8
by @gureenjoh
KIWON KUBUBUWA
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
PAGE 8
"Me kike yi mana a gida? Kin zo ƙarasa sauran rashin mutuncin da baki gama ba ne?"
"Afnaan"
Maama ta katse ta
"Maama kin kuwa san abin da tayi mana jiya?"
"Na sani, ai baƙon ka annabin ka in ji faɗar hausawa kika san ko alkhairi ya kawo ta?"
Shiga tayi bayan ta ƙarasa sallaman da ya maƙale ganin jawahir tana ɗan hararanta ta wuce ɗakinta kaya ta sauya zuwa doguwar riga marar nauyi ta fito ta shiga kitchen ta ɗau abincinta kasancewar akwai wuta sai ta shiga parlor inda jawahir take, a kujera ta zauna ta harde tana cin dambunta ko kallon juna basu yi ba, ita jawahir baƙin cikin dake ranta me girma ne na barin ta da Mom tayi anan gidan kuma ta ji zafin aibata mata Nannah da tayi ai ko ba komai ta raine ta, kuma ta bata duk wani so da kulawa da ita mom ɗin da ta haifeta a cikinta ta gagara bata.
"Afnaan"
Mama ta kira ta daga cikin ɗaki bayan ta tabbatar da ta gama cin abinci, zama suka yi ta riƙe hannunta cikin nata a hankali ta fara bata labarin Hajiya karima kaman yadda ta basu a maimakon labarin ya yi mata armashi har ya bata tausayi sai ya sake baƙanta ranta roƙon haj karimar akan Yayan nata sai taji sam bai zauna mata ba.
"Mama in har ni zan taya waennan roƙon yaya ya cigaba da tuƙa wannan fitsararriyar to wallahi zata shekara dubu a gidan nan... Yayana ya fi karfin wulaƙantarwarta yanzu ma albarkacinki ta ci"
Lallashinta mama ta hau yi sai dai fa ta nuna ba zata iya ba sai da taga ran maman ya ɓaci kan tace
"Mama kin fa san murdaddiyar halinshi idan ya juye ko ni ba iya tankwarashi nake ba sai ma muyi faɗa"
Murmushi mama tayi ita ta san tsakaninsu su biyu har abada ɗaya ba zai taɓa tagayyara ba idan ɗaya na nan, kuma ta san gaskiya Afnaan ɗin ta faɗa murdaddiyar halin Aliyu sai shi sai dai faɗan nasu kila ya saka shi sassautowa. Ita har ga Allah tausayin haj karimar ya sake rufeta ko daga ganin yadda jawahir ɗin ke sallah kaɗai ka san tarbiyarta sai a hankali.
Sai bayan Magrib Aliyu ya shigo gidan, Afnaan ta kai masa ruwan wanka bayan sun gama rigimarsu su mama na musu dariya ita dai jawahir dake zaune taburman Mama sai ta tsinci kanta da kallon Aliyun bata san yana sake fuska har haka ba, taɓe baki tayi har suka kawo tuwon nasu na dare da tun gama dambu mama tayi Miyar kukan bayan sun gama magana kuma da Afnaan taga ta fita zuwa kitchen ɗin da alama ita ce tayi tuwon ita dai ko kallon kwanon bata yi ba.
Bayan ya fito ya ci abinci suka je suka yi isha suka dawo ta miƙe taje taburman shi.
"Bestiena na kaina"
Yayi murmushi kaɗan
"Ya aka yi Naanu? Kina son wani abu ne?"
Kai ta gyaɗa
"Faɗi da marmaza nawa cikawa"
Tayi dariya
"shiyasa nake mugun son ka yayana"
Ya kalleta kaɗan ya ɗan yi murmushi
"Akan jawahir n..."
"Ta baki haƙuri akan kalaman ta na jiya?"
Girgiza kai Afnaan tayi sai ya ɗan taɓe baki yana dan haɗe rai yace
"Koma wurin zamanki idan dama abin da ya kawo ki kenan"
Kicin-kicin tayi da fuska, ya zare mata idanu yana hararanta Miƙewa tayi ta san ba sauraranta zai yi ba.
Tana zama sai ga Hajiya Karima, da fara'a mama ta tarbeta ta kuwa zauna bayan mama ta mata bismillah ta shiga cin tuwon babu ko dar don tsaftar gidan ya matukar gamsar da ita fiye da dayawa daga gidajen masu kuɗi, tana ci tana ɗan jan Afnaan da hira ko tanka juna basu yi ba da jawahir.
"Ke! Kin bata haƙurin?"
Shiru tayi sai da taga Hajiyar ta miƙe kan tayi saurin komawa bayan mama tana hawaye tace
"Ban...ban bata ba"
"Ubanki kike jira?"
Girgiza kai tayi lallai sai ta rama wannan cin zarafin wallahi sai ta rama alwashi taci ko ba jima ko ba dade, wani irin tsanar Afnaan ɗin take ji kaman ta shaƙe ta har sai ta ga ta daina motsi.
