20
by @gureenjoh
KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
Zuhraa
Hamrah
Igiyar Rayuwa
Noor Iman
Ruwan Sama..
Lelewal
GAMON JINI paid
And Now
Kowa Ya ga zabuwa..
PAGE 20
FREE BOOK
Tun daga nesa yake hangar kaman yaron nan da ya taɓa kade mahaifiyarshi har ta mutu, suna matsowa kusa kuwa ya taɓa shi wadda ya saka Raed firgita ya tashi kaman ze gudu, pastor Philip yayi saurin rikeshi yana cewa
"hey calm down we r not gonna harm u"
Pastor David yace
"Muhammad ya kake?"
Kallonsu Kawai Raed yake ya kasa magana don shi be sheda su ba, ganin da gaske be gane shi bane yasa yace
"Me kake yi anan haka Raed? Ji jikinka duk kashin shanu da ruwa? Me ya sameka a fuska haka?"
Se yaron ya sa kuka, duk wani tausayinshi ne ya kama su, lallashinshi suka yi tayi har yayi shiru yayi musu bayanin abunda ke faruwa Seda Philip yayi kuka da David ke faɗa mishi abunda yace don shi ba ɗan Nigeria bane ya je Mambila yawon buɗe idanu da yada addininsu ne shine ya sauka wurin Pastor David.
David ya ce cikin harshen turanci
"Tun daga sadda na kade mahaifiyarshi yaron ya kasa fita a raina, na sha zuwa don son ganinshi baban yake ce min baya nan ko yana makaranta in bashi kuɗi akan a mishi sayayya amma dubi yaron nan, kaman a bola yake rayuwa ko almajiri ya fishi kyaun gani.."
Yayi maganan yana share hawaye, Philip yace
"matsalanku kenan a Nijeria had it been a ƙasar mu ne taya hukuma zata bari a yi ma yaron nan Haka"
Bayan gama jimaminsu suka ce ya zo su je su yiwa baban nashi nasiha Sam ya ƙi ya san karshen shine a ciki, kyautar kuɗi suka bashi shima ya ƙi karɓa, A mota suka dauke shi zuwa gidan David suka bashi abinci ya hau ci hannu baka hannu ƙwarya, se kallon shi suke har ya gama suka saka shi yayi wanka Philip ya sa kayanshi a washing mashing bayan ya fita tas suka yi drying suka goge suka bashi ya maida jikinshi take yayi kyau.
A parlor suka zauna ya zauna a ƙasa ya kurawa TV da ake buga kwallo idanu, tsabar kallon da yake yiwa ball ɗin ko idanunshi baya son kaudawa be san time ya tafi ba seda ya ji kiran sallah a masallacin dake kusa da gidan David ɗin, da sauri ya miƙe yace ze tafi.
Seda suka bashi abinci ya sake ci kan suka maida shi inda suka ɗauko shi, a raɓe ya shiga gidan Badi'ah tace
"ka ci gaba da raɓe raɓe duk aikin da ka tara zan ga uban da ze maka ai, kuma babanka ya ce baka da abinci a gidan nan har nan da kwana biyu sbd kashe mishi sa da kayi kuma ka kiyayi sake haɗuwarku Duna kawai"
Kanshi kasa ya wuce ya ɗauko roban da yake diban ruwa ya fita ya fara jidowa Seda ya gama ya je ya kwanta a cikin dabobbin gwanin tausayi.
Daga haka David ya gane taimaka mishi, Philip ya koma amma da Tunanin Raed makale a cikin ranshi, rayuwar gidansu kuwa banda tsanani babu abunda ya ragu a gareshi, kasancewar shi yaro kuma abun ya mishi yawa yasa yayi developing Panic Attack..
Wani irin tsoron mutane yake, baya yadda ya kalli idanun kowa kullum a raɓe yake a wuri, idan kuwa ya tsorata numfashin shi se yayi ta seizing kaman ze mutu da kyar yake samu ya samu sauki se ya Haɗa kai da gwiwa yayi ta kuka.
A haka ya sake shekara biyu a gidan ya cika shekara bakwai, a lokacin ya san yana da wani abu guda ɗaya dake debe mishi kewa yake hana shi shiga damuwa wato ball, ze Haɗa ledojinshi ya sami wuri yayi ta bugawa to fa shine kaɗai zaka ga haƙorin shi yana murmushi se kuma in ya je wurin Daadida da ya kan Saci hanya yaje sama sama da kyar ze tsaya ta kulla mishi abinci a Leda ya tafi saboda kar a gane Babanshi ya kusa kashe shi.
