19
by @gureenjoh
KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
Zuhraa
Hamrah
Igiyar Rayuwa
Noor Iman
Ruwan Sama..
Lelewal
GAMON JINI paid
And Now
Kowa Ya ga zabuwa..
PAGE 19
FREE BOOK
Wannan shafi naku ne ɗaukacin masoyana da kuka tayani murnan kamalla bautar kasa ta lafiya, especially Gureenjo Novels group bazaku kirgu ba da na kirgo ku one by one sede in har kina karanta wannan just know that am really grateful and I sincerely appreciate...na gode sossai matsayinku a raina bazata kirgu ba kuma na ji daaɗi kwarai.. Allah ubangiji ya bar ƙauna😍🥰
18/03/1986
Zaune take dabas a ƙasa saboda bazata iya jumrewa tsugunon ba hawaye ne wani ke bin wani a fuskanta tana sa hannu ta share lokaci zuwa lokaci, yayinda wani farin bafulatani tsayayyen namiji tsaye a kanta yana zabga masifa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba ko damuwa da a gaban mahaifiyar shi yake be yi ba.
"Ke kin san Allah wallahi na gaji, na gaji da wannan jarabbaben jinya naki, ke kullu yaumin ciki, a yayin cikin in sha wahala in kashe kuɗi ki ishe mutane da laulayi kika tashi haihuwa ki haifo mace, nan ma suyi ta jinya suna karya tattalin arziki na har su zo su mutu to wallahi Allah ba ze yiwu ba wannan cikin zubda shi za'ayi a juye mahaifar"
Dattijuwar dake zaune daga kan kujerar tsuguno ta zabga tagumi tana aikin kallon shi tace
"Bukar kayi hakuri ka bari tunda tana son kayanta ta haihu baka san ko shine me tsayuwa ba.."
Katse ta yayi da sauri
"A'a mama dama tun farko kece kike ɗaure mata gindi shiyasa take jin daadi kuma take abunda ta ga dama"
Shiru matar tayi saboda ita karan kanta shakkar yaron na cikinta take yi, har ya juya ze fita ta kalli Mairamu dake kuka kaman ranta ze fita ta ɗaga ta kalle shi tace
"Bukar!"
Da mamaki ya waiwayo saboda ya sani idan yayi magana ya zauna kenan ba me juya ta har uwar da ta haifeshi amma yanzu tana kokarin fara shiga sabgar gidanshi da iyalinshi kenan suma su ma su samu Daman raina shi kenan, fuskanshi a tamke ya amsa.
Tace
"Don Allah kayi haƙuri akan wannan kaɗai mun yarda idan be tsaya ba tun kan ta samu wani cikin se a juya mahaifar"
Shiru yayi na mintuna kan yace
"Tunda kin matsa ai shikenan sede fa ni ba ruwana ba kobo na da ze yi ciwo a akan cikin nan kuma hidimar aurena yadda take yi haka zata yi.."
Kallonshi kawai Daadida ke yi har ya fice, duk sauran da suke tsatsaye har ita wacce aka kira da Maryam dake durkushe nannauyar ajiyar zuciya suka sauke, ɗaya rike da karfe varender ɗinta tace
"ke ma in banda jaraba tunda an ƙi samun namijin mama a hakura Haba!"
Na biyun tace
"Toh ina bakin ciki ze bari ke kuwa ba'a samu magajiya ko magaji ba"
Na ukun tace
"ni ba don ma haihuwar da take yi suna komawa ba da se ince wannan anya ba juya ba! To ko ni da nake Amarya yaushe na zo gidan nan har ina da biyu.."
Daadida tace
"ya isheni haka, babu ruwanku wannan tsakanin Maryam da mijinta ne.."
Baki suka taɓe kan kowacce ta juya ta shiga ɗakinta dake dauke da parlor da ciki ɗaya
Miƙewa Daadida tayi ta zo ta kama Mairamu ta mikar da ita da taimakonta suka koma ɗaki don haka laulayinta suke ba karamin wahala take sha ba..
