JIKAR BAUSHE

Page 13&14

by @meenatyandoma

J I K A R B A U S H E

©️®️ MEENAT A. YANDOMA

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

HARAMUN NE SARRAFAMIN LABARI TA KO WACE SIGA BA TARE DA IZININA BA. 'YAN YOUTUBE MA HAKA

🅿️ 13&14

... Ƙokarin sake dubawa ya ke amma ina, da saurin ya dauke hannuwansa sakamakon narkewa da madubin ya fara yi ya na nutsewa a cikin ƙasa.

Da gudu gudu ya fito daga dakin ya na laluben takalmanshi. Matarshi kuwa ganin halin da ya ke cike ya sakata tarbar shi.

"Mai gida lafiya kuwa? Ko dai baka lafiya" ?

Jajayen idanun da ya kafe ta da su ne ya na mai wurga mata harara ya sakata saurin hadiye maganar da ke a bakinta.

Lokaci daya jikinta ya hau tsuma. Zubewa tayi a kasa ta na neman gafara cike da tashin hankali.

Gogan naku kuwa bangare ta yayi tare da ficewa a farfajiyar gidan. Amintaccen yaron shi ya kira ba a jima ba sai ga shi ya iso.

Kamar yadda suka saba yau din ma tafiya suke cikin kasurgumin jejin da halittun cikinsa kadai sun isa firgitar da ruhin bil adama.

Ba su suka isa ba sai da duhun magriba ya fara.

Katon dutse ne wanda girmanshi ya zarta misali. Samanshi kuwa ba zaka iya hango karshen shi ba.

Kamar kullum idanunsu suka rufe sai gasu sun bayyana a tsakiyar dutsen, a gaban wani hirɗeɗen mutum mai zubin samudawa.

Tuntsirewa da dariya yayi wanda ta haddasawa dutsen fara girgiza. Ba shirin su Alhaji Biliya suka zube saman guiwarsu lokaci daya suka yi mai Sujjada.

Sake ke cewa da dariya ya yi tare da tsagaita wa.

"Madubin da muka sha wahalar ƙerawa ya tarwatse. Wannan kadan ne daga cikin musibun da zasu biyo baya"

Ya karasa maganar tare da hade girar sama tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa.

"Tsafi ya dafawa na kan tudu. A rikice na ke kuma a firgice, a taimaka a fitar da ni a hudu kamar yadda aka saba. Domin hakika ina cikin zallar tashin hankali da manya-manyan musibu. Yarinyar nan dai ta bayyana."

Ɗaga ma shi hannu ya yi. Dole ya dakata kanshi a kasa.

"Tun kafin ka san ta bayyana ni ne wanda ya fara sani. Hasali ma ta na shaƙar iskar nahiyar nan nasan ta shigo in da ake nemanta. Ka sani wannan budurwa ba cikar burinka ba ce ita din cikar nawa burin ce. Da ita ne kaɗai zan iya kaiwa kololuwar matsayin da ko wane matsafi ya ke da burin kaiwa. Yanzu haka a binciken da na yi na gani ce wa ta ɓata daga hannun wadanda suka tsinceta, babban abin da ke daure min kai shi ne ina ta shiga. In Ka Bari Muka Rasa ta Tabbas azabarka ta fi yawa yawa. Domin kai dukkan wata tsiyar da ka shuka da mutanen da ka rufewa baki ko mai zai warware"

Wani gumi ne ya shiga wanke Mai jiki, murya na kyarma ya soma fadar.

"A taimaka min da inda zan iya samun ta na maka alkawarin a cikin daren nan zan nemo ta"

Bushewa ya yi da dariyar da ta fi ta farko.

"Ka sani ni kaina bansan inda take ba. Abu daya na sani shi ne tana da matukar hatsari domin tare take da Maciji wanda na kasa gane shi waye. Nan da watanni biyu muddun baka kawowa ba ko mai ya biyo baya ka kuka da kanka."

Ya na gama fadar haka ya bace bat! Rarraba ido suka hau yi cike da tashin hankali. Ido suka sake rufewa sai ga su sun bayyana a karkashin dutsen.

"Ran shugaba ya dade. Me zai hana ka saka hukuma duk in da aka ganta a kamo maka ita, sai na ke ganin kamar zai fi sauki wurin samun ta"

"Amma Bille yanzu na tabbar baka da hankali. Hukuma zan saka ta nemomin yarinyar da nake kokarin salwantar da ita. Nemanta ya fi a ce min in kawo wani daga cikin dangi ko iyalina zai fi min sauki tunda su da ma na saba bayarwa bisa ga kawota da zanyi. Mu je cikin gari a duk in da ta ke zan nemo ta"

Abin hawa sun suka hau tare da baro jejin...

...Neman duniya su Momy sunyi ma Samu amma ko mai kama da ita ba su gani ba.

Kawu Hadi kuwa abin ya matukar bashi mamaki. Ganin tunda ya ke shi dai bai taba jin wani ya bace a wannan yanki ba.

Momy kuka ta fara ta na fadar ina zata saka kanta. Yarinyar da suka yi sanadin bacewar tunaninta kuma yanzu sunyi sanadin bacewarta.

Da kyar Luba ta rarrasheta ta dawo cikin hayyacinta. Amma har suka dawo gidan kawu Hadi kuka ta ke.

Kafar da zasu saka cikin fakon gidan daskarewa suka yi baki sake suke kallon ta. Ba su ba hatta Hadi ya dan rikice da wannan kulallallen lamarin.

Momy ce ta yi karfin halin kiran sunanta.

"Saaamuuu! Dama kina nan ko dai dama nan muka manta ki ba mu tafi tare da ke ba"

"Haba Yaya! Wane irin a nan muka barta. Bayan ganin idonki a tare muka tafi da yarinyar nan"

"Ku dakata! Tambayarta ya kamata mu yi wa ya maidota ba wai mu tsaya muna jayayya ba"

Ce war Kawu Hadi.

