KIWON KUBUBUWA

9

by @gureenjoh

KIWON KUBUBUWA

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            

         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

                   PAGE 9

"Sa..Sannunku da zuwa"

Ta faɗa a ɗan birkice.

"Yauwa ya jikin?"

"Ai na ma samu sauƙi kila da safe a bani sallama"

"Allah ya kara afuwa"

Kafin ta ba shi amsa Afnaan tace mata

"Sannu da jiki Allah ya kara sauƙi"

Ta amsa tana kallonta, daidai nan mahaifiyarsu ta shigo ta ji daaɗi ƙwarai na ganin Aliyu tayi ta mishi adu'ar Allah ya ba shi ladan zuwa dubiya basu wani zauna ba suka fice har lokacin Afnaan fushi take wai don ya hanata riƙe mishi hannu.

"Wai har yanzu fushi kike Naanu?"

Baki ta tura yace

"Kin fa girma baki ji ranar mama na cewa ko aurar dake aka yi zaki zauna ba?"

Ta sake tura baki gaba tana ɗan dira kafafu

"Ni...ni ka daina min wani maganar aure"

"Nima bana so kiyi maganan aure, karatu zaki yi ko?"

Kai ta gyaɗa tace

"Har sai Yayana ya ce ya isa"

"Don ni kenan ma zaki yi karatun?"

Ya faɗa da ɗan murmushi, itama tayi murmushi ajiyar zuciya mai nauyi ya sauƙe yana chusa hannayenshi cikin aljihu har suka isa kan hanya kowa da tunanin da yake yi.

A hankali Hajiya karima ta fara building wani bond a tsakanin families ɗin duk yadda Jawahir ta so ta fuske ko ta doje hakan be samu ba don haka kawai sai ta tura ta ta yini a gidan, da shawarar Nannah ta fara amfani hakan ya sa tayi kokari ainun wurin rage tsanar talaka a zahiri, ta rage rashin kunyar da take yi wa Aliyun ta kuma fara samun kusanci da Afnaan Dukda tayi mugun tsanar ta a zuciyarta fiye ma da kowa.

A gefe ɗaya kuwa Aliyu sossai ya dage wurin duka ayyukan shi ta yadda ba'a rufa wata biyu ba sai da ya biya duka kuɗin jarrabawowin Afnaan, ya kai Baba check up ya saya mishi sabbin magungunan da aka ɗaura shi a kai har ma ya ƙara musu abubuwan anfani iyayenshi basu da wani Adu'a sai na Allah ya sa mishi Albarka ya linka mishi fiye da yadda yake yi musu, Afnaan ƴar gata kuwa ta zama tamkar ɗiya a wurin Hajiya Karima ta yadda duk abin da zata saya da sunan Jawahir ta kan saya guda biyu ɗaya na Afnaan tun Aliyu yana nuna baya so har ya haƙura don Har ranta ta ɗauki Afnaan ɗiya, kuma har kayayyakin abinci ta kan aiko musu zasu iya cewa kirkinta na daban ne.

   Aliyu bai daina zuwa lesson ba duk da sauye sauye da ya matukar fahimta daga khadija a kullum idan ya zo ta kan ɗauki excuse ta kawo mishi ruwa da abin taɓawa idan ya ƙi ci haka zata mishi parkaging tayi ta roƙonshi idan ya karɓa kuwa Afnaan yake kawowa, Jabir yana matukar jin daaɗin Aikinshi yana kuma tabbatar da samuwar aikin har da mota bai sa abotarsu yayi rawa da Aliyu ba sai ma samun shakuwa da suka ƙara.

"Aliyu!"

Alhj sammani ya ƙira shi bayan ya sallame shi da kuɗin dakon shi ya juya zai tafi.

"Na'am Alhj"

"Aliyu haƙiƙa na gamsu da natsuwar ka na kuma yaba da hankalinka duk watannin nan da kayi kana min aiki ina lure da kai, ka ga wannan shago?"

Kai Aliyu ya gyaɗa

"Da shi na dogara da kuma shi nake ciyar da iyalina biyu da 'ya'ya takwas, tufafinsu, karatun su kuma Alhamdulillah albarka kam akwai shi sossai saboda ina kokarin ba Allah haƙƙinshi ban taɓa cutan wani ba kuma ban taɓa tauye mudu ba, a baya kafin samuwarka nayi yaran shago sun bi a kirga kowanne da irin kalar cutar da zai min, a yanzu girma ya zo min ga rashin lafiya ainun da nake fama, yawan zirga-zirga da miƙa kaza miƙa kaza ya sa in na koma gida kaman ba zan iya tashi ba sai kuma kuɗin magani suka zo suka soma shiga har suna kawo cikas ga tsare-tsare na, a yanzu dai zancen nan da nake maka yaron shago nake so shiyasa na ke tuntubarka idan har babu damuwa ka zo muyi harkar nan tare zan dinga biyanka a wata, mu fara a tare na satittika zuwa ka fahimci komai sai in bar maka a hannunka idan har ka amince"

