KIWON KUBUBUWA

10

by @gureenjoh

KIWON KUBUBUWA

FATIMA MUHAMMAD GURIN.             

         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

                   PAGE 10

THE BEGINING OF EVERYTHING

Kasa jurar yanayin da ta fitan yayi ya santa sarai zuwa zata yi ta dasa kuka hakan ya sa ya ɗaure yanayin shi ya miƙe da sauri ya fita dab zata shiga cikin gida ya tare ta.

"Naanu... Am sorry ban jin daaɗi ne"

Sai ta shiga damuwa bata iya tayi boren da take mishi ba a duk sanda suka yi faɗa ba.

"Meke damunka Ya Haidar?"

Ya lumshe fararen idanunshi da suka zama mixed of Red ya ɗan ware kanta yace

"Ki yi min Adu'a kawai, ki ɗan kai min ruwan sanyi toilet kar ki surka zan zo in yi wanka sai in saurari labarin ko?"

Kai ta gyaɗa da sauri ta wuce, ya sauke nannauyar numfashi yana dauke idanu daga kanta ɗakin ya koma ya ɗauki kayan wankanshi ya fice, ya ji daaɗin samun su Mama har sun shiga parlor hakan ya sa ya ɗauki ruwan kawai da ta gama ja ya shige bayi.

A waje ta zauna kan taburma tana jiran shi har ya gama ya shirya cikin jallabiyarshi ya zo ya zauna ta tura masa abincin, shinkafa ce da miyan alaiyahu suka yi yau, ya ɗan ci ƙadan kan ya rufe

"Naanu mu ga hannunki?"

Ba ko darr ta miƙa masa ya sa hannu ya fiddo da wani bangles da zobe mai kyau ya sanya mata

"Wannan na gani a kasuwa ya min kyau ainun kuma na san zai fi dacewa da hannunki shiyasa na saya"

Fuskanta ta washe har ga Allah duk abin gayu tana so kuma iya kokari yana yi akanta kyale kyalen 'ya mace na daidai kuɗi ya kan saya mata godiya ta mishi kan ta fara bashi labarin gidansu Jawahir.

Idanu kawai ya zuba mata yana kallo fuskanshi na nuna less interest akan labarin sannan kuma tunanin shi na rabuwa idan ya ji yadda take ta sake zuzuta kuɗi da tsaruwar komai na gidan har ma tana kamanta kanta da cewa da ma ita ce jawahir

"Ya isa..."

Ya faɗa a hankali yana dauke kanshi daga kanta ba tare da tsawa yayi maganan ba hakan yasa ta cigaba da murmushi

"Su Hajiya sun kyauta Allah ya saka amma Afnan bana so ki sake zuwa please"

Ta ɗan waro ido

"Ko mommy ce ta zo ta roƙi su mama?"

"Eh zan yi wa mama magana bana so. Can you do that for me?"

Kai ta gyaɗa a sanyaye yana lura da ita, Afnan rainon shi ce babu abin da bai sani ba game da halayenta amma zuciyarshi na rawa akan wannan alaka tasu da su Hajiya karima haka kawai yake jin baya so, suna chanzawa Afnan tunani kaman tana so ta raina inda Allah yayi ta abin da kuma baya fata kenan he prays always ta ga effort nashi a kansu kaman yadda iyayensu suke gani a kullum, amma ya mata uzuri da yaranta sannan at her age dole kowa yake fara gina burikanshi na rayuwa.

Har ya kwanta da wannan tunanin ya kwana da sassafe ya fice daga gidan zuwa kasuwa, ya samu Alhj sammani ya riga shi fita don dama jiya ya ce mishi ya zo da wuri yana so ya aikeshi.

Aiko kudi ya bashi masu yawa ya aikeshi charanchi samo wasu kayyaki da suke buƙata a shagon tuni ya fice ya nufi tashar motar da zata kaishi nan ɗin.

