BABI NA BIYAR
by @ummasghar
SAFEENATU*
NA
UMM ASGHAR
Arewa books @UmmAsghar
BABI NA BIYAR
Khadija ce ta kawo mana breakfast kafin ta wuce office. Riƙeta nayi ta kular mini da Imaduddeen ni kuma na shiga wanka. A cikin toilet ɗin na shirya cikin kayan data kawo mini. Lokacin dana fito har ta haɗawa Immy abinci ta lallaɓa shi ya ɗan ci babu laifi. Nima zama nayi naci abincin muna ƴar hira har na gama kafin tayi mana sallama akan sai ta taso daga office zata dawo. Wayata na ɗauka na ƙara gwada kiran Anty, luckily for me a wannan karon na sameta. Da sallama ta amsa kiran. Gaisheta nayi ta amsa cike da kulawa. Wai kawai daga jin muryarta sai naji idanuna sun cika da hawaye kuka na neman ƙwace mini.
Cikin rawar murya nace "Anty ina ta nemanki a waya bana samu daga ke har Baba jiya layinku a kashe."
"Safeenatu kuka kike yi? Wani abu ya faru a gidan ne?" Tace a rikice.
Kamar tambayar da nake jira kenan kawai sai na fara kuka, kuka nake yi kamar wacce aka aikowa da saƙon mutuwa. Gaba ɗaya na gama rikita Anty, tun tana lallashina akan nayi shiru na faɗa mata abinda ke faruwa har ta haƙura ta ƙyaleni nayi kukana ya isheni kafin cikin dasashiyar muryar data sha kuka ta ƙoshi nace mata "tun jiya na kasa samunki a waya, Immy ne baya da lafiya har anyi admitting ɗin mu a asibiti."
"Subhanallahi, me ya same shi? Jikin da sauƙi ko kuwa?" Tayi mini tambayar a rikice.
"Ya samu sauƙi Alhamdulillah ba kamar yadda muka zo ba jiya."
"Kin tabbata Safeenatu ko dai akwai abinda kike ɓoye mini ne?"
"Allah kuwa Anty da sauƙi."
"To kukan da kike yi na menene idan har ba jikin nashi bane?"
"Kewarki nake yi Anty, nauyin ne naji yayi mini yawa, na tsorata da yanayin da yake ciki a jiyan ina tsoro kada wani abu ya faru dashi gashi ba kya nan."
Ajiyar zuciya ta sauke tace "ko ina nan ban isa na tare abinda Allah ya hukunta zai faru ba Safeenah, addu'a zaki yi tayi mishi Allah ya bashi lafia, ki cigaba da kula da ƙannen ki kin ji. Allah yayi muku albarka ya ƙara haɗa mini kawunanku."
"Ameen Anty," na amsa ina jin wata irin nutsuwa tana saukar mini, nutsuwar dana rasa tunda Immy ya fara yin rashin lafiya.
"Yanzu ina Imaduddeen ɗin ko bacci yake yi?"
Girgiza kaina nayi nace "a'a idanun shi biyu."
"Ok, to bashi don idan ban ji muryar shi ba hankalina ba kwanciya zai yi ba."
Tashi nayi na kara mishi wayar a kunne nace "Anty zata yi maka magana Immy."
Sun ɗan jima tana yi mishi tambayoyi wanda duk akan yadda yake jin jikin nashi ne kafin tace ya bani wayar. Miƙo mini yayi na kara a kunnena sai ji nayi tace "ai jikin nashi ma da sauƙi shine zaki nemi ki ɗaga mini hankali."
Ƴar dariya nayi.
"Muma In Sha Allah ba wani daɗewa zamu yi ba zamu dawo tunda mun gama duk wasu sayyayar kayayyakin ku har an auno su sun taho jiya, yanzu Babanku ne zai gama wasu harkokin shi sannan mu taho."
A ɗan kunyace saboda maganar kayan aurenmu da tayi nace "Allah ya dawo daku lafiya Anty, muna missing ɗin ki, gidan baya yin daɗi idan babu ke a ciki."
"Ameen Safeenatu, a cigaba da kula dai kin ji."
"To," nace kafin muka yi sallama ina sauke ajiyar zuciya. Kusa da Imaduddeen na koma na zauna ina kallon yadda yaron ya rame lokaci guda, rashin lafiyar nan bata yi mishi kamun wasa ba.
Wurin ƙarfe goma na safe likitocin suka shigo yin ward round. Tashi nayi na matsa daga kusa dashi don suna da ɗan yawa. Tambayoyi suke yi mini akan yanayin jikin nashi ina basu amsa. Ɗaya daga ciki ne yace "are you his mother?"
