RUBUTU A KAN RUWA

15

by @gureenjoh

RUBUTU A KAN RUWA

  

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN

         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:

Zuhraa

Hamrah

Igiyar Rayuwa

Noor Iman

Ruwan Sama..

Lelewal

GAMON JINI paid

Kowa Ya ga zabuwa..

Diddigar ƙaya... Paid

And now..

RUBUTU A KAN RUWA

LAST FREE PAGE

Ba karamin zagi su Maryam suka sha wurin Asma'u ba sai dariya Aisha ke yi, Ammi kam banda Allah ya tsare gaba bata sake cewa komai ba, Wata kyakyawar mace da tayi kama da Abbanta sossai ta gani tana saukowa daga stairs hannunta riƙe da wata karamar fine girl, fuskanta ɗauke da murmushi take cewa

"Auta ke da waye kuma tun daga sama nake jiyo Muryar ki?".

Dama ya ya nan ta fara faɗa mata abunda ya faru kaman tana wurin, seda ta gama Aysher ta gaisheta ta amsa cikin kulawa tace

"Amma Aysher be kamata kina fuskantar irin wannan abu ki ƙi magana ba, duk haka ta faru ki faɗa a ɗau mataki da wuri kin ji?"

Kai ta gyaɗa, Asma'u ta dora mata da cewa wannan din itace Aunty Salma ƴaƴan ta biyar, Aunty salma na da kirki sossai sede Aisha ta lura bata da surutu kaman Aunty Asmeey tana nan so quite kaman Abba ne, a tare suka cigaba da hirarrakinsu bayan Aysher ta karɓi yarinyar me suna Hibba da hannu ɗaya yarinyar kuwa ta sake suna ta ɗan wasa, har Magrib suka tashi suka yi sallah suka dawo parlorn tana mamakin rashin shigowan Abba, se after isha suna cin abinci tsakar parlorn ya shigo da sallama.

Duk suka amsa, a ƙasa ya zauna chan gefe kusa da kafafun Ammi yana gaisheta, seda ta ɗan muskuta kan ta amsa da kalma ɗaya, Aunty salma ce ta gaishe shi ya amsa yana tambayarta yara, Asma'u ta gaishe shi ta ɗaura da

"A zuba maka abinci Big bro?"

Girgiza kai kawai yayi, ya jima zaune parlorn sede yayi operating waya ko ya amsa call be cewa ba'a ce mishi se lokaci lokaci salma ke ɗan mishi magana wanda yake amsawa ɗai-ɗai, Ammi kuwa ganin ya ƙi tashi yasa ta miƙe abinta tana cewa Aisha

"kin tabbatar kin haɗa komai a akwatin ki ko? Kar ki mance wani abin"

"Eh Ammi na haɗa"

"to ki tabbatar kan ku tafi kin shigo akwai sakon da zan baki"

Tana kai nan ta dubi salma

"ke kuma kwana zaki yi ne kam?"

Shagwaɓe fuska ta ɗan yi uwa me daaɗi

"Da se na fi kowa farin ciki wlh Ammi, Ammi kora ta ma kike? Zan tafi to amma babansu ne ze zo ya ɗauke ni"

Harara Ammi ta zabga mata tana cewa

"Ai kin san mu bama son namu iyayen muka barsu muka dawo gidan babanku da zama"

Asma'u da Aisha se dariya suke yayinda ita salma ta kara narke fuska, ita Kam Ammi tayi sama abinta.

A hankali ya maida kanshi kan wayanshi ya ɗan Tsurawa wayan idanu ba tare da yana yin komai ba, in da sabo ya ci ace ya saba sede ya rasa me yasa yake jin shi out cast idan Ammi na mishi haka, babu abunda ya fi tsana a al'ada irin wannan a rayuwar shi kuma ba ze lamunci ayiwa ɗan shi ba capital No.

Miƙewa yayi kawai fuskanshi sam ba walwala se ma sake tamketa da yayi.

"Se da safe Yaya"

Salma ta faɗa don ta san ba dawowa ze yi ba, da sauri Aysher ta miƙe ta haura seda ta shiga tayiwa Ammi sallama ta bata snacks da ta sa aka mata sbd zaman gidan Emran se da shiri da wasu designers Abaya guda biyu, sossai tayi mata godiya kan ta fito ta shiga ɗakinta ta janyo trolley dinta, Asma'u ta miƙe ta taya ta suka saukar zuwa mota, da gudu taje tayiwa Hajiya sallama sbd kar ta ajiye shi ta dawo, yana zaune ciki Asma'u ce ta sa a akwatin a boot, juyawa tayi wurin Hibba tana ce mata

"byebye baby"

Ba se yarinya ta soma miƙa mata hannu tana kuka ba, duk dariya suka yi Aunty salma na cewa

"wannan kam se ki sami lokaci Asma'u ta kawo min ke ki mana yini tunda jinin ku ya gama haɗuwa da Hibba uwar Ƴan kyuiyan duk duniya"

Tana buɗe motan ta cewa Asma'u

"Eyyaaa Aunty Asmy ko ban je ba watarana ki karɓota ki kawomin ita?"

