KOWA YA GA ZABUWA…

11

by @gureenjoh

KOWA YA GA ZABUWA...

   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            

         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:

Zuhraa

Hamrah

Igiyar Rayuwa

Noor Iman

Ruwan Sama..

Lelewal

GAMON JINI paid

And Now

Kowa Ya ga zabuwa..

                      PAGE 11

FREE BOOK

Ameeratuh kin hana ni baccin safe🤧 ga shinan kan ki zo min a mafarki🚶‍♀️🚶‍♀️

"Hidayat haba mana kar imaninki yayi ƙaranci ki dinga furta kalmomin da zaki je kiyi saɓo, Usman kwanan shi ya riga ya ƙare shine dalilin mutuwar shi Sam baki yi Sila ba sbd be yi gaggawa ba mu ma kuma ba jinkiri mu kayi ba, yau kwana bakwai kenan bakya ci bakya sha, sbd kuka dubi idanunki yadda suka koma ki kalla ki ga Aisha yadda take a firgice tun rasuwar nan shi karan kanshi junior  bakya bashi kulawar da ta dace idan ke kika Gaza su kuma fa?"

Idanunta da suke a sussuntume tun rasuwar ta ɗaga ta kalli ummi tace cikin wani irin murya

"haka ne! Na gode ummi yanzu ina ga lokaci yayi da zan yi abunda ya dace, ba zan yi faɗa da YUSUF yanzu ba amma ba shi yake nufin ya sha a banza ba, yanzu ne na fara koyo daga karatun da duniya take koyar dani, zan yi bita in hardace a duk sadda na tashi amsa jarabawar baze yiwa kowa daaɗi ba saboda da 100/100 zan fita, yanzu zan iya yin duk abunda ya dace saboda yarana biyun nan da kuma fansar jinin Usman... YUSUF! hmmm"

Dukda ummi bata fahimci maganan ta ba, ita dae tunda tayi magana yau da sauki, abinci wadda ummi na shigowa gidan hidayat ta mika mata envelope da Moh Raed ya ajiye mata Dukda bata san waye shi ba ya taimaka mata har aka gama gaisuwar usman ba'a rasa abinci da ruwa ba.

A gabanta ta ajiye Seda ta kalli abincin na seconds kan mutumin ya faɗo mata a rai, Allah kaɗai ya san daga ina yake ya tsaya ya taimakesu ba tare da neman komai a wurinsu ba, ko ma dae menene she's so much indebted to him.

A ranan ummi ta koma gidansu ganin Hidayat ta dena koke koken ta natsu, kan Ummi ta tafi babu abunda bata mata ba har abinci ta sake girka wani ta sa a food flask ta ajiye mata, yamma Lis tana yiwa Junior wanka Aisha da yanzu babu yawan maganan tan nan na zaune gefe tayi tagumi kaman wata babba.

Kaman an jefo shi haka ya faɗo gidan tun daga dukan da yayi musu ita da Usman bata sake ganinshi ba se a yau Usman na kwana na bakwai zuwa takwas a rami, yadda ya shigo yasa Aisha firgita ta tashi da gudu taje ta faɗa jikin hidayat tana kankameta kaman zata shide take cewa

"Abba! Abba kayi hakuri don Allah karka dakemu... Ya Usman ya mutu nima karka kasheni karka rabani da mamana!"

Hawaye ne ya sulmiyowa hidayat ta ɗago rinannun idanunta ta zube a fuskanshi, haɗe rai yayi kaman wani mala'ikan ɗaukan rai yace

"ke ya ma sunanki? Wallahi kika kuskura na rike ki se na lahira ya fi ki jin daaɗi"

Hidayat bata sake Kallonshi ba ta ɗago ta tana share mata hawayen dake zuba tace

"karki sake kuka Aishana ai yanzu kuma me dukanki se ruwan sama shi ɗin ma se in na bari, ki dena kukan nan bana so"

Har ya wuce ya dawo yace

"me kike cewa?"

