KOWA YA GA ZABUWA…

8

by @gureenjoh

KOWA YA GA ZABUWA...

   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            

         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:

Zuhraa

Hamrah

Igiyar Rayuwa

Noor Iman

Ruwan Sama..

Lelewal

GAMON JINI paid

And Now

Kowa Ya ga zabuwa..

                      PAGE 8

FREE BOOK

Taku biyu ya qara ya waiwayo ya kalli Farah yace

"baby let's help her she's really in need of that OK?"

Yamutsa fuska tayi kan ta sake mishi hannu ta koma gefe tayi folding hands nata kaman wata babba, girgiza kai yayi ya san fushi tayi sede jininshi ya kasa kyale shi yin biris da wanchan yarinyar, Aisha ya nufa yace

"uhm Gayamin! menene?"

Seda ta kalleshi kaɗan kan tace

"likita yace mamana zata haukace ko ta mutu in aka wuce awa shidda ba'a mata aiki ba gashi yanzu saura awa d'aya.."

Ta karashe da kuka, kallonta yake in disbelief yace

"likita yace haka? Ina babanki?"

"Yayana yaje ya nemo shi kuma na san ko ya same shi baze biya ba sede ya doke shi ya kore shi"

Lumshe kyawawan idanunshi yayi da suka ɗan sauya kaɗan ya mike daga kyakyawar durkuso da yayi a gabanta yace

"muje let's see the doctor"

Hannunta ya kama suka nufi ciki Farah na binsu daga baya baya sbd kyamar Aisha da take, office ɗin likitan ya shiga wadda yayi saurin mikewa daga ganin Moh Raed washe 32 ɗinshi yayi yana Mika mishi hannu sede Raed fuskewa yayi yace

"menene matsalar maman wannan?"

Bayani ya mishi akan an kawo ta an barta da yara gashi tana shirin zauce musu sbd jijjiga da take tayi, yayan yarinyar ma be yi goma ba amma yanzu ya tafi nemo uban su, lumshe idanu yayi da kaman ɗabi'ar shi ce kan ya ware su akan likitan, Seda ya ja iska kan ya tambayi kuɗin aikin.

A lokacin da likitan ya faɗa mishi wani takaici ne ya zo mishi wuya abunda ko dubu ɗari be yi ba, ba tare da ya zauna ba yayi call, se ga ɗaya daga cikin bounchers dake rike da folder ya zo, kudade masu yawa yayi dropping ma likitan yace

"prepare for the operation now!"

Ya juya kenan se kuma ya sake Juyowa, "make sure after the operation you change her to the Amenity ward give her all the care she needs, am very sure this will be morethan enough"

Ya karashe yana nuna kuɗin da yayi dropping ɗin.

Kai likitan yake ta gyaɗawa yana cewa

"in Shaa Allah"

Ficewa yayi yana me kallon agogon Gucci dake daure a hannunshi jirginsu to Paris is in a jiffy gashi he will like to help this little girl more, but he didn't have any other option.

Yana tsaye aka turo Hidayat, Aisha yake ta kokarin consoling sede ganin an fito da mamanta yasa ta sake jakar kayan haihuwar dake hannunta tayi wurin gadon da gudu, kallon Gadon yayi for seconds kan ya ɗauke kai, baze iya cewa ga kamannin maman ba he only saw her coily hair dake zube bisa pillow, her arched eyebrows a slim nose  nd her cherrie lips da suka yi jajazir a bushe alamun yunwa da rashin abinci me kyau

Ba tare da ya sake kallon gadon ba ya Riko Aisha yana rarrashinta, Farah dae bata ce musu komai ba don ba duka abunda suke faɗa take ji ba, hausa na musu wahala sossai gwara ma ita da ƴan uwanta dake chan gida Paris, dayake ita purse na dad ne duk inda zasu tare suke zuwa yasa ko wani shekara take shigowa Nigeria, yau daddyn ta is talking to stranger a gabanta har mantawa ma yayi da ita yau akwai daru, shima da ya san kayanshi in ya kalleta sede ya sakar mata soft smile, a tare ya Riko hannayensu zuwa mota lokacin har mutanen shi sun gama abunda ya shigo dasu asibitin, Manyan snacks ɗin Farah ya ɗiba dayawa ya zuba mata cikin wani fancy Leda ya Mika mata.

