14
by @gureenjoh
KIWON KUBUBUWA
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
PAGE 14
Ruwan kawai ya ɓalle murfin ya hau kwankwaɗa kaman dama chan shine babban abin da yake buƙata, yana gama sha ya cillar da gorar tare da komawa kan kujera ya zube nannauyar ajiyar zuciya na kufce mishi, gabaɗaya ji yake duniyarshi ta tsaya chakk kaman komai baya yi masa daaɗi, ya rasa Meyasa zuciyarsa ta kasa samun natsuwa da sukuni tun Shigowar Tahir rayuwar Naanu.
A hankali ya lumshe idanunshi kwakwalwarshi na hasko mishi irin murmushin da suke yiwa juna a ɗazu tun a wannan bugun numfashinsa ya sauya ji yake kaman Ranshi ne ke a wuyanshi a maƙale sai hadiyar rai yake Adam apple dinshi na wani irin sama da ƙasa
"Aliyu meke faruwa? Gabaɗaya kwanakin nan duk sanda zamu haɗu ko zamu yi waya you weren't ur self at all, ka sani fa barin kashi a ciki baya taɓa maganin yunwa turawa suka ce Two hands are better than one sannan problem shared Its problem solved zurfin ciki bashi da anfani"
Rinannun idanunsa da suka matuƙar turuwa ya ɗan buɗe
"Afnaan wants to be the dead of me J... Afnaan tana shirin ɓallo min ruwa! na gama tunanin cewa ban bar kowani space a zuciyarta na wani ɗa namiji ba bayan ni ashe ban sani ba shuka nake a idon makwarwa, Ka bani shawara J i can't handle this"
Yadda yayi maganan cikin wani irin sanyin yanayi da murya ya sa jikin jabir sake mutuwa gabaɗaya matsowa yayi ya riƙe hannunshi
"Na jima da tunanin Son Afnaan kake, soyayya kake mata da ya zarta na wa da ƙanwa kana yi mata kauna ne irin na mahaɗi ko ɓarin jiki, irin ƙaunar da da matuƙar wuya a samu mijin da ke yi wa matarshi sai dai gabaɗaya na ruɗe ne kwakwalwana na neman jirkicewa Dama ba iyayenku ɗaya ba? Akwai soyayya ne tsakanin Yaya da ƙanwa?"
Lips ɗin shi ya ɗan haɗe yana jin kanshi kaman zai rabe tsabar damuwa, a hankali ya fara tuna ranar da Baba ya ƙirashi akan Afnaan.
"Aliyu na fahimci kana son cutar da rayuwarka, Afnaan rainonka ce bana shakku ko haufin akan ba zata taɓa kin ka ba, tun daga ranar da ka ɗaura idanu a kanta ka tabbatar da cewa kaf duniya babu macen da zaka so bayan mahaifiyarka irin ita, girma take sai yaushe zaka bayyana mata sirrin ruhinka? Sai yaushe zaka fara nuna mata ba alaqar wa da ƙanwa ne kawai tsakanin ku ba?"
Yana tuna amsar da ya ba baba a kunyace
"Baba a idanuna har yanzu Afnaan yarinya ce, kuma ni karan kaina kullum a kame kame nake bani da takamammen sana'a bare aiki, bana so kuma in aureta in kasa bata jin daaɗin da ya kamata ina ji a jikina lokaci na zuwa da zamu yi wannan rayuwar cikin natsuwa da sukuni, sannan bana so in raba mata hankali sam ina so tayi focusing akan karatun ta har mu ga yadda hali zai yi"
Girgiza kai baba yayi shi dai har ga Allah bai so hakan ba, ta son shi fa dama tun kan su kai haka an ɗaura musu aure in yaso su bar tariya daga baya to amma Aliyun ya ƙi yace baya so a tauye ta, sai dai kam duk wani buƙata na duniya na Afnaan shine ya ɗauke mata fiye ma da yadda miji yake providing wa mata.
Yana tuna kalmar Baba na karshe
"Shikenan Aliyu amma ka san yanayin 'ya'yan yau sai a sake saka kula"
Godiya yayi ya miƙe ya fice.
