17
by @gureenjoh
KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
Zuhraa
Hamrah
Igiyar Rayuwa
Noor Iman
Ruwan Sama..
Lelewal
GAMON JINI paid
And Now
Kowa Ya ga zabuwa..
PAGE 17
FREE BOOK
"Ya Hamza..!"
Ta faɗa tana wara dukkan idanunta da ta saka musu kwalli waje, duk da yadda ya kara girma da jiki ya tara kasumba gwanin burgewa hakan be hanata shaida shi ba a kallo ɗaya sbd shine mutum na farko da ya fara nuna mata ƙauna a duniya bayan Abba kuma kullum yana ranta..
Shi kuwa kokarin ce mata sorry yake amma ganin ta kira sunanshi yasa ya ɗan dakata tare da sanya mata idanu na seconds se kuma ya waro su gabaɗaya yace
"Hidayat!"
Dariya suka saki a tare yace
"what a coincidence! Hidayat me kike yi a Paris? Taya kika zo?"
Tana murmushi tace
"labari ne mai tsawo"
Yace
"then mu je mu zauna se in ji da kyau, aurenki fa?"
Kanta ta ɗan dukar tace
"ya mutu"
Wani sihirtaccen murmushi ya saki tare da Juyawa ta bi bayanshi Sam ta mance ma da Aisha jiran ta take da ice cream ɗin da ya ɓare again, wurin wasu kujeru guda biyu suka je suka zauna yana tsokanarta akan ta ƙara girma tayi kyau tana ta dariya..
Daga inda yake zaune sanye da designers Riga da wando na kamfanin Versace idanunshi sanye da designer shade na Swarovski ba karamin kyau yayi ba barin ma sabon diamond ear ring da ya sauya dake ta kyalli, tun da ta mike ya tsinci idanunshi a kanta har ta shige be dauke ba, daidai fitowanta da karon da suka yi duk a kan idanunshi..
Ganin suna dariya da magana alamu sun san juna yasa ya ɗauke kai yana jan tsiririn tsaki, agogonshi ya kalla se ya ɗauke kai again, Aisha dake zaune ya sake kallo ya ɗaga kai ya kalli sun nemi wuri sun zauna suna ci gaba da dariya, wani irin ɓacin rai ne ya bijiro mishi da be san na menene ba, miƙewa yayi kaman ze nufi inda suke se ya fasa ya shiga shagon ya sayo wani ice cream ɗin ya zo ya ba Aisha duk yana kokarin hana idanunshi kallon ɓarayin da suke..
Ita kuwa Shap ta ma mance dasu, a hankali take ba Hamza labarin abubuwan da suka faru tun tana dauriya har ta fara kuka tana zuwa wurin rasuwar Abba ta dakata tana hawaye sossai, handkerchief hamza ya ciro ya mika mata ta saka hannu zata karɓa se suka Haɗa idanu..
Idanunshi sun sauya sossai wadda kallon cikinsu ya haddasa mata wani mummunar faɗuwar gaba, a table ɗin ya zo ya zube hannayenshi ya ɗan duƙa kaɗan yana kallonta ba tare da ya kalli hamza ba yace
"can u please get up mu tafi? U can't keep me waiting for u miss hidayat don't forget am ur boss"
Mikewa tayi da sauri tace
"Sorry sir..!"
Tsaki ya ja ba tare da ya kalli inda Hamza yake ba ya juya ya wuce.
Hamza yace
"who is he?"
A sanyaye tace
"my boss as he says, bari na tafi we continue in muka haɗu gobe"
Yace
"ur digits pls"
Ta karɓi phone nashi ta saka mishi tana kallon motan Raed da har ya tayar, da sauri ta karasa ta buɗe baya ta shiga bata gama rufe motar ba ya fisga da gudu ya bar wurin..
Har suka isa gida yana cin rai ko yaran babu wadda ya cewa kala, Kimorah da ya samu ce ta ɗan rage mishi damuwar da yake shirin bijiro mishi wadda ya mance ya kalar damuwar take tun da ya sa kafa ya bar gidan uban shi..
Washegari bayan ta gama duk abunda ya zama aikinta ta basu breakfast suna yi ita kuma ta shiga ta shirya, ta fito sanye da straight skirt brown da kuma blouse riga brown nd white se ta ɗaura kimono shara shara a kai ta saka gyale light Brown idanunta sanye da kwallin dake kara mata wani sirrin kyau yake kara musu haske da daukar idanu se lip balm da ta saka a baki..