Mikewa tayi tare da ajiyewa Aisha junior a cinyar ta ta kalleshi cikin idanu tace

"nace me taɓa ta kai har ma ni a yanzu kam se ruwan sama!"

"kina nufin ban isa taɓaku be kenan?"

Da mamaki yake maganan ganin ko ɗar babu a fuskanta se wani irin shakkar ta ya rufe shi da a da ne ze iya kai mata hannu zuwa yanzu.

"Yadda kunnuwanka suka ji"

"Ah lallai kan mage ya waye, karki manta a gidana kike kuma har yanzu ni mijinki ne, ita kuma wannan ƴata ce don haka ina da ikon yin yadda na ga dama a lokacin da na ga dama.."

Wani irin dariyar rainin hankali hidayat ta saki kan ta juya manyan idanunta tana kallon gidan tace

"Gida fa kace? Ai ni ban ga gida ba banda kasungumin daji me cike da namun dabba masu hatsari da ban tsoro, jikin hidayat kuwa daga kwana bakwai baya ka datse duk wani alakarka da ita, datsewa ta har Abada kuwa... Ashe se yau ka san Aisha ƴar ka ce? To kaji da kyau Aisha da Muhammad Raed ƴaƴan hidayat shine sunansu, basu san wanene yusuf ba kuma ba za su san shi ba. har Abada sunansu ya tashi daga Aisha Yusuf zuwa Aisha hidayat Abubakar, ni nice uban su kuma ni ce uwar su don haka ka kiyaye alakanta kanka dasu"

Gabaɗaya idanunshi a waje suke yana mamakin wannan sabuwar hidayat da be taɓa gani ba, kwarjininta da yadda take kallon shi cikin idanu babu tsoro se ma hango wani wutar bala'i dake tashi a cikin idanunta yasa yaji wani sanyi sanyi na kokarin lulluɓe shi.

Cikin karfin hali yace

"kin san a yau na sake ki zan iya auren mata huɗu rus? Kuma a yau na sake ki baki da wurin zuwa so dole ki dawo nan ɗin ki tsuguna a gabana ki roki gafara a lokacin kuma ina ga lokaci ya riga ya kure miki..."

Hannunta ta harɗe tace

"babu macen da zata iya zama Da Mugun Miji irin ka Yusuf idan ba hidayat ba har Abada ba'a yi macen da zata iya shigowa wannan kurkukun kaddarar ba, kuma ka ji da kyau idan har na saka kafafuna na fita daga gidan nan wallahi wallahi ko mutuwa zan yi a waje na gama taka harabar gidan nan kenan  gwara in mutu da in sake alakanta kaina da kai... Azzalumi, Fasiki, makashi..."

Tayi maganan hawaye na gangaro mata sede fa ba shi ya nuna gazawarta ba, hawayen na wutar bala'in dake cin ƙasar zuciyarta ne..

"Ni kike kira da waennan sunayen? Kije na sake ki saki BIYU"

Wani dariya tayi tare da haɗe hannunta ya bada sautin clap tace

"tafi nono fari, ko baka sakeni ba dama bani da ra'ayin ci gaba da zama da kai.."

Har ya fara tafiya tace

"Baka ji ba!"

Waiwayowa yayi tana murmushi tace

"Karka yi tunanin Idan hidayat ta tafi ta tafi kenan fa, Hidayat zata dawo idan har ta Rayu zata dawo ta zama WUTAR DAJIN da babu zato babu tsammani se de kawai a ganta ta mamaye dajin, se ta tabbatar ta yagalgala rayuwarka ta yadda baka yi zato ba, nayi alkawari ni hidayat daga yau a gareka kadangariyar bakin tulu ce a bar ni na ɓata ruwa a tabani kuwa a fashe tulun... Daga rana irin ta yau jinin Usman ba ze barka ba har se ka je inda ka tura shi....