"ALIYU"
J ya kira yana ɗan jijjigashi firgigit yayi a hankali yayi uttering
"Mama da Baba su ɗin iyayen Afnaan ne ba nawa ba"
Da wani irin hanzari Jabir ya miƙe tsaye ba wai bai tsammaci jin hakan ba sai dai a tunaninshi su ɗin iyayen Aliyu ne, amma kuma duba da Afnaan da ta kwaso kamannin Baba a fari da kuma kyaun Fulanin usul sai ya ji zuciyarshi na mishi rauni shima
"Am so sorry...!"
Kai Aliyu ya gyaɗa
"Tsawon rayuwata J na tashi ne da kaunar Afnaan, tun bata san kanta ba nake yi mata son da bana tunanin akwai wani mahaluki da yake yiwa mace irin shi, jin ta nake fiye da jinin jikina wani lokacin idan na kalleta sai in ji tamkar in tsaga jikina in sanya ta ciki in ɓoye, ba zan ɓoye maka ba tun Afnaan bata kai haka ba take hautsina tunani na sau dayawa tana saka ni tunanukan da ban shirya ba hakan ya sa na yi mata katanga da duk wani abu da ya shafi taɓa jiki wato body contact duk don in bata dama tayi karatu cikin natsuwa amma ka ga a karshe abin da ke shirin faruwa, Wannan mutumin yana kokarin lalata ginin da na gina da Tubali mai ƙwarin gaske na kuma bashi tabbaci amma sai ya zaɓi kokarin sabautani ya faɗo min a kai ya binne ni da rayuwata da raina"
Hawayen da yake dannewa ne ya ji shi a gefen idanunshi na hagu yayi hanzarin sa hannu ya ɗauke.
J da yaji kaman ya taya aminin nashi zub da hawaye yace cikin natsuwa
"Aliyu har yanzu lokaci bai ƙure ba idan dai har Afnaan ta san halarci ba zata zaɓi bare ta barka ba Dukda ita bata taɓa yi maka so na soyayya ba kasancewar bata san ba iyayenku ɗaya ba amma na san ba zata ƙi ka ba, duk wanda zai so ta wallahil azeem a bayan naka son ne... Ina ga yanzu ka ajiye ta ka nuna mata manufurka zata dawo hayyacinta ta watsar da wani wai Tahir"
Kai kawai Aliyu ya gyaɗa kan sara mishi yake haka ya miƙe ya kwanta samɓal har bacci ya sure shi, bai farka ba sai kusan Magrib Kuma J bai tashe shi ba sai da ya tashi alwala suka yi suka tafi masallaci tare
Bayan sun dawo da kyar J ya saka Aliyun taɓa abinci kaɗan kan ya bar gidan ya nufo gida.
Tana kwance daga kan taburma tana waya cikin kwanciyar hankali da Tahir da yake yi mata alƙawari in har dai an bashi ita shikenan duk wani matsalar shi ta kau ko allura bai so a kawo ta dashi don ya san in dai wannan yayantan ne zai mata komai to zasu shekara biyu basu yi aure ba, duk da ta ji ciwon maganan ƙasan ranta sai dai soyayya ya rufe mata ido ta ɗan murmusa kaɗan
"Kaman ka san yanzu bashi da abin yi wlh oganshi da yake jirawa shago ya rasu dole shago ya zama na magada su suke da iko da abin su, amma na san shi da kwazo kila ya nemi wani sana'ar kuma"
"wannan shine mai sana'a Goma kenan"
Suka yi dariya a tare don yadda yayi maganan kaman da zolaya.
"Kin san Allah farko yadda yake wani cin magani yake haɗa min rai na zaci shima son ki yake kin san maza da kishi sai kuma kika ce min iyayenku ɗaya amma dai duk babba mai hankali ya kalleshi zai san yana sonki"
"Na ce ka daina wannan maganan please babu wannan zancen tsakanin mu.."
Zare wayan da yayi ne ya sa ta miƙe a firgice.
Haɗa idanu suka yi, kawai tsayuwa yayi yana kallonta da idanunshi da suke a jirkice, wayan ya bi da kallo ya juya ya sake juyo shi ya sake daga kai yana kallonta cikin sanyin murya yace
"Afnaan!"
