16
FPG16
..... A ranar da ta cika kwana bakwai da haihuwa, matuƙar kayi nasarar kawo ta gare mu to a ranar zamu warware maka ƙullin da ka daɗe kana zullumi da neman sa ni a kai tsawon lokaci, idan kuma ka kuskure! to ka sa ni, dole a cikin biyu za'a yi ɗaya.. " Muryar na yankewa ya ji shi Tim! Zuwa ƙasa tamkar an yasar da buhu, daga haka kuma ya ji kamar an buga masa guduma a tsakiyar kansa wanda yayi sanadiyyar ɗaukewar jin sa dif! Komai ya daina motsi a ɗakin,ga tsananin duhu wanda ya mamaye Ɗakin wanda ko tafin hannun sa baya iya gani, cikin seconds kuma yaji wata irin iska mai ƙarfin gaske tamkar zata tada gidan baki ɗaya,ji yayi windown ta bugo da ƙarfi kamar zata cire tsabar yanda iskar ke kaɗawa da ƙarfin gaske..A hankali ya ji komai na lafawa har ya koma tamkar ba'a yi ba, haske ne ya gauraye ɗakin mai launin ja tamkar an kunna wutar itace, ga wani irin hayaƙi da ya gauraye ɗakin cikin wani irin ƙarni tamkar na jini, akan tsakiyar wani tamfatsetsen gado ya hango ni da aka lailaye shi da farin zanin gado wanda yayi color ɗaya da curtains ɗin ɗakin, ni kuma ganin yayi an sauyamin rigar bacci na zuwa launin Ja mai tsananin sheƙi da walwali a idon mai kallo,bacci nike hankali kwance kamar ba ni ba, daga haka kuma ɗakin ya sake mayewa da duhu a karo na biyu yayin da window ta buɗe hasken farin wata ya shigo tar yana haska ni tamkar ina waje, miƙewa Naseer yayi cikin jin wata irin matsananciyar sha'awa ta ya taho zuwa gare ni.. Bacci ni ke mai cike da nutsuwa wanda na jima banyi irin sa ba, a hankali na ji hannun Naseer ya fara taɓa ni cikin wani irin salo ya zame min rigar baccin da ke sanye a jiki na, daga nan yayi min rumfa tare da ɗora lips ɗinsa a nawa, cikin jin wani irin raɗaɗi na buɗe idona ina kallon sa zuruu! Saboda na kasa turesa, zafi nike ji sosai wanda ba kawai daga laɓɓansa ba, hatta hannayensa da jikin sa da ke goguwa da nawa jin nike yana manna mini wani abu tamkar wuta mai tsananin zafi a jikina, ganin na buɗe idona yasa shi sanya na shi idanun a cikin nawa masu ɗauke da zallar saƙon da na kasa fahimta... Ranƙwafowa yayi zuwa saitin kunne na cike da rauni a muryar sa ya raɗa min. "Ki zama jaruma kinji Safnah". A hankali na lumshe idanuna tare da sakin wa su hawaye ma su zafi da ƙuna a zuciya domin na kasa fahimtar irin wannan al'amari, shin wace rayuwa ce ni ke cikinta ni Safnah? Shin wai ni a duniyar mu ta mutane nike zaune a yanzu ko kuma na sauya zuwa wata duniyar ne? Tabbas na sauya duniya domin duk abinda yake faruwa da ni ban taɓa ji ko ganin wata amarya ta rayu a yanda nike yanzu ba...Wani abu na ji tamkar yankan reza mai tsananin kaifi wanda ya zarce har zuwa ƙwaƙwalwata a lokacin da Naseer ya yi huɗa zuwa cikin jikina, tunani na ne ya tsaya cak, jiki na ya ɗauki kakkarwa tamkar an jona ni a shocking, jariri ni ke kallo cikin ƙoƙon idanuna wanda daga nan kuma numfashi na ya yanke ban sake sanin a ina ni ke ba..Naseer kuma, yana gama sauke buƙatar sa yaji sa tamkar an zare masa laka ya faɗa kai na yaraf! Daga haka kuma ya ji an fara rolling