6
by @gureenjoh
KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
Zuhraa
Hamrah
Igiyar Rayuwa
Noor Iman
Ruwan Sama..
Lelewal
GAMON JINI paid
And Now
Kowa Ya ga zabuwa..
PAGE 6
FREE BOOK
"Hidayat! Ni kuwa zan so sanin wannan labari ko zan amfana da wani darasi na zamantekwar rayuwa"
Zata yi magana suka Haɗa idanu da Yusuf dake bautar ƙasa yanzu, irin kallon da yake aika mata yasa tayi saurin wucewa Dukda be taɓa dukanta ba sede ta san yana da manufa me girman gaske a kanta.
Hamza na ta aikin kiranta sede ko waiwaye bata yi ba, Yusuf ya kalla na seconds kan ya juya ya tafi.
Bayan ta dawo daga islamiyya tana shirin shiga gida Kenan taji an fisgo hannunta, a tsorace take Kallonshi har ya isa sashesu da ita a jikin gini ya bugata har Seda ta runtse idanu, manneta yayi sossai ba tare da ya damu da haramcin hakan ba yace
"ki buɗe kunnuwanki da kyau ki saurareni, ya zuwa yanzu kalar muguntar Umma da su khausar kawai kika sani baki san ni ba, amma idan kina so ki fara sani in kara ganinki da kowanni kalar namiji ki gani!"
Kai ta gyaɗa banda hawaye babu abunda ke zuba daga fuskanta sbd yana maganan ne yana tattaɓa jikinta, bayan ya saketa ta fice da gudu cikin kuka Abba be yi dacen mata da ƴaƴa ba, taya mutum me karamci irin shi ze samu ƴaƴa da mata irin umma da su Yusuf?
Ko da ta shiga gida bata dawo daidai ba khausar da duk suka ajiye islamiyya tunda Abba yayi tafiya tace ta yi mata custard a babban jug sbd shi suke son sha yanzu yanzu, ko jaka bata ajiye ba ta shiga kitchen har lokacin jikinta rawa yake na abunda Yusuf yayi mata hawaye kuwa wani na bin wani a fuskanta, ta gwammaci abunda su khausar ke mata sau dubu da abunda yusuf yayi mata yau ta ja Allah ya isa ya fi abinda ya fi a ranta.
Saboda yadda take a ruɗe garin dama custard abu kam yayi gudaje, Sam bata ma kula ba ta ɗauko ta kawo musu dayake haɗewa take da madara da sugar da garin, tana kawowa ta ajiye ta juya har ta ɗaura hannu kan handle na kofansu taji Fahariyya ta saki ashariya, a razane ta juyo gabanta na dukan uku uku.
"Aunty khausi kina ganin irin Gudajen dake cikin custard ɗin nan!"
Aunty khausi da Surayya har rige rigen karɓan cokalin suke, suna gani kuwa suka kirata ta dawo.
"Ɗauka ki shanye!"
Wara idanu tayi a duniya babu abunda bata iya sha irin custard, amai yake sakata hakuri take shirin basu, Khausar ta tsinka mata mari tace
"dauka nace!"
Dauka tayi sede ta kasa kaiwa baki, mikewa suka yi suka danneta suka ɗura mata shi cikin tsantsar mugunta, Surayya bata saki hancinta ba seda custard nan ya kare tas, mikewa tayi zata fice da gudu umma dake zaune tun ɗazu bata ce komai ba se yanzu tace
"dawo ki zauna, kika kuskura kika amayar min da madara da sugar na wlh se na lahira ya ciki jin daaɗi tunda ba guminki bane"
Zama tayi sede bata da wani iko da amanta, duk yadda tayi son dannewa kasawa tayi ta yunkura zata mike Salamatu ta saka mata ƙafa anan ta faɗi a kan hannunta, aman da take dannewa ya kwace mata ta sake shi anan.
Duk mikewa suka yi suna zazzare idanu sbd tas a jikin mus'ab ta kwararo shi, yana mikewa ya sake mata wani bahagon mari da Seda jini ya balle a hancinta, kasa magana yayi ya juya ya fice.