A gida kuwa fitanshi ba jimawa Mama ta fahimci kaman jikin baba babu daaɗi Dukda yana ta dauriya, abu kaman wasa mintuna na shuɗewa jiki na ƙara tsanani, nan take ya fice hayyacinshi hankali tashe Afnaan ke ta kiran Layin Aliyu sai dai baya shiga.

"Mama bari na samo napep mu kaishi asibiti kila kan mu isa in samu Yayan"

Da gudu ta fita hankali tashe tana sake kuma gwada Layin Aliyun sai dai har lokacin not reachable napep ta taro Allah ya sa da kuɗi hannun Mama don ya kan bata ta riƙe in case daga ita har Baba, mai machine ɗin ne ya taimaka musu da wani makocinsu aka saka shi a a napep suka nufi Medical center Katsina, su karan kansu nurses ɗin sun tsorata da yadda suka ganshi nan suka fara kokarin neman doctors aka rufu a kanshi, wata Nurse ce ta fito ta bata takarda

"Sayo wannan yanzun nan da hanzari"

Da gudu ta fice zuwa pharmacy sam bata kula da wani magidancin mutum dake tsaye ba ta ɗan ture shi hakan ya sa ya juyo yana sauƙe idanunshi a kanta ita kam ko kula shi bata yi ba ta miƙawa phermacist ɗin

"Don Allah yi sauri"

"dubu ashirin da biyar"

Wani irin zaro idanu tayi dubu  uku ne hannunsu, gefe ta koma ta sake fara kokarin neman Aliyu sai hawaye ya fara bin fuskanta, doguwar riga marar nauyi irin na madinan ne jikinta sai baƙin gyalen dogon riganta da ta saka jiya ta ɗora a kanta kafafunta ma silifas ne tsabar rudewa.

Dawowa tayi

"Don Allah ka riƙe wayan nan ka bani maganin babana ne yana emergency idan yayana ya zo zamu kawo maka wallahi"

Girgiza kai yayi

"Wayan da bai fi dubu biyar ba maganin dubu ashirin da biyar? A'a ba zaki bar ni cikin masifa ba"

Hawaye sossai take yi zata sake magana mutumin ɗazu da yake ta kallonta yace

"ka bata zan biya"

Da sauri ta kalleshi

"Na gode! Na gode sossai idan Yayana ya zo zai baka sa layinka anan"

Karɓa yayi ya saka ya bata ta karɓi maganin ta juya da gudu-gudu sauri-sauri ta fice daga wurin a hankali ya bi bayanta da kallo gabaɗaya Ranshi ya bashi ya samu matar aure haƙiƙa yanzu ne zai san yayi aure in ya auri wannan dalleliyar yarinyar, she's so cute, daga kallon skin ɗinta zai iya cewa Its so soft nd tender shi gabaɗaya Its love at First sight a ɓangaren shi.

Bayan kawo maganin sun jima anan suna safa da marwa, kowa da abin da yake saƙawa mama kam zuciyarta banda bugu babu abin da yake yi, sai maganganun su na jiya na dawo mata daki-daki kaman yanzu yake yi mata hakan na kara tsinka mata zuciya, wayar Aliyu Naanu ta cigaba da ƙira da kyar ta same shi a lokacin ma har azahar yayi kuma har lokacin likitoci basu fito daga kan baba ba

"Yaya kana ina? Me ya samu wayanka nake ta ƙira bana samu...?"

Cikin wani irin yanayi tayi maganan hakan ya sa gabanshi faɗuwa, gyara tsayuwarshi yayi gama sauke kayan da suka dawo dashi kenan gabaɗaya jikinshi yayi furu-furu na kasuwan kauye ga sauke kaya.

"Na tafi kauye ne, menene? Lafiya kam?"

Kaman jira yayi tambayar ta fara hawaye

"Muna asibiti da Baba"

Hankali tashe ya nemi izini daga Alhj sammani ya juya ya hau machine.