"Irin mu ba mu son zama cikin mutane domin ba su sonmu kyararmu suke. Maganar dawowa kuma ni da kaina na dawo domin nasan hanya"

"Zinatu kin rakito mana sabon bala'i yau muna ganin tashin hankalin da ya zarta tunaninmu. Ke mujiya ce da baki son zama cikin mutane? Ke nifa yarinyar nan bata kwanta min a rai ba, ina ganin ta dawo nake ce wa matar gidan nan duk yadda akayi aljanunta suka dawo da ita."

"Dada! Don girman Allah ki daina hada yarinyar nan da Mujiya. Mutum da ce karmu"

"Zinatu na daina amma ki sani bazan hada hanya daya da ajalina ba. Asim din ma ya muka kare da shi bare kuma wannan mai idanuwan Mujiyar. Wai na manta ashe kin hana a kirata haka"

Gyaran murya Alhaji Hadi ya yi

"Sai na ke ganin kamar abin da ke da mun Asim shi ne ya ke damun yarinyar nan. Me zai hana kafin ku koma gida a fara neman mata magani ko Allah zai sa ya dawo hayyacinta kunga in ta warke sai ku damkata ga danginta. Duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi, in kika yi wannan sadaukarwar sai ki ga kema Ubangiji ya taimake ki dangin Mahaifin Asim da ki ke nema Allah ya sadaki da su."

Hawayen da Momy ke kokarin boyewa ne suka kubce mata lokaci daya maganar da mijinta ya mata ta dawo mata sabuwa fil tamkar a lokacin ya ke mata ita.

"In kika haifi namiji wane suna ki ke so a saka mashi"

Murmushi ta yi domin ta jima ta na kaunar sunan Asim.

Shi ma din Dariya ya yi jin sunan da ta zaba. Sai dai lokaci daya dariyar ta koma bakin ciki fuskarshi ta murtuke.

Tambayar duniya Zinatu ta yi ma shi amma sai ya ce mata bakomai. Danginshi da gobara ta cinye ya ke tunawa. Hankalin Zinatu kara tashi yayi shikenan yaro ko yarinyar da zata haifa za su tashi su yi rayuwa ba tare da sun san dangin mahaifinsu ba.

"Zinatu!" Ya kira sunanta

Jiki a sanyaye ta amsa.

"Jikina ya na bani mutuwa zanyi nan da wani kankanin lokaci, Zinatu kiyi min alkawarin za ki kula da abin da za ki haifa ko bayan raina ke ce uwarshi ke ce Ubanshi kada ki kuskura ki bari yayi kukan maraice"

Tush! Ita ce ƙarar da ta dawo da Momy daga duniyar tunin da ta kula.

Kwalbar da Samu ta jefa wa Asim ce ya kauce ta daki bango ta tarwatse. Sai dai kafin su yi wani yunkuri Asim ya rarumi wata ƙatuwar kwalbar da aka cika da turaren wuta ya jefa wa Samu.

Cikin rashin sa a ta kauce kwalbar ta daki goshin Dada.

"Inna lillahi wa'inna ilaihi rajiun! Zinatu Sama ta fadomin wasu taurari kemin shawagi, ruwan Teku na ke hangowa jama'a ku kamani...

Ta karasa maganar ta na kokarin rungumar Tv.

...Tun daga kofar shiga gidanshi ya tabbatar tsohuwa ta yi mai mummunar illa. Domin layoyin da ya saka na tsari duk an kwashe su.

A guje ya afka cikin bukkarshi ya na mai kwalawa Samu kira, sai dai shurun da ya ji shi ya tabbatar mai da mai aukuwa ta afku.

Rufe idonuwansa ya yi tare da karanto wasu ɗalasimai. Ya dauki dakika goma kafin ya bude idanunshi a firgice ya yi dakin da Mahaifiyar Samu ke ciki.

Ganin ta ya yi a ƙame tamkar gunki ba shiri ya yi waje. Wata irin kara ya saki tare da zubewa a cikin kasa.

"In dai har za ki iya dawowa a matsayin ki na fatalwa ki kiyi abin da na kasheki gudun kada ki na raye kiyi shi to tabbas babu amfanin kashe ki da nayi. Tsohuwa kin shammace ni mafi munin shammata. Baƙin Hayakin da ya ga ya na tashi a garin ne ya saka shi daukar sandarshi ya yi gaba.

Dandazon mutane ne suna ta faman kona duk wasu kayan tsari da ya basu hatta maganin tsari na Macijin da ke shigowa da ya ba su kaf sun ƙone su.

Ba shakkar rashin daukar karfin ikon tsohuwa da muhimmanci da ya yi shi ya haddasa ma shi haka.

Daya daga cikin jama'arsa ne ya zube bisa guoiwowin shi

"Ya shugaba mun kona dukkan abubuwan da ka umurce mu mu kona"

Ba shiri Baushe ya sulale akan guiwowin shi tare da furtawa da karfi.

"Tsohuwaaa yanzu wasan ya fara. Ki jira haduwarmu, kin sakani dole in aikata abin da banyi niyya ba ya zame min dole in ta so da wanda na jima da boyewa."

Idanunsa ya rufe yana karanta wani abu lokaci daya bakin hadari ya rufe samaniya duhu mai tsanani gami da iska ne maai tsananin karfi ya balle ba ƙaƙƙautawa...

SAURA KADAN FREE PAGES SU KARE. WASU HAR SUN FARA BIYA ZAKU TURO DA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER

6051832238 KEYSTONE

AMINA ABUBAKAR

Meenat A. 'Yandoma

***