JIKAR BAUSHE

Page 15&16

by @meenatyandoma

J I K A R B A U S H E

©️®️ MEENAT A. YANDOMA

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

HARAMUN NE SARRAFAMIN LABARI TA KO WACE SIGA BA TARE DA IZININA BA. 'YAN YOUTUBE MA HAKA

🅿️ 15&16

...Karfin iskan ya saka mutane kwanciya tare da yi wa Rauhanin da ya bayyana Sujjada.

Tuntsurewa da dariya Baushe ya yi.

"Barka da sake dawowa a karo na biyu ya kai wannan Rauhanin"

Sanye ya ke da bakaken kaya a cikin suffar namiji, fuskarshi rufe da bakin mayafi.

"Ko da sau dubu zaka tadoni zan zo a gareka. Domin Ni ne babban Rauhanin Mahaifinka kafin ya bar duniya. Yanzu kuma kai zamu ci gaba da yi ma aiki, me kake bukata a cikin duniyar nan zan aikata" ya karasa maganar tare da rusunawa bisa kafafunshi.

"Tsohuwa ta shammace ni. Ta yi min mummunar illa. Kafin nan da wasu kwanaki ina bukatar ka kawo min ita da rayuwarta domin girbar abin da ta shuka."

Rufe bakin Baushe guguwa mai karfi ta taso tare da ɗaukar Rauhani.

Nan fa mutane kowa ya kara rikicewa ganin wannan badakalar da ke shirin faruwa...

...Dada kuwa ihu ta ke faman rusawa ganin goshinta ya haye yai suntum.

"Zinatu abin da yaran nan ke aikatawa kenan. Ba zan cigaba da zama da su su kashe ni ba, yanzu haka jin goshina nake kamar na wata tsohuwar gof tsabar hayewa da yayi."

"ni fa abin nan daure min kai ya ke. Yanzu a ce haka za su cigaba da rayuwa tamkar wuta da ruwa? Yaya ki duba ki ga abin da suka yi da muna asibiti"

"Zinatu ashe boyemin kuka yi a asibitin ma abin da suka aikata kenan? To ku bude kunnenku da kyau ko dai ku mika wannan yarinyar wurin hukuma ko kuma ni in gudu can ba tare da kunsan in da nake ba"

Shuru Zinatu ta yi domin kanta ya gama daure wa ga me da lamarin nan.

"Dada abin da na ke so ki fahimta kacokam nauyin yarinyar nan a kanmu ya ke domin mune muka yi sanadin daukewar tunaninta riketa za mu yi har zuwa ranar da Allah zai saka ta dawo cikin hayyacinta sai mu mikata ga danginta.

Kawu Hadi ne ya amshe zancen.

"Yaya lamarin nan da abin dubawa ne. Ya kama kiyi hakuri a ga abin da Allah zai yi. Ni da babu damuwa sai ku bar mini ita a wurina domin a nan garin ku ka sameta kinga ko da zaku tafi mai yiwuwa a samu danginta."

"Alhaji a barta ina? Aa wallahi ba dai cikin gidan nan ba. Wannan ko hada ido muka yi sai naji gabana ya yi mummunar faduwa gaskiya bazan iya rayuwa da ita a cikin gidan nan ba. Sai dai ni in tafi gidanmu da yarana ita kuma ta tsaya"

"Kwantar da hankalinki Zainaba. Ai babu wanda zai bar miki ita cikin gida. Wannan yarinyar banga alamun a cikin garin nan ta ke ba, nafi tunanin daga wata duniya ta zo wannan duniyar ta mu."

Momy ce ta katse su hanyar dakawa Asim tsawa.

"Ku tsuguna ku bawa Dada hakuri"

Tsaye yayi kememe yana hade fuska.

"Bazan iya ba. Domin wannan matar bata kauna ta in ku ka kara barinta ta kirani da mugun sunan da ta saba kirana sai na bata mamaki" Samu ta karasa maganar tare da zare wa Dada ido.

Dada kuwa a tsorace ta kauda kanta gefe tana mai runtse idanuwana.

Sauran mutanen da ke cikin dakin kallon kallo aka fara yi cike da mamakin abin da ke fitowa a bakin yarinyar. Hakan na nufin tunani ta ya fara dawowa ko kuma da gaske maganar Dada ta bayyana aljana suka tsinto.

Kafin su ankara Asim ya fice Samu kuwa dakin da ke cikin falon ta shige.