"Nope, i'm his sister," nace haɗe da ɗago kaina. Caraf sai muka haɗa ido. Kallon ido cikin ido muka yiwa juna kafin ya janye nashi idanun ya cigaba da rubutun da yake yi a cikin file ɗin Immy. "Ina Maman nashi take?" Ya sake cewa
"Bata nan tayi tafiya," nace ina jin gabana yana wata irin faɗuwa. Ban taɓa tunanin zan sake ganin shi ba sai gashi na haɗu dashi a inda ban taɓa zato ba bare tsammani.
'Ya Subhanallah,' na ambata a zuciyata. Mutumin ranar nan ne na wurin biki. Gaba ɗaya sai naji jikina ya ɗauki rawa har muryata ma.
Suka gama tambayoyinsu suka yi rubuce-rubucen su suka fita. Komawa nayi na zauna ina jin jikina yayi wani irin sanyi. Me ke shirin faruwa dani ni Safeenatu? Wani irin yanayi nake samun kaina ciki a duk lokacin da idanuna suka yi tozali da nashi. Da ƙyar na iya yakice tunanin mutumin nan a waccan ranar sai gashi na sake haɗuwa dashi ba tare dana shiryawa hakan ba.
Haka nan na koma wata irin sukuku dani domin lokaci bayan lokaci nake tunawa dashi da na kuma tunano shi sai naji gabana yana wata irin faɗuwa, abinda yasa naji gaba ɗaya zaman asibitin ya ishe ni.
Tunda nake a rayuwata ban taba ganin wani mutum walau mace ko namiji naji ya burge ni ba irin wannan likitan, haka nan dana rufe ido na kyakkyawar fuskarshi nake gani a cikin idanuna. Ni dai nasan ina son Hamza har zuciyata sai dai ban san me ya kawo mini jin baƙon yanayi akan wannan mutumin ba. Ban sani ba ko cewar da ake yi na idan wani abun alkhairi ya tunkaro ka sai kaga shaiɗan na nema yayi maka wasa da zuciya ke neman faruwa a kaina saboda yadda naji ya shige zuciyata yayi kwance kamar daman can wajen zaman shi ne.
Kun san a rayuwa kowanne ɗan adam yana da wasu mafarkai ko wani ra'ayi akan irin mutumin da yake so ya kasance abokin rayuwar shi sai dai ba kowanne lokaci bane wannan mafarkin ko ra'ayin yake zama tabbatacce ba. Ga wasu zaku ga akwai wasu qualities da suke nema ga abokin rayuwarsu, wasu suna son dogo fari kyakkyawa, wasu fararen maza basa burge su sai dai baƙi ko Chocolate color kamar yadda ake kiran baƙaƙe masu hasken fata, wasu kuma kyakkyawan mutum ma san baya burge su sukan ce kyawawan maza hatsari ne domin kuwa idanun kowacce mace akan su yake. To irin haka ce ta faru dani domin kuwa ina ganin wannan mutumin naji yanayin shi gaba ɗaya irin na mijin da nasha ɓata lokaci ina suffantawa kaina ne, shine kuma abinda ya ƙara saka zuciyata cikin ruɗani domin kuwa tun bayan haɗuwata da Hamza ban ƙara jin ina da wani preference akan irin mijin da nake so na aura ba.
"Ya Allah" na furta a cikin zuciyata. Me yake shirin faruwa dani ne? Wacce irin ƙaddara ce take tunkaro rayuwata a daidai lokacin da nake shirin fara sabuwar rayuwa da zaɓin zuciyata. Tunda nake da Hamza ban taɓa jin irin wannan strong feelings ɗin mai zafi ba akan shi, nasan ina son shi soyayya marar algus domin kuwa ni na zaɓawa kaina shi ba wani ya zaɓa mini ba, ba dole aka yi mini akan shi ba hasali ma idan da don ta Anty ne bashi ne mijin da taso na aura ba, wani abun Allah kuma har a wannan lokacin ban ji wani abu ya ragu daga yadda nake jin shi a cikin zuciyata ba. Shine kuma abinda yafi komai ɗaure mini kai, to dama zuciya is capable of loving more than one person at the same time ne ko ya abun yake.
Ɗaga kai nayi na kalli Immy sai naga ya samu bacci abinda yasa nayi tunanin shiga banďaki na yi alwala nayi tilawar AlQur'ani da zaman da nake yi ina tunanin da ba zai ƙareni da komai ba gara nayi abinda zai fisheni fid dunya wal akhira.
Karfe hudu nayi ƴan dubiya suka fara zuwa. Duka yayyenmu suna nan mun haɗu gabaki ɗaya ana hira sai dai yanayin dana tsinci kaina a ciki yasa na kasa sakewa dasu kamar yadda muka saba. Yaya Aisha ce ta kalleni tace "ke kuma lafiyarki tun zuwanmu ina lura dake baki da kuzari ko ƙanƙani ko hirar da ake yi ba kya shiga, ba dai wani abu ke damunki ba ko?"