Murmushi tayi me kyau tace

"Thank you..."

Se ta rasa sunan da zata kirashi shima murmushi yayi mata for the first time yace

"call me Daddy"

Tace

"thank you Daddy, idan mama ta tashi Allah yasa kar tayi faɗa na kula stranger"

Yana murmushin wayon yarinyar a ranshi yana kwaɗaita mata samun Ingantacciyar ilimi yace

"bazata yi ba idan kika ce mata Daddy Muhammad ne tell her masu sunan basa cuta bare cutarwa"

Godiya tayi mishi, ya ɗaga Farah dake ta fushi ya saka a mota kan ya shiga, Seda yaga shigar Aisha cikin ward ɗin kan yayiwa drivern umarni da su wuce.

Dayawa suna ganinshi Miskilin gaske marar fara'a da sakewa sede yana wasa da yaranshi sossai a ganinshi idan be musu ba wa ze musu? Shi kaɗai suke da a duniya matsayin uwa da uba da dangi, be taɓa Tunanin za'a samu worst uba irin nashi uban ba seda yanzu yaga Aisha ya tabbatar uban ta ma irin nashi ne, hakan yasa ta tsaya mishi a rai.

Daidai last flyover da zasu ɗauka zuwa hanyar Airport idanunshi ya faɗa kanshi, ko ba'a faɗa ba wannan shine Yayan Aisha, da sauri yacewa drivern

"wait!"

Parking suka yi, ya sauke glass yana kallon Usman dake bin mutane yana roko kaman almajiri, wani irin tausayin su ne ya sake mishi dabaibayi, ɗaya daga cikin masu tsaron shi da ya sauko don jin Abunda ogan nasu ke bukata ya kalla yace

"call that boy"

Da sauri yaje ya kira Usman Dukda a tsorace yake sede haka ya biyo shi yana share hawaye akai akai, ganin Raed yasa ya karasa yace

"Dan Allah ka taimaka min mamana bata da lafiya tana asibiti karta mutu ko ta haukace"

Dauke kai Raed yayi yana shafa hancinshi da bayan hannunshi, da kyar ya iya controlling kanshi kan ya juyo ga Usman dake ta kallonshi yace

"a ina ne asibitin? Ina babanku?"

Usman yace

"nima ban sani ba duka, na kasa gane hanyar gida kuma nima ban san sunan asibitin da mamana take ba"

Yanzu da be ga yaron nan ba da wannan uwar ta rasa shi kenan har Abada, eh har Abada mana baze gane gida ba ba kuma ze gane asibiti ba, idan uwar ta mutu ba taimako shikenan Aisha ma zata gantale, idan kuwa ta warke ta ina zata fara neman yaronta a birnin Kano?

"What a worthless father nd a heartless husband!"

Yayi exclaiming kan ya sake kallon Usman yace

"ur mom zata samu lafiya ok? just follow him he will get u back to her"

Yace

"ka san mamana?"

Raed ya ɗan yi murmushi yace

"yeah harda Aisha also"

Washe baki Usman yayi yace

"ka biya ma mamana kuɗin?"

Kai kawai Raed ya gyaɗa don be cika dogon surutu ba ko da yaran Nashi ma, wani irin farin ciki ne ya bayyana a fuskan Usman yace

"Allah ya biya ka da gidan Aljanna ya sa a mizani haka mama tace a gayawa duk mutumin kirkin da yayi mana abun alkhairi"

Murmushi kawai Raed yayi, Usman ya bi wadda aka Haɗa shi dashi zuwa motan karshe suka juya dashi zuwa asibiti yayinda Moh Raed yayi Airport.

