan na wuce zuwa toilet ɗin. Ko da na fito har ya ciro min wani lace mai bala'in kyau yana murmushi ya ce "Wannan ɗin zai miki kyau sosai, ina fata na iya zaɓe" murmushin nima na mayar masa na ce "Sosai ma, thank you so much" daga haka ya taimaka min da kansa na shirya muka je ƙasa muka ci abinci,bayan mun kambala muka kewaya can baya cikin wani irin haɗaɗɗen garden wanda ya ji shuke shuke kala da kala na ƙasashen waje, ga wa su kalolin bolb masu bada wani kalar haske gwanin burgewa tamkar ba safiya ba ce, murmushi ya sakar min ganin na saki baki da hanci ina kallon sabuwar duniyar da na tsinci kai na a ciki... "You like the place right?" Da sauri na gyaɗa kai na nima ina murmushin na ce "The place is so beautiful and breathtaking, thank you so much you light my day" Hannuna ya ja muka fara kewaya wurin wanda ya zamto tamkar wata duniya wadda ban san ma yanda zan fassara ta ba, wurin ya ƙayatu iya ƙayatu... In da wasu kalolin tsuntsaye ke kewayawa acan naja burki ina ta kallon su gwanin sha'awa.... Gefe ya koma yana making call wanda daga baya ya juyo ya ce "Safnah muje Mama ta iso" Naji daɗi sosai a raina jin cewa Mama ta zo ta ganni. Muna isowa na tarar da ita da kuma Deen, rungume ta nayi ina hawaye wanda ban san dalili ba na ce "I miss you Mama na" Dariya Deen yayi ya ce "Mama ko jiya fa haka tayi mana, yanzu sai na ga ta dawo tamkar wata ƙaramar yarinya mai saurin kuka" Murmushi Mama tayi ta ce "Deen ba zaka ga ne ciwon da yake rayuwar mace ba a lokacin da tayi nisa da iyayen ta da sunan aure, sai dai a hankali ake sabawa har ya koma jiki". Sai yanxu Naseer ya ƙara so cikin parlourn ya duƙa har ƙasa ya gaishe ta cike da girmamawa, bayan sun gama gaisawa ya ce "Ai jiya da muka je an ce kina can da baƙi shiyasa ba mu shiga ba" tana dariya ta ce "Haka fa akayi, ƙawaye na ne an gama hidima ka samu ka sallami jama'a, kuma a irin wannan shahararren buki na ku Kaga ya Kamata duk yanda ya samu hallara a biya masa kudin mota har da na guzuri ko kuma a saka shi mota a kai shi har gida..." Wani kallo Deen ya bi ta da shi na ban mamaki, sai da yaji tayi shiru sannan ya ce" Amma Mama duk wanda ya zo ai don Allah yazo ba dole sai an bashi kuɗin mota ba" "Eh to, amma ai ba wani abu ba ne kai Deen duk yana daga cikin abinda zai ƙara ɗaga ƙimar su da daraja a idanun mutane.." Shi dai Naseer Murmushi yayi ya ce "Wannan gaskiya ne Mama, ba matsala duk wanda yake buƙatar kuɗi ai sai a ba shi...." Taɓe baki Mama tayi ta ce "To in da fa akwai kuɗin, to ina fa! Duk hidimar ta lashe laƙume komai, wallahi Naseer kuɗin nan yanda kasan an kunna musu wuta haka suka ƙare nan ta ke" Gyaɗa kan shi yayi still da murmushi ɗauke a fuskar sa ya ce "Ba matsala Mama za'a bada wasu, Allah ya sa mu da ce" "To yayi an gode Allah ya biya ya saka da kairan, ya ba ku zaman lafiya" "Amin amin. Daman kuma wani sati zan koma Lagos wurin wani aiki, to da na ce zan barta tayi ko wata ɗaya amma yanxu kuma na canza shawara ba zan iya barin ta na tafi ba domin hankalina zai rabu gida biyu, to shi ne na ce ina neman izininku idan ba damuwa" "A'a! Allah yasa ga Naseer! To miye wani abin neman izini kai da matarka? Wallahi babu wata damuwa, Allah ya kai ku lafiya ya kuma baku zaman lafiya shi ne fatan mu, daman nan ɗin wa ta ke da shi? Babu sai wan ubanta kuma shima ba mazauni ba ne, mu kuma gashi ba'a nan ɗin muke zaune ba,... Safnah! Ki bi mijin ki sau da ƙafa dan Allah kinji ko? Ki yi zaman ki lafiya ki kwantar da hankali.... " miƙewa Deen yayi ransa a matuƙar ɓace ya ce" Hajiya ta shi mu tafi kinsan ana can za'a yi baƙi kada su zo bakya nan.. " wata harara ta maka masa ta ce" Ina ruwana da wa su baƙi ni, kawai ni dai Allah ya haɗa ni da gayyar tsiya en wahala,..." Ficewa yayi gaba ɗaya daga gidan ya koma mota ya zauna yana mamakin wannan sabuwar halayya ta hajiya. Shi ma dai Naseer ficewa yayi daga ɗakin ya bamu wuri. Kallo na tayi ta ce " Wai Safnah ya naji