13
by @gureenjoh
KIWON KUBUBUWA
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
PAGE 13
Yi yayi kaman bai gansu ba da farko har ya nufi shiga gida Tahir yayi hanzarin shan gabanshi yana duƙar da kai alamar nuna kunya irin na surikai ya miƙa masa hannu
"Barka da wannan lokaci yayanmu"
Ɗan kallon Afnaan da duk alamun tsoro sun bayyana a lamarin ta yayi ya kau da kai tare da miƙawa Tahir ɗin hannu ya ce
"Barka"
Daga haka ya zagaye shi ya wuce kai tsaye cikin gida yayi kawai sai ganinshi mama tayi, ganin tana ta kallonshi ya sa ya ɗan gaisheta da gida ta cigaba da kallonshi ya zagaye ya wuce zuwa bakin rijiya ya ɗibi ruwan wanka ya kai ya juyo zai koma ɗaki maman ta katse shi
"Ka kuwa ga Afnaan waje?"
"Uhmm"
Yana faɗin haka ya wuce ɗakinshi kayan wankanshi ya kwaso ya zo yayi wanka har ya fito yarinyar nan bata shigo ba hakan ya kara hasala shi ainun fiye da zato.
A chan waje kuwa bayan wucewan Haidar ta dube shi
"Zan tafi kar na kara laifi"
"Haba mana ai yanzu ya fahimci abin da ke tsakaninmu kuma nayi alkawari zan bar ki kiyi karatu ke dai burina shine ki bani haɗin kai ɗari bisa ɗari har mu ga mun mallaki juna ko kina so ki ƙare a auran talaka marar abin yi? Ke fa da matan manya kika yi kala dubi skin ɗinki so fresh please kar ki ɓata mana shiri ki cuce ni"
Shiru tayi tana tunanin yanayin Aliyu a sadda ya shige gida.
"Kayi hakuri don Allah ka tafi zan shiga gida"
Juyawa tayi yayi saurin riƙo hannunta
"Ba Za mu rabu a wannan yanayi ba har sai kin yi min dariya ko bakya so na ne Afnaan?"
Kai ta girgiza
"To yi min kyakyawar murmushinki mu ga"
Ta kuwa murmusa
"Ko ke fa, kin yi alƙawari zaki kunna wayar?"
"Eh zan kunna"
"okey take care of your self kin ji? Bye"
Ta juya ta nufi cikin gida daidai nan Aliyu ya taho zai shiga ɗakinshi bayan ya watsa ruwa, har ta wuce shi ya sanya hannu ya janyo hannunta zuwa ɗakinshi a tsakiyar ɗakin ya saki ya zuba mata dukkanin idanunshi da suka firgitata
"Afnaan"
Ta amsa a hankali
"Na'am"
"Afnaan me kike nufi? Wannan sabon ɗabi'ar me yake nufi? Ashe mutuncinki ne ki ke shiga motar wanda baki sani ba wani chan katon banza ya dinga kai ki school yana dawo da ke har kin yi wannan girman? Ashe har kin yi girman da idanu bai isa ya ladabtar dake ba? Wani rashin kunya kuka tsaya yi waje tun na dawo har nayi wanka?"
Dukda yadda ta tsorata saboda bai taɓa mata faɗa haka ba, muryarshi kaɗai da take ji cikin kwanyarta ta san ranshi gabaɗaya ya jagule kila ma dannewa yake bai kai mata duka ba, da kyar tayi gaining courage tace
"Ka yi haƙuri!"
"Ba haƙuri nake son ji ba, Afnaan tun yaushe Wanchan katon banzar ke kaiki makaranta yake dawo dake?"
"Ya kai sati uku"
Lip dinshi na ƙasa ya cije
"Afnaan hasbunallahu wani'imal wakeel"
Ya kasa cewa komai bayan nan sai
"Fita"
Ya nuna mata hanya, ta kasa ko kallon idanunshi haka ta wuce ta fita sum sum duk inda hankalinta ya kai ya tashi, bata san me kuma zata yi ba har ga Allah bata son bacin ran yayanta sai dai wani zuciyar tambayarta yake kwaɗonki zai yi ya cinye in baki saurari wani kin yi aure ba?