Umma bata barta ba seda ta kwashe aman tas ta wanke wurin da omo ta saka turaren wuta da room freshener kan ta samu ta shiga kitchen ta dinga zuba ruwan sanyi a kanta har haɓon ya tsaya, hannunta da take ji kaman ya samu matsala ta tallafe tana zub da hawaye, a haka ta ɗaura musu abincin dare cikin taka tsantsan don in tayi kuskure kashin ta ya gama bushewa.
Haka ta kwana kan safiya hannun yayi tsami amma babu wadda ya ɗaga mata ƙafa Seda tayi aikace aikace da duk take bata yi fashin school ba don idan bata je Bama se ta ci uban ta hannun umma.
A yammacin ranar ta fito don zuwa Islamiyya har ta kusa isa taji Muryarsa cikin sanyi yace
"Hidayat!"
Tayi saurin juyowa tana kirkirar murmushi tace
"ya hamza ina yini?"
Yace
"lafiya ƙalau ya school?"
Tace
"Alhamdulillah"
Kanta ta mayar kan hannunta dake kumbure tana Tunanin ta yadda zata dakatar dashi da shiga harkarta ba don komai ba se don bazata iya da tashin hankalin da Yusuf ke shirin kawowa rayuwarta ba.
Idanunshi ya saukar inda take kallo a matukar mamakance yace
"Subhanallah! Hidayat me a hannun ki haka?"
Tace
"faɗuwa ne nayi da sauki ma ai"
Yace
"please drop it! Wani irin da sauki ina ganin in ba gurɗewa kika yi ba to tsagewar kashi ne muje a duba miki"
Zata yi musu ya zare mata idanu kwarjininshi ya hanata, haka ta taka ta shiga motar shi da ya buɗe mata, haka kawai ta yarda dashi, gidan wani malami wadda ya kira da kakanshi ya kaita daga gani irin abubuwan da yake yi kenan.
Yana gani kuwa yace gocewar ƙashi ce gyara yayi mata tana ta zub da hawaye sede bata yi ihu ba hakanan babu wadda ya riƙe ta, umarni ya mata ta shiga gidan tace shi ya aiko ta, mikewa tayi ta shige.
Mutumin ya kallo hamza yace
"Ina ka samo yarinyar nan mazan fama? Ka kuwa san ban taɓa ganin yarinya me matuƙar dauriya irin ta ba? Gocewar ƙashi da za'a same shi yanzu ma wani babban se an tara gayya kan a gyara amma natan nan fa har tsami yayi amma hawaye kawai ta zubar"
Hamza ya gyara zama yace
"Rayuwar yarinyar akwai tausayi kaka daga kallo ɗaya zaka fahimci hakan, ni karan kaina na rasa takamaimen abunda ke damunta sede zan bincika in shaa Allah"
Kakan yace
"Allah sarki! Allah ya yaye mata"
Suka amsa da Ameen, se gata ta fito rike da Leda ƙarami.
Godiya ta mishi kan suka fice, a mota hamza ya matsa mata har Seda ta bashi labarinta da irin abunda take fuskanta, bata boye mishi har abunda yusuf yayi mata jiya ba.
Yana da wani kalar zafin zuciya hakan yasa aikinshi na soja ya karɓe shi.
Wani kalar tafasa jininshi ke yi yana ambaton
"innalillahi wainna ilahi rajiun"
Da kyar ya samu yayi controlling kanshi, ita kuwa se hawaye kawai take sharewa, har Suka isa unguwan su be iya cewa komai ba, zata sauka yace
"Hidayat!"
Da sauri ta kalleshi sbd irin muryar da yayi anfani dashi bata taɓa ji daga gareshi ba yace
"I want to help you! Tunda na fara ganinki na san akwai dalilin da Allah ya sa ya Haɗa mu, zaki Aure ni?"