Tana fitowa wayanta na kira, ɗagawa tayi tana nufan dining ɗin tace
"Good morning ya hamza"
Yace
"morning heedayaah"
Yadda ya kira sunan se da ya sakata murmushi yace
"kin fito ne?"
Tace
"nop yanzu dae nake shirin fita"
Yace
"ai ko ni kam zumudi ya hanani zama in yi abunda ya kamata yanzu haka ina cikin school ɗin ku ko zaki bani address dinku na zo na dauke ki?"
Girgiza kai tayi da sauri kaman yana gabanta tace
"noo karka damu zan fito yanzu kawai ka bani mintuna"
Yace
"as u says my queen"
Dariya tayi tana sauke wayan, Satan kallon shi tayi se suka Haɗa idanu..
A hankali tace
"good morning sir"
Be amsa ba, se yaran ya kalla yace
"Horry up girls I wanna drop u guys today"
Da sauri suka miƙe suna tattare jakukunansu da lunch box ɗinsu suka fice suna ce mata
"bye Miss hidayat"
Aisha ma tace
"bye mama"
Daga haka suka fice.
Mikewa yayi ya kwashi phones ɗinshi, idanunta ta ɗan ɗago daidai zuwa hannunshi na hagu da ya ɗan tara farce fari sol, ganganta ya zo har tana jin kamshinshi na hawa kanta da sauri ta fara wasa da fingers ɗinta kaman zata karye su..
Idanunshi ya ɗan zuba mata kaman ze yi magana se kuma ya fasa, stairs ya nufa har ya ɗaura hannu a kai yace cikin harshen turanci
"rayuwa ba baƙon abu bane a gareki, ya riga ya koya miki darasin da zaki hankalta.. Idan kin dauka ruwanki idan kuma kika sake wani kuskuren a karo na biyu shima matsalar ki ce, I just want to remind you cewa aiki kike min, and I'm using ur salary to sponsor you ba zan lamunci wasa a aiki ba bcs akwai dayawa masu nema na ɗauka na baki, idan tara samari shine abunda zaki fara then I have no any other option than to dismiss you.. Be careful miss hidayat"
Tun da ya fara magana gabanta ke faɗuwa, zuciyarta har wani rawa rawa yake me yake nufi? Tara samari!
Da sauri ta ɗago zata mishi bayani waye hamza se ta ga wayam baya wurin, ajiyar zuciya ta sauke ta fice ba tare da ta bi ta kan Breakfast ba dama junior wurin miss Mary take barin shi.
Har ta isa makaranta juya maganganun na Raed take tana so ta fahimci inda ya dosa sede ta kasa, da suka haɗu da hamza kuwa ta ma mance da wani Raed ta cigaba da bashi labari..
Ya tausaya mata kwarai, tace
"kai fa? Kayi aure?"
Yace
"uhmm last 3 months mahaifiyata ta sa aka ɗaura min aure da wata cousin ɗina they thought asiri kika yi min saboda ban san ina son ki dayawa ba seda aka ɗaura miki aure da Yusuf, karamin zaucewa nayi wadda sanadiyar shi har na bar aikin soja, yanzu ina maintaining company ɗin dad ɗina ne yanzu ma wani business deal ne ya kawo ni Paris, ashe Allah ya san abunda ya tanadar min anan"
Murmushi ta saki kawai tace
"Allah ya baku zaman lafiya"
Yace
"Ameen, but don't bother hakan ba shine ze hanani aurenki ba, I promised to marry you in shaa Allah I will stick to my promise bcs I still love you"
Lumshe idanunta tayi tare da ware su bisa gefen hanya tana kallon ɗaiɗaikun mutanen da suke wucewa ta jikin car ɗin..
"I'm sorry to say yanzu babu aure kusa a tsarin rayuwata, ba zan yi aure ba har se na gama karatu na ɗauki fansar ran Usman I cannot just forget abt that, kuma bana son wani cikas da ze dakatar dani daga wannan kudiri kayi hakuri ya hamza!"
Kallonta kawai yake she's now a grown up woman ba kaman sadda ya Santa ba, tana magana da hankali da kuma natsuwa, Sam maganan ta be dame shi ba yace
"na sani and I will help u with all my strength idan bukatar hakan ta taso har ki cimma Burin ki, I just want ur love nd care Hidayat..!"
