Chapter 44 KUSANCI
KUSANCI
NA
HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM
(Mrs Aliyu mayere)
.........page 44
Duk jikin Bakil ya yi sanyi kalau,yadda bai da wani karsashin cigaba da yin komai, bai san wace irin damuwa su ke ciki ba Saboda haka baya son ya ƙara musu wata damuwar, don haka ya yi ma Jawaheer wayau ya yi saurin komawa gida don baya so Dada Laure ta dawo ta tadda shi yasan duk da halin da su Nura ke ciki sai ta yi mu su wulakanci irin yadda ta saba, haka yabar gidan cikin damuwa.
Su Dada Laure kuwa tun barin su kotu, asibiti suka wuce da Adam, sun dade likita na duba Adam daga bisani ya rubuta magunguna na zazzaɓin cizon sauro da na ulcer, bayan sun sayi magungunan ne su ka taho gida. Duka gidan Bello Malami su ka yada zango, Haj Hadeeza da kanta ta haɗa ma Adam ruwan wanka ya shiga banɗaki ya shiga wanke dattin jikinsa me wari.
A yayinda tuni hadima me dafa abinci ta shiga dafa duk wani nau'in abinci da Adam yake so, su kuma duka suna falo banda la'antar Nura da iyalinsa babu abinda suke yi, Bello Malami ya dubi Dada yace "Ni har abada babu ni babu Nura ko iyalinsa, abinda ya yi min bazan taɓa yafe masa ba",Dada Laure ta gyara zamanta ta na zazzare idanu cikin kakkarfar murya tace "Hmmm ai hukuncin da zan ɗauka akan Nura wannan karon Zaiyi mamakina, don wannan tonon asiri da ya ja min bazan taɓa mantawa ba ba kuma zan daga masa kafar da zai cigaba da ci min kashi a cikin zuri'ata ba,tunda ba ya nufin mu da alheri to dole nasan abin yi da shi, don bazan zuba masa ido ya kassara ni ba".
Goggoji Hama wacce bata dade da shigowa gidan ba ita da mijinta Mallam Mamman ta yi saurin amshe maganar bayan ta gyara zamanta tace "Ai gaskiya Nura ya yi shirme, abinda ya aikata bai kamata ba ta ya ya zakayi ihu ka dabama kanka wuka, yanzu wa gari ya waya duk magana ta cika gari yanzu waye yake tsammani zai bari ɗansa ya auri Ummi, ya gama tona mata asiri ya watsar da darajar ta, wanda bai san abinda ya faru da ita ba ma yanzu ya sani, mu kanmu fa ba mu tsira ba, don har gida ake biyo Mallam ana yi masa Allah ya kyauta",
Mallam Mamman ya dubi Bello Malami yace "Ai shi Allah ba azzalumin sarki bane , kaga dai yanzu kotu ta wanke Adam yanzu babu wata maganar banza da wani Zaiyi a kansa, don yanzu mutane duk sun yarda da cewa sharri Ummi ta yi ma Adam, kaga dai gaskiya tayi halinta,duk mugun nufin Nura ya koma kansa yanzu fuskarsa ma bazai iya nunata a gun kowa ba".
Haka dai kowa ya yi ta faɗan albarkacin bakinsa,har aka gama abinci Kowa ya Ci ya koshi, sannan Adam ya shige dakinsa da ya sha gyara ya kwanta domin ya huta gajiya, sai dai zuciyarsa har yanzu cike take da tsabar tsanar Nura da Ummi, don wannan duka da yasha gun yansanda bazai taɓa mantawa ba,sai dai ya ji natsuwa sosai yadda aka goge masa wannan mugun laifin don da ya tabbata ya fito a me lefin baisan wane irin mummunan hukunci za'a yanke masa ba.
Kafin Dada Laure ta koma gida sai da ta umarci su Bello Malami su zo su sameta dukkan su gobe da safe, sannan ta tafi gida, su ma su Mallam Mamman sun ɗan ƙara jimawa kafin su tafi, haka su Haj Aseeya da Haj Bintu duk sun koma gidajensu bayan sun gama caccakar Zulaiha, tare da tabbatar da cewa sun ƙara datse duk wani abu dake tsakanin su, dama ba wata mu'amala suke yi ba, to wacce ba za'a rasa bama sun datse.