Iska ya ja a hankali kan yace
"Zauna"
Zama tayi ya janyo kujerar tsuguno ya zauna
"Afnaan ɗago ki kalleni magana nake so mu yi"
Ɗagowa tayi ta zuba mishi idanu sai ta hango kamar rama a jikinshi, ta hangi damuwa tsantsa da wani irin yanayi a cikin idanunshi marar fasaltuwa ta hangi tarin ɓacin ran da yake kokarin dannewa a hankali yace
"Afnaan tun tashin ki akwai abin da kika nema kika rasa a gidan nan?"
Ta girgiza kai
"Da talaucina da kuke magana da shi wanda kika tsinta a rayuwarki rana tsaka kin taɓa ganin abu kika nuna ko da ra'ayi ne ban saya miki ba? Afnaan me kike so ki yiwa kanki? Ina kike so ki jefa rayuwarki? Meyasa baki zaɓi ajiye kanki kusa ba? Kina so mu samu gagarumin matsala da ke?"
Idanunta da suka cika da kwalla ta rusunar tare da sake girgiza kai.
"Wani alƙawari kika yi min akan rayuwarki?"
"Zan yi karatu zan zame muku abin alfahari"
"Har kin manta kenan?"
Ba tare da ta kalleshi ba tace
"Tahir ya min alkawari zai barni nayi karatu sossai"
Da ƙarfi ya runtse idanunshi yana sake matse wayan da ya karɓa daga hannunta ɗin cikin hannunshi
"Amina"
Da sauri ta ɗago
"Menene matsayina a rayuwarki?"
Hawaye ne kawai taji ya zubo mata ba tare da dalili ba ko tsatsareta da yayi da idanu ne da ya sa take jin zuciyarta ya matse wuri guda gabaɗaya ya tattare a wuri ɗaya bata sani ba.
"Kana da matsayi mai girma a rayuwata, Dukda ina da iyaye kai na buɗi idanu na sani matsayin uwa,uba, wa,abokin shawara kuma mai share min hawaye wlh har a ƙasan raina duk yadda zan misaltaka ka wuce nan Yaya"
Idanunshi ya ɗan rusunar a kanta
"idan na roƙi alfarmar ki amince mu cigaba da gina wannan rayuwa ta fahimta a tsakaninmu, na baki lokaci har ki ji zuciyarki ta aminta cewa nawa zuciyar ya jima da zama mallakinki dole ne idan ana so a cire soyayyarki daga ciki sai an fasa ta an tatse duk wani jini dake ciki saboda wannan zuciya ta jima tana watsa jini duk magudanarta da kaunarki zaki yi min wannan alfarma??"
A razane ta miƙe tsaye
"Ban...ban gane ba kaina..kana shirin fasa min kwakwalwa me kake nufi yaya?"
Shima ya miƙe tsaye yana kallon cikin idanunta
"Ina nufin idan nace ki aureni zaki yi min wannan alfarma?"
"An taɓa aure tsakanin ɗan uwa da ƴar uwa da suka fito ciki ɗaya ne? Taya hakan zai kasance? Ta yaya?"
"Ni ba iyayenmu ɗaya dake ba sai dai iyayenki ne suka raine ni, na kuma tashi na girma da tarin ƙauna da soyayyarki kuma duk sun san da hakan, Afnaan na so ace kin kara mallakar hankalin kanki kan wannan maganan ya fito sai dai abin da kika ɗauko yayi min girma, ina sake roƙon ki zaki yi min wannan alfarma Dukda tarin talaucina da rashin aikin yi na?"
Kuka ta fashe dashi cikin tsananin ruɗu tana girgiza kai
"Ba zan iya ba, ba zan iya ba wallahi ka tsaya a matsayin da ku ka riga kuka ɗaura tunani a kai tun asali ka haƙura da zancen soyayya gareni ka zauna matsayin Yayana da bani dashi domin zuciyata Tahir ne kawai mahaɗinta shine nake yiwa son soyayya"
Tana kai nan ta wuce ɗaki da gudu tana kuka sossai.
Jiri ne ya kwashe shi ya tafi kaman zai faɗi amma sai ya yi saurin dafe jikin langa langar kitchen ɗin wani irin zafi yake ji cikin zuciyarshi kaman an caka mishi mashi.
"Aliyu"
Mama da tun zare wayan ta shigo sai dai duk basu kula da ita ba ta ƙirashi.
Ƙoƙari yayi sossai na danne yanayinshi sai dai ko kallonta da kyau baya yi yace
"Mama kin dawo?"
