5
by @gureenjoh
KIWON KUBUBUWA
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
PAGE 5
A matuƙar gajiye ya shigo gidan, ajiyar iliya kawai ya ajiye ya ɗibi kayan wankanshi ya shiga ciki ji yake duk gaɓoɓinshi na wani irin sassarawa haka dai ya cije ya ɗan saki fuska Dukda babu wani fara'a a kai, baje akan taburmai ya sami mutanen gidan a hankali ya miƙa gaisuwa yana ɗan sake yi wa Baba ya jiki shima cikin kulawa ya amsa. Afnaan dake zaune bakin murhu ce tayi hanzarin Miƙewa taje ta zari bokitin wanka ta nufi rijiyarsu, tana jin shi ya gaida iyayen nashi ɗaya bayan ɗaya kan ya nufo inda take.
"Sannu Yayana"
Ta furta.
Ya ɗan kalleta da gajiyayyun idanunsa sai ya tuna yaran da yaje yi wa lesson yau, yaran ba sa jin magana don sai da ya zane su yau din ma, ko Meyasa wasu iyayen suke tarbiyatar da yaransu sakaka haka? A yadda ya sa musu tsoro ya tabbatar gobe zasu natsu sossai don har magana yayi da mahaifiyarsu mai ɗan tsawo dangane da yaran kuma ta fahimce shi ta bashi goyon baya ɗari bisa ɗari ta kuma kara da ta san sun yi kuskure amma suna Fatan lokaci bai ƙure ba.
"Naanu kina lafiya?"
Bata amsa ba sai cigaba da jan ruwan tayi, ta zaro hannunta ta saka zata sake ja ya riƙe igiyar hakan ya sa ta ɗan kalleshi lumshe idanuwa yayi a lokaci ɗaya ya ware ya sauƙe su kanta, ko ba'a faɗa ba ya san tayi kuka
"Goggo Salame ko?"
Tayi murmushi
"Bestie babu komai fa. Albishir?"
Yana ƙarasa karɓar gugan ba don ya yarda ba yace
"Goro fari kal"
"yau muka gama mock saura mana exams ɗaya a school sai Waec, Neco da jamb"
Ta ƙarasa cikin fara'a sossai wanda hakan ya saka shi ɗan murmusawa, haka take ita da matukar wuya ta kai abu har cikin ranta, sam bata bari wani abu ya tsaya mata a rai matukar bai shafi ahalinta ba, yana son zuciyarta a haka saɓanin shi da ya san yana da matuƙar riƙo.
"Eyeee Naanu an kusa gama saka uniform da farin socks..."
"Toh ai ma Bestie Nursing school ma fa duk haka ne"
Ta faɗa tana kwaɓe fuska, zai yi magana suka ji maganar Goggo Salame kaman zata tsaga gidan ta dakawa Afnaan tsawa
"Toh kurna uwar zuba! ba zaki bar mutum ya sarara ba daga dawowa ko hutawa bai yi ba? Haba don Allah kika san ma ko kila rabonshi da abinci tun kari? Wani irin banzan daɓi'a ne wannan?"
Ɗan lumshe idanu Haidar yayi be juyo ba sai Baba ne yace
"Salame kin fiye son kananun magana ai in dai Haidar ne ban taɓa ganin ranar da ya gaji da Afnaan ba haka ita ma. Kika shiga tsakani ma sai dai ki ji kunya"
"Toh ma ina ruwanta su da suke maganansu ma su ya sunsu ko mu anan bamu ji bare ita dake chan bakin madafi Kenan ba kunnuwanta aka dama ba bare tayi masifar da ta saba"
Kawu ya karɓa tun kan baba ya ja numfashi daga maganar.
Juyawa Afnaan tayi ba tare da ta ce komai ba ta koma kitchen a lokacin Haidar ya ɗauki ruwan wankanshi ya shige bayi watarana matar nan zata iya ƙure haƙurin shi.
"Assalamu Alaikum! Assalamu Alaikum!!"
Ake ta nanatawa daga bakin kofa hakan ya sa kawu amsawa ya miƙe yana cewa baba bari ya duba kila maƙota ne zasu mishi ya jiki, akwai nepa don haka gidan da haske tarr daga zaure suka haɗe da mutanen kusan su biyar ne tsaye, ya miƙa musu hannu suka gaisa ya dube shi
"Kaine mahaifin Aliyu?"
"Eh matsayin mahaifinsa nake ina fata dai lafiya?"
"Lafiya ba lau ba, Sunana Shehu nine shugaban wurin kanikancin Aliyu Haidar"
"Toh...Toh"
Kawu ya faɗa.
"A gaskiya a kwanakin nan gabaɗaya mun rasa gane kan wurin gyaran namu an sako mu gaba da ɗauke-dauke babu wanda ya isa yayi ajiya na kayan mota ba a sace ba, to dama muna kan bincike na san Aliyu tun bai kai haka ba hakan ya sa da su iliya suka sameni da zargin shi ne ban yarda ba gaskiya amma sanin halin mutum na iya chanzawa ya sa muka sanya mishi idanu, ilai kuwa yau ya ɗauke wani sashe na mota ya ba da ajiya bayan ya taso ya zo ya karɓa ya taho dashi shiyasa muka biyo shi tun kan ya sayar don ba ma shi aka kawowa gyarar motar ba Salmanu ne"
"Zancen banza kenan! Aliyun ne zai muku sata??"
