JIKAR BAUSHE

Page 9&10

by @meenatyandoma

J I K A R B A U S H E

©️®️ MEENAT A. YANDOMA

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

HARAMUN NE SARRAFAMIN LABARI TA KO WACE SIGA BA TARE DA IZININA BA. 'YAN YOUTUBE MA HAKA

*GARABASA =* GARABASA =

Ina yan sari da masu siyen dai-dai ga dama gareku

MUNADA PAD SOFTCARE MAI MATUQAR KYAU DA BIYAN BUQATA LONG CE SANNAN GUM DINTA MAI MATUQAR DANQO

KAN FARASHIN SARI 50 PIECES #2500

100 PIECES #5K

PADS DINMU SABBINE FIL EXPIRE 2028

LOCATION KATSINA TITIN QOFAR GUGA

CALL OR CHAT ***

🅿️ 9&10

...Ganin tawagar tsuntsayen sun tunkaro inda suke gadan gadan ya saka Momy karfin halin waigowa.

Gabanta ne ya yi mummunar faduwa, zuciyarta ta yi tsalle tamkar zata Faso kirjinta ta fado, sakamakon ganin idanuwan Asiim sun rikide.

tsuwwar tsuntsayen ce ta saka Dada rufe idanunta cike da fidda ran rayuwa, su ma duk idanuwansu suka rufe suna Jiran tsammani.

Shurun da suka ji ce ta saka su bude ido. Dan ja da Baya suka yi sakamakon ganin dattijuwar da ke dogara Sanda tana korar tsuntsaye. Wani iron kuka suka rika yi tare da juyawa suna barin wurin da azababben gudu.

"Ya ta wurin nan na da matukar hatsari, me ya sakaku daukar dogon lokaci a nan?"

Wasu yawu Luba ta hadiye domin kallo Daya ta yiwa rubabbiyar tsohuwar gabanta ya yi mummunar faduwa.

Momy ce Mai karfin halin sanar da ita yadda abubuwa suka wakana a wurin.

"Ku kai ta asibiti jininta na daf da karewa Ku tabbatar kun kula da ita domin wannan da kuke gani tamkar numfashinku ce, muddun kuka bari wani Abu ya sameta tamkar ya Sami rayuwarku ne. Kun ga wadancan tsuntsayen? Da banzo ba tabbas zasu halaka duk halittar da ke wurin nan ne"

Kuka Dada ke yi tana Kara tsinewa iskokan Asiim domin kullum cikin sabbin tashin hankali suke.

"Baiwar Allah na ba mu sanki ba. Amma na ji kina bamu labarin wannan budurwar da ke kwance a kasa, me ye alakarki da ita?"

Murmushim da ya Kara fiddo da ainahin mubinta ta yi kafin ta Dora da fadar.

"Tambayoyi ba naki bane. Ki yi saurin barin wurin nan ina Mai Kara jaddada Miki" maganar Asiim da suka jiyo ce ta saka su juyawa su Duka.

Sai dai juyowar da zasu yi tsohuwar ta yi batan dabo tamkar bata tana wanzuwa a wurin ba.

Asiim da Luba kama budurwar suka yi domin shigar da ita mota. "Aahhh!" Asiim ya fada da karfi tare da sakinta ya na Shafa hanunshi da ya ke ji tamkar ya kama rushin wuta.

"Lafiyarka kuwa. Duk masifar da muke ciki ba zasu Bari mu bar wurin nan ba cikin gaggawa. Me ya saka ka saketa"

"Momy wannan yarinyar ba mutual ba ce. Duba fa ki ga kayan da ke a jikin ta sun sha banban da irin Wanda jama'armu ke sakaw a. Ni bazan dauketa ba sai dai Ku kamamu je kawaii"

"Mara mutumci me mugun Hali irin na ubanshi, ni Bari in kama a sakata ko Dan mu bar wurin nan "

"Ki ga me mugun Hali a cikin duhun dare yayin da kika fita zuwa toilet" ya karasa maganar tare da shigewa gaban mota

"Ya zage ni zagina ya ke Zinatu. Duk ranar da Allah ya hadamu da dangin ubanka ko Kwana Daya ba za ka Kara a tare da mu ba"

"Dangin Ubanna ko a mafarki kika gansu sai kin firgice. Ki ma daina Fatan ganinsu"

"Ka rufe min Baki na ce"

Momy ta daka Mai tawagar da ta sakashi hadiye sauran maganar da ke bakinshi.

Kasancewar sun kusa Shiga cikin garin Kai tsaye asibiti suka nufa. E&A (Emergency and Accident) aka nufa da ita. Likitoci ne kusan mutum uku a kanta. Jinin da ake bukata ne ya saka Momy Umurtar Asiim ya je a diba na shi in ya zo Daya.