ɗin shi a hankali har sai da ya dire ƙasa baki ɗaya ya kasance ni ka ɗai na rage a gadon, still idanuwanshi a buɗe ya na kallo yaga ɗakin ya ɗinke ɗif! da duhu, a hankali ainahin hasken ɗakin nawa na asali ya bayyana duk bolb ɗin suka kawo haske fari, windown ta rufe gadon ya dawo normal nima rigar jiki na ta dawo yanda take, cikin ƙanƙanin lokaci komai ya koma tamkar ba'a yi ba,da sauri Naseer ya miƙe jin hankalin sa ya dawo jikin sa yayo kaina yana mai ƙure ni da kallo kamar mai neman wani abu, ganin cewa tabbas bacci ni ke yasa shi sauke ajiyar zuciya ya faɗa gefena ya lumshe ido ba jimawa bacci ya ɗauke sa.....Gefen Xuhra kuwa, zaune ta ke tsakiyar gadonta ga robar ice-cream a gabanta wadda ta buɗe fridge ta gan su a ciki ta ɗaukko. Kashe data tayi da ke kan network ɗin ta shiga call-log ta kira numbern Yah Umar, kallon agogo yayi daga can ɓangaren sa wanda ya nuna masa goma saura na dare, cike da fargaba ya yi answering da cewa "Fatan lafiya Xuhra?" zumburo baki tayi gaba kamar yana gabanta ta ce "Haba Yah Umar kamar ya fata lafiya kuma..." "Eh to, naga cewa mun gaisa ɗazu around 6pm" "To ai mantawa nayi in faɗa maka cewa gobe ina da zuwa Sokoto wurin PPA ɗina.." "Eh to, ya akayi?" "Yah Umar sai dai ka zo ka tafi dani ko? Ko kuma Deen ya kai ni don bazan iya kai mota ta har Sokoto ba" cike da Mamaki ya ce. "Shifa mijin naki miye amfaninsa Xuhra? Ya ma san da zancen?" sa ke turo baki tayi ta ce "To ai ni Yah Umar ba ruwana da shi, bana ma ganinsa, bana shiga harkarsa baya shiga tawa" Jinjina kai yayi kamar tana ganinsa ya ce "Na fahimce ki hakan ma yayi, amma kin san wani abu?" Da sauri ta girgiza kanta ta ce "A'a". "Dokar Allah Xuhra babu ruwanta da auren soyayya akayi ko na ƙiyayya, wallahi matuƙar kika kauce ba wani excuse wuta zaki shiga, saboda haka yanzu da kike da igiyoyinsa uku akan ki to duk inda zakije ki tambaye sa idan ya barki sai kije idan ma bai barki ki share da shi kawai ki yi ta harkokin ki,daga baya duk sanda ya baki takardar ki shikenan baki da wani nauyin sa kin huta,saboda haka ki faɗamai cewa kina da tafiya gobe, shi kuma tunda har yasan buƙatunki akan wuyansa suke dole ne ya je ya kai ki da kansa ko baya so, .. " Wasu irin hawaye ne masu zafi suka wanke mata fuska cikin karyewar gwiwa ta ce." Yah Umar ni gaskiya ba zan iya ba, girma na zai faɗi... "." Da girman ki ya faɗi da kuma azabar wuta wanne kike so? Kina so ki shiga wuta Xuhra??" Da sauri ta girgiza kanta ta ce "A'a, bana so" Murmushi yayi marar sauti sannan ya ce "To ki daure ki faɗamasa, daga zaran kunje kun dawo shikenan fa kawai ki sake sanya shi a kwandon shara kin ga ne ai? Kuma kina iya a motar har kuje ku dawo kiyi kamar ma baya a motar" Gyaɗa kanta tayi alamar gamsuwa ta ce "To ai ni ko numbernsa banda ita"