Yau ya tashi baya jin daaɗi hakan ya sa yace da ya tsaya zuwa jeji dibowa dabbobin abinci gwara ya korasu suje su ci tunda ya kan fitar dasu, fita dasu yayi zuwa chan wajen gari se ya kaɗa su ya samu wuri ya kwanta tun jiya da rana be ci komai ba yunwa yake ji ga zazzaɓi dake damunshi wadda damuwa da yake ciki ne ya haddasa mishi.. Mutanen gari sun maida shi wani soko,gaula wasu har kallon marar cikakken hankali suke mishi hakan yasa yake iya yinshi wurin gujewa mutane.
Yannenshi ko kusa dasu be isa zuwa ba daga me hanbari se me duka, yadikkonanshi babu wacce ta taɓa faɗan abun arziki a kanshi duk bautar da yake musu haka nan uban da ya haifeshi be san zafinshi ba.
Kuka yayi sossai a wurin yayi ta jan numfashi daga karshe ya tashi ya kaɗa shanayen suka koma gida, ba tare da ya san a kiwon da suka yi da wasu shanayen akwai wani ciwo dake jikin waenchan wadda suka sakawa nashi ba.
Dare shanaye basu barshi ya rintsa ba kan safe wasu abubuwa kaman bulalai suka fiffito musu a kafafu nan take biyu suka cika, hmm misalta irin halin da ya shiga ɓata lokaci ne..
Duka shanayen suka kamu ko da hantsi yayi lokacin da Babanshi ya zo duba shanayen kaman yadda ya saba abunda ya gani ne ya kusa sumar dashi.. Kasa magana yayi yasa aka kira likitan su yazo yayiwa sauran shanayen Allura Sede ana gamawa uku suka sake mutuwa Wayyoooo zubewa kawai Bukar yayi a sume aka fita dashi..
Badi'ah dake kallon yadda Raed ke numfashi da kyar yana fusga ne tace
"Wallahi ka shiga uku Raed idan babanka ya dawo ya sameka a gidan nan, ka ga yadda ka kashe shanayen nan haka ze kashe ka, dama jiya ya gama gayamin ya tsaneka tsanar da be taɓa yiwa kowa ba baka da anfani a gareshi, ko kallon ka baya son yi yanzu kaga se ya kashe ka da hujja..."
A tsorace yake kallonta.. Suka yi dariya suka tafa da Naja.. Naja tace
"yau fa shikenan kwanan wani ya kare kaman yadda mamanka ta tafi har Abada"
Mikewa yayi a tsorace ya rabe su ya fice sbd magana shine abu na karshe da zaka ji daga gareshi..
Tunda ya fita yake ta tafiya in yaga mutane se ya raɓe ya wuce idan kuwa namiji ne se ya dauka Babanshi ne ya fara ihu yana cewa yayi haƙuri baze sake ba.. Mutane dayawa sede su ce Allah sarki Allah ya baka lafiya yaro.
Gidan David ya tafi duk uban nisan dake tsakaninsu, ya same su da Philip sede ya kasa karasawa se kuka,idan sun matso se ya matsa gabaɗaya ya rikice barin ma in ya tuna yadda aka fita da Babanshi ai in ya warke ya dawo shi ba a sume za'a fita dashi ba sede a mace.
Philip da ze wuce Kano ne yace
"Pastor I think I will be going with this boy, can't u see he's depressed and he's seriously sick.. Daga ka ganshi zaka san panic attack na damunshi idan uban shi baya sonshi ni ina son shi I will take him with me"
Duk yadda David ya so ƙi Philip ma nacewa yayi yace idan yaron ya girma ya dawo da kanshi amma yanzu ba ze bari ya koma ba.
Sanadiyar fitan shi Mambila kenan suka tafi Kano sun ɗan kwana biyu Seda Visa ɗinshi da komai nashi ya fita kan suka wuce US anan Philip yake rayuwa da matarshi da kuma ƴarshi mace wadda shekara huɗu Raed ya bata.