Mama bata ce mata komai ba don dama fatanta Aliyu ya gansu tare ta san ko ma menene tsaf zai taka masa birki a yanzu ranta fess sai dai ta shiga mamakin ganin damuwa tsantsa a fuskar Afnaan ɗin har suka shiga suka kwanta.
Sai da ta bari kowa yayi bacci ta zaro wayan ta kunna an yi setting komai, kaman jira kuwa tana kunnawa sai ga kiranshi fitowa tayi harabar gidan ta ɗan maƙale gefen kitchen suka fara hira, tun tana shakka har ta sake tuni ya mantar da ita damuwar fushin Aliyu sai bata labarin yadda kasashen waje suke da kuma irin sonta da ya mamaye ilahirin jikinshi yake sun jima sossai sai da taji motsi kaman Aliyu zai fito ta kashe ta koma ɗaki sum sum ta kwanta.
Washegari kaman Jawahir ta san tana son ganinta sai gata, a ɗaki suka zauna tun kan Afnaan ta kawo mata zancen ita ta riga ta.
"Ya kuke ciki da mutumin naki?"
Numfashi ta sauƙe
"Jiya Yaya ya gan mu tare har fushi yayi Dukda bai min faɗa sossai ba kuma har yanzu fushi yake da ni don da safe ko amsa gaisuwata bai yi ba, wlh ina jin ba daaɗi har raina yadda muka tashi cikin shakuwa da kaunar juna bana so komai ya shiga tsakanin wannan amincin"
"Toh ya zaki yi da soyayyar Tahir ɗin in kin hakura da shi? Haka zaki yi ta zama gaban Ya haidar dinne? Ai duk fushin shi na lokaci kankani ne tunda ba auren ki zai yi ba"
Kallon baki da hankali ta mata na Magananta na ƙarshen.
Kan tayi shiru haka Jawahir ta cigaba da bata ƙwarin gwiwa bata barta ba sai da ta tabbatar ta aminta da cewa bata yi kuskure ba sai ma Aliyun ne yake kan kuskure na fushi da ita akan abin da ta isa ta kuma kai tayi wato saurayi.
Gabaɗaya Aliyu ya zama marar kuzari a kwanakin da suka biyo baya, gabaɗaya bai san inda zai kama ba don sossai ya fahimci an sauya tunanin Afnaan, yau shi ne ne da Afnaan basu yi magana ba tsawon sati biyu amma ko a jikinta ko ta fahimci cewa fushi yake ta bashi hakuri su fahimci juna yadda suka saba, goggo Salame sun koma hakan ya sa a yanzu a ɗakinta take shan love ɗinta har video call suke yi. Yau yake shirin sake zama da ita don ya ci alwashi idan har ba zata shiga taitayinta a faɗa da nasiha ba to tabbas zai buɗe mata wuta haka kawai rana tsaka wani bai isa ya lalata mata tarbiya haka kawai ba. Kafin yayi mata magana ashe mama ta ajiye ta
"Afnaan halayen ki na kwanakin nan har tsoro suke bani, menene ya shiga kan ki ne? Ina lure da cewa gaaba kike da yayanki saboda me?"
Shiru tayi
"Ina magana kin min banza don ubanki??"
Zaro idanu Afnaan tayi don mama macece mai sanyi bata cika yiwa mutum faɗa ba haka bata dagawa kowa murya wannan kam Baba ne ko Aliyu amma duba abin da Mama take son yi mata saboda abin da ba laifinta ba
"Mama shine in na gaishe shi baya amsawa"
Wani irin takaici ne ya zo wa mama wuya kaman ta rufe Afnaan ɗin da ɗan banzan duka
"Me kika yi masa?"
Tayi shiru ai bata ankara ba taji saukan mari a Bakinta da karfi, da sauri ta dafe tana jin hawaye na soma yi mata ambaliya
"Afnaan yaushe kika zama haka? Aljanu ne a kanki ko menene? Nace uban me kika yi masa?"
"Mama wai don ya ganni da Tahir kuma fa a gabanki Tahir ya roki na mishi rakiya daga nan ya hau ni da masifa kuma na bashi haƙuri amma ya ƙi to ni me zan mishi?"