Daidai zuwanshi ko magana bai kai ga yi ba likitocin suka fito suna share gumi, babban ciki ya kalli Aliyu "Ka sameni a office"

Kai ya gyaɗa bai yi magana ba ya juya ya bi bayan likitan jikinshi a mugun sanyaye.

"Aliyu ba zan ɓoye maka ba mahaifinka ba lallai ya farka ba in har ba'a samu donor ba, duk kodojin sun daina wani aiki magani ko allurai yanzu ba zasu yi wani tasiri a jikinshi ba"

"Innalillahi wainna ilaihi rajiun"

Ya furta cikin wani irin murya, kan shi ya duƙar ƙasa Adams Apple dinshi na wani irin hawa da sauƙa danne hawayen dake taho mishi yayi, yana tuna maganganunsu da Baban na shekaranjiya da dare don jiya basu wani samu lokaci tare ba, maganan da suka yi shekaran jiyan kuwa yayi matukar taka rawa a halin da ya tsinci kanshi jiya iya ƙoƙari yayi wurin ganin ya hana kanshi zubar kwalla haka ya miƙe ya fito kawai sai bai koma wurin su mama ba don bai san ya zai yi musu ba.

Yana fita jabir ya ƙirashi daga yanayin muryarshi ya san babu lafiya a hankali ya faɗa mishi abin da ke faruwa take yace gashinan zuwa, chan baya inda ba mutane Aliyu yaje ƙasar wani bishiya kawai ya zauna, gabaɗaya duniyar tayi mishi zafi tsananin raɗaɗin rashin kuɗi yake ji don tabbas da yana da kuɗi da yanzu ba wannan maganan ake yi ba, tunanin hakan ya sa yaji wani irin zazzafar hawaye ya sauƙa mishi Allah kaɗai ya san me yake ji a Ranshi.

Ko da jabir ya zo da kyar ya same shi duk yadda yayi dashi akan su koma ciki ya ƙi yace idan har ya je gaban su mama a wannan yanayi tabbas zasu sake rikicewa ne, sai shi J ɗin ne ya koma wurinsu.

Har yamma suna nan cikin wannan yanayin don Baba kam ICU aka tura shi, Aliyu sai dab Magrib yaje gida duk abubuwan buƙatun su na asibiti ya harhada ya ɗaukawa baba wasu kaya sai yaji wani irin hawaye na sauƙa mishi da kyar ya danne ya fito kenan sai ga Hajiya karima da Jawahir, gaisawa suka yi da kalma ɗaya ya amsa na jawahir kan yacewa Hajiya da tace

"Yau hiran dare muka kawowa su Mama don gaskiya nayi kewan tuwon ta"

"Ai basa nan"

"sun fita ne?"

Ɗan shiru yayi sarai ta san miskilancin Aliyu.

"Toh ko mu ɗan jira su don dai na san bata dare waje"

"Suna asibiti baba babu lafiya"

"Ya subhallah tun yaushe? Chan zaka yi?"

"Eh"

"Toh mu je kawai"

Haka ba yadda ya iya ya shiga motar gidan gaba tare da drivern su su kuma suna baya har asibitin sai a lokacin ya yarda suka hadu da Su Mama gaisuwa kuma ya sa basu kula ba bare su tambayeshi abin da likita ya faɗa sun samu maman jabir ma ta zo, taburma suka shimfida daga waje suka zazzauna dama maman jabir da abinci ta zo su suka samu suka sa mama ta ɗan ci haka Afnan ma da kyar ta ci kaɗan don jikin baban bai taɓa ɗaga musu hankali irin yau ba.

Aliyu da su ke zaune da jabir daga wani ɓangare ya ɗauki waya ya shiga neman Layin kawu habu ringing na karshe ya daga suka gaisa kan ya faɗa mishi jikin baba ya tashi kuma bai ɓoye mishi abinda likita ya faɗa ba, ya kuwa tabbatar mishi da sassafe yana nan shigowa.