First jinya ya fara yi sbd yadda ko cikin dare numfashi se ya sarƙe mishi ga mafarke mafarke, ga yawan tsorata rashin son mutane in kuwa ya ga baƙin fata nan take se ya ruɗe.
Yana jinyar yana samun sauki a hankali Philip ya sa shi school sede be son boko Sam, da kyar ya gama grade 5 yace shi kam ya gama karatu da Philip ya tambayeshi abunda yake so yace ball.
Nan yayi enrolling ɗinshi ya samu trainee wani irin baiwar kwallo yake dashi, nan take ya fara fita wasanni in kana son farin cikinshi ka mishi hiran kwallo, abu guda ɗaya da be bari ba sallah, ya kan Haɗa salloli biyar da dare yayi Dukda be ga kowa nayi ba a gidan.
Wani irin shakuwa ke shiga tsakaninsu da Rabecca don da ita kaɗai yake hira har yayi dariya, itace ƙawarshi a komai..
Wasa wasa be sake maganan Gidansu ba seda ya zama shahararren ɗan kwallo ba wadda be san 'R MAI NAGGE' ba se lokacin ya samu Pastor Philip yace yana so ya je gida.
Be hana shi ba ya shirya ya tafi Gembu, gidan Daadida ya fara zuwa ya kuwa ci sa'a tana wurin har lokacin rungume shi tayi tayi ta kuka a jikinshi tana mamakin yadda ya wani girma ya zama namiji sede kana ganinshi ba addini ba komai rayuwar Turai kawai..
Da kyar yake iya Haɗa hausa ya tambayi Babanshi fa.
Shiru ta ɗan yi kan tace
"Babanka babu inda be shiga ba a garin nan don nemanka saboda ya ɗauki mataki a kanka don cutar da ta shigi shanayen nan sune sukayi sanadiyar karyewar arzikinshi duk dabbobbinshi sun mutu, abinci ma gagararsu yake a gidan shiyasa ya ɗauki laifin komai ya ɗaura maka ban san ko yanzu ya huce ba amma duk sadda ze shigo nan se yayi magana marar daaɗi game da kai"
Shiru Raed yayi yana kallonta yace
"kin yafe mai kenan"
Tace
"Raed ai ko me bukar yayi min ɗa na ne Dukda ya bakanta min sossai har yanzu kuma zuciyata kuna take in na tuna sede Bukar ko ban yi fushi dashi ba ko ban mishi baki ba Allah ba ze barshi ba ina ga in na mishi baki? Ina mishi tsoron fushin ubangiji Raed"
Rumgumeta yayi yace
"ban taɓa ganin mutum irin ki ba lallai uwa uwa ce Allah ya ji kan mama"
Ta amsa da "Ameen zaka je wurin mahaifin naka ko?"
Kai ya gyaɗa ya mike ya je ɗakin da ta sauke shi yayi wanka ya sake kaya, three quarter ne as usual da shirt lokacin Daada ce ma a kanshi a murɗe ya saka ɗan kunne ga sarka a wuyan shi kana ganin shi dae zaka danganta shi da arne.
Haka ya fito duk Yadda Daadida ta so ya sauya ki yayi yace mata ma sune kayan shi gabaɗaya, ko da ya fita jama'a suka gane shi da kyar ya tsira ya samu ya je kofan gidansu.
Da sallama ya shiga, da Badi'ah ya fara cin karo se kwakwalwanshi ta fara tuna mishi karshen maganganunta gareshi tayi wani kala kaman tsohuwar da ta shekara saba'in, Zarah na tsaye tana zaginta ko sallamar shi basu ji ba seda ya sake suka juyo suna hadiye masifar da suke yi da junansu, ihu suka kurma kowacce ta ruga ɗakinta Badi'ah na cewa
"Malam! Malam!! Fito ka ga wani gardi kasurgumin kirista da ya shigo mana kai tsaye gida"
Da sauri Bukar ya fito riƙe da sandarshi yace
"kai me haka? Me ya shigo da kai cikin gidana?"
Raed yace cikin hausar shi da ta bace
"Baaba Raed ne baka gane ni ba?"
Wani ashariya ya lailayo ya maka tare da sake kiran sunanshi da karfi, Raed ya amsa se ga su Badi'ah sun fito su ma suna maimaita Raed!