Ya kira sunan a hankali, ajiyar zuciya ta sauke tace
"zan yi shawara akan hakan na gode"
Kai ya gyaɗa yace
"I would like to see Junior and Aisha gashi flight ɗin yamma zan bi na koma Nigeria"
Ko karen hauka ne ya cije ta bazata kaishi gidan Raed ba, a hankali tace
"eyyaa next time in shaa Allah"
Murmushi kawai yayi sun ɗan taɓa hira suka yi sallama, kuɗi ya bata ta ƙi karɓa se da yayi da gaske kan ta amsa ta Mishi godiya ta shige school..
Bayan ta dawo ta hau ayyukan ta kan yaran su dawo, tana cikin kitchen take ta jin ringing na landline ɗinsu wanke hannayenta tayi ta fito ta zo ta ɗauka ta saka a kunne se tace
"Assalamu Alaikum warahmatullah"
Shiru aka ɗan yi kan taji muryar wata dattijuwa tace
"Wa'alaikumussalam warahmatullah yau sallama ake min daga gidan Raed?"
Muryar wata dattijuwa ya ratsa kunnuwanta, a natse tace
"Ina yini hajiya!"
Matar na hawaye har muryarta ya bayyana hakan tace
"lafiya ƙalau Alhamdulillah ƴan nan wacece ke?"
Hidaya na mamakin halin da matar ta shiga kawai daga jin hausa da kuma sallama a gidan na Raed tace
"Sunana hidayat, ni ce sabuwar nanny ɗin su Norah"
Kuka kawai matar ta saki sossai tana cewa
"Alhamdulillah adu'ata da na jima ina yi ne Allah ya amsa mini, ke ɗin kaman haske ce don Allah Don Annabi ki taimaki rayuwar waennan bayin na Allah, rayuwar su ya gama tabarbarewa bani da yadda zan yi ne nake Kallonsu a haka... Hidayat ki min alkawari zaki cecesu ki fitar dasu daga cikin baƙin duhun da suke ciki"
Hidayat tace
"kiyi hakuri hajiya ki dena kukan nan, in Shaa Allah zan yi miki duk abunda kike bukata in har be fita a musulunci ba"
Godiya tayi ta mata kaman zata fito ta wayan ta duƙa mata, hakan ya taɓa zuciyar hidayat sossai a hankali matar tace
"sunana Hafsah amma ƴaƴana da jikokina suna kirana Daadida"
Kwarai ta taɓa jin sunan na Daadida eh ta taɓa ji wurin Raed, itace kullum yake yiwa masifa cikin waya..
"Nice na haifi mahaifin Raed"
Shiru hidayat tayi tana sauraran ta, ashe suna da dangi da ƴan uwa kuma musulmai shine suke rayuwa cikin ɓata?
"Rayuwar Raed abun a tausayawa ne kwarai da gaske, sbd be taso cikin farin ciki kaman kowanni yaro ba, ya rasa mahaifiyarshi tun yana shekara uku banda azaba da baƙar rayuwa be san komai ba a wurin yadikkonanshi da Mahaifinshi karan kanshi... Labarin Raed labari ne me tsawo da ba ze yiwu a waya ba sede abunda na sani baƙar Gaaba ce me tsanani tsakanin shi da Mahaifinshi hakanan be san komai ba game da addini, gashi yayi auren wuri da yara suma mahaifiyarsu ba musulma bace ƴar marikinshi ne ya aura kuma ta mutu ta bar mishi yaran babu addini.."
Tayi shiru tana fyace majina tace
"Kiyi mini alkawari za kiyi wannan aikin jihadin? Wlh Allah ne kaɗai ya san sakamakonki in kika taimaki rayuwar waennan Bayin Allahn"
Ajiyar zuciya me karfi hidayat ta sauke, no wonder rayuwarsu yake a haka, ashe akwai binnannen abu a ƙasa cikin sanyin murya tace
"in shaa Allahu zan yi iya kokarina wurin ganin na taimakesu saboda Allah"
Godiya sossai Daadida ta mata suka yi sallama akan zata ke kiranta irin wannan lokacin a landline ɗin gidan..