Kaman yadda suka saba karfe goma suka tafi su Hajiya karima suka maida su gida akan sai da safe zasu dawo Aliyun suka bari kan su tafiya Hajiya karima ta ajiye mishi envelope duk yadda ya so kar ta bari bata saurare shi ba ta fice, tuni bayan tafiyan su jabir ya ga alert dubu talatin daga jabir ɗin hawaye yaji ya cika mishi idanu ya san ya ƙi bashi ne don kada ya ƙi karɓa hakan ya sa ya tura mishi a account, envelope na Hajiya karima ya buɗe itama kudi ne har dubu hamsin.

Idanu ya lumshe yana musu Adu'a a ranshi chan dare aka barshi shiga wurin baban banda na'urori da oxygen babu abin da yake aiki a kanshi, haka ya kwana yi wa mahaifinshi Adu'a, da safe jiki ya sake rikicewa tuni kuɗi suka soma tafiya don ba karamin abubuwa ake rubutawa ba.

Karfe takwas ko da suka iso ya ɗan zama stable basu san da sake rikicewar jikin ba, Aliyu bai iya ya bar asibitin kaman yadda ya saba ba, tara sai ga drivern Hajiya karima da abinci... Bai jima da tafiya ba Goggo Salame ta iso asibitin bata ko zauna ba sai ga kawu Habu nan suka shiga jimami. Har dare baba bai san wanda ke kanshi ba, a lokacin Mahaifiyar su Khadija ta kira ganin kwana biyu bai zo ba kuma bai kira ta ba nan ya faɗa mata tace ai nan mahaifin su khadija ke aiki bari su zo su duba shi.

Dare kuwa asibitin na ɗan cike Dukda kawu da goggo Salame basu zo da kowa na miji, mata ko 'ya'yan su ba, Su khadija da Mamansu suna nan da abinci, Hajiya karima ma sun zo da jawahir da abinci  sai jabir da mamanshi lallai sun ga kara har kusan sha biyu kan suka watse inda mahaifin su khadjiya shima yayi nashi bajintar don yana jin yadda yaran suka yabon karatun Aliyun da yadda ya taimake su a ci gaban karatuttukansu na makaranta da ma ɗabi'ar su ta gida, har yanzu Aliyu wanka kawai yaje ya iya yi ya dawo ko abinci ba wai zama yake ya ci ba sai Mama ce ke mishi dole ya taɓa kaɗan, ko kuma Afnaan da ba ya son ganin kukanta, dare duk yadda kawu yayi dashi ya je ya huta ya ƙi haka suka tafi suka bar su su biyu a kanshi, karfe huɗu na daren Alhamis wayewan garin juma'a ya farka.

Cikin ikon Allah ya iya gane kawu, bayan sun gaisa ya shiga mishi magana a hankali sun jima suna tattaunawa kan Aliyu na ƙasa, bayan sun gama yace Aliyu yayi mishi alwala ya fara rama sallolin da aka biyo shi ana kiran sallah a masallaci kawu yace bari yaje Aliyu yayi sallah anan, A kusan tare da Baba suka tada Sallar asuban bayan sun yi raka'atanil fajir har Aliyu ya idar bai ji motsin baba na ruku'u ko sujud ba Dukda a kishingide ne, Miƙewa yayi yaje ya ɗan taɓa shi sai yaga idanun shi a kafe a sama yana kallon wuri guda, wani irin tsitsinkewa jijiyoyinshi suka shiga yi jinin shi na wani irin gudu, numfashi yake kokarin ja cikin kasa gaskata abin da yake gani, Shigowar kawu ya tabbatar da komai don salati yake yana kuka shi ya rufe mishi idanu ya kira likita suka tabbatar da rasuwar......

                        

                           🖤Gureenjoh🖤