Numfashi Aliyu ya sauƙe sai ya ɗan yi murmushi yace

"Zan yi shawara da iyayena Alhj"

"Toh...Toh babu damuwa amma don Allah kar ya wuce yau ina sauraronka gobe"

Kai ya gyaɗa Alhj sammani yayi murmushi har Aliyu ya fice yana kallonshi da yaba rashin son magananshi.

Direct gida yayo da sallama ya kutsa kai gidan ya ɗan dakata yana kallon Jawahir dake taya Afnaan gyaran ganye Dukda ma ba wai ta iya bane sai shirme take, suka amsa sallamar suna kallonshi

"Sannu da dawowa Ya Haidar"

Suka faɗa a kusan tare Afnaan gabaɗaya hankalinta na kanshi yayinda Jawahir bata yi mishi kallo biyu ba.

"Sannu"

Ya faɗa a dake sbd jawahir ɗin da har yanzu ba sake mata yake ba don tsaff yana kule da har yanzu ba wai ta sauya bane ba kuma har zuciyarta ta ɗau damarar chanzawa bane kawai ba yadda ta iya ne.

Parlor ya wuce inda ya samu mama da Baba suna zaune suna hira abin su, murmushi me sanyi ya sake Allah kaɗai ya san irin sanyin da yake ji a zuciyarshi a duk sanda ya ɗaga idanu ya kalli mutanen nan biyu.

Cike da tarin ƙauna suke amsa gaisuwar tashi a hankali ya musu bayanin sabon aikin da Alhj sammani ke so ya mishi sai ya ɗora da

"A gaskiya dama ina so ne in ajiye aikin tuƙin nan tunda yanzu babu inda bata sani ba a Katsina dama kuma akan hakan aka dauke ni, zan ke zama mishi daga safe zuwa karfe biyar sai in je in yi musu lesson na awa ɗaya da rabi"

Sossai suka gamsu ai ya ma yi kokari da jawahir ainun ya kuma yi haƙuri, da dare Hajiya karima da kanta ta zo ɗaukar jawahir inda baba da kanshi ya mata bayani bata nuna damuwa ba sam ta kuma roki da ko da Aliyu baya mata aiki wannan zumuncin da suka ƙulla kar ya tafi a banza sun kuma tabbatar mata da koyaushe ne she's very welcome, haƙiƙa tana matukar yabon gudun duniyar su don dukkansu bayan Aliyu ko gidanta babu wanda ya taba takawa har Afnaan in tayi magana su ce school, ita kuwa idan ta zo har abinci musamman ake ajiye mata ta kuma ci cikin kwanciyar hankali.

Washegari da safe Alhj sammani ya samu Aliyu a kofan shagon shi kuma hakan ya matukar yi mishi daaɗi nan take ya buɗe suka fara sayar da kaya komai Aliyu na kula da yadda yake yi, kafin a ce sati Aliyu ya gama fahimtar komai da komai har ma Alhj sammani in ya je sai dai ya samu wuri ya kishingida yana kallon Aliyu, har babban ɗan shi yayi zama a shagon nan sai dai barnan da ya mishi ya fi na kowa muni amma ji wannan yaro haka yake ayyanawa a Ranshi a duk sadda yaga yadda Aliyu ke yin abu gaskiya da gaskiya.

     Yau su Afnaan suka yi jamb tana ta adu'ar samun nasara don nursing ta san ba abu bane mai sauƙi sam, hakan ya sa ko bayan tayi jamb tana cigaba da adu'ar Allah ya bata sa'a har ma da neco da waec ɗinta tana kuma oppressing su Mama har ma da Yayanta akan kowa ya sanya ta cikin Adu'a, Bayan rubuta jamb ɗinta da sati Result ya fita kuma Alhamdulillah ta samu 200+ murna ba'a magana.

Tun da ya shiga gidan fuskan khadija ya nuna mishi akwai magana Bakinta yadda take yawan murmushi kaman wacce aka yi wa albishir da aljannah, hakika tun bayan zaman shi da mahaifiyarsu ya ankarar da ita akan yaran tayi matukar jajircewa da taimakon shi wurin ganin yaran sun sauya abin ka da yaro tuni sun natsu, kuma sai hallayyar khadija ya sauya daga marar kunya zuwa mai kunya, dama chan bata da magana haka ma har yanzu yana lura da ita da kyar ta hakura suka gama lesson kan tace

"Uncle guess what?"

