77
Jikinsa rawa yake sosai idanunsa sun ka’da sun yi jajur. Ya lumshe idonsa yana jin yarda hawaye suke zuba a kwarmin idonsa. Takaicinsa guda najasar da Safna ta dinga banka masa da sunan maganin mallaka. Da sauri Amani ta d’aga kai tana kallon yarda yake fusgar leb’ensa Ya kasa controlling fushinsa, don muraran kake hango tsananin tashin hankalin da zuciyarsa take ciki. Ya kasa aiwatar da komai sai huci ta hanci da kuma fisgar leb’ensa…. Kallon Safna kawai yake da wani irin yanayi da mutum ba zai iya fassara shi ba. Da sauri Amani ta ja shi jikinta tana murza hannunsa so take ta dawo cikin hayyacinsa Amma ta lura kamar baya tare da tunaninsa hakan yasa ta nemo tata nutsuwar ta dasawa zuciyarta ta shiga karanta addu’oi tana jan hannunsa Innalillahi kawai take furta masa ta zaunar da shi a gefen Didi da itama take cikin nata tashin hankalin…. “Na haramta aure Har abada tsakani na da ke Safna, koda ke ce autar mata!” Haka Ya fa’di kalmomin cikin wata irin murya da take fita da amo Mara da’di. Safna da bata San me take ba ta tuntsire da dariya tana sake fusgar gashin kanta… A fusace Ya jata da k’arfin gaske zuwa gate. Da sauri Didi ta dakatar da shi daga k’udirinsa kada ka fara Moddi barta da halinta, ka barta iyayenta su zo suga Shukar da tayi ta fara tsiro, ka bari a kira su a waya a gaya musu su zo su kwashe ta, abinda ta yi kuma ita da Allah tun yanzu ta fara ganin sakamakonta….” Cak Ya tsaya ya kasa juyawa don ba haka Ya so ba, so yayi Didi ta bari Ya ci Uban Safna Ya mata dukan da za’a kasa shaidata idan an ganta Amma ta togace shi da kalamanta. Hakan yasa ya ja ya tsaya yana jin yarda jijiyoyin kansa suke sake d’aurewa. Umma T ta kalli Amani ta ce “Ki ja shi ku koma ‘daki Ya samu nutsuwa yana cikin yanayin firgici da tashin hankali. Allah ya sanyaya masa Amma koma waye e hakan ne zai faru da shi….” Ta fa’da tana d’auke hawayen idonta. A yau ne burinta Ya cika, a yau ne duk abubuwan da suka dabaibaye
Moddinsu ta tabbata zai bar shi, zai dawo cikakken mutum ba mutum mutumi ba… Sun sha wahala sosai da Safna, itace jarrabawar su a rayuwa sai dai da suka barta da halinta ga shi nan tun ba aje ko ina ba Sun girbi abinda ta shuka. Tabbas Hukumullahi laa ajabun.
Jikin Amani a sanyaye ta k’arasa inda Moddi yake ta kama hannunsa a hankali. Ajiyar zuciya Ya saki kawai Ya samu kansa da mata wata irin zazzafar runguma abinda yafi buk’ata kenan a lokacin, Ya ji shi a tare da ita ko damuwar da yake ciki zata ragu. Amani bata hanashi ba, duk da tana jin kunya sai dai yanayin da yake ciki ba zai saka ta hana shi rungumar ta ba… ajiyar zuciya kawai yake saki. A hankali Ya furta “I need you mu shiga ciki….” Duk da ita ka’dai taji maganar sai da kunya ta kamata. Ya ja hannunta da sauri suka nufi part d’insù ba tare da ya sake kallon Safna ba don wata irin tsanarta yake ji sosai a ransa, da yana da iko zai iya kasheta ko zai samu sassauci a zuciyarsa….
A wani irin yanayi Ya kusanceta, yanayin da ta tabbatar na tashin hankalin da yake ciki ne. Bata hanashi ba duk da tana jin yana wahalar da ita, amma hakan da yake ta tabbatar shi zai saka ya samu sauk’in zuciyarsa….