"Kiyi haƙuri"
Girgiza kai Afnaan tayi kan ta waiga ga Aliyu
"Don Allah Yaya kayi haƙuri"
Taɓe baki Afnaan tayi wai Yaya alhali jiyan nan take kiranshi da Aliyun shi gatsal tsabar rashin kunya.
Hajiya karima ce tace
"Afnaan kuyi haƙuri, Aliyu ba zan gaji ba don ni ce nake nema don darajar manzon Allah kuyi haƙuri"
Nauyi Afnaan taji a ranta hakan ya sa ta kalli hajiyar
"Babu damuwa in shaa Allahu gobe zai ci gaba da zuwa kar ki ɗaga hankalinki Hajiya"
Ta ƙi kallon Aliyun da ya ɗan zare ido yana kallonta mama da Baba sai murmushi suke don sun san kwanan zancen.
"Daga yau bana son wani Hajiya Mommy zaki ke kirana kin ji ɗiyata?"
Kai ta gyaɗa tana murmushi har waje suka yi musu rakiya suka tafi da kyar Jawahir tace
"Sai da safe".
Suna tafiya ya kai hannu ya rankwashi Afnaan yana cewa
"Ai sai ki shirya gobe ki tafi madadina"
"Babaaa ba ka kalle shi ba zai burma min kaina"
Baba yace
"uhm uhm ba ruwana faɗawa mamarku da bata gajiya da shan kunya a rabon faɗarku"
Dariya duk suka yi kuma a zuciyar Aliyu tun da har Afnaan tace ya wuce ya wuce ɗin...
Washegari da wuri yaje kaman na shekaranjiya yana zaune ta fito kusan da irin shigar banzan da tayi ranar farko da ya fara ganinta, fuskanshi dake a tsananin tamke ke faɗar mata da gaba cike da shakkarshi ta matso tace
"Morning"
Girgiza kai yayi ya waigo ya kalleta sai da taji idanun a jikinta, a ranta ta raya na shiga ukuna da wannan Talakan ko me kuma nayi zai kakkafeni da mayun idanun nan..
"Koma ki sanyo hijabin nan na hannun ki in kin dawo kuma kiyi sallama kan ki yi gaisuwar gadaran"
Wani kullutun baƙin ciki ne ya tsaya mata a wuya.
(Driverna! Drivern gidanmu) ta raya hakan tana jin wani kuka na zuwar mata Mommy bata sonta bata ƙaunarta bata kaunar farin cikinta.
Komawa tayi gudun jidalinsu daga shi har mahaifiyar tata ta sanyo hijabin Mom dake zaune a parlorn ta saki murmushi bayan fitan ta haƙiƙa da Aliyu zai yarda da ta bashi Auren Jawahir shi ne kaɗai zai gyara mata zama yadda take so, Toh ya status na karatun shi? Numfashi da sauƙar tare da sanyawa a ranta zata taimakesu kaman yadda suka ɗaura ɗamarar taimakonta.
Da wani irin ƙarfi ta buga motar bayan ta gaisheshi ya gyaɗa kai kaman sarki, dirowa yayi yana shrugging Kafada irin in kin ɓallah ma na gidanku babu abinda ya shafeni kan ya buɗe driver seat ya shiga ya zauna ya tayar suka fice, bata da wayan chatting yau don haka ta miƙa hannu ta kunna mpn motar wakar Rema da selena ne ya fara playing na calmdown, shi ba mutum bane me son hayaniya yaushe ma ya yi natsuwar Sauraron wakoki, shi fa duk duniya babu abin da yake so irin shiru sai neman kuɗin da ya saka a gaba don haka tuni kidar ya fara hawa kanshi har ga Allah ya so barin mata kayanta sai ya ga ba zai iya ba ya miƙa hannu ya kashe.
"Me hakan? Motar tawa ma sai ka fini iko da ita kake so?"
Be tanka ba bayan taɓe baki da ya ɗan yi.
Kife kai tayi ta fashe da kuka har suka isa makarantar ko da ya kaita dept kawarta Nuwaira ta nema ta faɗa jikinta tana kuka kan ta karɓi wayanta ta yi kiran Nannah ɗinta directly
Hankali tashe Nannah ta kira sunanta
"Baby lafiya? Me ya sameki? Ko Mommynkin ce?"
"Nanna Don Allah ki cewa Dad ya dawo dani in ba haka ba gab zuciyata take da bugawa, she wants to push me down to depression yanzu ko karatun bana fahimta, ta kwace Phone ɗina, tayi freezing acct na babban wai ina kashe kuɗi sossai and yanzu..."