Kaman yadda bukar ya faɗa hakan kuwa ta kasance, bukar mutum ne me tsananin zafi, Haɗa rai da rashin mutunci kwata kwata akan dukiyar shi bashi da mutunci, haka matanshi su su huɗu rass babu wacce ke ganin hakwaranshi da sunan dariya, ba mutan gidan ba har na waje shakkar shi suke, mahaifiyar da ta haife shi ma bata tsira ba Dukda ba ze zage ta ba sede itama yana shimfiɗa mata doka, amma matan suna shan bauta da aiki.
Mairamu ce ta farko wacce tunda ya aureta in ta samu ciki baya zama in ya zauna kuma ta haihu ƴaƴan basa zama se su sha ciwo na watanni kaɗan su koma, a haka ya auro na biyu badi'ah yaranta huɗu mata.
Se Naja'atu itama yaranta uku mata se Amaryar zarah yaranta biyu suma mata ne, suna tsananin kishi da Maryam saboda yadda daga mijin har surkar suke nuna sun fi kauna da sonta Dukda shi Bukar ba gane mishi suke ba sede kam zasu iya cewa hakan saboda ganin bayan Daadida ita ce kaɗai kan ɗan tankwara shi kaɗan amma sauran ko gwadawa basu isa yi ba.
A gidan ko wani karshen wata ana kawo hatsi buhu guda, idan har Rogo ya jingine musu su zasu yi wahalar maida shi gari sede ya dinga turo abun miya sun dinga cin rogon kenan har se buhun ya kare se ya sake jingine wani hatsin, yana jingine shinkafa gumi, Gero, dawa, masara duk abunda yayi niyya amma fa guda ɗaya idan sun gama aikin se su raba ko wacce ran girkin ta ta san yadda zata sarrafashi kowa ya ci, ko Maggi ne zaka sa a miya se ka jira ya shigo kan ya kirga ya baka, haka in nama ne a kirge yake wai don kar a mishi Almubazzaranci.
Sannan wankin shi shima in ya taru matan yake jibge ma wa haka zasu raba su dirza, sannan aikin wurin dabbobbinshi da tsabar yawansu aka mishi lakabi da MAI NAGGE wato me shanu, yadda in har ka shigo garin mambila kace Gidan Bukar mai nagge kowa ya sani, tsabar zafin shi har dabbobin su kan san da shigowar shi, in kana so kuyi rashin M ka raina shi ko ka mishi wasa da dukiya.
Mairamu ta raini cikin nan nata cikin tsanani da azaba saboda laulayi me zafi take yi, hakanan ga ayyukan gidan tunda tunkunyar gidan lamba goma ce, daga shara har wanke wanke bata iya sede Daadida ta karɓa mata wadda da kyar take barin ta yi don ta dinga rokonta kenan akan ta bari ba se tayi ba se in ta nace ne zata sakar mata
Ranan girkin ta haka zata tashi tun da duhu ta fara shara ta gama ta ɗaura koko na kari bayan nan tayi wanke wanke ta zo ta ɗaura abincin rana, tana saukewa za'a maida ruwan na dare, gashi wani lokacin se ana tsaka da yi za'a shigo da buhun hatsi saboda baya so a mishi asara ko kwari su shiga hakan ya sa baya bari hatsi ya kwana yana shigowa ya gani kin shiga uku da sababi.
Kaman yau cikinta na cikin wata na hudu har ya fara fitowa, zaune take tana wanke wanke hannunta na rawa saboda cimar cikinta ya ƙi shi, Jan masara ne kuma tunda aka kawo banda koko da safiya bata iya cin komai saboda cikin ya ƙi jan masara.
Shigowa yayi da gyaran murya wadda ya sa duka sauran matan gyara zama suna shiga taitauyinsu, kallon kwatar buhun gero da ya ajiye musu yayi ya sake haɗe rai yace
"wannan kuma kason waye ne don wulakanci zata bar min dukiya a gantale?"