Harara Asma'u ta zabga mata tana cewa a nawa? Duk dariya suka yi ta shiga motar tana ɗaga musu hannu, daidaita zamanta tayi ganin sun hau titi sossai, gabaɗaya se motar be yi mata daaɗi ba Dukda ta san Abban ba ma'abocin sakin fuska bane sede da kallo ɗaya a yanzu zaka san akwai abunda ya taɓa Ranshi har suka isa gida babu wanda ya tanka se sautin karatu dake tashi kasa ƙasa..

A tsakiyar parlor suka samu Naina tana kai kawo ganinsu tare yasa ta ja ta tsaya, tana sanye da doguwar riga baƙa shara shara da alama tana hutu ne sbd abun cikinta.

"Emran ina kuka fito?"

Tayi tambayar tana tsatsaresu da idanu, ita fa ba wawuya bace kuma auren soyayya suka yi da mijinta ba haɗi ba, kuma ta san kishi taya za'ayi wannan ƴar kauyen take zama gaban motar da ta saba zama cikin har tana haɗa kafada da mijinta?

"What sort of question is this? Ashe kece mijin..."

"Dole zaka ce haka, wlh dole zaka ce hakan saboda kun san baku kulla gaskiya ba, sau nawa kuna fita ku yini tare? Dabba ka maida ni ko ban san me nake yi ba? Ko jiya tare kuka yini wallahi yau se kun faɗa min me kuke kullawa.."

"Abunda jakar kwakwalwanki ya faɗa miki shi muke yi, Wallahi Naina ki kiyaye ni nayi iya lallaɓakin da zan yi and i will not take it lightly kika ce zaki tsallake iyakarki"

A tsorace Aisha ke kallon su ganin tana kokarin haddasa fitina a tsakanin ma'auratan hawaye ne ke bin fuskanta sam bata gane abunda Nainar take nufi dasu ba, wace kuma irin macece zata tsaya sa'insa da mijinta murya a sama?

"Ni kake kira jaka imran? Ni Naina kake cewa jaka akan wannan banza kazamar ballazar? Wallahi zan yi ajalin yarinyar nan yau se in ga karshen karuwanci da mij..."

Marin da ya ɗauke ta dashi a bazata ne ya ɗauke maganar dib sbd gigita da tayi bata san ta kai ƙasa ba, bata ji a kab rayuwarta an taɓa kai hannu jikinta se a yau... Gabaɗaya bata gani daidai haka bata ji daidai

Ɗagowa tayi cikin matsanancin rawar murya ta ce

"N...ni ka mara? A kan w..wannan"

Ta karashe tana nuna Aisha da gabaɗaya hannayenta ke kan Bakinta idanunta gabaɗaya sun firfito cike da tsoro da firgita, daga Abban har Naina babu wanda fuskanshi ke da daaɗin kallo a cikinsu

"zan iya miki fiye da haka tun da kin ce baki san abunda zaki ke furtawa a kaina ba Naina, sanin kanki ne ni ba mazinaci ba ne ko a da ban yi zina ba bare yanzu, idan kwakwalwarki ta sake kimtsa miki abu a gaba ki tauna kan ki furta min don wlh ba zan ɗauki wannan raini da rashin kunyar ba"

Tsam ta miƙe tana jin mararta na Murɗawa da karfi kan Aisha tayi

"Wallahi wallahi na rantse da Allah se nayi ajalin ƴar iskar yarinyar nan..jaka sakarya wacce uwarta ta wofintar da rayuwarta saboda dukiya, dabbar da ko a me sharar takalmi na ba zan ɗauke ta ba"

Haukacewa tayi ta soma fashe fashe a parlorn duk abunda ta samu se ta wurga wa Aisha, da sauri ya janyo hannunta ya tura ta ɗakinta a rikice ta zube a wurin ta fashe da matsanancin kuka, Me ke shirin faruwa? Saboda maraici ne duk hakan? Ashe ta kai abun wulakantawa haka a idanun Naina?

Ita kam seda tayi son ranta da tsine tsine babu abunda bata faɗa ba yana tsaye ya harde hannu yana kallonta, duk haukar ta tsoron shi take hakan yasa bata yi kanshi ba, ta fashe da tsananin kuka daga karshe tare da zarrar keyn motarta ta fice be ce mata ci kanki ba, se jajayen idanunsa da ya runtse da karfi...

Tana tuƙi tana kuka har ta isa gidansu a parlor ta samu iyayenta kawai ta zube jikin Dad dinta tana kuka me gunji an yi mata abunda ba'a taɓa mata ba a rayuwa, ita Emran ya mara akan wanchan karuwar yarinyar.

A rikice suka rufu suna tambayarta me ya sameta? Me aka mata har Nameer da Shigowar shi kenan yaga parking nata da yadda tayi cikin gida da gudu, mararta dake ciwo ta dafe ta ɗago tana kallon mahaifinta, a razane ya ɗaura tafin hannunshi samar fuskanta

"wa ya mare ki Naina?" Tambayar se ya sake hasala ta ta sake fashewa da kuka irin wanda bata taba yi ba.

"Wayyo cikina Daddy, mommy cikina zan mutu"

A take suka sake rikicewa basu ankara ba se jini da suka ga yana malala daga jikinta, kan kace me jikin ya rikice se ta koma yaraf ta sume, da gudu Nameer yayi mota da ita iyayensu suka rufa musu baya se asibiti...

Danƙari! Aisha kina ruwa tsundum...

To fa anan free Page ya kare, mallaki naki ki ji ya zata kaya a gidan Abba

In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰

                          🖤Gureenjoh🖤