004
by @jeeddah3256
TAREEQ IMAM
Na
Jeeddah Aliyu
Arewabook@jeeddah3256
004.
Ummi tai sauri runtse idanuwanta tana jin wani irin ɗaci a maƙogwaronta, wannan ɗaci haka take jinsa a duk lokaci da Tareeq ya aikata wani mummunan laifi. Kafin ta lallaɓo kalmar da za ta faɗa ta ji saukar murya Aayya a dodon kunnenta tana cewa da Gifty.
"Ke Tahreem yaushe kika fara koyon saƙa da mugun zare ina ruwan Tareeq dake da zai miki wannan ta'adi ina sane da ko kallon kirki baya hada shi da k....
Da sauri Fadila ta katse Aayya cikin fusata.
"Kar ma ki fara Aayya saboda kin fi kowa sani tun ba yau ba Tareeq yake zaluntar Gifty, saboda naga take-takenki ki ce tai masa ƙazafi abinda kowa ya sani ne tun da sanda Gifty ta zo duniya Tareeq yake cin zalinta, har kawo yau bai fasa cutar ta ba."
"Ya Fadila kenan kamar kin manta da wacece Aayya, ga fa gaskiya baro-baro tana gani za tai fatali da ita ta shigo da son zuciya ita haka ALLAH ya yi ta da bala'in son zuciya."
"Ya isa Baby!
Ummi ta katse Baby cikin tsawa, banaso nasake jin ɗaya daga cikinku ta sake magana a motar nan."
"Ai da kin barsu, su ci gaba da zagina iya son ransu haba ina dalili kowanne ɗan banza ya kwaso sharar sa sai akan Tareeq, baki yana neman ya yi masa yawa to ta ALLAH dai ba ta mutum ba masu kambun baka."
Tuƙuƙin da Ummi take ji a cikin zuciyarta ya hanata tankawa Aayya har suka iso gida Aayya tana ci gaba da masifa.
Kai tsaye Fadila ɗakinta ta wuce da Gifty, Yayin da Ummi ta wuce nata ɗaki tana zuwa ta ciro wayarta da ta bari tana charging kan bedside drawer, yadda take jin haushi da takaicin Tareeq kamar in ta rutsa shi baza ta bar shi da numfashi ba.
Dialling number Alhaji Imam wali tayi gani take wannan issue ba zai yu ta barshi zuwa wayewar gari ba, tabbas sai ta ɗauki mummunan mataki akan Tareeq ba zata zuba mai ido ya zo ya illata mata ƴa ba. Gara tun wuri shi da ya ɗaure masa gindi yake tsula ɗibar albarka iri-iri yasan irin ta'asar da yai wa ƴar marainiyar ALLAH.
Ringing ɗaya zuwa biyu Alhaji Imam Wali yai picking cikin sanyi murya yai sallama, a daƙile Ummi ta amsa ya zarce da tambayar lafiyarta da ta yara ba ta amsa masa ba saboda ba shi ne maƙasudin kira da tai mai ba. Kai tsaye ta zarce da faɗar.
"Alhaji na kira ne domin ka san hali da ake ciki, ka yiwa tufka hanci idan ba haka ba wallahi-tallahi duk mataki da na ɗauka akan ɗanka kada ka ga laifina....
"Ɗan dakata mana Amina kin fi kowa sani na tsani rashin natsuwa a al'amurrana, duk tsiyarki da masifarki kya bari mu gaisa cikin mutunci da lumana har fa tambayarki lafiyar gidana nai amma tsabar masifa ta ciyoki ba ki amsa min ba."
"Idan har ka damu da sani lafiyar gidanka kira za ka yi ba wai sai na kira ka da tawa matsala ba ka zarce da faɗar taka."
"Shike nan Amina nima ina so ki gaggauta faɗar dalilin kira na domin bani da lokaci ɓatawa akanki, ina da ayyuka masu tarin muhimmanci a gabana."
"Ba laifi dama nasan har gaba da abada ba za ka yi lokacina ba....
"Amina Please just go straight to the point!
Alhaji Usman Wali ya katse mata numfashi cikin hasala.
Sosai ran Ummi ya ƙara ɓaci a dalili yadda ya daka mata tsawa kamar wata ƴarsa ko baiwa furucin da yake amfani dashi ko kusa bai yi kama da na wadda ke magana da matarsa ba, dakyar ta saita natsuwarta cikin muryar da ke bayyanar da tsanani fushi da ɓacin rai ta ce
"Inaso ka gargaɗi shalelen ɗanka kada ya kuskura hannunsa ya sake sauka akan Tahreem.