A asibiti kuwa gaban ɗakin da Hidayat take Aisha ta tsuguna rungume da jakan maman, lokaci lokaci take murmushin jin daaɗin mamanta zata Samu lafiya, taɓata taji an yi da sauri ta ɗago se taga senior nurse na jiyan nan ce, ta mike tana kallonta se kuma tace

"Ina yini?"

Matar tayi murmushi tace

"Maman ki zata samu lafiya ko"

Tace

"haka Daddy yace in shaa Allah"

Matar tace

"masha Allah" a zaton ta ma daddyn baban su take nufi don ita bata ga Raed ba.

Tace

"mu je in miki wanka ki sauya kayan nan, na kawo miki na ƴata ina yayanki?"

Murna Aisha ta fara kan tace

"Na gode, yayana kuma ya tafi wurin Abba"

Janta senior nurse tayi zuwa toilet nasu na nurses ta mata wanka ta sauya mata kayan da na yaran nata da ta kawowa har Usman, ba karamin tausayi suka bata ba rashin sutura babban matsala ce.

Suna fitowa se ga Usman, da gudu taje ta rungume shi suna murnan ganin juna, ba karamin so da shakuwa bane ke tsakaninsu, shima wanka senior nurse ɗin ta mishi ta sauya mishi kaya.

Godiya suka mata tana ta murmushi cike da yabon irin tarbiyar da yaran suke samu.

Bayan sun dawo sun samu an fito da Hidayat, ɗakin Amenity aka kaita itama Senior nurse ɗin nan ta kaisu taburma ta samo ta shimfiɗa tace su zauna anan kar su damu mamansu da surutu kuma kar su fita ko ina, ɗakin Amenityn harda bayi ta nuna musu yadda zasu yi fitsari in suna ji.

Tana fita Usman ya ja Aisha suka je suka yi alwala suka zo suka yi sallah Dukda basu san ma nawa zasu yi ba don lokacin la'asar ne kuma tun asuba basu yi sallan ba amma dayake yara ne ina ruwansu, ledan da Daddy ya bata ta janyo suka ci Samosa da doughnuts daddaya ba karamin daaɗi abun ya musu ba ba sabon ba, a bayi suka sha ruwa suka dawo suka kwanta akan taburman se bacci.

Wuraren 8 na dare ta fara motsi alamun alluran ya fara saketa, a hankali ta buɗe idanunta da suka kara faɗawa saboda ciwo ta kurawa ceiling Seda ta kwashe kusan mintuna talatin a haka Kan kwakwalwanta ya iya fara aiki, idan ta lissafa daidai kwana tayi ba'a hayyacinta ba ta kuma yini ba'a hayyacinta ba, ina yaranta? Me suka ci?

Wannan Tunanin yasa ta fara kokarin mikewa zaune, daidai lokacin wata nurse ta shigo duba ta, da sauri ta zo ta taimaka mata ta ɗan jingina da pillow cikin karfin hali tace

"Nurse ina yarana?"

Nurse ɗin ta kalli su Aisha tace

"ba su ne waennan ba?"

Da sauri Hidayat ta kalli wurin su se ta sauke wani irin ajiyar zuciya, nurse ɗin na dariya tace

"amma baki tambayi na ciki da kika kwanta dashi ba fa?"

Murmushi Hidayat ta ɗan yi wadda be ko yi mata kyau ba sbd yaƙe ne tace

"su na sani kafin shi dole in fara damuwa dasu tukuna shi ya biyo baya"

Nurse ɗin tace

"yana nursery shima be da cikakken lafiya"

Kai hidayat ta gyaɗa tace

"Allah ya bashi lafiya"

Nurse ɗin ta sake cewa

"ga ruwan zafi da kayan tea Aunty jamila tace kiyi anfani dasu"

Kallon kayan tayi Dukda bata fahimci wacece hakan ba ta gyaɗa kai, dukda tana da tambayoyi fal a ranta sede daga bakin su Usman take so taji komai.