Yadda yayi maganan da ƙarfi cikin wani irin kufula kasancewarshi mai saurin fushi ya sa duk su Baba suka ji, saura kaɗan trayn abincin hannun Afnaan ya kife tayi hanzarin direwa zuciyarta na wani irin tsinkewa tana jin numfashinta kaman zai bar jikinta, kusan yanayi ɗaya suka shiga da mama da Baba tuni Salame ta isa zauren yayinda baba ya bi bayanta Afnaan dai ta kasa motsi har mama ma ta janyo mayafi ta yafa ta nufi zauren jikinta gabaɗaya na ɗaukar mazari.
"Shi kuwa, Shi ɗin ma'asumi ne da ba zai yi Sata ba? Mutum ne fa kamar kowa"
Wani daga gefe ya faɗa
"Talaka ma sai faɗin rai da girman kai ashe ɓarawo ne an ji jiki"
Wani ma daga gefe ya faɗa.
Tuni hawaye sun wankewa Afnaan fuska jin irin kalaman da suke jifan yayan nata da su.
"Mutunci kuka zo ku ci mana ashe bamu sani ba? Toh wlh kun ci ƙarya kun kwana gidan ƙarya ku tozarta mu Dukda muna talakawa sai dai ba titi kuka gan mu ba bare ku wulakantamu.."
Faɗa sossai Kawu Habu ya fara Baba ya riƙe hannunshi jin Oga Shehu na yiwa waenda suke maganan faɗa akan ba abin da ya kawo shi ba kenan baya son jin bakinsu.
"Yanzu kuna da hujjar ɗaurawa babana irin wannan Ƙazafin?"
"Kwarai kuwa baba... Iliya ya ganshi a lokacin da ya fita dashi bayan ya ba da ajiya ya zo ya sanar da ni muka je shagon mai shagon ya tabbatar da Aliyu ne ya bashi ajiya, har a lokacin ban tabbatar ba sai da Aliyu ya zo ya ɗauka muka bi shi a baya har ya shigo gidan nan... Ni ban zo don tashin hankali ba ba kuma tozarci ya kawo ni ba, kawai ya ba mu part ɗin motar kuma ya dakata da aiki da mu na lokaci kaɗan mu gani"
Sam basu san Aliyun na wurin ba don tun maganan kawu na farko ya sanya jallabiyarshi ko da ya fito fitan su mama ya riska hakan ya sa ya bi bayansu sai ya tsaya daga bayan idanunshi a runtse.
"Bari na wuce"
Abin da ya iya faɗa kenan yana jin wani ɗaci na taso masa tun daga ƙasan zuciyarsa har kan harshensa, gabaɗaya idanunshi sun rine jijiyoyin kanshi sun fito raɗa-raɗa, but he's trying to be calm chan ƙasan ranshi Allah kaɗai ya san me yake ji ba'a taɓa cin zarafinshi haka ba, yaushe ma ya shiga mutanen bare a mishi irin wannan cin kashin? Me yayiwa su iliya da basu da buri sai na ganin sun datse mishi hanyar samu?
A hankali ya taka ya ratsa su ya buɗe ɗakinshi ya shiga ya ajiye abin wankanshi kan ya ɗauki part ɗin motar ya fito, a gaban Oga Shehu ya ajiye suka saki salati banda iyayenshi da suka ƙage wuri guda.
Rinannun idanunshi ya ɗago ya kalli iliya
"Haƙiƙa ka kasance mutum na farko da yayi min abin da har duniya ta tashi ba zan taɓa mantawa ba, Sai dai na bar ka da wanda yayi ni kuma yayi ka kaman yadda gabaɗaya muka tsaya anan ina matuƙar jin daaɗi da tabbacin haka zamu tsaya gabanshi ya yi mana hisabi... Ku ɗauka ku fice daga gidan nan!"
Ya ƙarasa yana nuna musu hanya yatsar da ya ɗaga sai rawa yake. Oga shehu zai yi magana ya daka musu wani gigitaccen tsawa da har su Baba suka tsorata
"Har Abada bana fata Allah ya sake haɗa fuskata da taku ku fitar mana daga gida na ce!!"
Ɗauka suka yi don sossai sun firgita basu san yana iya juyewa haka ba, a natsattse mai sanyi suka sanshi sai kuma rashin magana da suka yanke girman kai ne da faɗin rai yadda ya tsararre su da razanannun idanusa da suka kara girma ya sa har Oga Shehu be ce komai ba suka ɗauka suka fice.