Tun komawar Nura gida yana dakin zaure shi da Mallam Isah wanda ya dade yana tausar shi tare da bashi hakuri, ya dade tare da shi kafin ya tafi gida shi ma zuciyarsa cike take da damuwa da kunci gami da tausayin Nura da iyalinsa. Jikin Nura ciwo yake masa kamar yadda zuciyarsa ke zafi duk duniyar tayi masa zafi matuƙar zafi. Duka sallolinsa a cikin daki ya yi ya kasa fita yaje masallaci, ya na jin dawowar Dada Laure.
Wanda ba'a dade ba Ayyah ta yi sallama lokaci ɗaya gami da tura Kofar dakin ta shiga.
Nura na kudundune a ƙasa, ta nemi waje ta zauna kusa da shi gami da kiran sunanta, ya amsa ba tare da ya dago ya dubeta ba saboda baya son taga hawayen da suke zuba masa wanda ya kasa tsaida su, asalima bai san suna zuba ba.
Ayyah ta sami ƙarfin guiwa sosai ta danne ta ta damuwar, tace "Nura duk abinda Allah ya ƙaddara ma bawa babu yadda Zaiyi, hakuri da addu'a gami da karbar wannan ƙaddarar itace kaɗai mafita, ba kai ba ba mu ba, duniya ma tasan an zalunce ka, ka sani kuma Allah baya zalunci ya kuma sanya zalunci abin haramtawa a tsakanin mu saboda haka ko adade ko a jima sai Allah ya yi sakayyarsa a gare mu , sai Allah ya fitar ma da Ummi hakkinta,don haka Na zo na rokeka don Allah ka sama zuciyarka hakuri ka sami ƙarfin guiwar da zaka taushi Zulaiha da Ummi ka daina wannan damuwar ", a hankali Nura ya sa hannu ya goge hawayensa gami da tashi ya zauna sosai ya na fuskantar Ayyah yace murya na rawa,
"Ayyah babu abinda ke min zafi da kuna da ya wuce yadda gani a raye amma na kasa kwatoma Ummi hakkinta, na kasa tabbatar da adalci akanta "
Ayyah ta girgiza kai tace "Allah shi ne me kwato mata hakkinta, sakayyarsa kuma itace sakayya domin shi baya amsar cin hanci balle ya yi abinda mutum ke so don haka mu yi hakuri mu jira sakayyarsa", Nura ya yi shuru ya na jin wata irin tsanar zuri'ar Malami, ya na jin tamkar ya binne kansa ka da wani ya ƙara ganinsa, Ayyah tace "Yau zan koma gida", Nura ya yi saurin kallonta yace "Da daddaren nan Ayyah, ai da kin bari sai gobe idan Allah ya kaimu".
Ta girgiza kai tace "A'a Gara dai na tafi yanzu, saboda Dada ta dawo ta na ta wasu maganganu marasa dad'i, Gara na tafi saboda ina jin gaf nake da na tanka mata", shuru ya yi baice komai ba har Ayyah ta tashi tana kallonsa tace "Allah ya ƙara muku hakuri da dangana Nura, Allah ya shiga lamarinku".ba ta jira komai ba ta juya ta fice.
Sai cikin dare sosai sannan Nura ya lallaba ya shiga cikin gidan. Ga tsammanin sa duk nisan daren nan daga Zulaiha har Ummi idanunsu biyu, ita Zulaiha ta na kan tabarmar da take sallah da alama nafila ta gama, ta na ta jan casbaha, zuwa lokacin idanunta har sun kekashe, babu ko kwayar hawaye ɗaya a cikinsu.
Gefenta ya samu ya zauna, ya na yi mata wani irin kallo me cike da tausayi, ta juyo suka haɗa ido, duk jikinta ya ƙara sanyi kalau saboda yadda taga Nura ya koma, cikin kankanin lokaci gaba ɗaya duk ya zabge ya rame ya fita hayyacinsa.
"Kinci abinci?"