Nurse ɗin ta juya ta fice, Hidayat ta kalli ɗakin ta sake kallo ta san Amenity sbd Abba irin wuraren yake kwanciya kuma ta san yana da tsada don harda frigde da TV da kuma Ac to wa ze biya mata nan?

Kallon Su Aisha tayi se ta fara kiran sunayen su, a tare suka farka ai suna ganinta zaune suka zo da gudu, ɗaya ya zagaya ta ɓangaren dama Aisha ta zo ta hagu  ta kuwa rungumesu a kirjinta hannayenta a kawunansu, Aisha tace

"Mama kin tashi?"

Kai ta gyaɗa, Usman yace

"Mama muna ta damuwa karki mutu ko ki haukace"

Tace

"in na mutu wa ze kular min Daku babana? Ai in shaa Allah tare zamu Rayu har zuwa mutuwarmu"

Aisha tace

"mu girma mu yi kuɗi mu sayi irin motan Daddy, mu dinga kamshi kaman shi ko?"

Shiru hidayat tayi chan ta ɗago su da sauri tace

"Aisha waye Daddy? Waye ya biya kudin aiki na da kuɗin ɗakin nan? Wa ya muku wanka ya sa muku kayan nan? Wa ya baku abinci?"

Waro idanu duk suka yi suna kallonta, se ta gane tambayar sun yi musu yawa kwakwalwansu ya kasa dauka, Tace

"me ya faru da bani da lafiya? Kun san na hana karya ko? Kuma me karya Allah na ƙona shi so bana son karya"

Aisha tace

"Ya Usman ya tafi neman Abba, be dawo ba na fita ina ta kuka se ga Daddy shine ya biya likita, ya bani wannan"

Taje ta ɗauko snacks da ya saura dayawa ta kawowa hidayat karɓa tayi ta buɗe tace

"na shiga uku! Waye kuma Daddy?"

Aisha tace

"cewa fa yayi sunanshi Daddy Muhammad kuma yace in kin tambaya in ce miki me sunan baya cuta baya cutarwa"

Kallon Aisha kawai take, Usman yace

"nima na je neman Abba ban ganshi ba, Naga kuma ana samun kudi idan aka roka shine nima nake ta roko in tara in kawo se na ganshi, shine ya saka aka dawo dani a mota me sanyi"

Hidayat dae ta kalli wannan ta kalli wanchan, karshe ta lumshe idanu kan tace a zuciyarta

"Allah na gode maka da ka turo mana wannan mutumin Aljannan ya taimaka mana Allah Kaine abun godiya ya Allah"

Se ta buɗe idanu tace

"Usman me yasa kayi roko ban hana roko ba?"

Se ya fara hawaye yace

"Mama bana so ki mutu ne"

Tace

"ya isa, karka sake ka ji?"

Kai ya gyaɗa ta sa hannu ta share mishi hawaye yunwar da take ji yasa ta kalli kayan tea ɗin se ta kalli su Aisha tace

"waye kuma Aunty jamila?"

Nan suka bata labarinta se ta fahimci senior nurse ce, Usman ta sa ya kawo mata abu ta kurkure bakinta don ba brush, da taimakon su ta hada tea ta samu ta sha da Samosa a zuciyarta banda Adu'a da fatan alkhairi babu abunda take yiwa wannan Muhammad ɗin kwarai ya ci sunan nashi, kuma in shaa Allahu har Abada bazata taɓa mantawa da shi ba.

Jaka ta saka Aisha ta miko mata, buɗewan da zata yi se tayi tozali da wani farin envelope, a hankali ta buɗe a firgice tayi watsi dashi kaman wacce ta taɓa wuta kan ta furta

"innalillahi wainna ilahi rajiun"

#like

#share

#comment

                   🖤Gureenjoh🖤