Badi'ah tace
"ka ganta chan uwar laulayin duk duniya"
Ɗagowa Maryam tayi tace
"kayi hkuri ba wai na ƙi yi bane ayyuka ne suka min yawa ga rashin karfi saboda bana iya cin jan masaran nan"
Yace
"ke kika jiyo ni de abunda na sani in ga hatsina a gyare tass"
Yana kai nan ya juya ya fice.
Hawaye take tana aikin da wahala, daga karshe kaman kullum se Daadida ce ta fito ta taimaka mata da dare kuma ta shirya ta tafi turaka..
A kullum Adu'ar Daadida be wuce Allah ya sauya mata hallayyarshi ba sbd baƙin bafulatani ne ba a fuska ba a zuciya saboda yana da arzikin da ze iya fidda kunci a gidanshi sede hannun shi a dunkule yake, yana da halin daukar masu aiki sede ba ze yi ba, yana da ilimin Addini amma ta rasa meyasa baya aiki dashi shi kuma haka Allah ya halicce shi yaranshi in sun ganshi kaman sun ga mala'ika, baya son yara mata iyakacinsu dashi cimarsu bayan nan duk wata hidamar ƴarki ki san yadda zaki yi.
Wahalar da ta sha a cikin ba ƙarami ba gashi bata da kowa banda mijin saboda Fulanin tashi ne en uwanta kuma sun tafi bata san inda suka yi ba, da shi ta dogara wannan yasa yake anfani da rashin kowan yake mata yadda yake so, har dukanta ya taɓa yi da cikin saboda ɗan hatsaniya da suka samu da Zarah ta lauye maganan.
Cikinta yana wata tara amma har lokacin babu hidimar da ya ɗauke mata, idan taje garken na dabbobinshi shara sede ta saka gwiwowinta a cikin kashi take iya sharar gabaɗaya jikinta se ya samu kashin dabobbin kan ta gama tun tana amai kaman zata amaye hanjin cikinta har ta koma daure dankwali a hanci da bakinta kan ta iya sharewa.
Uban wankin shi ne jibge take tiƙa Dukda bayanta dake a sage cikinta kuma na juya banda idanu da hanci babu abunda zaka gani a jikinta se fari kaman aljana in ji faɗar Kishoyoyinta da ta rasa me ta tsare musu suka sako ta a gaba bayan ita ce uwargida ma.
"Mairamu ki aje wankin nan ki zo ki huta hakanan ko ba ɗazu kika ce baki jin daaɗi ba?"
Cewar daadida cikin tausaya mata
Tace
"Daadida bari na gama kin san in ya shigo ya samu ma magana ne"
Zarah dake surfe ta taɓe baki ta fara wake waken habaice sbd haushin yadda surkuwar tasu ta fi damuwa da Mairamu suke ji ba kaɗan ba.
Badi'ah tace
"mu da muke ba ƴaƴa ba aikin ya kashe mu ba"
Naja tace
"Ai karshen alawa dae ƙasa Allah kuma ya sa shi ɗan ba me jin maganan na gaba da shi bane da tuni an sa ya kora mu waje"
Mairamu ta miƙe tsaye tana rike baya tace
"amma dae ya kamata ku dinga sanin maganan da Zaku ke faɗawa Daadida ko bata haife ku ba ta haifi uban ƴaƴayenku bare ma a haihuwa duk ta haife ku.."
Zarah da ta fi raina ta akan kowa tace
"don ta haifeshi se me? Shi ɗin ya ɗauke ta uwa ne? Ta je ta fama da damuwar ta ba ta zo ta tare a gidan surakai ba mana taga in mun bita mun faɗa mata magana ko ba haka ba?"
Tayi maganan tana kallon Su Naja a tare suka ce
"kwarai kuwa"
Maryam zata sake magana Daadida ta hanata tace ta je ta zauna zata karasa wankin.