Seda bukar ya tabbatar shine kan ya ɗaga sandar hannunshi ya lailaya ya muka shi, kara ya saki yana tarewa tare da cewa
"Holy christ! What the Fuck"
Aiko se bukar ya sake haukacewa
"Ni kake zagi da yaren yahudanci? Yahudu ka koma Raed? Dama Alkawari nayi duk randa na ganka se na maka dukan karya ni da kayi Muhammadu Allah ya isa tsakanina da kai, wuta bal bal wallahi kuma ka fitar min daga gida"
Badi'ah tace
"Raed ashe ridda kayi? La'ilaha illallahu wannan yanzu malam se ya ambaci sunanshi ya Haɗa da naka? Ƴaƴayenmu da suke fama da Gidajen miji ai se auren nasu ya karasa lalacewa aka ji jininmu ya zama Kaɗo"
Zarah da Naja ma suka tofa nasu albarkacin suna cewa
"kaci amanar Mairamu wallahi da tana nan na san mutuwa ce kawai sakamakon wannan bakin cikin da zaka kunso mata"
Bukar ya fashe da kuka yace
"Allah sarki Mairamu, wallahi Muhammadu ka sake jingina sunanka da ni ban yafe ba, na tsaneka! Bana so na sake ganinka cikin gidana ko kuma wallahi in yi ajalinka..."
Raed da tsabar bacin rai har jijiyoyin kanshi suka nuna ne ya kallesu daya bayan daya yace
"ban san wani irin zuciyoyi ne a kirjinku ba, duk abubuwan da kuka min ba wai na manta bane sede anything deserve a second chance! Na yarda every disappointment is a blessing a sadda na ga sanadiyarku na samu daukaka na kuma cika burina na zama ɗan kwallo hakan ya sa ni dawowa gareku, amma ashe halinku be sauya ba.. As from today zan fita a rayuwarku kamar yadda bakwa son ganina I hate u guys so.. Fuck all of u..!"
Ya faɗa da karfi kan ya juya ya fice..
Duk baki suka saki suna Kallonshi har ya tafi yana zuwa gidan Daadida ya fara hada kaya duk yadda tayi dashi ya tsaya ƙi yayi itama be barta ba ya ɗauko ta suka zo Kano tare.
Ya so su tafi America sede ta ƙi se ya saya mata gida ya sa me aikin gidansu na chan ya sama mishi workers Hausawa ya zube mata daga driver, me girki, da me gadi.
Gida ne babba me tsananin kyau don yana da kudade ba na wasa ba kuma ba abunda yake yi dasu banda saye saye, be bar gidan ba seda ya tabbatar ko ashana se sun shekara basu nema ba kan ya koma America..yana zuwa kuma yayi papers a court ya cire sunan Mahaifinshi a nashi ya koma 'MOH RAED'
Bayan wani lokaci soyayya me karfi ta kullu tsakanin shi da Rabecca inda aka yi musu aure na church.
Shekarar farko ta haifi Norah, tare da ita suka je Kano wurin Daadida taji daaɗin ganinsu Dukda bata jin daaɗin rayuwar da Raed yake sede ba yadda ta iya daga ta kawo mishi maganan yake ajiyewa gefe ya kamo wata.
Kwanan su biyu da zuwa ranar Juma'a zata fita sadakar da ta saba ana yi mata masa na mutane ɗari da hamsin bayan sati bibbiyu se ta fita zuwa unguwan masu bukata ta raba musu da Adu'ar Allah ya shirya mata kan zuri'a ya kare su, ya kuma sa su gane daga Raed har bukar da su kan yi waya tana kiranshi tunda ta gayamishi Raed ya dawo da ita Kano ya saya mata gida yace shi da taka inda take har abada sede in ta zo mambila.
Ita ta rasa wani irin zuri'a take da, hakan ya sa take dagewa wurin musu Adu'a duk yadda take so Raed ya sauko ya nemi Babanshi su sulhunta a matsayinshi na ɗa Me bukatar albarka iyaye ya ki Sam.
Bin ta yayi wurin sadakar se hakan ya bashi sha'awa ya kalleta yace
"Daadida shi kuma wannan me anfaninshi?"