Kitchen ta koma ta cigaba da aiki cike da tunanuka iri iri, tana cikin shirya dining yaran suka shigo Norah da Aisha suka mata sannu yayinda Farrah ta shige ɗakinta ba tare da ta kula ta ba, Norah da yanzu ta kan ɗan taimaka mata da wani abu ne ta shiga ta taya Farrah wanka yayinda Aisha tayi da kanta suka zo suka fara cin abinci..
Ita dae hidayat Tunanin ta yadda zata fara shiga rayuwar Raed har ta sauya shi take, mutumin da idan tana ganganshi jininta kaman tsinkewa yake, idan taji muryarshi gabanta har faɗuwa yake idan kuwa ya tsura mata waennan idanun nashi masu yanayi da na snake se taji kaman fitsari ze kufce mata shine tayi alkawarin sauyawa! Ta ina zata fara kuma ta yaya?
Bayan sun gama cin abincin ta tattare ta saka Aisha da Norah Alwala suka zo suka yi sallah, bacci suka yi se bayan la'asar suka fara lessons nasu na Qur'ani da ta saba musu.
Bayan sun gama suna zaune a parlorn na sama ya shigo babu sallama, a gajiya yake tilis har layi yake sbd zazzafar wasar da suka yi yau ya haɗu kuma da ƴar damuwar da yake dankare chan kasan ranshi wadda ya kasa cisgewa, da ita suka fara Haɗa idanu Norah tace
"laaaaa dad u didn't say salam"
Ɗan kallon yarinyar yayi cikin rashin fahimta, tana kallon hidayat tace
"Miss hidayat ina kin ce dole ne musulmi yayiwa ɗan uwanshi musulmi sallama idan ze shiga wuri kuma na ciki ma dole ne su amsa?"
Hidayat ba tare da ta kalleshi ba tace
"kwarai kuwa Norah kuma akwai lada a cikin sallama"
Aisha tace
"eh ai kuma idan baka da lada dayawa bazaka shiga aljanna ba"
Norah ta gyaɗa kai, duk be kallesu ba se ita ne ya zubewa gajiyayyun idanunshi yace
"idan mutum ya mance fa?"
Husky musculine Muryarshi ya dake ta, a hankali ta ɗaura idanunta a kanshi cikin kankan da murya tace
"se ya koma da baya yayo in an amsa se ya shigo"
Juyawa yayi ya fice se ya dawo yace
"Assalamu Alaikum"
Duka suka amsa Mishi suna murmurshi..
Norah da Aisha suka ce
"welcome daad"
Kai ya gyaɗa kawai ya shige room ɗinshi, ajiyar zuciya me karfi hidayat ta sauke bata taɓa zaton ze koma ya sake sallama ba, idan ko hakane zata yi anfani da yaran sossai wurin ganin ta sauya shi..
Tana cikin Tunaninta Farrah da ta bishi ɗakin ta fito da gudu tace
"Daadddy is throwing up"
Dukkansu mikewa suka yi Norah tace
"is he sick?"
Hidayat da tunda ta kalleshi take Tunanin wani abun na damunshi ta wuce ɗakin ba tare da Tunanin komai ba.
Duƙe yake gaban washing hand base se amai yake kwararawa a wahalace, a gefen shi ta tsaya tace
"sannu!"
Kai ya gyaɗa mata har ya gama, ruwa ta saka mishi a hannu ya wanke fuskanshi da bakinshi yace
"I wanna take shower"
Fita tayi gabaɗaya a ɗakin taje wurin miss Mary ta sakata kiran family doctor ɗinsu don daga gani dauriya kawai yake, ko da ta dawo a tsaye ta samu Su Norah duk suna cikin damuwa, Norah ta tura ta duba ko ya gama shiryawa ta dawo tace mata ya kwanta ya rufe da blanket yana ta rawar ɗari..
Cikin mintuna likitan ya zo ya hau dubashi nan ya hada allura ya mishi ya ba Paul takarda ya sayo magani, bayan ya fito ya cewa hidayat a tabbatar ya sha tea kan ya hadiye maganin don da yunwa a tare dashi..
Bayan Paul ya dawo ya bata maganin, kitchen ta shiga gabanta na faɗuwa ta Haɗa tea ɗin ta ɗauko ta nufi ɗakin, da sallama ta tura kofan ɗakin...
#Vote
#share
#comment
🖤Gureenjoh🖤