13
KURURUWA A KUNNEN KURMA🥀 🥀
A 2025NOVEL
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHEEM
(OUM AMEER)
Wattpad:@ Ummu-Ameer
Arewabooks: @Aminatuibrahimbawa
From d experience writer of:
Zaytoonah
Abarwa rai
Gudun wuce sa'a
Kibiyar so
Kulsum
Bahiyya
Nuudarr
Littafin kuɗi ne. #500 kacal, zaki iya turawa ta wannan asusun 3132703269 Ibrahim Amina Bawa, sai ki tura shaidar biya ta wannan Layin ***. 🙏🙏
FREE PAGE 13
Dangin Mummy Saratu ba ƙaramin farin ciki suka tsinci kan su a ciki ba, ganin irin kalar family ɗin mijin Xuhra, duk yanda suka yi expecting ashe ba haka abin yake ba. Cikin mutuntawa Umma ta ƙara rusunawa ta kalli Hajiya Kakale wadda ita ce tsohuwa sosai a wurin ta ce. "Hajiya da fatan mun same ku lafiya?" Jinjina kai Hajiya Kakale tayi cikin farin ciki ta ce "Lafiya lau Alhamdulillah! Sannun ku da hanya, da fatan an iso lafiya?" "wallahi lafiya ƙalau mun gode Allah. Da ɗa ashe abu haka ya kasance ko Hajiya? Ka na naka Allah yana nashi iko, kuma ta Allah ita ce haƙƙun...." "Sosai kuwa Hajiya am, tsarin Allah shi ne daidai mutane ne ba su ga ne ba, sai su ɗauka duk abinda suka so ya faru suka ga ya farun sai su ɗauka kamar wayon su ne ko dabarar su. To kinga dai Usman ya zama mijin Faɗimatou babu zato babu tsammani wanda mu alhamdllh, mun karɓa kuma mungode Allah yasa hakan shi ne mafi alheri ". Jinjina kai Umma tayi ta ce" Amin amin yah Allah, muma mun karɓa da hannu biyu kuma muna godiya, muna kuma fatan Allah yasa hakan shi ne alheri, muna roƙo da Safnahr da ita Xuhra Allah ya ba su zaman lafiya da haƙuri a gidajen auren na su " Cikin jin dadi Mummy Asmau ta ce" Amin amin yah Allah, muna godiya sannun ku da zuwa, muna muku maraba " Murmushi Ramlatu tayi ta ce." Muma mun gode, ga kayan amarya nan tayi haƙuri da abinda ya samu abun ne ya zo mana a ƙurarren lokaci... "." Kai haba ba komai, ai fatan zaman lafiya duk shine kan koma muna fata aure yayi albarka " daga haka Mummy Asma ta wuce ita da matar yayan ta suka shiga jera musu abinci da sha a katafaren parlourn mummy daga nan ta wuce wurin shirin Xuhra domin ɗaukar harma. Bayan sun shiga sun sha ruwa sun taɓa abubuwan da aka ajiye musu hajiya Kakale ta shigo tare da samun wuri ta zauna ta ce "Hajiya kin ganni nan, ni ce kakar Faɗimatou ni na haifi uwarta, wannan da ta kawo muku ruwa Asma'u ita ce auta ta mijin ta rasuwa yayi shekaru biyu da Suka gabata, akwai yayyunta maza biyu sai yayan Saratun guda ɗaya, mu en asalin ɗakin gari ne yankin jihar ke ni Kebbi amma yanzu mun zama en nan garin saboda yanayin zama amma kuma muna kan je can mu dawo.... " Murmushi Umma tayi ta ce Allah sarki! Mu kuma en Gusau ne, ni ɗin abokiyar zaman mahaifiyar Usman ce amma kuma ɗa na ne a wurina yake domin ni ce na yaye shi har yanxu a wurina ya ke" jinjina kai Hajiya Kakale tayi ta ce "Kaji in da ake zama na domin Allah, to matan yanzu ai komai zaki yi cewa zata yi ba zata taɓa yarda da kishiya ba..." Dariya Umma tayi ta ce "Mudai kam Allah ya kauda wannan a tsakanin mu,... Wannan kuma Hajiya Halima ƙanwar alhaji ce wato marigayi mahaifin Usman ɗin,...." Kalma Hajiya Kakale ta ɗauka ta ce "Allahu Akbar! Ashe mahafinsa ya rasu, Allah ya ji kansa da rahama" "Amin amin yah Allah..." Daga haka kawai sai ta fara sharɓar hawaye tana jinjina kai tana faɗin "Allah sarki Alhaji! Ai hajiya am mutuwa tayi mana yankan ƙauna...." A hankali Ramlatu