"Miye zaki yi da wata number? Ki je ki sanar masa a ɗakin sa mana" Ɗan jim! Tayi tana tunanin irin rashin mutuncinda tayi ta yi masa kwanakin nan har da tayar motar sa fa ta sace jiya,.... "Hello, kina Ji na kuwa?" Gyaɗa kanta tayi jiki sanyaye ta ce "Ina jinka Yah Umar, to zan je amma duk da haka ni dai ka turomin numbern in case" Jinjina kai yayi ya ce. "Ok to zan tura miki yanxu..." "Yah Umar gobe fa kada ka je ko ina nagayawa Yah Abdul shima a chart ɗazu" "To yayi Xuhra, Allah ya kawo ki lafiya" "Amin" Daga haka ya yanke kiran, tana nan sai ga numbern ta shigo wadda ta haddasa mata wani irin matsanancin faɗuwar gaba.. Da Emojin tsaki tayi saving numbern sannan tayi dailing numbern tare da ɗosanata a kunnenta yayinda ƙirjinta ya shiga dukan uku-uku.. Xunnurain kuwa, Kwance yake lamo! Ya kunna karatun ƙur'ani ya na saurare yayinda can ƙasan zuciyar sa ya cika da tunanin Xuhra, neman hanyar da zai rabu da ita yake nema ya rasa, tun da yake bai taɓa jin ya tsani wani mutum ba a rayuwar sa kamar ta, tabbas su ɗin ba su da ce da juna ba kuma har abada ba za su da ce ba, yayi gabas tayi yamma ya yi kudu ta yi arewa, idan har yace zai ci gaba da zama da ita to tabbas watarana za'a tarar da shi zuciyar shi ta buga... Yana nan yana tunani yaji karatun ya yanke kira ya shigo, sai da tayi ringing ta gama sannan ya shiga true caller ya duba suna 'FaɗimatouXuhra Ibrahim' sunan da ya gani kenan... Tunani ya fara da cewa wacece wannan mai kiran na shi? a hankali ƙwaƙwalwarsa ta hasko mi shi sunan Xuhra da su Umma ke yawan kira ma'ana fitsararriyar yarinyar da ke zaune a gidan sa kenan. Zaune ya miƙe sannan ya mayar da wayar ya ajiye zuciyar sa na tambayar ko kiran me take masa oho! System ɗinsa ya buɗe yana duba saƙon da aka yi masa tun daren jiya wanda bai samu ya duba. Ita kuma ganin tayi masa kusan 3miss calls bai ɗaga ba, yasa ta fito cikin ɗar-ɗar ta nufi ɗakin nasa, nan ma knocking tayi almost 3times ba respond sannan daga ƙarshe ta yanke shawara ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shiga, tamkar zata tsulo fitsari tsabar tsoro.. Tana shiga suka haɗa ido hakan yasa ta dururuce ta ja ta tsaya cak a jikin ƙofar ta ce "I..I'm sorry, I.. I bagged in without your permission..." Ganin yanda ya zuba mata ido yana kallonta shi ne abinda ya ƙara rikitar da ita wanda bata hango komai a cikin idanuwansa ba face zallar tsana. Ganin tayi shiru yasa ya mayarda kallon sa gun system ɗinda ke gabansa tamkar ba mutum ce a gaban sa ba,... Jiki sanyaye ta ce "Gobe ina da zuwa Sokoto wurin PPA ɗina,kuma Yah Umar yace dole sai kai zan sanarwa ka kai ni" Daga haka tayi shiru tana jira taji mi zai ce, ta shafe kusan 30mnt bai sake ma marmarin ɗagowa ya kalle ta ba ballantana tayi tunanin saƙon ta ya isa...Marairaice murya tayi ta ce "Please..." "Get out!" ya faɗa calmly kamar mai raɗa,Hannayenta ta harɗe wuri ɗaya alamar roƙo ta ce "Please consider me kada hakan ya bani probl..." Cike da tsantsar nuna ɓacin rai a kalamansa ya nuna mata ƙofa ya ce "Out I said.." Daga haka ta fito da gudu ta koma ɗakin ta, tayi ta kuka kamar ranta zai fita daga nan har barci ɓarawo ya sace ta.....Ni kuwa, Daren yau sam bai ƙaremin da kyau ba, domin kuwa, na kwana cikin wasu irin mafarkai ma su ban al'ajabi waɗan da ma ba zan iya fassarawa ba, tsoro, ruɗani, da