Kuskurenka ɗaya Yusuf! Shine na taɓa wutsiyar damisar dake bacci cikin yunwar kwana da kwanaki.. Ka ga ko me kwatarka se Allah.."

Gabanshi ta karaso ta Haɗa yatsunta biyu suka bada wani sautin ɗas har sau uku kan tace

"put this at the back of your thick lunatic skull!! Zan dawo.. Hidayat zata dawo"

Tana kai nan ta juya ta ɗauki junior tare da kama hannun Aisha suka shige ɗaki, sabbin kayansu na suna ta fitar musu tare da shirya su a wani jaka ta Haɗa na Junior ma daban, wani Waist bag wadda daga gani ya ji jiki ta dauka ta ɗaura a kwankwasonta kan ta goya junior ta dauki hijab ta sakawa Aisha ta dauki nata ta saka suka fito..

Tunda ta kama tafiya ko waiwayen gidan bata sake ba, tana fita kuwa taji wani sabon iskar ƴanci ya lulluɓe ta, tafiyar kafa suka yi sossai in Aisha ta gaji su huta, ruwa kuwa in sun ga masallaci se su je randar wurin su sha.

Dab magrib suka isa gidan Abba, tana da yakinin baza su karɓe ta ba sede bata da wurin zuwa da ya wuce nan, bata da ko sisi a jikinta.

Da sallama ta shiga parlorn ganin umma da Surayya tayi zaune suna kallo Dukda chanje chanje da ta gani na ja baya a garesu hakan be hana ta duƙawa ba tace

"Umma ina yini?"

Wani taɓe baki umma dake aika mata da kallon uku saura kwata tayi tace

"da ban wuni ba kya ganni?"

Tayi maganan tana dauke kai, Surraya ta maka mata harara don har yau takaicin dukan da taci take yi tace

"me ya kawoki wurin mu? Ina da kafafunki kika je police station kika sa suka mana tsakani? Me kika zo nema yanzu kuma"

"Daga gida nake!"

Ta faɗa kanta kasa..

"Eh na san daga gida kike tunda gidan Yusuf ɗin ba daji bane, shine kika kamo hanya kika zo mana da magariban nan?"

Cewar umma.

"Ya sakeni"

Wani irin dariya umma da Surayya suka yi kan Surayya tace

"to mu ina ruwan mu don ya sakeki, shine zaki zo mana nan? Kinga ki je chan ki san yadda zaki yi"

Umma tace

"nan gidanku ne? Ko kina da gado a gidan nan ne? Me gidan nan kin kashe shi kuma a iya sanina bakya daga cikin ƴaƴansa"

Kanta kasa tace

"Don Allah kuyi hakuri bani da kowa a duniyan nan se ku, in kuka gujeni ban san inda zan yi ba"

Umma na mikewa tsaye tace

"au kin san da hakan kika kaso aurenki kika zo mana? Bama ki da kunya wallahi..."

Surayya tace

"kinga babu abunda ya hadamu dake, babu abunda ya Haɗa ƴar tsintuwa da ƴaƴan halak ki je chan ki san nayi"

Hawaye masu zafi ne suka zubo mata, laifin iyayenta ne ba nata ba, kowa ana haifanshi cikin gata da kauna amma sun tauye mata wannan farin cikin, a hankali tace

"don Allah karku min haka, ku taimakeni bani da wani gida a duniyan nan se nan"

Umma tace

"ke kinga tsinto ki aka yi, kuma wadda ya tsinto kin nan ya mutu don haka baki da wani alaka da gidan nan don gida namu ne in har mu ke da iko dashi kuwa baki da matsuguni ko na kwayar zarra a cikin gidan nan"

Hawayenta gudu suka kara, a Tunaninta umma zasu karɓeta ko da bauta zata ke musu bazata rasa na baiwa Aisha ba, cikin zub da hawaye tace