Da sauri na girgiza ka ina cewa "a'a bani da wata damuwa, sai dai ko gajiya da rashin samun isashen bacci ya haifar mini." Don fa sai nake ganin kamar idan na buɗe baki nayi magana zasu fahimci halin da nake ciki.
"To Allah ya kyauta," tace yayin da suka cigaba da hirarsu ni dai ina sauraren su.
Gaba daya yau a takure nake jina, zaman asibitin duk ya gundure ni. Wallahi da da yadda zan yi gida zan koma don bana farin ciki da al'amarin dake neman tunkaroni sam.
Mun daɗe tare dasu kafin suka yi mana sallama suka tafi sai Khadija kawai aka bari don tace ita sai ƙarfe shida tayi cif kafin ta tashi ta bar nan. Hira muka cigaba dayi tana bani labarin an yiwa Sadiq ɗin ta transfer zuwa Abuja. Sosai na tayata murna don dama ba son zaman shi a kudu take yi ba. Kallona tayi ta tambaye ni "wai ni Feenah meke damunki? Kada kuma kice mini babu komai ko kuma gajiya ce kamar yadda kika fadawa Yaya Aisha ɗazu don kar ki manta na sanki fiye da yadda kika san kanki na kuma san cewa kina da damuwa sai dai idan ba zaki faɗa mini ba."
Shiru nayi ina tunanin amsar da zan bata don ban shirya faɗa mata ainahin abinda yake damuna ba, saboda ban san wacce irin ɗauka zata yi mini ba, besides wannan wani sirrina ne da bai dace ace kowa yaji ba har Anty kuwa. To me ma zance mata saboda Allah, ai da kunya na buɗe baki na faɗa mata wannan maganar. Kai sam bama zai yiwu ba.
"Kinga fa Safeenah ban ce lallai sai kin faɗa mini damuwarki ba, babu dalilin wannan dogon tunani," ta fada a hassale alamun ranta ya ɓaci da shiru na, ko dama can kuma Khadija ba mai haƙuri bace abu ƙalilan ke ɓata mata rai.
"Kiyi haƙuri ba wai bana son faɗa miki damuwata bane sai don ban san ta yadda zan fara faɗa miki ba ban kuma san yadda zaki ɗauki al'amarin ba, na san ba lallai ba ne ki fahimce ni."
"Haba Feenah, idan baki faɗa mini damuwarki ba wa gareki da zaki faɗawa, kada ki manta fa bamu taɓa ɓoyewa junanmu sirrin mu kuma Alhamdulillah muna warware matsalarmu ba tare da mun bari wani yaji ba, to don me zaki ɓoye mini damuwarki a yanzu alhali ko shawara na baki zaki ji daɗi ko bata yi miki maganin matsalarki ba zaki ji sauƙi a cikin zuciyarki."
Ajiyar zuciya na sauke, na buɗe baki kenan da niyyar yin magana ya turo ƙofa ya shigo ɗakin tare da yin siririyar sallama.
Tuni ɗan sauran kuzarin dake gareni ya tafi. Duk wani taku nashi yana tafiya ne tare da bugun zuciyata, har ya qaraso gaban gadon da Imaduddeen yake ya tsaya. "To me ya shigo yi a yanzu kuma?" Nake tambayar zuciyata sai dai bani da mai bani amsar wannan tambayar.
Sannu yayi mishi sannan ya cigaba da yi mishi tambayoyi akan yanayin jikin shi yana bashi amsa.
Daurewa nayi na tattaro dukkan nutsuwata na kauda hankalina daga garesu. Wayata na ɗauka ina ƴan danne-dannen da ban san me nake yi ba, bai wani daɗe ba ya fita daga ɗakin ba tare da yace mana komai ba.
Wata hirar na ɗauko da son bagarar da waccan maganar sai dai ina lura da Khadija zancen ɗazun take son a cigaba sai dai naƙi yarda ko kallonta nayi.
Ɗaukar wayata nayi na buɗe chats ɗina na WhatsApp don yau ko sau ɗaya ban buɗe ba sai dai idanuwan Khadija dake yawo a jikina yasa na ajiye wayar babu shiri.
Kallonta nayi nace "malama ya da kallon?" Tare da ɗage mata gira.
Tsaki tayi tace "bana son wasa fa Feenah, kin sani sarai fa magana ce muke yi kafin shigowar likita shine kike nema ki raina mini wayo."
Ajiyar zuciya na sauke kafin nace "bafa wani abu bane mai muhimmanci kawai dai yanzu da ranar aurenmu take ƙara matsowa ne nake jin kamar i'm not ready for it, da ace Baba zai yarda dana nemi an ɗaga auren to nasan abu ne ba mai yiwuwa ba, ban ma isa na fara tunkarar shi da wannan maganar ba." Na samu kaina da faɗa mata hakan don banga ta yadda zan fara faɗa mata waccan maganar ba, a dai bar kaza cikin gashinta kawai. Some things are better left unsaid........
UmmAsghar