kuma tambayoyin da babu amsa. A duk lokacin da na lumshe ido, hoton tsohuwar da ke cikin akwatinnan ne yake bayyana cikin mafarkina wai tana kallona da idanun da ke ɗauke da saƙo, saƙon da zuciya ta ta kasa fahimta. Washe gari bayan haske ya gama kewaye ko ina duhu ya yaye, da ƙyar na iya buɗe idanuwana waɗan da suka kumbura suka yi sasul tamkar na kwana ina kuka, waigawa na yi ta gefena amma banga Naseer ba, da ƙyar na yunƙura zuwa bakin gado na saukar da ƙafafuna waɗanda suka min jinjinjin kamar an ɗora min falalen dutse, mamaki ne ya kamani ganin yanda suka kumbura sosai kamar fulawa ta kumburo, ga wani irin suka da kunkuruna ke yi kamar ana daddatsa mini shi, lumshe idona nayi domin ji nike kamar ba zan iya ta shi ba. Ƙarar buɗe ƙofa da naji shi ya sa ka ni ɗagowa na buɗe idanuwana tsammani na Naseer ne. Wata mace ce ta shigo, ita ba mai shekaru ba kuma yarinya ba,Sanye da baƙin hijabi, fuskar ta ɗauke da murmushi, amma kuma idanunta na ɓoye wani sirri kamar yanda zuciya ta take kitsa min..... "Ina kwana Safnah," ta ce min murya cikin nutsuwa tare da samun wuri kusa da ƙafafuna ta zauna a ƙasa, samun kai na nayi da amsata a hankali, "Lafiya lau." daga haka na yi shiru ina ci gaba da kallonta yayinda zuciya ta ta cika da tsoron ta....ƙara yin ƙasa da kanta tayi cikin ladabi ta ce "Sun ce ni ce wadda zan kula da ke daga yau...." Ta iyar da maganar tana mai shafa wata takarda a hannunta wadda ban san ta mi ce ce ba, na yi zurfi sosai da kallon takardar tamkar idanuwana za su zazzago ta sake ce min. "Sunan nawa Habibah ne, amma ki kirani da Yayah." Wata irin murya naji daga zuciyata tana cewa; ki ji tsoron wannan mace, amma ta wani ɓangaren kuma, abin mamaki sai na ji na aminta da ita,domin kuwa har yanzu da take zaune a gaba na babu abu ɗaya dake faruwa da ni wanda ya fita daga cikin tunani na, komai na nan yanda yake, har cikin zuciya ta naji ina so in sanar mata abinda yake damuna wata ƙila ta iya magancemin matsala ta. "Yayah…" Na furta a hankali ina mai kallon cikin idanuwanta, murya a raunane na ce "Dan Allah me ke faruwa da ni da kuma mijina? Me yasa a yau nake jin kamar ba aure na yi ba, illa kamar an sayar da ni ne cikin wata sabuwar al'umma waɗan da ba su yi daidai da duniyata ba?? Miyasa nike ji tunani na ya sauya har rayuwa ta ma baki ɗaya tamkar bani da wani dangi sai ni ka ɗai...." Wani ɗan ƙaramin bokiti ta fitar daga cikin hijabinta wanda sai yanxu ne na lura da shi, ƙafafuwana ta riƙa a hankali ta ɗaga ta ɗora su kan jikin ta,wani ƙyalle ta fito da shi mai tsananin haske yana wata irin walwalniya tamkar an yanko wani ɓangare daga jikin labulen da na gani ranar da nayi mafarkin Naseer ya ɗaure ni da chains. Cikin bokitin ta tsoma shi ta fitar a hankali tana matsamini ƙafafuna da shi, ni dai babu abinda nike sai binta da ido na koma kamar wata mutum mutumi. Ɗagowa tayi ta kalle ni sannan ta ce " Safnah Naseer ba mutum bane kamar kowa irin yadda kike tunani,Kuma ba aure kika yi ba... shiga kika yi." "Shiga?" na yi saurin maimaitawa murya na rawa cike