ta waigo ta kalli Ilham ta yi mata ido akan kukan da Umma ta fara.... Kallon Ilham tayi ta ce "Umma kin san inda zamu je da nisa sosai, kuyi ku tashi mu tafi dan Allah kada fa muyi dare" Jinjina kai tayi tare da sharce majina ta nuna Ilham ta ce "Wannan ɗin ƙanwar Usman ɗin ce ta ɗakin Maryam, wannan kuma Ramlatu ta waje na ce, sai wannan ita ce Fatima ƙanwar Maryam ɗin sai Hajiya Hauwa ita ce yayar ta, sai Siddeeq da muka taho da shi yana waje" "Allah sarki! Allah ya karawa rayuwa albarka, ai kam Usmanu yayi mata domin Xuhra ba dai nutsuwa ba, wallahi yarinya ce mai hankali da matuƙar haƙuri kamar uwar ta, ga baiwar karatu Allah ya bata, kinsan ƙasar waje tayi karatu..." Cike da jin dadi Hajiya Hauwa ta ce "Allah sarki! Ashe waje tayo karatu ma baiwar Allah" "Af! Ai Xuhra duk gidan nan mahafinta yafi ji da ita, ita fa tun matakin ƙaramin ajin yara a can ta fara shi har sai yanzu da ta kambala ta dawo, shiyasa ƙwaƙwalwar nan ta ta akwai karatu sosai, Usman zai more da yaran sa" Sosai wannan labarin yayi wa su Ilham daɗi ko a nan sun san cewa ta cunawa Safnah, saidai addu'ar su ɗaya ce Allah yasa kada ta riƙa yi musu wulakanci tana ɗaukar su marasa daraja a gareta. Duk yanda su Ilham ɗin ke kaffa kaffa akan kada su ɗau lokaci, ba su aune ba sai dai suka ji kiran sallah azahar tayi, saboda Umma da hajiya Kakale da suka tsinke da surutu kamar sunyi shekaru da sanin juna, suna batun fitowa ne Mummy Hindou ta shigo tana ta basu haƙuri akan cewa baƙi tayi tunɗazu sai yanzu ta samu ta fito, daman cikin shirin ta ta fito na tafiya domin Daddy yace da ita za'a tafi. Ita daman Hajiya Shafa tana dawowa daga gidan Safnah ta je ta shirya suka bi hanya ita da Deen ta fake akan cewa wai bari tayi harama ta riga su isa domin ta shirya musu abinci kafin su iso, don kawai kada ma ta haɗu da dangin Usman ɗin. Ƙarfe biyu Daidai mummy Asma'u ta fito janye da hannun Xuhra wanda ya sha kunshi ya yi kyau sosai, fuskar ta lulluɓe ta ke a cikin hijabi wadda tayi sharkaf da kuka bayan sun fito daga sashen Daddy. Gabanta Ramlatu taje ta tsaya tare da leƙa ta ta cikin hijab ɗin tana murmushi ta ce, "Masha Allah! Laƙuwwata illah billah! Ubangiji yayi riƙo da hannayenki yasa ku zamowa juna alheri amin" Duk mutanen gidan kowa ya fito an yi cirko cirko ana yi mata fatan alheri. Daman Abdulmalik tun safe yana can wurin kicaniyar loda kayanta a mota da shi da wasu maaikatan gidan na su, sai Umar wanda shi ne yace zai kai ta a motar sa, Shima Baba Hayatu cewa yayi sai an ɗaga da ita zai bi bayan ta a motar shi. Motar Umar ɗin ce Hajiya Kakale ta shiga ita da Xuhra da Ummah sai Mummy Hindou a gaba, sai Ilham, Aydah, Aunty Rabi'atou a motar ta tare da driver da kuma Irfan, sai Mummy Asma'u, Ramlatu da kuma hajiya Hauwa a motar Siddeeq sai su Hajiya Halima a dayar motar. Hilux biyu suka yi daban ta kayayyakinta tundaga akwatuna har zuwa duk wani abunda tasan tana da buƙata da shi wanda duk wannan Aikin mummy Asma'u ne. Bayan an gama loda komai suka ɗau harma suka yi wa Gusau tsinke. Ba su suka isa gusau ba sai kusan Ƙarfe takwas na dare, koda suka iso har duhu ya gama mamaye sararin samaniya, direct gida suka nufa da ita wanda ko da suka je sun tarar da en uwa da abokan arziki ana ta yi mata maraba, sashen Alhaji Mami tasa aka yi musu iso wanda yasha gyara sosai tamkar mai part ɗin yana raye. Jikin mummy hindou ne ya