Duk abubuwan da Bukar ke yi babu abunda yafi komai ƙona ranta irin yadda yake da mahaifiyarshi, mace ta dauki cikin ka ta Rena ta haife ka girma kana mata yadda ka ga dama? Anya yana son gamawa da duniya lafiya kuwa? Ai iyaye ba abun wasa bane.
Karshe dai Daadidan ce ta mishi wankin ta shanya, cikin dare Mairamu dake dakinshi nakuda ya tasar mata, duk yadda tayi dashi da ya taimaka ya kira mata ko Daadida ne yace in ya fita a ɗakin wutar Allah ta ci shi.
Da kyar ta iya mikewa cikin azaba ta fito ruwa har yana bin kafafunta ta fara bubbugawa Daadida wadda yayi sanadiyar farkawar matan suka fito suna kallo har Daadida ta shiga da ita, ta sha baƙar wahala kan ta haihu gab asuba kukan yaron ya karade ilahirin gidan.
Fitowa Daadida tayi ta shiga ɗakinta ta kwaso abubuwan da zata bukata wurin karasa ayyukan badi'ah tace
"ta juye kenan to Allah ya ji kan rai tun kan lokacin yayi"
Har Daadida ta saka hannu a kofan ɗakinta wurin komawa ta juyo tace
"Tabbas ta juye santalelen lafiyayyen ɗa namiji kuma in shaa Allah shine me jan ragamarku nan gaba shine kuma shugaban ƴaƴayenku, ranshi a Hannun Allah yake ba hannun ki ba bare ki fara mishi hasashen mutuwa ke ba Alanmusuru ba"
Shiru duk suka yi suna kallonta saboda maganan ya dakesu, shiganta suka kalli juna Naja tace
"kaman namiji fa tace?"
Badi'ah tace
"kwarai abunda tace kenan"
Zarah tace
"Ah bamu ga ta zama ba fa"
A ruɗe kowacce tayi ɗakinta sbd kalmomin Daadida na zama magaji kuma shugaban gidan abun be musu daaɗi ba Sam ya kuma dake su.
Ko da gari ya waye Daadida ta fito taje tayi sallama kofar ɗakin Bukar ya leko kai yace
"Mama lafiya kuwa?"
Tace
"yarinyar nan ta sauka kuma tunda ta haihun nan bata wani jin daaɗi ya kamata ka kaita asibiti a duba ta"
Yace
"wa? Tabb ai abunda kuma ba zan iya ba kenan mama ba zan kashe kuɗina a banza ba"
Tace
"yaron ma fa bashi da cikakken lafiya Bukar Haba don Allah ka ji tausayinsu mana"
Karkaɗa kunnenshi yayi yace
"Me kika ce?"
Tace
"nace yaron bashi da cikakken lafiya"
Wara idanunshi yayi yace
"kina nufin namiji ta haifa?"
Kai kawai ta gyaɗa mai ganin kaman ya ruɗe ai se ya sheke da dariya wadda ya saka badi'ah, zarah da najah Kallonshi cikin dumbin mamaki.
Jiki na rawa yayi ɗakin Mairamu Daadida tayi musu wani kallo na ba kun gani ba kan ta bi bayanshi, aiko farar ɗaya yaron ya shiga ranshi matuka gaya.
A take ya kaisu asibiti aka duba lafiya su aka rubuta magunguna ya sayo, har kaji biyu ya yanka mata Daadida ta sarrafa mata shi ta samu ta ɗan ci cikin mamakin sabon halayyar Bukar ɗin lallai ɗan ta ya zo da albarka.
Hidima kam ya musu har ran sunan shi ya naɗama yaron suna Muhammad Daadida kuwa tace Raed za'a kira shi tunda dae ya tabbata shine shugaba in ba Bukar.
Abunda ba'a taɓa yi ba aka yi a gidan hidimar suna da yanka rago se akan Raed, ba tare da sun san wani baƙin hassada da kyashi da kuma tsanar Muhammad ɗin da Mairamu Bukar da Daadida suka kara musu ba.
