Page 11&12
J I K A R B A U S H E
©️®️ MEENAT A. YANDOMA
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
HARAMUN NE SARRAFAMIN LABARI TA KO WACE SIGA BA TARE DA IZININA BA. 'YAN YOUTUBE MA HAKA
*GARABASA =* GARABASA =
Ina yan sari da masu siyen dai-dai ga dama gareku
MUNADA PAD SOFTCARE MAI MATUQAR KYAU DA BIYAN BUQATA LONG CE SANNAN GUM DINTA MAI MATUQAR DANQO
KAN FARASHIN SARI 50 PIECES #2500
100 PIECES #5K
PADS DINMU SABBINE FIL EXPIRE 2028
LOCATION KATSINA TITIN QOFAR GUGA
CALL OR CHAT ***
🅿️ 11&12
...Wayar ya mayar aljihu tare da fita asibitin da sauri.
Labarin rikicin da ake tuni ya kaiwa likitoci. Ba karamar firgita suka yi ba kasancewar wannan ne karo na farko da suka hadu da irin wannan matsalar.
Da kyar Security suka rirrike Asiim da hargowar damko Samu. Wasa-wasa sai ga fada na kokarin komawa tsakaninsa da Security.
Momy kuwa ganin jinin da take fiddawa kanta suka yi aka saka mata bandeji da magani jinin ya tsaya.
Asiim kuwa tsakar asibitin suka fitar da shi likitan ta hau balbala masifar abin da ya haddasa fadan.
Su dai mutanen da ke makwaftaka da su kowa jinin jikinsa ya sha domin a gabansu komai ya faru.
Luba jikinta ya yi matukar sanyi ji ta ke anya kuwa wannan budurwar haduwarmu da ita alkhairi ce, kada fa maganar Dada ta zama gaskiya mu je mu dauko mugun iri mu aje a kusa da mu.
Kamar Momy ta san ne take sakawa cikin zuciya, dafa kafadarta ta yi.
"Kada ki yi tunanin komai, mu riketa da zuciya Daya komai ya yi tsanani maganinshi Allah."
Babu yadda Luba ta iya dole ta yi shuru domin ba halinta ba ne yin jayayya da yayar Tata.
Ƙaton Macijin da ke karkashin fulawowi ne ya sirnano kai tsaye zuwa wani ward da ke cike da jama'a. Ba tare da an ganshi ba ya shige cikin zanen da aka rufe wata dattijuwa, kafin su ankara sai gani suka yi gadon da take zaune ya na girgiza tamkar zai karshe.
Cikin sauri danginsa suka yi kanta suna kururuwar girgizata, sai dai ina domin mai aukuwa ta auku. Wata daga cikin masu jinyar ce ta ga lokacin da hirdeden Macijin ya fita ta taga.
Lokacin da likitoci suka zo rai ya yi halinshi. Su Momy kuwa kururuwar da suka ji a dakin da ke makwaftaka da su ya tabbatar masu ba lafiya.
Labarin sarin Macijin da suka ji ce ta saka kafafun luba kasa daukarta dole ta zame kasa.
"Ko dai Macijin da ke kashe matan Asiim ne? Ni dai a tsora ce nake wannan musiba ta mana yawa"
Ta karasa maganar tamkar za ta fashe da kuka.
"Luba daga Jin Maciji a asibiti sai ki ce kamar wanda ke bibiyarmu. Ki sani nan ma suna da macizai, ki daina fadar haka kada ma wani ya ji ki saka mu a matsala"
Shuru ta yi cike da matukar damuwa domin ta san akwai matsala.
Daren ranar har gari ya waye ba su yi ido biyu da Asiim ba. Tun Momy na damuwa har ta fara tunanin ko dai ya tafi gidan kawu Hadi.
Cikin ikon Allah ganin jikin Samu ta ji sauki a safiyar aka sallame su, kai tsaye gidan suka nufa tare da tulin magunguna.
"Kada kayi min wasa da hankali. Da gaske ka ga yarinyar da idonka" Alhaji Biliya ya karasa maganar hade da gargadi.
"Shugaba ganin idona na ganta, dama na fada maka yarinyar nan ba zata yi wahalar samu ba. Amma yanzu abin da ya kamata mu je wurin na kan tudu mu ji yadda zai ce."