"Eh Aliyu"
Hawaye ne taji yana silalo mata da sauri ya zagaye ta ya wuce kawai ta bi bayanshi da kallo.
Ɗakin Afnaan ta kurawa idanu na tsawon mintuna kan ta wuce nata tana share hawaye ina ma da Malam yana nan kila ya iya kashe wannan wuta. Kila ya iya tankwara Afnaan kila ya iya ɗaukar ko wani mataki don kawai ganin rayuwar ɗayan su bai taɓe ba? Dukkansu basu taɓa nuna wariya tsakaninsu ba dukkansu basu taɓa fifita ɗaya kan daya ba idan har da amana wallahi ko wuta Aliyu yace Afnaan ta shiga ita mai shiga ce.
Washegari da safe ko neman ta babu wanda yayi, Aliyu tun da ya fita Sallar Asuba bai dawo gidan ba, mama na ɗaki cikin damuwa Afnaan ta sulale ta bar gidan gabaɗaya fuskanta a suntume saboda kuka a haka ta isa gidan su jawahir ta samu tana bacci ta shiga tashinta
"Jawahir Don Allah ki tashi ki bani shawara kaina zai fashe"
Da sauri jawahir ta miƙe tana riƙe ta
"Menene? Dukanki Yaya Haidar ɗin ya yi?"
Girgiza kai tayi
"Da ma duka ne da sauƙi wallahi Ya haidar ashe ba iyayenmu ɗaya ba? Riƙonshi su mama suka yi?"
Tsananin mamaki da rudu jawahir ma ta shiga sai dai sanin ba iya nan zancen ya tsaya ba ta matso tana sake riƙe ta
"Uhmm me aka yi kuma?"
"JAWAHIR BESTIE WAI SO NA YAKE?"
Ta rushe da wani kukan
"Wai Duk su mama sun sani..."
"Ke kina son shi ne Afnaan?"
Ta tambaya idanunta gabaɗaya waje
"Ban taɓa son shi ba, soyayyar dake tsakaninmu na yaya da ƙanwa ne ban taɓa mishi soyayyar aure ba kuma bana jin zan iya jawahir yanzu Mama haushina take ji"
"Meyasa zata ji haushinki? An tambayeki kin ce kina son shi ne?"
Girgiza kai tayi tana kuka
"Yaya na da matukar muhimmanci a rayuwata yana da wani gurbi da babu mai iya cike shi, sai dai ni ba soyayyar aure nake mishi ba wallahi ba zan iya aurenshi ba bana son shi Tahir nake so kar su ce zasu yi min dole"
"Ba Zasu yi ba, idan har yana sonki ai zai so abinda kike so Afnaan idan kuma yana son farin cikinki zai barki da Tahir"
Kwantar mata da hankali tayi tayi ta kuma tabbatar mata da ta tsaya akan bata son shi ta san ba zasu yi mata dole ba, kuma duk fushin su na lokaci kankani ne zasu zo su sauƙa su mance komai idan ma suka ga tana taimakonsu karkashin inuwar Tahir.
Sossai taji daaɗin shawarwarin barin ma da ta ƙira Tahir da wayan jawahir take bashi labarin abin da ya faru, ya tabbatar mata gobe da yamma zai tura kawunshi Safana wurin kawu Habu kuma shima zai zo su yi magana don babu mai mata dole..
Da wannan ta lallaɓo ta dawo gida tana cikin sanɗa don shigewa ɗaki ta tsinci maganan mama
"Daga ina kike Afnan?"
A razane ta matsa baya
"Ma..maa gidan s...su jawahir"
"Uban wa kika tambaya kika fita?"
Tayi shiru
"Afnan nima kina so in mutu ko?"
Tayi shiru tuna kalamanta na jiya ga Aliyu yasa mama kam rushewa da kuka ta nufeta ta rufeta da Duka
"Wani aljani ne jikinki? Wani shaidanin yake juya miki kwakwalwa kin san girman hakki? AFNAAN KASHENI ZAKI YI NIMA KAWAI KI HUTA...."
na so ya fi haka don ina ga a Page 15 free pages zasu kare sai dai headache ya sakani gaba sai kun ji ni gobe in shaa Allah. A zo a yiwa Afnaan ruqiya kar aljanun nan su kaita su baro ta tamm
🖤Gureenjoh🖤