Cikin rawar jiki ya sabule ya tsuguna a wurin gaban Baba da hawaye ke sauƙo mishi, ya kasa magana sai rawan da jikinshi ya cigaba da yi tamkar wanda aka ƙwararawa ruwan ƙanƙara a tsakiyar bazara. Mama ce ta isa ta dafa shi sai ya runtse idanu sautin kukan Afnaan gabaɗaya na kara birkita shi ji yake ina ma zai iya kukan da yayi, Meyasa su iliya zasu mishi haka? Saboda kawai sun ga yana aiki tukuru ba tare da gajiyawa ba? Sun san menene yake yiwa aikin da jini da ƙarfi? Sun san kudin na isar shi ko baya isar shi? Hawaye ne ya gangaro mishi a daga ƙwarmin idanshi na hagu yayi hanzarin daukewa ya jefa lebenshi na ƙasa cikin baki yana cizawa
"Afnaan bani ruwa"
Da gudu ta juya ta je ta ɗauko ta Miƙewa baban ya duƙa da kanshi ya ɗaurawa Aliyun a baki ya sha sossai kan ya cire.
"Khairan in shaa Allah... Haƙiƙa nayi matukar baƙin ciki a yau, ba na rasa aikin ka ba ba kuma na tunanin inda zamu sake maƙalewa ba sai na wannan mugun Ƙazafi na saata, ina roƙon Allah ya tozarta su fiye da yadda suka yi mini ya darsa musu ciwo da ɗacin rai fiye da yadda na ji a yanzu... Kayi haƙuri kayi haƙuri!"
Kai ya gyaɗa duk sun san ba zai sake maganar ba ko da kuwa za'a hada mishi duka duniya don su tambayeshi ba zai taɓa magana ba ko ya kare kanshi haka banzar zuciyar shi take, kuma haka zai kwana ciki rawar jiki da ɗacin rai.
Goggo Salame ne take ta tsitsine musu yayinda kawu habu yake jin kaman yaje ya kwaso musu yan sanda tsabar tafasa, Mama ce ta miƙar da shi ta ja shi har ɗakinshi ya zauna kawai be ce komai ba. Afnaan ta juya ta shiga cikin gida kitchen ta je ta haɗo mishi abinci tana ji su Baba sun shigo sai mai da zance baya goggo Salame take hakan na sake tuƙa ran Afnaan lokaci lokaci sai ta share hawaye ta ja Allah ya isa har ta gama ta ɗauka ta nufi ɗakinshi Mama na fitowa ta shiga.
"Afnaan ki je"
Ya faɗa jin ta ajiye tray ɗin ta ƙi motsawa.
"Ba zan iya ba Yaya, ba zan iya tafiya na bar ka cikin wannan hali ba"
Juyowa yayi ya zuba mata duka idanunshi da basu dawo daidai ba sai ya sake runtsewa
"Ban san me nayi musu da na chanchanci haka ba duk iya tunanin da zan yi na yi but na kasa gane dalili"
Nufanshi tayi ta zauna daga gabanshi
"Ba su da wani dalili sai na zalunci, shekara nawa kana tare da su ashe ko kowa ya yarda shi ogan ba zai yi bincike ba wanene zai zauna da kai bai san kyawawan halayenka ba yaya? Ka daure ka cire wannan maganan a ranka kar ya taɓa mana lafiyarka ba mu san ya zamu yi ba hakan ta faru, kai ne haskenmu bama fata ko da kuda ne ya sauka a kanka don zai iya haddasa mana zama cikin tsananin duhu"
Ajiyar zuciya me nauyi ya sauke
Ta janyo tray ɗin
"Ba zan iya ci ba Naanu"
"Nima wallahi ba zan ci ba in har baka ci ba Yaya"
Idanu ya sauke ta sani ba zai iya barin ta ta kwana da yunwa ba ko da kuwa menene dalili bare har shi ya yi yunkurin wasa da rantsuwarta alhali ya santa sarai abincin ya ja suka ci a tare har suka gama babu wanda ya sake magana, ya miƙe ya gabatar da isha'in da bai yi ba kan ya juyo ya kalleta
"Yau kuma anan zaki kwana ne bestie?"
Tayi murmushi tace
"in zaka bar ni tsaff sai in kwana bana so in tafi ka faɗa tunanin abin da ya faru har ranka ya zo ya ɓaci mood ɗinka ya sake chanzawa"
"Hakan ba zai faru ba Naanun Yaya na riga na rufe baabinsu in shaa Allah"
Murmushi ta saki ya ɗan mayar mata tace
"idan da Ka yi zan ji a jikina Yaayaa"
Ya ɗan sake murmusawa kan ya gyaɗa kai ta tattare kwanonin ta fice, panadol ya sha ya kwanta sai dai tuni bacci ya kaura daga idanunshi wayanshi ne ya hau ruri sai dai ko ji bai yi ba, duk yadda ya so ya daure kasawa yayi wani zuciyar na jin zafi kwarai wani zuciyar kuwa na ta aikin tambayar shi yanzu me zai yi bayan dako da lesson? Ta ina zai yi rising kudaɗen da yake ciyar da su ya shayar dasu ya tufatar da su ya kuma biya kuɗin jinyar baba ya biya na karatun Afnaan? Sai hawaye suka fara Sintiri a kan fuskanshi suna shiga har cikin kunnuwansa.
🖤Gureenjoh🖤