Fiddo ido ya yi cike da tashin hankali, shi zasu yi ma sanadin mutuwa Ba tun yau ba ya Sabi duk ranar da aka ji Mai ciwo a jiki a ranar zai bar duniya.

Kafin su Ankara ya sulale daga asibitin.Da suka ga dai zata ita Rasa rayuwarta Kawu Hadi suka Kira ba jimawa sai ga shi. Nan suka kwashe kaf abin da ya faru suka sanar da shi.

Bayan an dibi jininshi ne suka ga Asiim ya dawo ya na shan kamshi tamkar bai San laifin da yayi ba.

Kofar dakin suka tura nan suka yi tozali da ita kwance an saka bandeji an nade kanta. Nurse ta shigo da sauri tare da duba karin jinin ko ya na tafiya

"Subhanallahi! Bayan fitar likita wa ya taba wurin nan?"

Kallon kallo aka Shiga yi domin shigarsu dakin Kenan.

Da sauri ta fita ta Kira likita. Gumin da ke wanke ma shi fuska ya sharce tare da fidda jinin da ke faman tsiyaya kasa ba tare da Shiga jikinta ba.

"Ku iske ni office." Ya fada tare da ficewa da sauri.

Kacokam nutsuwarsu suka tattara zuwa gareshi.

Farin gilas din dake fuskarshi ya gyarama Zama tare da harde hannuwa.

"Me ye tsakaninku da mara lafiyar"

"Matsayin diyata take" Momy ta fada.

"Sai dai kuyi hakuri. Ku dauki wannan a matsayin Kaddara, duk abin da kuka ga ya faru da bawa da sanin Allah.wasu abubuwan suna faruwa ne domin Ubangiji ya jarrabamu ya ga shin za mu cinye Kaddarar da ya jarabemu..."

"Ka ga likita! Mu je Kai tsaye ka tsaya sai hanya hanya kake mana sanar da mu ainahin abin da ke faduwa"

Murmushi likitan ya yi domin in da sabo ya Saba da halin dattawa.

"Ku yi hakuri Ku dauki wannan a matsayin Kaddara. Yarinyarku ta hadu da mummunar ciwo nan na shafewar tunani, ma'ana ta yi loosing memory, in ma zata iya tuna wani Abu to fa kalilan ne"

Tamkar wadda ta zauna a saman allura haka Momy ta Mike tare da dafe kirji.

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun! Ina zan Nemo danginta WA zai fada mana wace ce ita"

Jiki a sanyaye suka fito daga office din. Jin abin da ya faru Dada tsalle ta yi ta dire akan ba zasu zauna da yarinyar da ba su San wace ce ita ba. Haka kawai su je su kwaso aljana ko mugun iri.

Da kyar Momy ta shawo kanta ta amince zasu zauna da ita. A bisa sharadin da tunaninta ya dawo zata tattara ta tafi.

Ganin duhun dare ya Fara Dada da Asiim daukarsu Alhaji Hadi ya yi su tafi Gidan. Sai dai fadan da Asiim da Dada suka Fara ne ya saka Asiim dawowa cikin asibitin ya nufi dakin da aka kwantar da su.

Hade fuska Momy ta yi domin ta San za a Rina, da wuya su jitu da Dada musamman yau da suke ta faman fada.

Lemun kwalbar da Hadi ya siyo musu ne ya dauki Daya ya Kai Baki.

Idanuwanta ta Fara kyaftawa alamun zata Farka, da sauri Momy ta Matson tare da riko Mata hannu.

Zaune ta mike tana binsu da kallo.

"Sannu yarinya me ke Miki ciwo"

Shuru ta yi tana jingina da Bango. "Za ki ita tuna sunanki kuwa" Luba ta jefa Mata tambayar.

"Samu" ta fada cikin siririyar murya.

"Bayan shi fa zaki ita tuna ko wani cikin danginki ne?" Girgiza Kai ta yi tare da rufe idanunta Jin wani irin zafi ya Mata dirar mikiya.

Kwalbar da ke a hannunshi ya saki ta tarwatse a kasa. Nan fa hankalinsu ya dawo wurinshi. Jajayen idanunshi da suka Fara rikida ya watsa Mata.

Kamar walkiya kafin su ankara ta diro daga sama gadon tare da ridar kwalbar lemu ta hadata da Bango, fashewa ta yi ya rage saura bare a hannunta.

Asiim ta nufa da niyyar daka Mashi ita a wuya, da karfin tsiya ya banketa tare da daukar fasheshshiyar kwalbar zai daka Mata ita a wuya.

A firgice Momy ta fizge samu kwalmar ta same ta a hannu ta ke jini ya Fara ambaliya.

Duk abin da ke faruwa ya na labe ta bayan window ya na kallo. Don haka da sauri ya fiddo wayar shi hannunsa har kyarma ya ke tare da Danna Kira.

"Wallahi ita ce. Yarinyar da muke nema ruwa a jallo na Samo ta Alhaji...