"Kafin nan mu je asibitin In ganewa idona. Ina dai yarinyar nan ce tabbas bazan taba faduwa a siyasata ba, abinda ya wahalar da ni wurin nema sai gashi yau da da kafarshi ya iske Ni har inda nake"
Babu bata lokaci suka nufi asibitin.
Su Momy kuwa kiran Hadi suka yi tare da sanar mashi anyi sallama su ma gasu nan zuwa.
Unguwa ce ta masu hannu da shuni tun daga kan gine gina zaka fahimci jama'ar da ke cikinta sun shirya ma zaman duniya.
Mai motar da suka dauko haya har kofar gidan ya aje su, da mamakin su sai ganin Asiim suka yi ya fito daga gidan. Ganin irin kallon tuhumar da Momy ke jefa mai ya saka shi kauda kai.
"Inna lillahi wa Inna lillahi rajiun! Wace ce wannan mai idanuwan Mujiyar? Ina kuka samota wannan ai mujiya ce." Dada ta karasa maganar tare da dafe kirji.
"Amma yanzu Dada bakinki ba zai iya gani ya yi shuru ba. Kin jima kina kiran Asiim mai idanun macizai sai ga macizai sun addabemu, yanzu kuma Mujiya kike kira mana?
"Wannan ai rashin son gaskiya ne. Ku kanku kunsan yarinyar nan idanuwan mujiya gareta. Zinatu! Me na ke gani a hannun ki kamar ciwo?"
"Rauni ne na ji bayan tafiyarki"
Ganin Dada na kokarin nemo masu hanyar jin yadda ciwon ya kasance ta yi saurin kauda maganar da fadar.
"Kawu ya kamata mu je wurin malamin nan domin ina tunanin zuwa jibi za mu koma gida."
"Ba damuwa idan rana ta yi sanyi sai mu karasa, amma fa wurinshi akwai layi in muka je dole mu jira."
Ta karasa maganar tare da kafe Samu da ke ta daman jinsi da ido.
Dada fur ta ki yadda su sake hada ido da Samu, musamman da ta tambayi sunanta aka ce mata samu.
"Ce min za kuyi kun sami Samu manana sabuwar wahala. Da ganin idanunta kasan ta hada dangi da shedanu"
Shuru suka yi don duk wanda ya tanka yanZu zata hau rikici da shi. Samu dai kallonsu kawai ta ke ba tare da gane ainahin abin da Dada ke nufi ba.
Gogan naku kuwa tunda ya ji maganar zuwa wurin Malam ya ji maganar zuwa wurin Malam ya hade girar sama da ta kasa.
Sai da marece ya yi kafin su nufi hanyar gidan malamin. Sunyi tafiya mai nisa kafin su iso karamin kauyen sai dai tun daga nesa suka fara hango cacirindon mutane da ke kewaye da gidan.
Wani daga cikin jama'ar wurin ke tabbatar masu da rasuwar malamin sakamakon sarar bakon Maciji da ya shigo daren jiya.
Jiki a sanyaye suka koma cikin mota sai dai me babu samu ba dalilinta.
A rikice Momy ke tambayar mutane ko sunga wata budurwa sai dai su duk wanda aka tambaya ce wa ya ke ko mai kama da ita bai gani ba.
A rikice suka rarrabu suna neman ta.
Ina banda Asiim da ke tsaye ya na farin cikin bacewarta.
...Su Alhaji Biliya kuwa sun nemi Budurwar a cikin asibitin sai daisama ko kasa.
Wani likita ne ke tabbatar masu an sallame su don haka da sauri suka nufi gida.
Kai tsaye asirtaccen dakinshi da ba wanda ke shiga ya shige tare da dauko wani madubi. Duk iya kar kokarin da yayi ya gano in da yarinyar ta ke abin ya ci tura, daga karshe da ya matsa wani hirɗeɗen Maciji ya gani ya biyo wata baƙar Mujiya.
Tsabar firgici da ya shiga sakin madubin ya yi ya fadi ƙasa yayi ratsa ratsa...
FREE PAGES GAF SUKE DA KAREWA. WASU HAR SUN FARA BIYA. WANNAN LITTAFI 500 CE GA DUK MAI BUKATA,GA ACCOUNT NUMBER NAN
6051832238 KEYSTONE
AMINA ABUBAKAR