Ta ja wani ajiyar zuciya da suka ja a tare da Hajiya Hadizar da hankalinta idan yayi dubu ya tashi kan ta cigaba
"Now ta kawo wani talakan driver da shi da kanwarshi suka yi min duka kuma ta sakani dole na bashi haƙuri yanzu ko motata ban da right da ita sai abin da banzan ya faɗa Nannah Baƙin cikina bana iya mishi fitsara kaman Dodo yake ga baƙi ga muni ga munin hali"
A tare suka sauke kwalla da Nannah ɗin
"A gaskiya Karima bata kyauta ba sam... Kuma ba zan iya zuba ido ta cigaba a haka ba zan shirya mu zo nigerian da Dad ɗinki dole ta sassauta wasu abubuwan dole ne wannan.. Yanzu dai ki kwantar da hankalinki kinji? Zamu yi maganin su ɗaya bayan ɗaya kar ki sake nuna kin tsani kanwar ko ta karimar ta saka ki zuwa gidan dole zaki samu dama ne ki rama wulakancin nan don ban yarda ki yafe zalunci ba"
Tuni fuskanta ya washe
"Shiyasa nake mugun ƙaunar ki Nannah na"
Basu sake wani magana ba suka kashe don ma Nuwairar itama ɗiyar masu kuɗi ce wayan lode yake da kati ba na wasa ba da ko maganan ba zasu samu damar yi ba sbd International call.
Itama sake nuna mata take ai talakawan Nigeria suka samu right sai su nuna miki iko da isa akan dukiyar ki amma yanzu tayi lullubin biri ta kwantar da kai in ba haka ba ita zata cigaba da azbtuwa daga wurin Mom har shi ɗin kuma shawarar Nuwaira ma ya gamsar da ita ɗari bisa ɗari.
Da gangan Nuwaira ta hana drivern ta zuwa suka shiga motan Jawahir ɗin sai su yi hira su daka shewa su kashe talakawa kuwa sun sha zagi ba na wasa ba har sai da ya shiga unguwarsu jawahir ɗin a Goruba Road kan Nuwaira ta juyo
"Afffff ka ga na manta ni gida zaka ajiye ni Barhim estate..."
Bata jira cewar shi ba ta juya ga Jawahir
"Kinga besty hira yayi daaɗi har mun zo kofar gidanku ban sani ba"
Ko kallonsu bai yi ba ya juya ya nufi Barhim ɗin sai da ya shiga ya wani ɗago ido ya watsawa Jawahir a take ta nemi birkicewa har bata san ta faɗi Street da house number ba, tsaki mai karfi ya ja kan ya taka motar har zuwa kofan gidan yayi parking ta sauƙa
"Bye Besty"
Wani irin gudu ya hau yi da motar da ya hautsina hanjin cikin jawahir tayi tsuru-tsuru bai tsaya ba sai a gaban gate nasu birkin da ya ci sai da tsiririn jikinta ya hantsila ta bugi goshinta da gaban kujera, ya ɗago ya ce cikin gargaɗi
"Ko da wasa kar na sake ganinki da wannan fitsararriyar yarinyar"
"Toh Ubana"
Da sauri ya juyo gabaɗaya sai ta makure jikin kujera tana rufe fuskanta...
"Uhmmmm zan zama uban naki a sadda kika bari na sake ganin naku Marar kunyar banza kawai"
Ya shiga yayi parking bai jira ta ba ya fice daga motar da ma gidan gabaɗaya...
Har yamma yayi ya je gidan su Khadijah Ranshi bai daina zafi ba, zama yayi a sanda Humaira da zainab suka zauna ya dube su
"Khadijah fah?"
"Ai yau uncle Asthma ɗin ta ya tashi a school tana asibiti"
Kai ya gyaɗa ya fara yi musu lesson ɗin bayan ya gama yace su cewa mamansu yana yi ma Khadijah sannu daga haka ya fice daga gidan.
Washegari ma kusan ya bugi bakin jawahir na rashin kunya haka dai yayi ta danne zuciya har suka dawo ya sake zuwa gidan lesson suka ce ba'a sallami khadija ba ko da ya dawo gida ya kira Layin jabir ya bashi number ɗin mamansu ta faɗa mishi suna Asibitin K Dara Amenity room 10.
Afnaan yace ta zo ta mishi rakiya cike da murna ta ɗauki hijab ɗinta suka fice, hannunshi take ƙoƙarin riƙewa kaman yadda suka saba in sun fita tare barin ma dare sai yayi saurin janyewa, a hankali ta ɗago ta kalleshi sai ya kau da ido
"Ke fa yanzu kin girma Naanu"
Bata ce komai ba suka hau abin hawa har junction na KDara ya tsaya ya sayi fruit kan suka ƙarasa asibitin ita ta ma zaci wani da ya sani ko namiji ne sai ta ci karo da yarinya ko tace buduruwar da zasu iya yin shekaru guda da ita.
A bazata khadija ta ganshi a ɗakin ai da wani irin hanzari ta miƙe zaune har yana cewa
"Ke kula mana sai kin faɗo?"
🖤Gureenjoh🖤