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun"
Abin da Mama ta faɗa kenan kan ta gyaɗa kai tace
"Tashi ki bani wuri tun kan in taka ki... Ki je ki zauna ki yi nazarin laifukanki kuma ki gyara tun kan dare ya miki na baki nan da kwana uku wallahi idan baki dawo asalin Afnan da na sani wacce muka ba tarbiya daidai gwargwado ba sai na lahira ya fiki jin daaɗi a gidan nan wawuya kawai wacce bata san zuru ba"
Miƙewa tayi ta fice tana kuka sossai ko da ta isa ɗaki katifanta ta faɗa tana kuka tana jin baƙin cikin da bata taɓa ji ba a ranta ji take kaman duk su mama basa ƙaunarta, ji take sun takura mata rayuwa ainun su barta mana tayi rayuwarta mai kyau da ta tsarawa kanta tun da dai yanzu ta mallaki hankalin kanta.
Tana cikin kukan Tahir ya ƙira ta nan ta bashi labarin abin da ke faruwa bayan ya matsa shima faɗa ya dinga yi ai dukkansu daga ita har Aliyu suna da right Meyasa laifinta mama zata gani? Taji daaɗi da ya goya mata baya, har alkawari ya mata in Aliyun ma ba zai biya mata karatu ba shi a shirye yake ya biya mata tayi har ma Phd in ana yi na Nursing. suna gama waya ta kira jawahir da bata ɓoyewa komai na sabon rayuwar da ta riski kanta itama ta bata goyon baya da ƙwarin gwiwar ta tsaya kan matsayarta tana kan gaskiya ne kar a tauyeta. Washegari ta fita tana ayyukan gida yadda ta saba bayan ta gaishe da mama bata amsa ba Aliyu ya shigo gidan gabaɗaya yana cikin damuwa ya sanar da mama rasuwar uban gidanshi Alhj sammani, ya kwanta lafiya Dukda dama ya jima yana ciwo sai tashi aka yi aka samu gawa hankalin mama kwarai ya tashi tayi ta jimami kan ta shirya akan su tafi tare ta yiwa iyalanshi gaisuwa ci kanku Afnaan bata ce ba. Daga mama har Aliyu danne kansu suke na kar su rufeta da Duka saboda sun san at this age duka ba zai taɓa zama solution ba sai dai ya kangarar bare shi aliyu da baya ji har abada zai iya ɗaga hannunshi kan Afnaan bai yi ba tun yarantarta a yanzu ba zai iya ba.
Haka suka fice suka barta kwana uku suna zuwa gaisuwa a kuma kwana na ukun ne Aliyu ya ba da keyn shagon wa magada suka sallame shi da daidai kuɗinshi, a yanzu ya dawo kuma cikin tasku don fa wani sabon wahalar neman abin yi ne kuma ya sake buɗe mishi bayan lesson na su khadija baya komai.
Yau cikon kwana uku da mama ta bata ta zaci abin wasa nan mama ta kirata ta kira Aliyu
"Afnaan kin ba yayanki haƙurin laifin da kika mishi? Kuma kin yi alƙawari ba zaki sake ba kaman yadda muka yi dake?"
Kanta ƙasa ta ɗan tura baki
"Mama na riga na bashi hakuri tun ranan kuma ni ban yi mishi laifin komai ba"
"Amina"
Mama ta kirata da ainihin sunanta
"Amina ki bashi hakuri kuma ki yi alkawarin ba zaki sake ba in kin sake kuma duk hukuncin da yayi miki daidai ne"
Shi Aliyu wallahi sandarewa kawai yayi kanshi ya dau zafi barin ma da ya ji tana cewa
"Mama b..."
Kan ta ƙarasa maman ta janyo cable na reciever dinsu ta rufe ta da duka, tana dukanta tana zub da hawaye
"Afnaan lalata tarbiyar ki kike kokarin yi? Baki tashi hakan ba sai da mahaifinku ya faɗi ya mutu? Yaushe kika zama haka? Waye yake ɓata miki tunani yake kokarin lalata miki rayuwa? Kin kuwa san matsayin Aliyu a rayuwarki?"