Tace
"Raed Sadaka maganin masifa ce, tana daga cikin abunda Allah yake so me shi ya taimaki marar shi sadaka na da falala dayawa don in kana yi bazaka taɓa taɓe wa ba"
Tun daga sannan ya gane shekara shekara yake zuwa Nijeria yayi sadaka, Norah na da 9yrs rabecca ta haifi Farrah yana son familyn shi kaman me, barin ma Yayanshi yana son kayanshi har baze misaltu ba duk abunda suke so shi ake yi, yana sallah sede be taɓa saka Norah yi ba, tare ma suke zuwa church da Rabecca da father...
Bayan Farrah na da 3yrs rabecca ta sake ciki inda garin haihuwa ta rasu ita da abunda ke cikin nata, tashin hankalin da Raed ya shiga Seda Father ya ɗauko Daadida don ciwon shi sabo ya dawo ya taɓa career ɗinshi sossai don Seda ya shekara biyu be yi kwallo ba.
Da kyar yayi tawakkali yake kula da yaranshi iya yinshi shine duk wani gata nasu, be jima ba da mahaifiyar rabecca ma ta mutu inda suka dawo Paris suke cigaba da rayuwa don tun bayan warkewarshi PSG suka saye shi.
DAWOWA LABARI
"Toh Hidayat kinji waye Muhammad Raed..."
Kuka ya hana Hidayat magana kaman yadda Daadida ma take kukan haka suka katse wayan
Haɗe kai da gwiwa tayi tana kuka sossai wani irin uba ne wannan? Wannan Anya ubane? To ko asiri ne? Amma kuma in da asirin ne ma Hali ya tarar.. Allah sarki Raed ashe ya fuskanci abunda ya fi nata me yasa labarin su yayi kamanceceniya?
"Miss hidayat"
Norah ta sake faɗa karo na uku tana jijjigata ɗagowa tayi tana zub da hawaye yaran karan kansu wani irin son su da tausayinsu ne ya karu a zuciyarta, ganin Norah ya sa ta kara sake wani kukan tana kallonta..
Norah tace
"Miss hidayat why are u crying? Look at Aisha is also crying since bcs of u?"
Se ta janyo Aishan kawai ta rungume tana cigaba da kukanta wannan labari ba karamin taɓa ta yayi ba. Farrah ficewa tayi da gudu zuwa dakin Mahaifinsu tana buɗewa tace
"Dad miss hidayat have been crying since!"..
Idanunshi ya zuba mata ganin kaman ta ɗan shiga damuwa don ko murnan ganin Father bata yi ba tukuna, se ma hannunshi da ta rike tace
"Dad come nd see Aisha begins to cry also".
Mikewa yayi yace
"ok I will go nd check now stay with grandpa"
Fita yayi daga ɗakin ba tare da ya damu ya sa riga ba cikin mamakin abunda ya sakata kuka, Seda yayi knocking kan ya buɗe ya shiga har tsakiyar ɗakin yacewa Norah
"Norah u nd Aisha should go my room nd greet grandpa"
Hannun Aisha ta ja suka fice daga ɗakin, wuri ya samu ya tsaya tare da zube hannayenshi cikin aljihu three quarter ɗin a sanyaye yace
"Hidayat..!"
Da sauri ta ɗago ganinshi kaɗai se taji kaman rewinding labarin shi ake mata, ji take kaman ta tashi taje ta faɗa jikinshi tayi mishi kukan irin halin da ya tsinci kanshi a ciki kila shi be samu yayi kukan enough ba.
Kau da kanta tayi daga gareshi don in ta cigaba da kallon narkakkun idanunshi dake bisa kanta, in har ta cigaba da kallon natsatsiyar kyakyawar fuskanshi in har ta cigaba da kallon broad hard chest ɗinshi babu abunda ze hanata karasawa ta rungume shi, an zalunce shi sossai an cuci rayuwarshi cuta me girma..
Karasowa yayi haka kawai yake jin damuwar kukan nata har ƙasan ranshi se zuciyarshi ya bashi maybe ta tuna rayuwarta ne.
Bata san wani rashin na iyaye ma rahama ne ba,(kaman yadda shi ya ɗauka) da gwiwa ɗaya ya tsuguna gabanta ya sake ambatan sunanta a tausashe ya ce
"Hidayat! But can u please stop this crying? Can you take a deep breath and relax? What ever you are going through is going to be okay. You'll be Okey, you'll feel happy again. Please you have to take care of your self..."
Wayyo Allah ji tayi kaman ta kurma ihu....
#like
#share
#comment
🖤Gureenjoh🖤