KOWA YA GA ZABUWA…

5

by @gureenjoh

KOWA YA GA ZABUWA...

   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            

         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:

Zuhraa

Hamrah

Igiyar Rayuwa

Noor Iman

Ruwan Sama..

Lelewal

GAMON JINI paid

And Now

Kowa Ya ga zabuwa..

                      PAGE 5

FREE BOOK

Ba ƙaramin tashi hankalin Abba yayi ba, nema har police station ta ya ze fara cewa Allah ya kasa riƙe alkawarin da ya ɗauka na riƙon marainiyar nan har karshen rayuwarta? Cikin haka ya ga call da sabon layi kaman ba ze ɗaga ba se kuma ya ɗauka.

"Alhaji kana magana ne da mahaifin Ummi kawar ƴar wajenka Hidayat ce kawai muka gansu bayan an tashi gashi har yanzu ta ƙi yarda a maida ta gida"

Ajiyar zuciya ya sauke kan ya tambayi kwatancen gidan, nan ya faɗa mishi unguwan da kyar ya iya cewa drivern "mu je dorayi malam isa"

Bayan sun isa mahaifin Ummi ya musu iso zuwa cikin gidan, karamin gida ne na masu rufin asirin Allah machine ɗinshi na Parke daga gefe, har parlor suka shiga ya saka ummansu ummi ta kira mishi su, hidayat na ganin Abba ta fara hawaye, itama ummi na tayata riƙe hannunta tayi tace

"bana so a dakeki Hidayat amma ya zan yi?"

Haka suna gani Abba ya janye ta suka tafi, a mota cikin karaya da ganin yadda take hawaye yace

"Hidayat! Tunda kika fara wayau Na taɓa tauye miki wani hakki na uba akan ƴarsa?"

Kai ta girgiza cikin sanyi yace

"to menene? Gayamin yanzu me yasa bakya son komawa gida?"

Cikin kuka tace

"Abba Umma zata kasheni in na faɗa maka"

Idanu ya kura mata na lokaci kaɗan kan yace

"in shaa Allahu babu abunda zata miki, ba zan bari ba gayamin kin ji?"

Kai ta gyaɗa kan tace

"Abba bani jin daaɗi ban yiwa Surayya assignment nata ba nima ummi ce ta min sbd takardar a wurinta ya kwana, teacher ɗin beat for the assignment na san in na koma umma ma dukana zata yi"

Driver ya girgiza kai, yace

"kayi hakuri Alhj amma zan bada sheda don akwai ranar ma da bata yi mata assignment ba aka dake ta a gabana hajiya ta zane yarinyar nan hidayat, wani abu dake ci min tuwo a ƙwarya shine yadda suke hana yarinyar nan zama a kujera gashi bani da halin magana, nayi sau ɗaya hajiya tace in tsaya matsayi na ko in rasa aiki na"

Abba cikin wani yanayi yace

"menene shi da yake ci maka tuwo a ƙwarya?"

Driver yace

"Alhj Hidayat bata isa ta zauna akan seat na kujeran ba, a inda kafafun ka suke ɗin nan wurin tsugununta kenan a kullum sannan bata da kulan makaranta"

Da sauri Abba ya kalli inda kafafunshi suke ya juya ya kalli hidayat hawaye ya cika idanunshi yace

"hidayat me kuma take miki? Ki gayamin kinji?"

Abubuwan da ake mata ta bashi labarin wasu, he was totally speechless har suka isa gida be iya ya ce komai ba, sashenshi yayi da Hidayat abincin da aka yi don shi ya bata ta ci ya dinga saka mata namomin har ta cinye, shi yaje har ɗakin su ya ɗauko mata kaya ya saka ta tayi wanka a toilet ɗinshi ta sauya, shi ya wanke mata uniform ɗinta Kal ya shanya.

A lokacin daya dawo ya samu tayi bacci nan kasa ya ɗaga ta ya maida ta kan gado haka ya zuba mata idanu yana kallo, yanzu har yarinyar nan tayi girman da za'a iya zalunta? Umma bata tsoron wani abu ya samu wannan ƴar batalikar Allahn? Fisabilillahi this loving soul kyakyawar yarinya na nunawa sa'a.

Babu irin Tunanin da be yi ba akan matakin da ze ɗauka, har Tunanin ƙara aure Seda yayi daga karshe ya yanke hukuncin da zuciyarshi ta fi bashi ita ce daidai.