Ko motsi Aliyu be yi ba sai da yaga maman ta harzuka sossai zata iya yi mata illa kan ya janye maman sautin shi a hankali yake fita
"Mama kiyi haƙuri har da laifina, na kasa ɗaukar matakin da ya kamata matsayina na babba kiyi hakuri duk zamu gyara"
Jefar da wayan tayi ta shige daki tana kuka shi kuwa Afnaan da ta cigaba da kuka ya zubawa idanunshi da duka suka yi wani irin sauyawa tana ɗagowa ta kalleshi
"Meyasa ka tsane ni yanzu? Me nayi maka da zaka shiga tsakanina da Mama Yaya Aliyu? Ashe dama ba so na kake ba?"
tana kai nan ta miƙe ta fice fuuu daga parlorn da kallo ya bi ta har ta ɓace fita yayi ya fara laluben Layin Tahir a wayan Baba sai dai bai samu ba, ko ba'a faɗa mishi ba ya san shine yake hurewa Afnaan kunne kuma tabbas duk ranar da ya sake ganinshi gidan sai dai kuma ayi wacce za'a yi.
Washegari sai ga mama da kaya wai zata tafi Safana Aliyu ya kula da gidan, kan ya fita sai da ya ja wa Afnaan kunne akan ko kofa kar ta taka in ba tana son gamuwa da ɓacin Ranshi da bata taɓa gani bane bata ce komai bar ya fice, wayanta ta fidda ta fara kalle kalle a tiktok aiko Tahir na ganinta online ya kirata suka fara hira, a hankali ta faɗa mishi ita kaɗai ce gida saboda daaɗin hira yace mata gashinan mintuna biyu kawai zai yi ya wuce ganinta kawai yake so yayi.
Aliyu zaune da Jabir a office ɗin shi da zai iya cewa wannan ne zuwanshi na biyu tun samuwar aikin tattaunawa suke akan makarantar Afnaan na nursing da yake nema mata nan katsinar don jabir ya san wani a wurin damuwanshi a san da zamansu waec na fita sai kamalla komai bayan sun gama suka ɗan taɓa hiran duniya kan Aliyu ya miƙe yana ce mishi zai tafi Afnaan ita kaɗai a gida.
"Jira mu wuce kawai ni fa ina ciki da wata dalibarka"
"wacce ɗalibata?"
Sun fito a tare ya furta
"Khadija hankalin yarinyar yayi min gata da natsuwa"
Dan shiru Aliyu yayi a yadda ya karanci khadija tana son shi ba tun yau ba, don daga yanayin tafiya, magana, natsuwa, kulawa da ma himmar da take nunawa a kanshi na daban ne, duk wani abu da zai nuna maka alama ta mace na son namiji ya ganshi wurin khadija shima ya yaba da komai nata tabbas ba don zuciyarshi already ba nashi bane da ya danka mata amma zai yiwa jabir farin cikin samunta
"Aikam sai ka fara yaƙi tun kan wani yayi maka kafan baya"
Daga nan bai sake magana ba har suka shiga motar jabir suka nufi gidansu Aliyu ɗin tun daga nesa ya hangi Tahir da Afnaan tsaye suna zance ba zai ce ga abin da ya ji ba sai dai gabaɗaya jikinshi ya dauki rawa kokarin magana jabir yayi ganin yanayinshi ya sa ya taka birki
"Al..."
Buɗe kofa yake kokarin yi idanunshi kafe a kansu tuni jabir yayi locking kofan ya san zuciyar Aliyu farin sani don akwai randa suka ɗauka Aljannu yake dasu ko farfadiya a garejinsu
"Bude min kofa jabir!!"
"No Aliyu ba zan buɗe ba, baka cikin natsuwarka karka taɓa yanke kowani hukunci ne cikin fushi. Fushi ba solution bane wa koma menene please calm down ka ji? Kayi ta hasbunallahu"
Juya motar kawai jabir yayi Ya sanya hannu ya kunna karatun qur'ani, shi karan kanshi Aliyu kokarin calming kanshi yake yi har suka isa gidansu jabir ɗakinshi ya kaishi ya ɗauko ruwan sanyi ya miƙa mishi....
🖤Gureenjoh🖤