Fuskanshi kadaran hadaran don har yanzu ba dariya yake musu ba kai shi fa fara'arshi bayan mama da Baba sai Afnaan sai kuma jabir da shima lokaci lokaci yake yi wa babu wanda yake gani.

"I guess akan jamb ne. You pass?"

Tsallen murna kaɗan tayi hakwaranta duka a waje tace

"Yesss 315 and fa na fi cin physics... unbelievable!"

Sai a lokacin yayi murmushi me faɗi ya tuna murnar Afnaan na jiya har tsalle tayi ta rukunkume shi, lumshe idanu yayi ya buɗe kan yayi mata Fatan alkhairi

"Sisternka da kuka zo asibiti hall na jamb ɗin mu ɗaya ban samu na mata magana ba ita kuma bata gane ni ba did she pass?"

Kai ya gyaɗa fuskanshi har lokacin da murmushi yace

"Yeah 200+"

"woowww na mata murna ko da shike dama na san dole ta ci ai tana da kai"

Ɗan kallonta yayi yana saisaita fuskanshi yace

"Wa yake koya miki zare magana haka?"

Dariya tayi ya girgiza kai ya miƙe ya musu sallama ya fice.

Karfe takwas na safiyar Asabar sai ga Hajiya karima har ciki ta shiga suka gaggaisa mama na cewa ta zauna mana ta girgiza kai

"Ai Mamansu ba zama ya kawo ni ba, na zo daukar ɗiyata ne yau kam ta yi mana yini"

Murmushi sossai Afnaan ke yi sai taji tana kiyssta yadda gidan zai zama, Allah ya sani bata taɓa zuwa gidan Ƴan gayu ba sai dai hange 'yan ajin su a kullum idan suna hirarrakinsu musamman na novel da ma waenda suka taɓa zuwa gidajen masu kuɗi wani lokacin har mafarki take gata ciki Dukda bata taɓa nuna interest a fili ba.

"Toh kuma gashi Aliyu ya fita kasuwa, Babansu ma ya ɗan fita"

"Haba Mamansu ai in kin amince shikenan na san suma ba zasu ƙi ba, sau ɗayan nan dai"

Kai mama ta gyaɗa kan tace

"Toh ai shikenan sai kun dawo"

Afnaan sai danne zumudinta take, da sauri ta shirya cikin bakin dogon riga da ya matukar zama mata wadda Mommyn ce ma ta saya mata tare da jawahir ta yafa gyalen kai ka ce itace ɗiyar masu kudin yadda tayi mugun kyau, turarenta da yayanta ya saya mata ta fesa ta fito.

"Masha Allah! Ɗiyata ba dai kyau ba"

Murmushi kawai tayiwa mommyn suka fice Dukda mama ta so ce mata ta kula sossai sai kuma idanun Hajiya karimar ya hana.

Baki da hanci duka ta saki tana karewa gidan da ya tsaru iya tsaruwa kallo, a ranta take ta maimaita wow wow aljannar duniya, ai bata gama rudewa ba sai da suka shiga ciki daga karshe ma sai da Hajiya karimar ta kama hannunta tana ɗan murmushi, har ɗakin jawahir dake rufe a bargo tana bacci suka shiga

"Tashi maza ga sisternki ta zo baccin safen nan da hana sai an yi kenan ko?"

"Mommyyy don Allah yau dai ki barni nayi bacci na... Har sai yaushe zaki gane bambamcin rayuwarmu da na waenchan talak..."

"Commm'on tashi Afnaan ce ta zo"

Miƙewa tayi sam Afnaan bata kula da sauran maganan da jawahir ɗin ta so furtawa ba, sai kallon tafkeken ɗakin na jawahir take lallai dole ta raina talaka.

"Kin zo?"

Kai Afnaan ta gyaɗa don har yanzu ba sun sake bane har chan da juna.

Dira tayi ta shiga bayi tayi brush ta dawo da shara-sharan shirt ɗinta na bacci, call tayi akan a kawo musu abin kari daga kitchen daga ita har Afnaan satar kallon juna suke yi, ita Jawahir gani take wannan kyaun na Afnaan ita ya kamata ace tana dashi jikin hutu da na masu kuɗi ne, amma sai Allah ya ba Afnaan(Nace su jawahir shi Allah kuma ina ruwanshi, ba kowani so bane samu)

Ita kuwa Afnaan gani take Allah ya gama sallaman su jawahir sai ta tuna a baya chan kan rayuwarsu ya ɗan daidaita irin baƙar wuyan da suka ci, akwai tsakanin da har Abinci sau ɗaya sun ci a yini, tayi government school, ta saka tsoffin kaya da sallah baba yayi ciwo kaman zai mutu babu kudin magani ba dalili, gashi lokacin ƙarfin Aliyu be kawo kaman yanzu ba Dukda yayi matuƙar kokari.