da tsananin mamaki da ruɗani....Jinjina kai tayi ta ce "Eh,kin shiga wani dangi ne,Dangin da ba kowa ne ke fita daga cikinsa ba wanda Idan kika fahimta, zaki rayu, Idan kuma baki fahimta ba... to ki shirya.... Ki shirya Safnah....." daga haka ta miƙe ta fice hannuna ya shiga kakkarwa ina so in riƙe ta in hanata tafiya domin dole ta tsaya ta fayyace mini komai... Sai dai inaaa! Ta riga ta fita, da sauri na yunƙura da gudu na bi bayanta wanda lokaci ɗaya naji duk ciwon da ni ke ji ya tafiyar sa tamkar an yi ruwa an ɗauke, ƙafafuwana da suka kumbura sun sace kamar an sacce balloon, har harabar Gidan na fito baki ɗaya amma ba Yaya ba labarinta dukkan ma'aikata na kuma duk wanda na tambaya baya cewa komai tamkar ma basa gani na hakan nike tunani domin banga sun bani attention ɗinsu mai nuni da cewa ina magana da su ba, komawa nayi cikin gidan na dinga bin kowa ne ɗaki ina dubawa kamar wata taɓaɓɓiya ina ihun kiran sunan ta ina faɗin "Yayah.. Yayah..." Amma babu amsa... wani ɗaki da ke can wani lungu ne nayi ta yunƙurin buɗewa yaƙi buɗuwa, nayi-nayi amma ya ƙi ya buɗe duk da cewa ga key a jikin ƙofar, ɗaga kai na nayi a hankali ina bin ƙofar da kallo caraf ido na ya sauka a kan rubutun da akayi can saman ginin ɗakin da manyan bold baƙi 'ƊAKIN DUHU' abinda na gani kenan a rubuce wanda yayi sanadiyyar durƙushewa ta akan ƙafafuna guda biyu na fashe da wani irin mugun kuka ina girgiza kai na tamkar zan yi hauka a raina ina faɗin... 'Yanzu na fahimci wannan ba rayuwar gaskiya ba ce,Wannan ba aure bane,Wannan wani ƙangi ne da aka jefa ni a ciki. Duk da akwai abinci, kaya, da dukiya ta morewa, zuciyata tana kulle a cikin akwati, ga hoton fuskata a cikin akwatin kamar na yi shekaru ɗari biyu a duniya. Naseer ba kamar kowa ba ne? Kenan shi aljani ne ko me? "Sannan wannan ɗakin" na faɗa a fili ina mai sake ɗagowa na kalli ƙofar sannan na kalli rubutun da kyau.. Ina ƙara tambayar kai na 'Wacece Yayah ita ma karan kanta? Itama ɗin aljana ce kenan kamar Naseer? Ba aure na yi ba shiga nayi? Ina ne na shiga ɗin??...' Da sauri na miƙe tsaye na shiga ja baya ganin yanda ƙofar ta shiga jijjiga da ƙarfi tamkar zata ruguzo kai na.....Gefen Xuhra kuwa. Tana gama sallar asuba ta shiga shiri kamar wadda zata yi tafiyar wata ɗaya, ƙarfe bakwai ta fito da akwatinta ta ajiye gangar motar sa ta ja ta tsaya tashiga dakon fitowarsa, tana nan taga har 9am ta kusa bai fito ba yasa ta ciro wayar ta ta fara kiran shi, baccin sa yake hankali kwance wanda har ya gama shiryawa ma ne ya hango ta tsaye bakin motar, hakan yasa ya cire kayansa ya kwanta sai bacci. Tana nan goma, sha ɗaya, sha biyu.. A hankali taja akwatinta ta koma ciki tana mai fashewa da kukan baƙin ciki. Haka ta wuni sukuku abin duniya duk yabi ya ishe ta, ga Yah Umar da ya gama ɓata mata rai wai wani tayi haƙuri ta lallaɓashi... Ita yanzu ta gama gane Yah Umar ɗin ma kamar tsoron sa ya ke, hakan yasa ta kashe wayar ta wai ita tayi fushi. The next day ma hakan ce ta faru har dare bata ji motsin shi ba, cikin kuka ta kira Umma wanda ringing