Wani kalar zare idanu tayi kan ta fice da gudu, murmushi ya saki tunda ta gama bashi labarin yake Tunanin ta hanyar da ze iya taimakon ta, hanya mafi sauki kuma shine aure, yana da tabbacin tunda me gidan ya san irin rayuwar da take yi a gidan Dukda ya musu faɗa da barazana sede yana da tabbacin ba bari zasu yi ba So aure ne kadai ze tsallakar da ita wannan siradi, shi kuma yayi alkawarin aurenta ya inganta mata rayuwa.
Wasa wasa hamza ya sabar mata da soyayyar shi me sanyi, Yusuf ya kamata sau biyu ya kikkifa mata maruka sede ba shi ze hana gobe ta saurari hamza ba.
Ranar da Abba ya dawo washegari da yamma suna tsaye da hamza a hanyar ta ta islamiyya se ga Yusuf yana zuwa ya ɗaga hannu ya kifa mata mari yace
"ke tsintacciya marar galihu ashe gargaɗina be shige k...."
Wasu tagwayen maruka da ya saka shi faɗuwa hamza ya sakar mishi kan ya hau naushinshi kaman ya samu jaki, ihu ta kurma tana rokon shi ya kyale shi in ba haka ba ta shiga uku a rikice tana kuka, hamza be barshi ba seda ya karya hannun da yake taɓa ta dashi ɗin.
Da kyar aka kwace shi, kuka kawai take tana
'Na shiga uku!'
Hamza ze yi magana Wayanshi na wurin aiki ya ɗauki ringing da sauri ya saisaita nunfashinshi kan ya ɗaga umarnin tafiya zuwa Zaria aka bashi, ba son barin ta yake ba amma bashi da yadda ze yi, yana kallonta yace
"zan je zaria three weeks work Ina dawowa zan turo su Abba na"
Bata iya ta ce mishi komai ba har ya tafi, kuka take tayi mutane suka kama Yusuf zuwa gida Abba na ganinshi basu zauna ba aka yi asibiti dashi cikin tashin hankali, kwanan shi biyar aka sallamoshi a parlornshi duka ya tara su yana kallon Yusuf yace
"Yusuf me ya faru da kai haka? Kai da wa har ya maka irin wannan raunin?"
Kanshi a ƙasa cikin ladabin kule yace
"Abba kayi hakuri wacce nayi hakan don ita ban burge ta ba babu anfanin tone tone"
Abba yace.
"Tambayarka nayi kuma bana son wani kwana kwana amsa zaka bani"
Ya kara yin kasa da kai yace
"Abba sanadiyar Hidayat wannan abunda ya same ni ya faru, wallahi Abba ina son hidayat ina son mata alkhairi da rayuwa me kyau sede ban san meyasa ta fara biye biyen da ba shine ba, tana da wani saurayi Hamza tun ranar da na fara ganinsu tare na kirata nace mata a matsayina na wanta ina bata shawarar idan sonta yake ya turo magabatanshi ne a yi magana ba kullum ya dinga tareta a hanya yana hure mata kunne ba don ko islamiyya ta dena zuwa, ranar ma har daukarta yayi a mota suka fita se dab magrib ya dawo da ita"
Su umma suka saki salati, Abba kuwa kallon Yusuf kawai yake, cikin damuwar karya ya cigaba.
"Five days back ina dawowa daga aiki kawai na sake ganinsu don naje in hukuntata a matsayin yaya gareta yarinyar nan ta hau min rashin kunya harda cewa ina ruwana da rayuwarta bamu Haɗa komai ba bare in ce zan mata wa'azi, hannu na sa zan janyota mu taho gida kawai saurayin ya rufeni da duka saboda shi Soja ne"
Hawayen da ya gangaro mishi ya share yace
"Abba na san ina son hidayat so na tsakani da Allah, ba zan so ta auri wadda bata da tabbaci a kanshi ba sede ni me iya hakura ne in bar mishi ita, in har shine farin cikinta na bar mishi ita ya aureta"
Abba yace
"Over my dead body Yusuf! Ko shine kaɗai namiji da ya saura a duniya wlh wallahi ba zan bashi auren hidayat ba, hidayat bata da miji se kai"
Ihu ta kurma zata yi magana umma ta gwabe mata baki se kuka da take yi kaman ranta ze fita, kasa shiru tayi tace
"Abba dan Allah karka aura min ya Yusuf wallahi bana son shi"
Abba na kallonta da mamaki yace
"se wa kike so?"