Sallaman mai aikin ne ya katse su, ta shigo ta tiren abinci ta ajiye ta fice.

Jawahir ne ta sakata dole sauka Dukda ta ce mata ta karya da kosai da koko amma sai da ta sakata zama gaban abincin fakar ido tayi ta dauƙeta a hoto ita da abincin tayi posting a status ɗinta ba tare da ta sa Caption ba.

Nan fa mutanenta 'yan uwan masu kuɗi😅 aka fara tambayarta ita kuma wacece? 'Yar waye? Amma skin ɗin nan nata ba Nigeria take ba, Nuwaira ce kawai ta amsawa da Afnaan kenan Don ranta ya zo wuya wani irin hassadar yabon Afnaan ɗin da ake yake shiganta sai taji tsanar ta fiye da farko da ta rasa dalili bayan talauci. Sossai ta yaki zuciyarta ta sauƙa suka karya tana ɗan jan Afnaan ɗin da hira bayan sun gama ta ajiye mata system ɗinta wai tayi kallo ita zata yi wanka ta kuwa fara kallon wani indian Series da ake zuba soyayya tuni hankalinta ya ɗauku, Dukda ta sha jin labarin soyayya lokaci zuwa lokaci tana ɗan kallo a hausa films da sauransu amma bai taɓa buga kanta irin yau ba sai ta fara tunanin ita ya nata zai kasance? Irin wannan shauƙin da zaka riska a sanda kake kallon soyayyar wasu abin burgewa. Bata taɓa kula saurayi ba don Alkawari ta yiwa yayanta masu naci sun yi har sun gaji, murmushi take har dimple ɗinta na bayyana yayinda jawahir ke zaune gefe tana ɗaukar duk wani motsinta tana turawa Nuwaira, ta ɗauki sanda take murmushi ta tura mata tare da rubutawa a ƙasa

"Ɗan kauye ya zo birni"

Dariya Nuwaira ta turo tana cewa

"Keee ba dole ba Babu a house gidan miji ba tabbas"

Har a fili Jawahir ta fashe da dariya ita dai Baiwar Allah Afnaan ba ma ta san namanta suke ci ba...

Yininta gidan ta matukar yi mata daaɗi, Acn da ta sha har kaman kar ta fita rana bare a yi zancen komawa gidansu saboda tsananin zafin da ake yi a Katsina, haka ba yadda ta iya bayan isha suka maida ta da tarin snacks da kaya kunce da jawahir ta ciro mata dogayen riguna don idan ba su ba kayan jawahir ba zai yiwa Afnaan ba sbd yadda ta fi ta kauri da ma albarkatun jiki.

"Mama ina Ya Haidar ne tun da muka shigo ban ji shi ba yau akwai hiraaaa"

Ta faɗa with excitiment.

"Tun la'asar ya dawo yana ɗaki ina ga masallaci kawai yake fita ko dazu na leƙa na tambayi ko a kawo mishi abinci daki ne yace a'a zai fito kin ga har yanzu shiru na ma zaci zuwan su Hajiya karima zai sa ya leƙo a gaisa"

Zurumm haka Afnaan ta miƙe don so take ta bashi labarin yau din from A-Z da zafin shi kan ta manta wasu da sauri tayi ɗakinshi Mama na bin ta da kallo tayi murmushi kawai ta girgiza kai.

Da sallama ta tura ɗakin yana a kwance ne rigingine sai dai kaman bai ji sallamar ta ba sai motsin Shigowar ta hakan yasa yayi wani irin juyi ya koma a kife yana lumshe idanu.

"Besty...! Ya Haidarrr tashi tashi ka sha labari ashe haka gidansu jawahir yake?"

"Baki iya sallama bane?"

Ya faɗa a ɗan kausashe ba tare da ya juyo ba

"Nayi fa wallahi baka ji ba?"

Shiru ya mata.

Matsowa tayi

"Lafiya kuwa Yaya?"

"Tafi cikin gida zan shigo yanzu"

"Baka da lafiya ne yaya?"

Ta faɗa tana kai hannunta kan kafadarshi a razane ta cire hannun tana miƙewa tsaye saboda tsawar da ya daka mata

"I said get out zan shigo ko??"

Da sauri ta fita a ɗakin kawai sai ta fara hawaye.

                       

                           🖤Gureenjoh🖤