ɗaya zuwa biyu ta ɗaga da sallama a bakinta, da sauri ta share hawayenta duk da cewa voice ɗinta bai isa ya ɓoye yanayin da take ciki ba, ta ce "Umma ina wuni" Daga can ɓangaren Umma ta amsa "Lafiya lau Xuhra ya kika wuni, yau tun safe da muka gaisa bamu sake gaisawa ba" "Uhm! Umma Yah Amratu da jiki?" "Amratu jiki Alhamdulillah, kin ganta nan dai haihuwar nan bata nesa in sha Allah" "Eyyah! Allah ya kawo mai sauƙi" "Amin" "Umma daman cewa na yi dan Allah ki roƙar min shi ya taimaka ya kai ni Sokoto gobe, da na mishi magana cewa yayi ba yanzu ba ni kuma ina da wani babban uzuri Umma wanda shi ya san da shi..." Jinjina kai Umma tayi ta ce "In sha Allahu gobe kamar kinje Sokoto kin gama Xuhra sha kurumin ki, bari yanzu na kira sa..." "Dan Allah Umma karki mi shi magana da faɗa kada yaji bai ji daɗi ba..." "Allahu akbar! Kaji mata masu tarbiyya da kaifin hankali. Yo a matan yanzu wace mace ce zata tsaya damuwa da fushin mijinta matuƙar dai ita burinta zai cika, Allah ubangiji yayi miki albarka ya ƙara miki haƙuri, bari yanzun nan zan kira sa gobe in sha Allah kin tafi Sokoto kin gama" Cike da kissa ta ƙara yin ƙasa da murya ta yi ta rattaba mata godiya,daga ƙarshe suka yanke wayar ranta fes!. Usman kuwa, yana gidan gonar kajin sa yaga kiran Umma ya shigo wayar sa, cike da ladabi ya amsa yana mai yi mata sallama, Kuka ta fara masa tana faɗin "Yanzu Usman dan Allah duk yanda yarinyar nan ke matuƙar tsantseni akan ɓacin ranka hakan bai isa yasa ace ka aminta ka kaita gidan su ba har sai da ta kai mahaifiyar ta ta kira ni tana neman arziki haba Usman..." jikinsa ne yayi sanyi jin yanda take kuka duk da cewa hakan ba baƙon abu ba ne a wurin sa," Hajiya ki yi haƙuri in sha Allah zan kai ta.. "." To shi kenan, Allah yayi maka albarka, gobe-goben nan fa ka shirya ka kaita kaji ko.. "." In sha Allah Hajiya" "To na gode, mu kwana lafiya" Mamaki ne gami da al'ajabi suka taru suka mamaye masa zuciya, lallai ma yarinyar nan! Wato shi ne ta sanarwa mummynta ta haɗa shi da Hajiya ko? Lallai zata sha mamakin da sai ya gigita ƙwaƙwalwarta, yayi alƙawarin sai ta yi da na sanin haɗa tafiya da shi! A hankali ya ja guntun tsaki sannan ya fita yayiwa Khalifa magana ɗaya daga cikin yaran da ke kula masa da gidan gonar sannan ya hau mashin ɗinsa ya ja ya koma gida. Tsoro ne ya cika mata zuciya jin ƙarar buɗe gate wanda ya tabbatar mata da cewa shi ne ya dawo,cike da fargaba ta zauna cikin zullumin kada ya zo ya yi mata rashin mutunci, sai dai shiru kamar bai san tana gidan ba, hakan yasa ta shiga ɗar-ɗar cewa Allah dai yasa Umma tayi masa maganar. Washe gari, still bata yanke ƙauna ba ta shirya wuraren bakwai ta fito janye da trolly ɗinta,bata fi 30mnt ba sai ga shi ya fito sanye cikin Kaftan waɗan da suka yi matuƙar karɓar jikinsa, fuskar nan tuƙun-tuƙun kamar bai taɓa sanin yanda ake dariya ba... Taɓe baki tayi ta ja gefe ya buɗe motar, akwatin ta ɗauka ta saka a booth sannan ta zagayo ta buɗe front seat ta shiga ta hakimce, ƙala baice mata ba yaje ya buɗe gate ya fitar da motar ya zo ya rufe gidan baki ɗaya sannan ya ja suka kama hanya, ba wanda yayi wa wani magana har suka wuce Mafara, suna kai wani garin da bata san sunan sa ba ta kalle shi cikin yatsina ta ce "Ina jin fitsari ina jin yunwa" Bai kalle ta ba sai da suka yi nisa sosai suka kai tsakiyar daji ya ja ya faka gefe, kallon sa tayi cike da Mamaki tace "Miye zan yi a nan ɗin?"