Chan ɗakin shi ya bar hidayat a time ɗin karfe wurin tara na dare ya tura kofan ɗakin umma ya shiga, tana tsaye jikin wardrobe tana duba abu ganin yanayin fuskanshi yasa ta rufe wardrobe ɗin ta bashi hankalinta yace

"Amina ashe ba kya tsoron haɗuwar ki da ubangiji? Amina ina abun cuta a jikin Hidayat? Me ta sani nan duniya? Me ta yi miki da zaki dinga zaluntarta? Mahaifiyarta ranta ba'a hannunta yake ba da a hannunta yake na tabbatar bazata taɓa zaɓan tafiya ta bar yarinyar ba, kema kuma haka naki ran ba'a hannun ki yake ba ko yanzu Allah ze iya ɗaukewa idan aka yiwa naki abunda kike yiwa ɗan wani zaki ji daaɗi? Kiji tsoron Allah ki Sani Allah baya zalunci kuma baya barin me yi..."

Dakatar dashi tayi tace

"yanzu ita hidayat ɗin ce ta ce maka ina zaluntarta da har zaka zo ka cika ni da wa'azi? Allah na tuba ai idan zan mutu in bar yarana ma ba zan bar su a titi da kokonton ko ƴaƴan sunnah suke ba ko ƴaƴan zina, dangi gaba da baya Alhamdulillah, ita fa? Wa ya san daga inda uwarta ta yayumo ciki ta kawo kai kuma me tausayi da imani ba dangin iya ba na Baba ka ɗauka ka rike ta mutu ta barmu babu wani hujja ko haske, yarinya kyau kaman ita tayi kanta, wa ma ya sani ko kai ne ka yayumo mata cikin aka korota daga garin su ta zo ka saka ni riƙeta har ta mutu ta bar ƴar Zi...."

Marin da ya sauke mata ne ya hanata karasawa, a zafafe yake kallonta yace

"dama abunda ke zuciyarki kenan shine se yau kika amayar? Ina me baƙin cikin Haɗa zuri'a dake Amina baki da zuciyar imani da tausayi, wa ma ya sani irin wahalar da baiwar Allahn nan ta sha hannunki? Ki tattara kayan ki ki koma gidanku idan aka karanta miki karatun da ya kamata se ki dawo ki gyara rayuwarki karki ɓata min rayuwar yara da wannan halin kafurcin"

Yana kai nan ya juya ze fita da gudu ta sha gabanshi tace

"ni ka mara akan wanchan ƴar shegiya..?"

Kara zabga mata mari yayi yace

"idan har zaki cigaba da kiran hidayat da irin sunayen nan hannuna ba ze gaji da hukunta ki ba"

Ihu ta kurma tace

"Wallahi ba zan tafi ba se da hujjah, ba zan bar gidan nan ba har se ka ban hujjar tafiya"

Yace

"hujja kike so? OK ki je na sake ki saki ɗaya"

Hannu ta sa a kai ta kurma ihu

"akan ts...." Fasa faɗar tsinanniyar tayi ganin ya sake ɗaga hannu tayi saurin cewa

"yanzu akan hidayat ka sakeni Abubakar? Akan wannan yarinyar?"

Yace

"ba saki kaɗai ba, zan auro wacce zata kula da ita tunda ina da damar hakan"

Me umma zata yi! kuka wiwi kaman yarinya Alhj ya ce ze yi aure, a haka ya fita ya barta, a kofar ɗakin ya samu sauran yaran be kula su ba ya fice abun shi, suna ji suna gani umma ta Haɗa akwati ta fice.

A ranan a sashen Abba hidayat ta kwana bayan tafiyan umma ma fita yayi ya sayo musu gasashen kaji da su ice cream ya biya super market ya sayi sabon lunch box hadadde, Washegari a sashenshi ta ci abincinta suka fito mota a tare, yaran basu ɗauko mata lunch box ba ya kalli khausar bayan sun gaishe shi yace

"koma ki ɗauko wa hidayat basket ɗinta"

Juyawa tayi bakin ciki kaman ya kashe ta, haka ta je ta ɗauko ta kawo musab dake zaune a gaba ya kalla yace

"mus'ab koma baya"

Fita yayi ya koma baya da kanshi ya saka hidayat a gaba yace

"as from today wurin zamanta kenan Habibu driver duk ranar da ka kuskura muka haɗu ko daga nesa ne ban hange ta ɗaga gaba ba a bakin aikin ka, sannan duk ranar da ta sake fita ba lunch box baka gayamin ba shima a bakin aikin ka"

Yana kai nan yayi musu waving bayan ya ba kowa kuɗin break ɗinshi suka fice.