Raed na wata biyu wata matsala ta fara kunno kai na ɗauki ɗaiɗai da ake yiwa dabbobinshi don kullum se ya kirge su tsab, ranan da ya kirga yaga ba rago ɗaya tashin duniya ne kawai ba'a yi a gidan ba don duk ya tarasu ya kwashewa duk wadda ya taɓa mishi dabba albarka se washegari aka sake zare akuya ɗaya.
Horon abinci ya musu yace kar yaga an hura mishi wuta a gidanshi in dae har da iccenshi da kuma kayan abincinshi za'a yi anfani, gwara ma Mairamu albarkacin shayarwa ya turo mata biredi da shayi wadda ita kuma ta raba da Daadida don har ita hukuncin shi be tsallake ba.
Bayan kwana biyu aka sake dibar kaji biyar, ranan tarasu yayi yayi rantsuwar idan ba'a fitar mishi da ɓarawo ba duk ze sake su su bar mai gida da yaran su duka.
Badi'ah ce ta fara magana tace
"to ni de ban son in yi magana ne ace na ce amma tsakani da Allah banda Mairamu da Daadida dake shiga wurin dabobbin nan cikin mu ba me shiga daga shara se shara"
Zarah tace
"Najah mu faɗa"
Najah ta girgiza mata kai yace cikin tsawa
"me Zaku faɗa ɗin maza a faɗa in Ji"
Zarah ta fara in ina.. Tace
"dama gab asubahin yau ne na tashi da nufin zuwa bayi shine na leƙa window Naga an buɗewa wani kofa ya fita rike da wani kwando a hannunshi kuma da aka dawo ɗakin Mairamu Naga an shiga Dukda ban kalli fuskar ko waye ba"
Ta Yi shiru kan ta sake cewa
"ranar da Akuya ta ɓata kuwa da ni da Naja muna zaune daga wurin shiga turken Mairamu ta zo ta wuce mu ta shiga kuma ta jima kan ta fito ko kan fitowanta diran abu muka ji kaman ta gini da kuma kukan awaki amma mun leƙa tace mana ta ɗan yi tuntube ne garin kwashe kayan Raed daga kan gini shine akuya suka razana don ta kusa faɗa musu ko Naja?"
Najah ta gyaɗa kai tace
"hakane wallahi"
Badi'ah tace
"in de kuwa haka ne to itace me alamar tambaya Kato kuwa a kanta"
Wani kallo Bukar ya watsa mata yace
"me zaki yi min da dabbobi? Me kika nema kika rasa da zaki fara min ɗauki ɗai ɗai da dabbobi to kiji da kyau wallahi wallahi dabba na ɗaya ya sake ɓata zaki yi mamakin mataki da zan ɗauka"
Daga haka suka watse ko sauraran ta be yi ba, tayi kuka tayi kuka har taji ba daaɗi saboda kazafi komin kankantarshi akwai ciwo Daadida ce tayi ta lallashinta.
Wasa wasa aka gane satar dabobbin bukar wadda Mairamu ke shan azabar hakan saboda yadda yake gana mata wahalhalu akan hakan har sakinta yayi tayi ta kuka tana bashi hakuri don bata da inda zata je karshe yace ta zauna sede ta nemi abunda zata ci da kuɗin dabobbin shi da take sacewa kuma ɗaya ya kara ɓata se ta bar gidan.
Haka suke raba abincin Daadida don ita bata da sana'ar da take yi kaman sauran matan waye ma ze bata jari, ga damuwa da ya mata yawa ga wahalan aiki don duk ayyukan da suke rabawa ita kaɗai take yinsu.
A hankali a hankali bukar ya fitar da Mairamu da Raed a ranshi saboda laifukan da take mishi da yake ganin cin fuska ne, dukanta yake ba ruwanshi in abu ya samu dabbobinshi sanadiyar ta don ita kuma ke hidimar su tsab.