..."Fitar min a mota.." Cike da tsoro ta ce "Daman fa Ƙarya nake ba fitsarin da ni ke ji..." "Fitar min a mota na ce! Marar kunyar Ƙarya kawai" ya sake faɗa cikin wani sauti wanda yayi sanadiyyar gigita tunanin ta, jiki na rawa ta buɗe ƙofar ta fita tana kallon ikon Allah wanda ko takalmi babu a ƙafarta,... Kafin tayi wani yunƙuri har ya ja motar ya wuce abinsa... Da mugun gudu ta bi motar kamar da gaske zata iya cimma sa ɗin, ganin cikin ƙyaftawar ido har ya ɓacewa ganin ta yasa ta fara kururuwar neman agaji wanda yake kamar ihun ka banza ne a kunnen kurma domin babu kowa a dokar dajin wanda zai tsaya ya taimaka mata... cikin gigicewa ta fara tafiya da ƙafa tana famar taron duk motar da ta wuce amma babu mai tsayawa duk da yake sai ta jima sosai ta ke ganin wulgawar mota, wani irin zafin rana take ji daman kuma ga shi ba ta saba da wahala ba, cikin lokaci ƙanƙani duk ta gigice ta fita hayyacinta wanda ba abinda take in ba kuka ba, ga wani irin tsoro da ya dabaibaye mata zuciya.,duk in da ta samu jefa ƙafa ta ke, bata yi aune ba taga wa su kalar mutane kwatsam a gabanta waɗanda bata san ko su su waye ba, takubba ne rataye a kafaɗunsu ga wasu irin layu da suka da za ga damtsen hannun su ga kuma wa su manyan sanduna a hannayensu, wata irin gigitacciyar tsawa ɗaya daga cikin su ya buga mata wadda tayi sanadiyyar saka ta sakin fitsari ba shiri...........
To fa! Yau ake yinta wai matar ɗan sanda ta haifi ɓarawo! Shin jama'a wanene Naseer? Sannan wacece Yayah? Wanne sani ne za'a bayyanarwa Naseer idan yayi Nasarar kai Malika gare su? Tukunna ma su waye su? Shin zama a haifi Malikar ko kuwa? Miye wannan akwatin Ja yake nufi mai ɗauke da saƙo guda uku? Safnah fa ba aure tayi ba in ji Yaya! To ina ne ɗin ta shiga? Shin idan ta fahimta zata rayu idan bata fahimta ba kuma ta shirya? Miye hakan yake nufi... Ɗakin duhu....hakan na nuni da cewa Safnah da gaske ta fita duniyar mutane ta koma wata duniya ta daban ko ya ne? Kai jama'a wai ya ya ne? Na san tabbas ku na so ku ji duk amsar waɗannan tambayoyin, ko ba haka ba??? To ɓangaren Usman da Xuhra fa? Wai anya auren nan zai ci gaba kuwa? Usman fa yayi mugun nisan da baya jin kira? Ya kawo ta dokar daji ya tafi ya barta, ko me zai faru da ita oho! Su wanene waɗannan mutanen? Anya Xuhra zata iya gafartawa Usman kuwa idan ma an samu ta rayu????
ALHAMDULILLAH! A nan muka kawo ƙarshen free pages in sha Allah, mai buƙatar ci gaba da karatun kururuwa a kunnen kurma littafi mai cike da ruɗani, sarƙaƙiya, faɗakarwa da kuma bada nishaɗi zai iya biyan kuɗin sa #500 only ta wannan asusun; 3132703269, First bank, Ibrahim Amina Bawa, sai kuma shaidar biya ta wannan Layin ***. 🙏 🙏 🙏 🙏..
OUM AMEER