Idonsa a lumshe ta ji yana sakin ajiyar zuciya a hankali Ya furta “Don Allah Amani ko da wasa kada ki fara zuwa wajen Malamai, koda da sunan su Miki addu’a ne, daga haka suke jirkita muku tunaninku, shi kuma Allah sai ya musu abinda suke so don ya gwada mizanin imaninsu a zuciyarsu, talala ce ubangiji yake musu, ba wani abu da wani boka ko Malam ya isa ya maka wanda baya cikin k’addararka, duk abinda Ya samu bawa dama k’addararsa ce, zan so ki zan kuma kula da ke, ina tabbatar Miki ina Miki k’aunar da ba sai kin kai sunana wajen Boka ko Malam ba zaki mallake ni… don Allah mu yi tsarkakken zama Wanda ba k’ullatar juna a cikinsa…..” Ya fa’da yana sakin hawaye a hankali. Amani kallonsa kawai take kafin ta saka hannu ta Shafa kumatunsa tana daga kwancen ta fara kwantar masa da hankali. “Ya Allah kada ka jarrabeni da zuwa wajen Malami Ya Allah da na aikata haka gwara ka ‘dauketa rayuwata…” Wata irin runguma Moddi Ya kai mata…. A hankali Ya furta “Alhamdulillah…” shiru ya biyo baya na tsawon lokaci kafin ta ji Ya yi magana… “Idan kin ga Ina miki abinda ba kya so, feel free ki gaya min, I will try my best naga na daina Miki kin ji?” Murmushi ta saki ta ce “In sha Allah.”
Asubar fari Didi ta saka Umma T ta kira gidansu Safna, don kwana ta yi bata yi barci ba tana musu iface iface da son ficewa daga cikin gidan. Umma T ta ce musu su zo akwai matsala… Umman Safna hankali tashe ta nufo gidan ita da wasu brothers D’in Safna. Cikin tashin hankali suke kallon Safnan. Ummansu ta ce “Cab’di wato tsiyar da kishiyar ki ta Miki kenan? Ta haukatar min da y’a to wallahi ba zai yiwu ba….” Didi ta mata wani banzan kallo ta ce “Shin baki ji irin abubuwan da take fa’da ba ne?” Amma Umman Safna ta bursunawa idonta toka ta ce bata San zancen ba sharri ake wa y’arta. Ai kuwa kamar abin almara Safna ta fara furta abubuwan da take da asirin da Ummanta ce take kawo mata…,” Da sauri Umman ta kai hannu ta rufe mata baki cikin borin kunya ta ce mazan su kamata su saka a mota su tafi. “Sharri ne dai kun yiwa y’ata tunda ba tun yau kuke son ku rabata da danku ba, to ga gida nan ta bar muku Allah ya isa abinda kuka mata….” Umma Dijatu ta ce “Eeh lallai wannan fa Shine tabarmar kunya da hauka ake na’deta, yanzu ke baki ji kunya ba, sharri ai ‘d’an aike ne gashi nan ya juyo ya dawo kan ki, yanzu sai ku koma wajen bokan Ya mata magani Ya aureta. Mahaukata kawai mushirikai da basu yarda da Allah ba…..” Haka suka yi ta cacar baki… suka tafi duk da Safna na turjewa tana ihun kiran ba zata tafi ta bar gidan Moddi ba, Moddi nata ne ita ka’dai….
Suna fita Didi ta saki ajiyar zuciya tana lumshe ido. Abinda Ya tsaya mata shekara da shekaru taji Ya sauka daga k’irjinta. Hawaye wani na bin wani tana tuno abubuwan da Safna ta dinga yi. K’iri k’iri ta rabata da ‘danta ta dinga cusa musu bak’in ciki da takaici da yake Allah ba azzalumi ba ne sai gashi komai Ya juye kanta. Allah kenan. Da k’yar ta ja k’afa ta koma cikin sashenta. Su Dijatu suka bi bayanta zuciyarsu fari tas yau dai Sun rabu da Safna Sun rabu da k’aya…