"Idan kuma naƙi fa?"
Alhaji Imam Wali yai sauri tarar numfashinta.
"To wallahi-tallahi duk abin da nai masa shi ya jawo.
"Idan kin fasa kin rena ALLAH Amina dan ALLAH dan ƙaunarki da Annabi kafin na dawo ki yi gunduwa-gunduwa da naman jikin Tareeq, hakan ne kawai zai ƙara gamsar da ni zallar ƙiyayyar da kike min. Tun-tuni na gane ki Amina sanadin ƙiyayyar da ki ke min ce ta shafi Tareeq, saboda kin fahimci ta hakan ce kawai za ki ƙara ƙuntata min."
"Wannan kuma matsalarka ce Imam Wali amma ina mai tabbatar ma da cewa ko ban yi gunduwa-gunduwa da Tareeq ba, tabbas za ka dawo ka tarar da mummunan rauni a jikinsa tamkar dai yadda yai wa Tahreem, saboda ita ma ƴa ce kamar yadda yake ɗa ba kuma gata ya fi ta dashi ba."
Tana gama magana ta datse kiran, tare da saka wayarta Flight mode gudu kada ma ya sake kiranta.
Sororo Alhaji Imam Wali ya yi tare da ƙurawa wayar hannunsa ido, zuciyarsa na masa wani irin bugawa sau da dama sai zuciya ta ciyo shi ya ji tamkar ya datse igiyoyin aurensa da ke kan Ummi, sai kuma wani ɓangare na zuciyarsa ya hane sa. Yana matuƙar ƙaunar Amina ita ce jini da bargo jikinsa yana mata azababbiyar soyayya da fatar baki ba za ta iya misaltawa ba. Sanadin gundarin so da yake mata yasa ya shanye shekaru masu yawan gaske yana haƙuri da zazzafar ƙiyayyar da take masa.
An ce zuciyar mace rauni ne da ita bata zurfafa ƙiyayya, amma ban da ta Ummi shekaru 26 da yin aurensu kawo yanzu ba abin da ya sauya daga matsananciyar ƙiyayya da take mai, a takaice ma sai daɗa ƙaruwa take har abin yana ƙoƙarin shafar gudan jininsa.
Zuciyarsa ko kusa ta kasa jurewa bata yi la'akari da yawan shekarun shi ba, ko kuma babban matsayinsa sai da ta raunata masa zuciya ta haddasa masa sakin wasu irin zafafa hawaye suka tsiyayo daga kwarmin idonshi, zuwa ga kumatunsa yasa ɗan yatsa ya laƙato su.
Wani irin tausayin kanshi yake ji har ya fara tuhumar kanshi da kanshi ta hanyar furta.
"Miyasa na kasa haƙura da son da nake miki Amina, har ta kaini da cilasta miki aurena?"
Wannan tambayar duk da ya kwana da sani amsarta amma a kusan kodayaushe cikin yi wa kansa ita yake. Sai yanzu ya ƙara tabbatar da so abin banza ne bai ga amfani da yai mai ba sai ma jefa shi da ya yi cikin ƙunci da takaici.
Da wani irin fushi Ummi ta jefar da wayarta akan gado, ta miƙe ta shiga bathroom ruwa ke sauka jikinta daga shower da ta kunna sanyi su na ratsa fatar jikinta hakan ne ya haddasa wa zuciyarta yin sanyi, har ta shiga backward ɗin abin da ya faru tsakaninta da mai gidanta, ta rasa dalili da yasa a kodayaushe cikin samun misunderstanding suke ta kuma rasa dalili da yasa a kodayaushe take zurfafa tsana da take masa wacce ita kanta a yanzu ta fara bata tsoro da firgici musamman da ta gano ƙiyayya da take wa Imam Wali bata da bambanci da wacce take wa ɗan ta jini jikinta Tareeq.
Sai dai ta laƙanta tsanar da tai wa Tareeq a bisa yawan ƙiriniyarsa.
Fadila ta haɗa ruwan wanka, ta yiwa Gifty wanka Baby taje ɗakin Gifty ta ɗauko mata sleeping dress ta kawo mata, koda suka fito daga bathroom hatta da abinci Baby ta ɗebo mata sai da Fadila da Baby suka tabbatar duk wani abu na al'ada da suke wa Gifty kafin kwanciya bacci sai da suka yi mata kafin suka barta ta kwanta.