Ya tambayeta lokaci ɗaya ya na ƙoƙarin kauda idanunsa a kanta, ta girgiza kai tace "Babu wanda ya iya cin komai har Mallam da Jawaheer ba su ci abinci ba su kayi bacci". Ta yaye hijabinta ta aje ta mike tsaye tana cewa "Kaima ai babu abinda ka ci, na ki zuwa inda kake ne saboda ina son na baka lokacin da zaka yi kuka harka share hawayenka", ya juyar da kai yana kallon Ummi yadda itama ta ƙara kwantsamewa bakinta ya bushe kallo ɗaya zaka yi mata ka tabbatar da cewa tana cikin tsaka me wuya, a hankali ta maida idanunta ta kulle tana jin wani irin zafi daga cikin zuciyata.
"Ummina ki yi hakuri, duk yadda na so da na kwato Miki hakkinki bazan iya ba,saboda a yanzu Ummi kuɗi su ne komai, kudi suke tsarkake me laifi daga laifinsa su kuma maida me gaskiya makaryaci kuma kaskantacce, yau itace rana ta farko da na ji ina son nayi kuɗi saboda na fahimci su ne martaba da kima, su ne kuma malullubin dukkan aibu".
Zulaiha ta dawo da kwanon tuwo da miya ta aje a gabansa, lokaci ɗaya Nura ya cigaba da cewa "Allah zai yi Miki sakayya zai fitar Miki da hakkinki, damuwar da ke zuciyarki ki yi ƙoƙarin ragewa don nasan bazai yiwu ki cire ba, domin an wulakanta mu an jefa mana damuwa da tashin hankalin da har abada bazai bar zuciyar mu ba, amma mu yi hakuri domin Allah ya na tare da masu hakuri kowa kuma yabarma Allah lamarinsa bazai taɓa yin nadama ba, kiyi hakuri kiyi hakuri Allah ya baki lafiya, ina tabbatar miki zan tsaya tsayin daka wajen ganin rayuwarki tayi kyau a gaba in sha Allah yadda na fara alfahari da ke zan cigaba da alfahari da ke har abada",
Zulaiha ta aje ruwan da taje ta debo, ta zauna kusa da shi ta na ƙoƙarin zuba masa abincin, amma sai ya girgiza kai yace "kada ki zuba". Tayi masa wani kallo me cike da tausayi tace "Kayi hakuri don Allah ka taimaka ka ci abincin nan, kai ne kadai garkuwar mu, Mallam idan ka fadi ciwo ya danneka ya zamu yi, ina zamu sa kanmu", ji tayi wani abu ya tokare zuciyarta, daker ta hadiye yawun bakinta, sannan ta yi ƙasa da kanta, duk abin duniya ya yi mata zafi. Baya jin cin abincin domin bakinsa babu dad'i amma yanayin da zulaiha ta nuna yasa ya furta "Zuba min tare da ke mu ci". Ba tayi musu ba ta zuba abincin sannan ta gyara zamanta tasa hannu tace
"Mu ci".
Ya waiwayo ya na kallon Ummi da har zuwa lokacin idanunta su ke a rufe, duk sanda ya dubeta yakan ji wata irin damuwa da tashin hankali mara misaltuwa a tare da shi, cikin nauyin baki yace "Ummina tashi ki ci abinci", ta girgiza kai alamar ba zata ci ba.
Ya matso kusa da ita sosai yace "Tashi ki ci, idan ba haka ba ni ma ba zan ci ba", jin hakan yasa ta buɗe idanunta, wasu siraran hawaye su ka gangaro daga cikinsu.
Ba tare da tace uffan ba ta ja jiki daker cikin azabar ciwo ta zauna a karkace tunda bata iya zaunawa dai dai, ta jingina bayanta da jikin bango, duk da haka wani irin azaba take ji.
A haka Nura ya dinga dibar tuwon da hannunsa ya na ba Ummi a baki, zulaiha dai hawayenta ya tsaya sai kunan zuciya da tsananin baƙin ciki kawai dake kwance a cikin zuciyarta, tausayin yarta da mijinta take ji fiye da yadda take jin tausayin kanta.