A mota sun yi shiru ne sbd sun san ko an koma habu ya faɗawa Abba in ya tashi dukansu babu umma me karɓansu, a school ne suka Taran mata suka mata kacha kacha Aunty khausi har niyyar dukanta tayi aka raba su.

Wasa wasa satin umma uku Abba kaman be san da zaman ta a gidansu ba, gidansu irin gidan hayan nan ne masu ɗakuna dayawa, magana har ya soma yi mata yawa ga takura gashi bata samun sakewa kaman tana gidanta, tasha alwashi Kala kala akan Hidayat, tun tana Tunanin Abba ze zo ya ɗauke ta har ta sadakar ta fara kama kafafu da manyanshi bayan sati daya aka samu suka zauna.

Ya gindaya mata sharuɗa akan hidayat ta ji ta amince ta bashi hakuri sossai kan ya amince ta dawo, a lokacin har wani fari da kumatu hidayat ta kara irin kulawar da Abba ke bata ko yaranshi be baiwa ba, ya mata sayayya ba na wasa ba Dukda ya kan Haɗa da su khausar sede nata fa na daban ne.

Tunda umma ta dawo bata shiga sabgar hidaya ba haka itama, shakkan umma da take yasa bata bari ma su haɗu, bayan dawowanta da sati biyu aka tura Abba wani aiki a France ya tattara ya tafi tare da kara jadaddawa umma kula da Hidayat ya kuma tabbatar mata ko tsawa me karfi umma tayi mata ta gayamishi in ya dawo.

Umma ce zaune tana Tunanin abunda zata yiwa hidayat don Wlh abunda ta mata ba ze taɓa tafiya a banza ba, wasa ma ake ace ta hakura komai ya wuce, hidayat ɗin ita wacece? Hmm

Bayan ta gama nazari ta tashi tayi kitchen, ruwan ta me kankara ta samo ta fito tayi gaban TV ta samu cable su Surayya na kallonta, tayi ɗakin su a kwance ta samu hidayat bisa shimfiɗarta tunda Abba ya fice take a haka a ɗarare ta san umma kaman yunwar cikinta, tana cikin tunani kawai taji ruwan sanyi a jikinta bata gama dawowa daidai ba ta fara jin saukan cable, ihu ta kwala ta fara kokarin gudu sede umma ta fi karfinta haka ta rike ta Tsam ta hau jibganta kaman Allah ya aiko ta, Seda tayi mata laga laga kan ta janyota parlor.

"Fahariyya kawo min wuƙa"

Wani irin zaro idanu hidayat tayi anan ta fara

"Umma Don Allah kiyi hakuri, umma karki kashe ni wallahi ba zan sake ba, umma kiyi hakuri.."

Idanunta rufe take ta baiwa umma hakuri ta ruɗe ta gigice, bata kara sarewa ba seda fahariyya ta kawo wuƙa umma ta saka khausar kama mata kafafu, fahariyya ta kama hannayenta suka Mikar da ita Salamatu da Surayya suka danne ta da kyau, kaman zata shiɗe take rokon umma kar ta yanka ta.

"Zaki sake ko da ambatan sunana a gaban Abba?"

Da sauri ta girgiza kai tana cewa

"A'a a'a umma ba zan sake ba"

"A'a zaki sake gwara in yanke ki tsab in birne ya dawo in ce kin gudu"

"Ki rufa mun asiri umma ki taimakeni karki kasheni, Wayyoooo..!"

Umma ta gyara wuyanta ta saka wukan nan, kokawa hidayat ta fara yi da numfashinta don tsoro, a take fitsari ya kufce mata, umma kuwa ko ajikinta ta didara mata wukan nan a take ya shiga wadda yayi daidai da sumewar hidayat.

Yusuf da ya turo kofa ya shigo kenan daga Maiduguri ganin abunda suke shirin yi yasa yayi sauri ya karɓeta, ɗaukanta yayi zuwa asibiti suka watse da dariya umma harda hawaye, su Surayya na kwatanta yadda hidayat ɗin take yi.