Raed na shekara uku har ya iya tafiya da magana sede be isa ya fita tsakar gida ba mugunta babu irin wadda matan gidan da ƴaƴayensu basu mishi, wani lokacin ma har da wuta ko ruwan zafi.
Wani rana kaddara ya sa Mairamu shiga ɗakin Bukar don gyara mai, dama aikinta ne amma fa se in ya faɗa kamin nan sannan kuma yana kofan ɗaki yana jiran ta har ta gama to yana sauri wani cinikayya da ze yi se be rufe ɗakin ba ya fice, ita kuwa ta gama duk ayyukan ta tace to akan ya dawo kuma ya sakata bari kawai ta shiga tayi shine ta shiga tayi ba tare da ta san ajali ke dibar ta ba.
Ta shiga ta gyara fes ta fito ta koma daki wurin Daadida, chan bayan la'asar Bukar ya shigo ya shiga ɗakin shi kusan mintuna biyar ya fito ya fara kwala kiran Matan gidan gabaɗaya a razane suka fito jin muryarshi a haukace.
Yace
"ina kudade ne?"
A gigice yayi maganan.
Duk a tsorace suka ce
"wani kuɗi malam?"
Yace
"tambaya ta ma kuke yi? Ku fito min da kuɗina ko kuma wallahi dukkanku rayukanku ya ɓaci wallahi wallahi akan kudin nan babu abunda ba zan yi ba ku fito mun da kudade na"
Duk rantse rantse suka fara ya daka tsawa yace
"wa ya shigar min ɗaki a cikinku?"
Dukkansu Mairamu suka nuna aiko kan tayi magana ya fara sauke mata maruka har Raed dake hannunta ya faɗi, a gigice ya kwala kara itama tana kuka take ce mishi wallahi bata ɗaukar mishi kudi ba shi kuwa yana cewa se ta fitar da kudadenshi har dubu ɗari uku wallahi se ta fitar.
Duk yadda Daadida tayi kokarin hanashi dukanta kasawa tayi karshe itama tura ta yayi ta faɗi ta kuma kasa tashi saboda kwankwasonta da yayi mugun bugawa se ta saka kukan bakin ciki kawai.
Haɗa Mairamun yayi da Raed ya ja su kaman kayan wanki zuwa kofar gida ya watsa su wadda dab titi ne kuma Raed ne ya sauka bisa titin, dukda azabar da Mairamu ke ciki a gigice tayi kanshi ta ɗauke shi sede ta kasa mikewa, horn me karfi take ji amma ba yadda zata iya sake tashi hakan ya sa ta cilla shi gefen titi ita kuma ta runtse idanu tana ambaton Allah.
Me motan ya kasa riƙe Birkin shi don da full spead ya zo hakan ya sa ya mata mugun bugawa a take ta some, ya ɗauke ta da Raed zuwa asibiti tare da wani ɗan unguwa, sede suna isa ma aka tabbatar da ai ta cika sossai pastorn ya firgita da mutuwar gashi musulma hakan ya sa be koma gidan bukar ba seda yayi Involving police aka dawo da gawa inda aka nemi bukar.
Aiko yace se an biya diyya, nan pastor David ya biya kusan 2mil kuma bukar ya amsa cikin jin daaɗi wannan abu ya sawa Daadida hawan jinin da seda ta fi wata biyu tana jinya, a wata biyun nan azabar da Raed ya sha wurin yaddikonanshi ba'a magana sun dena kiranshi da sunanshi sede ɗan ɓarauniya ko Duna (saboda baƙin fata ne dashi kalar na Daadida don iyayen shi duka biyu farare ne)
Ko da Daadida ta samu sauki ita da Bukar idanu ne, tana kula da Raed sossai babu kuma irin cin kashin da su Najah basa mata sana'a ta fara sossai tana biyawa Raed duk wani bukatar shi don ba ruwan uban dashi.