Nura ya na ba ummi shi ma ya na ci, itama zulaiha tana ci har suka koshi, ya bata ruwa ta sha, da kansa ya tashi ya ƙara gyara mata wajen kwanciyarta Zulaiha ta kwashe komai ta fita da su, sannan ta dawo.
Har Nura ya maida Ummi ta kwanta, ya na jin a zuciyarsa Ummi zata cigaba da samun kulawa ta musamman daga gare shi, kamar yadda sonta da tausayinta su ka ƙara kama zuciyarsa, domin a dalilin faruwar wannan ibtila'in ya na jin babu wani ɗansa ko yarsa da zai so sama da irin son da yake ma Ummi.
A lokacin aka fara kiran sallar farko na asubahi, Nura ya mike yana kallon Zulaiha yace "Zulaiha daga wannan rana ina son ki sani ba mu da kowa sai junanmmu, kisa a ranki cewa babu abinda mu ka haɗa da zuri'ar Malami, a yau na yarda na kuma amince ba ni da yan'uwa", Zulaiha ta jinjina kai kafin tayi magana ya dage labule ya fice ya dauki buta ya yi alwala ya wuce masallaci.
**********
Karfe goma sha ɗaya na safe gaba ɗaya dakin Dada Laure ya cika da ƴaƴanta ko wanne ya na kan kujera cike da izza da nuna dagawa, gefe ɗaya Mallam Mamman Malami ne shi ma ya na zaune ya amsa kiran Dada. Yanayin Dada Laure kaɗai zaka duba kasan ta shirya tsaf wajen yin yankan kauna domin babu annuri ko kaɗan akan fuskar ta maimakon hakama fuskar ta ta a hade take tamkar bata taɓa dariya ba. A haka take har zuwa lokacin da Nura ya yi sallama shi ma ya amsa kiran Dadar ne. Sai dai babu wanda ya amsa masa sallamar, ganin ya dogare yaƙi shigowa domin cika umarnin Allah tunda ya yi sallama har sau uku ba'a amsa ba bazai shiga ba, Mallam Mamman ne ya dubi bakin kofar da yake tsaye yace "ka shigo mana, ka tsaya", Nura yace murya shake "Banji an amsa sallamata ba ne shi yasa ban shigo ba", Dada Laure ta saki wani dogon tsaki tace "ka gama kininbibinka, wai kai na Allah ko?, hmmm to wa'alaikumussalam, Sarkin malaman duniya shigo".
Nura ya hadiye komai ya cire takalmin ƙafarsa ya shigo dakin, ya tsaya ya kalli duk wanda ke cikin dakin, yanayinsu ya tabbatar masa ba arziki bane ya haɗa su, babu wanda ya yi masa kallon arziki, hakan yasa ya koma gefe, shi a ƙasa ya zauna domin babu yadda za'ayi mahaifiyarsa na sama shi ma ya zauna a sama. Saɓanin su Bello Malami da bayan zaman kujerar ma harda wani karkada kafafu suke yi.
Cikin wata raunanniyar murya Nura ya dubi Dada Laure yace "Gani Dada".
Ta tabe baki gami da gyara zamanta tace "Ai na ganka, ka zo a lokacin da kaga dama tunda ba ni da daraja a gunka, su waɗanda nake da daraja a gunsu ai gasu a gabana tun tsawon lokaci", Nura baice uffan ba ya cigaba da saurarenta, bayan ta ƙara muskutawa ta na kallonsa
"Bayan abin kunyar da yarka Ummi tayi, ka zaɓi ayi mutuwar kasko to ta Allah ba taka ba, duk yadda kaso daka bankade asirina da na ahalina to Allah ya kare ni,tunda kotu ta faɗa maka kaji ni da na haife ka na faɗa maka baka ji ba, to kotu ta wanke Adam an tabbatar da cewa sharri kayi masa, abin kunya duk ya ƙare a kanku, ka watsa sirrin yarka wanda nayi imani babu wani mutumin Kwarai da zai zo ya nemi aurenta sai dai ta ƙare a haka a gantale, mugun nufin ka ya ƙare a kanka tunda Allah ba azzalumin sarki bane".