"don Allah umma kiyi hakuri, ni amana ce a hannun ku bani da wani gata a duniyan nan se naku, ku kaɗai ne gata na"

Surayya tace

"mu ba gatan ki bane! Mu Ba gatan ki bane kije chan ki nemi gatan ki, ah to"

Umma tace

"se yanzu kika san mu gatan ki ne? Shafaffiya da mai, ina har korata kika sa aka yi a cikin gidan nan? Ko kin manta ne In tuna miki, ina ce wata biyu baya kika sa aka yi mana tsakani dake bayan kin sa an fitar mana da jini? Tun da wuri ki san Inda dare ya miki da inda gari zata waye miki"

Dole ta sake jarrabawa saboda yaranta tana tsoron su faɗa mummunan hali idan har ta bar gidan Abba, da ita kaɗai ce zata iya ficewa sede Su Junior..

Cikin rawar murya tace

"Umma kuyi hakuri bani da Inda zan je, ku rufamin asiri ko saboda Aisha da Junior ku barni in zauna Anan in muka tafi a wannan lokacin komai ze iya faruwa damu"

"babu ruwan mu da abunda ze sameku, duk abunda ze sameku sede ya sameku kinga tashi ki fitar min daga gida.."

Umma tayi maganan tana nuna kofa..

Mikewa hidayat tayi daga ita har Aisha hawaye kawai suke yi, zuciyarta yayi nauyi matuka, a hankali wani irin tsanar ahalin da ta taso a ciki na mamayeta, ficewa suka yi daga gidan suka kama tafiya ba tare da sun san inda zasu ba.

Har magrib yayi suna yawo, gida ta gani ta shiga da sallama sede sallamar duniyan nan sun ƙi amsa mata Dukda suna zazzaune ne suna kallonta tana Kallonsu, bata ga laifin su ba sanin yadda duniya ta zama se ta fice, a haka ta jera Gidaje kusan biyar don ta samu tayi sallah sede sun ƙi amsa mata sallama ma bare ta roke su.

Masallaci ta samu lokacin ana kiran isha anan sukayi magrib da isha, suna nan zaune cikin wani irin hali junior na bayanta Aisha na cikin jikinta har wurin karfe goma me gadin masallacin ya zo yace

"baiwar Allah ku kara gaba lokacin rufe masallacin yayi"

Rokon shi ta fara akan ya bari su kwana na yau kaɗai Sam ya ƙi haka suka mike suka fito.

Tafiya suke tayi ba tare da sanin inda zasu ba, ko kula da inda suke zuwan bata yi tunani ya ci karfinta, damuwa yayi mata yawa, garin yayi shiru banda hasken farin wata babu abunda yake sararin na duniya kowa na cikin gidanshi a killace banda ita da yaranta.

"Kai baba..! Wanchan yarinyar tayi Sak yadda honor ya tsara mana wacce yake bukata"

Maganan da ya shiga kunnenta kenan ya sakata tsayuwa Chakk ta kalli hagu da damanta ko ɗan tsuntsu babu.. Wadda aka kira da baban ne yace

"wai wannan gansamemiya taya tayi kama da kiyasin shi? Ka manta yarinya yace wacce bata kai goma ba?"

Na farkon yace

"kai dallah chan kalli hannun matar"

"kai kai kai wallahi da gaskiyarka wannan ma ai har ta wuce yadda ya kiyasta mana, kaga mu je mu kwaceta mu kaita kila a yau ma zasu yi abunda zasu yi da ita don zaɓe ya riga ya gama karatowa"

Basu gama maganan ba Hidayat ta damke hannun Aisha tace

"Aisha zamu fara gudu, kiyi gudu da iyakar karfin ki in ba haka ba zamu rasa juna..."

A take suka runtuma da gudu mutanen suka biyo bayansu suma da mugun gudu.....

#like

#share

#comment

                     🖤Gureenjo🖤