Sai around 1:30am su Aliyu suka baro joint kowanne a ƙofar gidansu Lil-prince ya sauke shi kafin ya juya akalar motar ya nufi nasu gida, can cikin bacci ɗan Bala maigadi tare da securities ɗin ke on duty a main gate suka ji ana bugun gate da ƙarfin bala'i tamkar za a ɓalla shi sun san aikin Tareeq ne, da mugun gudu ɗan Bala yazo ya buɗe mai.
Wani mugun kallo ya watsawa masa sa'ili da ya buɗe masa gate suka yi 2 eyes "Barka da dawowa maigida farin zaki magajin Daddy."
Ɗan Bala ya faɗa yana sosai ƙeya.
"Banaso kutumar b*... uba ɗan Bala tun yaushe nake tsaye anan ina bugun gate kayi banza da ni sai kace gidan mallakin tsohonka ne."
"Allah ya huci zuciyar magajin Daddy wallahi bacci ne ya ɗauke ni..
"I'll you shut up my friend, ko nan gidan ubanka ne da za ka kwanta bacci?"
Tareeq ya katse shi a tsawace duk da ran Ɗan Bala ya ɓaci da yadda Tareeq ya zage shi tare da buga masa tsawa amma haka ya danne cikin karya harshe ya shiga bashi haƙuri.
Tsaki kawai ya yi ya ture ɗan Bala a gefe ya shiga gida kusan securities shidda ya gani suna kai da kawo lungu da saƙon gidan, domin ƙara tabbatar da tsaro duk gaisuwa da suke masa bai amsa ba ya nufi flat ɗin shi.
Tun daga parlour ya soma cire kayan jikinsa yana watsi dasu duk inda yaga dama. Daga shi sai boxer ya ƙarasa bedroom kafin ya kwanta saida ya yi wanka ya saka wayarshi charging wacce tun kafin ya fita ya saka ta a Flight mode.
Tun Asuba da Ummi ta tashi Sallah kawai tayi ta nufi ɗakin Fadila taga hali da Gifty take ciki saboda jiya da ita ta kwana a ranta.
Koda ta shiga ɗakin ta tarar da Fadila ta tashi tana zaune gun da tayi sallah tana azkar, Gifty kuma tana kan gado tana bacci, gefen kanta Ummi ta zauna tana shafar jar sumar kanta cike da kulawa.
"Ina kwana Ummi?"
Fadila ta gaida Ummi tare da baro gun da take zaune ta dawo gefen gadon ta zauna.
"Lafiya ƙalau Fadila ya jikin Tahreem?" wallahi ko kaɗan ban runtse ba da yarinya nan na kwana araina."
"Al-hamdulillah Ummi ta ji sauƙi sosai naga kamar magani da tasha akwai na bacci shiyasa na barta ta ɗan ƙara hutawa zuwa 7 o'clock in tashe ta tai sallah."
"Shike nan Fadila ki barta amma ki tabbata ƙarfe 7 ɗin ki tashe ta."
"To Ummi."
Daga haka Ummi ta baro ɗakin.
Sani ya yi ya aikata babban laifi a wurin Ummi shiyasa yau ya yi shiri zuwa School da wuri, yana gudun kada Ummi ta rutsa shi.
Misali ƙarfe takwas Tareeq Imam Wali ya iso cikin makaranta ya hango ana assembly, cikin tafiyar shi ta kasaita da izza hannuwanshi zube ciki aljihun wandon uniform ɗinsa, ya wuce cikin tawagar 'yan ajinsu{SS2}, tsabar neman magana yasa hannu ya jawo Shariff Idris Kankia ya fito dashi daga cikin jerin ɗalibai ya kuma maye gurbinsa.
Kasancewar Sadik yaro ne da baya so fitina uffan bai ce dashi ba ya koma ƙarshe layi ya tsaya, tun tsayuwa Tareeq wuri yake neman faɗa ya tokari wannan ya ja kunnen wannan idan ka kalli shi ya ɗaga ma gira ko ya kashe idonshi ɗaya duk bayani da principal ke yi ba ko ɗaya da ya ji.
Can idanuwanshi suka sauka akan fuskar Nana wacce ke nesa dashi kaɗan, tun shigowarshi ta ganshi tasha jinin jikinta lokaci-lokaci take satar kallonshi. Da zarar ta ga zai kallo gefenta sai tai sauri kauda kai, a karo na ba adadi ta ɗago da zimmar satar kallonshi karaf suka haɗa ido sai lokaci ya lura da tana tsaye a wuri.
Mugun kallon da ya watsa mata sai da yai sanadiyyar da gabanta ya yi mummunan faɗuwa, tsoronsa ya bayyana ƙarara a cikin ƙwa
yar idonta.
#Nadama
#Soyayya
#Batulci
#TareeqImam.
#***.