Tace
"Abba hamza yace ze turo iyayenshi in ya dawo daga tafiya don Allah Abba karka aura min yaya Yusuf"
Cikin tsantsar yarinyata take zancen, Abba yace
"Eh lallai wannan ko waye ne ya ɓata min hidayat, aurenki kuwa har Abada ya haramta a gareshi wallahi billahi"
Duk yadda hidayat taso fahimtar da Abba be fahimta ba saboda Yusuf ya riga ya sharewa kanshi Fage, Abba ya riga yayi amanna Yusuf na kaunar ta kuma ba ze cutar da ita ba.
Ganin zata iya birkicewa yasa Abban ma ya yanke za'ayi bukin da na Khausar da saura wata guda in ya so ta karasa secondary ɗin a ɗakinta.
Hmmm a wata gudan nan mutuwa ne kawai bata yi ba, hidimar gidan babu abunda basu sakar mata ba, ga cin zali, ga muguntar Yusuf, ga auren dake ta matsowa duk duniya kuwa babu wadda ta tsana irin Yusuf.
Hamza ya dawo ya zo gidan sede Abba ya ja mishi federal warning a kanta be hakura ba musamman da yaji wadda Abban ya zaɓa mata, haka ya dinga turo mutane Abba ya ki sauraran su karshe iyayenshi suka ce ko ita ce autar mata ba zasu kara komawa gidan neman mishi aurenta ba.
Rana bata karya ranar Juma'a aka sheda daurin aurenta da Yusuf wadda ya sakata doguwar suma, Seda ta sha jini har Leda biyu sanadiyar bukin nan, se a lokacin kuma Abba ya bar fushin da ya ɗauka da ita me tsanani da be taɓa yi ba.
Kwatanta irin zamanta da Yusuf ɓata lokaci ne, Tsananin azabar Rayuwa, yunwa, matsi, mugunta, musgunawa babu abunda bata fuskanta, ga zina da a kullum take Rokon Allah kar ya sakawa yaran mutane a kan nata yaran, tun tana damuwa har ta dena, kayan ɗakinta da ya fi na khausar kullum suna hanyar gidan da ɗauki ɗaiɗai suka karar da komai na gidan nata.
Ita bata san wani amarci ba se baƙar azabar sex irin na Yusuf, bata yi wata biyar ba ciki ya bayyana nan Yusuf yace bata isa ba shi baya son yara.
Duk yadda ya so ta zubar ki tayi se azabanta ya karu, duka kam har bata san sau nawa ta sha a hannunshi ba, ze daki cikinta har se ya so kashe ta Amma da Allah yayi Usman me zuwa duniya ne Seda ya zo, kan haihuwar Usman Abba ya haɗu da kaddarar hatsari inda ya kwanta ciwon da shine yayi ajalinshi, da sana'o'in da take ta samu ta hada mishi abunda ya kamata ita tayi mishi huduba da suna Usman.
Usman na da shekara da watannin da basu wuce uku zuwa biyar ba ta sake samun wani cikin, Yusuf be farga ba seda cikin ya shiga wata biyar, irin dukan da ya mata Seda tayi ta bleeding kaman bazata haife ta ba, da taimakon Allah itama ta haifeta ita ma itace duk wahalar yarinyar uban be san dasu ba, ya kuma yi rantsuwar abincinshi basu da rabo ita kaɗai yake ciyarwa banda yaran. Wallahi ko makiyinta bata mishi fatan rayuwa irin tata. Tunda ta haifi Aisha be sake kusantarta ba se wata rana da ya sha abubuwan shaye shayenshi lokacin Aisha na shekara biyar ya faɗo mata inda kaddarar wannan cikin ya samu, zaginta a kullum yake daga an taɓa ta se ciki..