bakya cewa komai ne? Ko bakya son tafiyar ne?" girgiza kai na nayi na ce "Ba komai Mama" jakar ta ta zuge ta fito min da wasu ƙullukan magunguna ta ɗora min a jiki na, sannan ta janyo Ghana must go da ke gabanta ta turo min ta ce, kin gan su nan, wallahi kayan kusan dubu ɗari bakwai ne, wannan ki riƙa marmasa masa a tea domin nasan girki en aiki ne ke yi, to a tea zaki riƙa haɗowa da kanki ki kawo masa shi zai sa ki ƙara samun kansa sai yanda kika ce, wannan kuma ke zaki riƙa tirarawa, wannan kuma ɗan matsi ne.... " Haka ta zauna ta ɓata lokacin ta tayi ta zayyana min su da amfanin su, sai dai ni a gareni tayi aikin banza, domin kwata kwata tunda na sanyo ƙafa ta wani al'amarin son kasancewa da miji a shimfiɗa bai taɓa zuwa rayuwa ta ba, ko kaɗan ban taɓa yin wannan tunanin ba wanda ban san miyasa ba, wataƙila shima Naseer ɗin bai da buƙata da ni ne ban sani ba... "Safnah, waɗan nan da na yi miki bayanin su daga baya daga zaran kin tabbatar akwai ciki kada ki ƙara amfani da su kinji ko! Kada ki je ki janyo mana salalan tsiya, amma dan Allah ki dage komai kiyi shi yanda na lissafa miki" Gyaɗa kaina nayi na ce "Zanyi in sha Allah, muje kiga gidan ko Mama" tashi tayi ta na faɗin "Muje kam, in samu in kashe ƙwarƙwatan ido wannan irin aljannar duniya" Ko ina sai da na kai ta hatta garden ɗin da ya kai ni ɗazu sai da na kai ta wanda babu komai a zuciyar ta face zallar farin ciki da jin daɗin irin daular da na samu, duk inda mukaje taga ya burgeta sai ta ce na mata hoto ko kuma in ɗauke mu selfie da wayarta ta miliyoyan kuɗi da ta saya, bayan mun gama zagawa Naseer ya aiko da jakar kuɗi sak irin wancan da ya taɓa bani gabanin bukinmu ya ce a saka mata a mota, farin ciki tamkar zata taka rawa haka taji,wannan ne yasa burin da ta ke da shi ya ninku fiye da ƙima. Tana shiga Motar Deen ya kalle ta ya ce "Mama miye a jakar nan ne?" kallon shi tashi kamar ba zata tanka ba sai kuma ta ce "Saƙo ne Safnah ta bayar zan kaiwa wata ƙawarta a Gusau" jinjina kai yayi alamar gamsuwa daga nan ya kunna motar... Hannuna na saƙala a nata tare da fashewa da kuka na ce "Mama! zan yi kewar ki sosai Mama, Kai ma Deen" Sun glasses ɗin shi ya ƙwama sannan ya waigo ya kalle ni ya ce "Dan Allah, Malam ban son gulma, kije Allah ya bada zaman lafiya, Yan miƙdad ya ce in faɗa miki ya wuce, Sa'adu ma shima ya wuce tun da asuba zai koma Zaria yace a sanar miki gimbiya domin yayi ta kira baki yi picking ba" Marairaicewa tayi ta ce "Wallahi ban gani ba, amma zan kira shi Allah ya kai ku lafiya" "Ameen" Daga haka ya ja motar ina nan tsaye sai da suka fice daga gidan baki ɗaya sannan Naseer ya zo ya jani muka sake komawa Garden ɗin. Gefen su Umma kuwa, ƙarfe goma na safe a gidan su Xuhra ta yi mu su tare da kayan lefen su na arziki, Mummy Hindou da ta zauna ta zuba ido tana jira taga wasu kalolin mutane sai abin ya bata mamaki, domin dukkan su babu mai shigar banza, kayan kwalaye kuwa tunda aka fara jera masu su sai da suka gaji tamkar za'a buɗe shago guda, daman jiya da suka isa gidan ɗan uwan Ummar matansa suka ce ya kamata a haɗa da kayan an gani ana so domin ya zama tamkar yankan nama guda a cikin miya wanda idan baka yi shi a aure gani ake tamkar an rasa wani gagarumin abu musamman Sokoto da suka mayar da wannan al'ada kamar ibada, hakan yasa Umma ta sake sabon lissafi wanda sai da ta saka a sake turo mata da kuɗi ta zuba tayi siyayyar, ta ce Xuhra ta yi mata 'ya kuma duk abinda take buƙata matuƙar bai fi ƙarfi ba kuma bai saɓa ƙa' ida ba sai an yi mata shi ko miye shi. Ga akwati sai saiti biyu ma su bakwai, komai sun yi shi cike da tsari da wayewa wanda dukkan familyn Xuhra ba su zata ba. Ga su Ruƙayya en gayu da su kalar wayayyi wanda komai iya kushenka ba ka isa ka soke su ba sai dai abinda ba'a rasa ba domin shi ɗan adam tara yake bai cika goma ba, ga Umma ta shawo wankan ta uwar ango guda wanda duk ka kalleta sai ka ƙara kallon ta..........
OUM AMEER