Raed na five yrs wani babban al'amari ya faru wadda yayi sanadiyar da har Daadida ta bar gidan wadda su Najah suka zuga Bukar akan kar ya barta ta tafi da danshi aiko ya hana tafiya da Raed, taurin zuciyarshi kuwa ya hana shi ganin laifin da ya aikata babba.
Raed ya taso ne cikin tsananin ƙaunar kwallo yana son ball ta yadda ko a cikin gida yake zaka ga yana buge bugen ƴan ledojin da yake Haɗawa ya maida su kwallo, dama Daadida ce ke koya mishi karatu a gida wadda yayi nasi zuwa sabbi da kuma ayatul kursiyu sede tunda ta tafi kuma yaddikonanshi sun hana shi zuwa wurinta da sau ɗaya yaje suka mishi sharrin da ya sa Bukar kusa kashe shi shima be kara zuwa ba.
A hankali ya mance sauran wadda ya iyan ma banda Falaq nasi da kuma qulhuwa se ayatul kursiyu da salatin annabi saboda ba'a sashi a Arabi ba bare boko su sauran yayyun shi mata da suke yi ma saboda iyayensu mata ne ke biya musu shi da bashi dashi se dae zaman gida da bauta.
Ya bautu iya bautuwa Sanna ya azabtu ya kai ya kawo a turken awaki yake kwana saboda ɗakin mamanshi da ɗakin Daadida su Badi'ah rabewa yaransu suka yi be isa ya shiga ba.
Wata rana baban ya kalleshi yana kwallo ya rufe shi da duka akan abun Yahudawa ze kawo mishi gida, kaca kaca ya mishi da kyar ya iya bacci, da safe da hidimar gidan ya tashi shi ke diban ruwa yayi shara, ya share ɗakin dabbobi ya wanke ya kuma ciyar dasu.
Se ya gama diban ruwa ya zo ze huta se yaga sun yashe ruwan masu wanka sun yi masu zubarwa sun zubar haka ze sake komawa ya sake dibowa gashi da kadan kadan yake dibowa don bucket yafi karfinshi, kuma kullum se an yi abunda ze sa Bukar dukanshi kaman Allah ya aiko shi.
Akwai wani rana da ya zo ya ajiye ruwan dabbobi ze fara saka su sha Badi'ah tayi kiranshi ya je ta bashi kudi akan ya je ya sayo mata cingam ya fice ko da ya dawo ya samu shanu ɗaya ya sha ruwan kuma se ya ganshi kwance.
Yaje ya taɓa shanun don be saba gani suna bacci haka ba sede shanu kam be motsa ba, Najah ce ta shigo ta rabka salatin da ya saka Raed mikewa a razane, Bukar ya shigo wurin da shigowanshi kenan yaji salatin wani ashariya ya zabga ganin katuwar bijiminshi kwance ba rai.
"Me ka sa a ruwan?"
A razane cikin tsananin kaɗuwa da tsoron uban yace
"ban saka komai ba...wallahi Baba ban sa komai ba!"
Gigitaccen mari ya ɗauke shi dashi wadda ya saka ya dena ji na wucin gadi.
"Zaka fara yi min irin muguntar da uwarka tayi min ko? To wallahi uban ka zan ci"
Da gudu yaje ya ciro murɗaɗɗiyar igiya na ɗaure saniya ya fara jibgarshi ko damuwa da ɗan shekara Biyar zuwa shidda ne be yi ba, be yi la'akari da tun farko kula da dabbobin ba aikin da ze iya bane.
Da kyar Raed ya samu ya gudu ya fita a gidan yana ta kuka ya samu wani lungu ya dukunkune kaman maraya yana kukan raɗaɗin da jikinshi ke mishi yana kiran Daadida da Mamah (maamanshi)
Kai Har 4 thousand words🤔 gaskiya na yi kokari😉
#like
#share
#comment
🖤Gureenjoh🖤