"Zinatu sai na ke ga kamar yarinyar nan ba za ki iya riketa ba. Me zai hana mu kaita wurin hukuma su can sai su riketa kafin danginta su bayyana"

"Kawu! Ba zan iya bada yarinyar nan ba tana a cikin hali irin haka. In na yi haka Ubangiji sai ya kamani laifi, abin da ya fi mu nemar masu magani ita da Asim."

"To in haka ne me zai hana kafin ku tafi mu je wurin wani mai magani da na ji ana zanceshi a nesa kadan da mu."

"Kawu in dai malami ne zanje. Matsalata daya a ce ya na haɗawa da shirka"

"To a yanzu kam ba na ce ba. Ko me kenan mu bari da safe sai mu je."

Daren ranar sun raba dare suna fira kafin kowa ya nufi makwancinshi. Cikin bacci ta ji kamar tsuntsu ya fita a tagar da ke kusa da ita.

Cikin magagin bacci ta fara bude ido, karasa budesu ta yi da sauri sakamakon ganin wata ƙatuwar Mujiya ta fice daga dakin da gudu.

Kafafunta ta zuro daga saman gado sai dai fizgar kafarta aka yi da karfi aka watsota kasan gadon.

Kugunta da ya bugu ne ya sakata bude baki za tayi ihu sai dai ƙatuwar Mujiyar da ta gani a gabanta tana kara zare mata ido ne ya sakata hadiye wasu yawu.

Motsin da Momy ta fara ne ya saka Mujiyar bacewa. Ganin Dada da ta gani a kasan gadon ne ya sakata saukowa da sauri.

"Dada lafiya kuwa me ya sauko dake ƙasa a wannan tsohon dare."

Zazzare ido ta hau yi don ji ta yi ta kasa furta ainahin abinda ya faru da ita.

"Daga gado na fado, Zinatu kamani in Mike ji nake kamar mahadar kuguna ta rabe."

"Subhanallahi! " Saman gadon ta mayar da ita ta na jero mata sannu. Sai dai da mamaki ta ke kallon Dada da ta cusa kanta a karkashin fulo ta danne.

Duk ƙoƙarin Momy ganin Dada ta fito da kanta ta sha iska amma abin ya faskara don ce wa ta yi a barta yau haka take buƙatar yin baccin.

Ba yadda ta iya dole ta kyaleta tare da yi mata addu'a suka koma bacci.

Fizge-fizge ya ke cikin mawuyacin hali ya fado daga saman gadon a galabaice. Ilahirin jikinshi ya fara rikiɗa ga wani irin kamshin jini da ya ke ji ya na fitowa daga dakin da Samu ta ke.

Sulalawa ya yi cikin dakin ya na fiddo harshe. Sai dai ƙatuwar Mujiyar da ya gani saman window din dakin ce ta saka Macijin gyara shiri.

Farmakar juna suke cikin zafin Nama suke fatali da duk wasu kaya da ke cikin dakin. Shammatar Macijin ta yi tare da saka yatsun kafarta ta shure shi suka yi sama.

...Gudu suke tsalawa akan titin tamkar zasu tashi sama. Alhaji Biliya ne ya kalli yaron na shi

"Ka rage wannan gudun kamar mace na ke hangowa nesa da mu"

"Ita mace ce fa. Amma bazan tsaya ba domin a cikin tsohon daren nan ba dai mutum ba sai dai aljana. Oga jira ka ga yadda za ayi." Da mugun gudu yayi kan tsohuwar dake dogara sanda da kyar saboda tsabar tsufa.

Da ya san abin da zai faru da bai tunkaro inda ta ke ba domin kafin ya karaso inda take guguwa mai karfi ta taso tare da watsa motar can cikin jeji ta bugu da wani icce.

Kyalkyacewa da dariya tsohuwa tayi.

"A tunaninka zan bari ka cimma cikar burinka ba tare da nawa burin ya cika ba. " Sake tuntsurewa ta yi da dariya tare da bacewa.

Cikin bacci Dada ta ji kamar mutum a kanta. A firgice ta bude idanu tana mai ja da baya

Cikin firgice hannunta na kyarma ta nuna ta "Tsohuwa! Da ma kina nan...

SAURA KADAN FREE PAGES SU KARE. WASU HAR SUN FARA BIYA ZAKU TURO DA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER

6051832238 KEYSTONE

AMINA ABUBAKAR

Meenat A. 'Yandoma

***