Duk da maganganun Dada na tafasa zuciyar Nura to fa ya daure ya na ta hadiye duk takaicinsa, domin dai ko ma menene Dada uwace duk lalacewarta akwai girman hakkinta rataye a wuyansa, wanda a kullum yake fatan ya sauke, ko da ita ba zata sauke nata nauyin ba wannan ita da mahaliccinta.
Dada Laure ta ƙara fuskantar sa rai a bace, fuska cike da tsana tace "Nura ba ka da wani rufin asiri duk duniya da ya wuce na zuri'ar Malami, wanda idan aka cire zuri'ar Malami a cikin rayuwarka ba zaka kai labari ba, domin dai sanin kanka ne baka da dangin uba ba ka da kowa su din malamin da ka tsana ka ke hassada tare da kiyayyarsu su ne rufin asirinka, tunda ko banza ubansu Bello shi ne ya dauke ka ya yi maka dukkan gata duk da babu abinda ya haɗa da kai amma ya zaɓi ya rungume ka ya kuma so ka fiye da ya'yansa da ya haifa, amma da yake ɗan Adam butulu ne shi ne don ƙasa ta rufe masa ido zaka wulakanta zuri'a sa zaka sa su zama abin kyama saboda baƙin halinka". Haka Dada Laure ta runtse idanunta ta yi ta gorantama Nura komai tun daga ranar da ya shigo gidan Malami har zuwa yau da yake tsugune a gabanta sai data faɗa ta kuma goranta masa, babu kalma daya da zai iya mayar mata, don haka kawai sai hawaye ne ke sauka daga kwarmin idanunsa masu matukar zafi, har zuwa lokacin kuma bai buɗe baki ya furta ko kalma ɗaya ba, su Bello Malami kuwa har wani ƙara shan kamshi suke suna ƙara baza manyan riguna, Mallam Mamman kuwa baiyi tunanin takama Dada Laure birki ba duk da yasan maganganun da take yi basu dace ba, amma sai gyada kai kawai yake yi yana nuna alamun duk abinda take faɗa daidaine. Dada ta cigaba da cewa "saboda haka a yau ina baka umarnin ka tattara ka tashi daga gidan malami, tunda baka son zuri'ar Malami baka sona, to zama damu bai dace da kai ba,don haka ka tattara ka tashi ka koma duk inda ka ke ganin zaka fi samun natsuwa, dama dai nan ba gidan mahaifinka ba ne don babu abinda yake dashi dakin ma da mu ka zauna bayan aurenmu mahaifina ne ya gina masa, to ka bar musu gidansu tunda baka da gado a cikinsa, inda ma marigayi ya baka ka hakura da shi don dai dama ka sani har ƙasa ta nade ba zaka taɓa iya gina ko da daki ɗaya ba a wajen don haka kabarma magada kayansu ".
Gaban Nura ya yi matuƙar faduwa jikinsa ya shiga rawa, ya na jin duk duniya a lokacin ba za'a sami wanda ya fishi tashin hankali da damuwa ba, yanzu Dada Laure uwar da ta haife shi take irin wannan furucin a kansa. Ya dago fuska sharkaf da hawaye ya zubama fuskarta ido, cike yake da kakabi da mamakin wai itace ta haife shi, ya dawo da kallonsa ga yan'uwana da babu wanda ya nuna alamun tausayi da kauna a gare shi, ko nuna alamun abinda Dada tayi bata yi dai dai ba.
Ya dire idanunsa akan Mallam Mamman da ya rasa wace irin zuciya ce dashi da baya iya gayawa wanda yake tare da shi gaskiya, duk kuma da kasancewarsa shi ne babba a cikin zuri'ar Malami amma girman nasa ya yi gardama, haɗa idon da suka yi da Mallam Mamman yasa ya yi saurin gyara zamansa ya na cewa "Kaima Nura ai kayi kuskure bai kamata ace inuwar da ka ke hutawa za kayi ma kashi ba, haba", Nura ya yi ƙasa da kansa ya sa hannu ya goge hawayen dake fita masa.
Yar Gidan Imam ✍️