Daga wannan rana da aka yiwa hidayat ɗinki a wuya ko muryar umma taji se jikinta yayi reacting, wani irin tsoron ta take ji kaman rai, su kuma suka samu abun yi.

Yusuf shi de baya hana su Idan ba ya ga dukanta da gaske gasken zasu yi ba, sannan shi baya mata Dukda yana da zafin zuciya sossai.

Ko da Abba ya dawo ko ya tambaye ta ana mata wani abu da gudu take cewa a'a, a haka hidayat tayi rayuwa, tana da shekara goma ta fara musu girki.

Idan be yi daaɗi ba zata daku kuma ta cinye, ko zata amayo hanjinta se ta ci, a hankali a hankali suka sallami me aikinsu gabaɗaya, zata yi breakfast a ci tayi shara, su tafi school su dawo kan islamiyya tayi musu abincin rana tayi wanken wanken safe, kullum se an dake ta a islamiyya sbd letti, tana dawowa zata yi na dare tayi wanke wanken rana, ta wanke musu uniform duka.

Bata da maraba da baiwa a gidan, abunda har yau ta kasa ganewa shine a idanun Abba yusuf kaman ya maida ta ciki amma a bayan idanunshi babu ruwanshi da ita Dukda baya duka ko zaginta, sbd yawan damuwa da yawan kukanta yasa har mutanen layi kan gane tana cikin damuwa.

Bayan wani lokaci!

tana da shekara goma sha huɗu a lokacin Dukda khausar ta gama secondary har an sanya mata rana ma amma har a lokacin hidayat ce ke bautar gidan, wanke wanke take da sauri sbd ta riga tayi letti a islamiyya, tsautsayi ya saka ta fasawa umma cup na tangaran kirjinta da suke a cike Dukda yarantanta ta dafe a fili ta furta

"innalillahi wainna ilahi rajiun"

Bata rufe baki ba umma ta shigo kitchen ɗin, mari ta saukar mata hagu da dama nan ta hauta da wani irin faɗa, kasa bata hakuri tayi ai ko umma tace dawa Allah ya Haɗata ai dama ta lura kwanan nan hidayat ɗin ta fara kwaso halayen rashin kunya zata yi maganinta ta fitar mata dashi a kanta, duka ta yi mata kaman zata kashe ta.

Bayan ta gama wanke wanken da kyar ta fito, ta sanya uniform sbd in ta zauna a gidan ma ba natsuwa zata samu ba, tana tafiya kaman iska ze yarda ita lokaci lokaci ta kan share hawaye, banda raɗaɗi babu abunda fatar jikinta ke yi.

Bata hankara ba taji an sha gabanta.

"Baiwar Allah! Hawayenki ko kogi ne ina Tunanin yana gab da yankewa"

Baya ta matsa tana kallon shi don bata san shi ba.

Yayi murmushi yace

"is ok don't be afraid, sunana hamza I'm a military officer kullum idan har zan tsaya anan a irin wannan lokaci na kan tsinkayi wucewarki cikin zub da hawaye hakan ya kwaɗaita min jin matsalar ki Ko Allah ze sa in iya taimakonki"

Kallonshi kawai take, this is the first time wani yake mata magana cikin kamala da tsantsar kulawa, in aka cire Abba da ummi ƙawarta, tabbas tana bukatar comfort kuma daga gani Ɗayan nan ta aminta dashi sede labarin ta na da tsai.

"Labarina bashi da wani armashin saurara babu abunda ze kara maka banda damuwa da tunani, so ka ga babu amfanin ji"

Kallonta yake da mamaki yace

"amma tukuna shekarunki nawa?"

Tace

"sha huɗu"

Kara wara idanu yayi wadda har ya sakata murmushi yace

"amma shine kika iya zaro zance haka?"

Tana murmushi ta kauda idanunta daga kanshi tare da harɗe hannu tace

"lokuta da dama ba mu muke iya abubuwa dayawa a gashin kanmu ba se abunda rayuwa ta koya maka kake iyawa, rayuwata ba irin ta kowa bace hakan yasa bana sa'a da sa'anni na a fannin komai na rayuwa"

"wow please what's ur name?"

Tace

"HIDAYAT"

#like

#share

#comment

                   🖤Gureenjo🖤