ƙara yin sanyi domin ganin gidan iyayen sa haƙiƙa wannan ma an bata mamaki, sosai taji daɗi a ranta, daman ba wai tana ƙin Usman ba ne a'a kawai dai tayi judging ɗin sa ne according to yanda su Aydah ɗin suka yi ta ɓata shi. Suna nan sai ga Ruƙayya ita da Amratu sun shiga jera musu warmers ɗin abinci wanda abincin yakai kala uku. Ba musu suka baje suka narki abinci son ran su wanda hatta Aydah kowa ne kalar abincin sai da ta taɓa Xuhra dai ce akayi ta daga daƙyar Mummy Asma ta samu ta saka ta ta yi loma biyu zuwa uku. Bayan sun gama sun yi salloli su Mami suka shigo aka shiga gaggaisawa da juna cike da mutuntawa.... Tunda suka iso Umar yana can shi kuma ɗakin Usman shima an kai mishi abinci ya samu ya ci yayi sallah. Gidan na su Usman ya ɗauke shi suka tafi wanda Umar ba ƙaramin mamakin ganin wannan zungureren gida yayi ba sai dai ya barwa ransa sani, kuma yayi wa er uwarsa murna da kuma addu'a Allah yasa ya zama gidan ta har mutuwa. Bayan sun dawo ne misalin Ƙarfe goma sha biyu na dare suka zauna suna tattaunawa wanda nan Umar ɗin ya bawa Xunnurain labarin Xuhra tundaga sama har ƙasa, daga ƙarshe ya roƙeshi akan yayita haƙuri da Ita domin wata rana komai zai zama kamar ba'a yi ba. Washe gari ma a nan gidan suka wuni sai da aka gama gyara mata gidanta tsab misalin Ƙarfe takwas su hajiya Kakale suka fito da ita zuwa gidan mijin ta wanda Alhamdulillah! Sun yi matuƙar farin ciki ganin irin muhallinda ta samu wanda ba su taɓa zata ba.... Kuka take kamar wadda za'a kaiwa lahira da ranta jiki na mazari tana kiran "Dan Allah Aydah don't go and leave me here, ina jin tsoro sosai, dan Allah Grandma kada ku bar ni a nan..." kallon ta mummy hindou tayi ta ce "Kiyi haƙuri Xuhra in sha Allah babu abinda zai faru sai alheri, gobe ai ma zamu dawo a nan zamu wuni sai jibi mu tafi gida kinji ko" gyaɗa kanta tayi ta ce "Na gode mummy" Daga nan suka samu suka samfe suka barta. Shi kuma Usman ganin Umar yasa dole ya shirya cikin manyan kayansa ya taho Kanoma ya ajiye sa, har ya sauka sai kuma ya kira shi ya ce "Malam ango ka manta kayan ka" Harararsa Usman ɗin yayi sannan ya ce "Ka manta angogu ne ba ango ba..." ɗage shoulders Bilal yayi sannan ya ce, "That’s your own cup of tea, Ni dai kwashe kayanka dan Allah" Buɗe bayan motar yayi ya kwashi kayan ya nufi cikin gidan zuciyar sa na wani irin bugawa da ƙarfi tamkar wanda yake jin tsoron haɗuwa da wani abu, jiyo muryar Kanoma yayi yana faɗin. "Allah bada sa'a, kada a manta a yi addu'a angon Xuhra". Tamkar ya Juya baya ya kwasa masa mari haka yake ji... Tsayawa yayi ya saurara da kyau, inda ya jiyo sheshshekar kuka can yayi wa tsinke, a hankali ya murɗa handle ɗin door ɗin ya shiga ɗauke da sallama a bakinsa... A can ƙasan lungun gado ya hango ta ta makure wuri ɗaya tanata kuka kamar wata karamar yarinya... A nan bakin ƙofar ya yasar da ledojin hannun sa sannan ya ja baya ya jingina jikin sa a jikin ƙofar tare da harɗe Hannayensa a ƙirjinsa ya zuba ido yana kallon ta kamar ba zai yi magana ba.... Ya jima a haka sannan daga ƙarshe ya buɗe baki kamar wanda zai yi maganar arziki ya ce "Ke! Miye zaki wani zauna kina damuna da kukan Gulma a nan? Wadda ta saba rayuwa a turai tun tana er ƙaramarta yanzu miye na kuka don an kawo ta wani gida da haƙoranta talatin a baki...? To kima daina wahalar da kanki because you are not welcome in my web.......!
OUM AMEER