ƘADDARAR RAMLAH

23

by @nanadiso10

ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA ASHIRIN DA UKU

Arewabook @nanadiso10

Kullum cikin kuka nake, zuciyata cike da baƙin ciki da gajiya. Yanzu haka, ba ni jin daɗin komai a rayuwa. Wani lokacin ina ji kamar mutuwa ce kadai mafita. In bi mamata in huta da wannan wahala da azabar da nake ciki kullum.

Na zama kamar baiwa a gidanmu. Aiki kawai nake kamar wadda ba ta da wani amfani sai gyara da kwashe-kwashe. Momy na nuna min tsana sosai fiye da yadda zuciya zata iya ɗauka.

Mun gama jarabawar WAEC, yau kusan makonni uku kenan. Amma rayuwa ta ƙara tsananta. Abba kullum cikin zargi da tuhumata yake, ko motsi kawai na yi, sai Momy ta ga laifi a cikinsa.

A cikin waɗannan makonnin, na zama kamar jaka, babu kima. Na rasa komai tun da Abba ya kwace wayata. Wayar ce kaɗai nake amfani da ita don in ɗan ji daɗi a lokacin da muke jiran sakamakon jarabawar. Yanzu komai ya lalace.

Gaba ɗaya na cika da damuwa, ba kudi, ba walwala. Abokiyata Fatima ce kadai take ban 'yar tallafi ta bani kuɗin makaranta da sauransu. Amma yanzu itama ta tafi ƙasar waje gurin yayarta. Na zauna ni kaɗai, hawaye na gangarowa ba tare da ya tsaya ba...

Yaya Billy Kuwa Tsuntsuwar ƙiyayya da take ɗawainiya da zuciyar ta a kaina ta kai matakin da kalmomi ba za su iya warwarewa ba. Sau da dama na gane ta na ƙoƙarin zubamin wani abu cikin shayi ko lemo, amma Allah ya tsare ni. Duk lokacin da na lura da wani abu ba daidai ba, sai kawai na daina sha cikin hikima. Na gane cewa a hannunta babu amincewa, zuciyarta cike take da wata irin ƙiyayya mai zafi.

Ranar Juma’ar nan, ta zo da wani sabon sharri. Tace wai na satar mata dubu ɗari. Kafin a ce kwabo, gida ya rikide hayaniya ta cika ko ina! Aka nemi kuɗin nan har ƙasa, aka rasa. Duk da nasan ƙarya take, hakan bai hana Abba zafafa fushinsa akaina ba. Ya zarge ni da sata. Na tsaya gefe, zuciyata na rawar jiki, na rasa kalmar kare kaina daga abin da ban aikata ba.

Rayuwata ta cushe da ƙunci. Bana da ko sisin kwabo da zan iya siyan pant ko mai da zan shafawa jikina. Ranar da na nemi Momy tabani kudi, sai ta kalleni da raini, ta ce: “Je gurin ‘yan bariki, su ne zasu baki.” Wannan magana ta fasa zuciyata ƙiririƙi. Wace irin uwa ce ke fadi wa ‘yarta haka?

Abba kuwa sai ya mara mata baya. Ya ce tunda na fara sata, to ko naira biyar ba zai sake bani ba. Na shanye ƙuncina. Na fi kowa jin zafin yadda ya yarda da duk wata magana da ta fito daga bakin Momy. Shi kuwa bai san Momy ba kamar yadda na santa mace ce da ta kware wajen ƙirƙira da tsara sharri.

A cikin wannan duhu da zuciyata ke ciki, akwai fitila guda ɗaya da ke haskaka Shamsiyya, makociyarmu. Ita kadai ce take nuna min dan tausayawa. Watarana tana taimaka min da aikace-aikace, tana bani kwarin gwiwa. Ita ce kadai ta tabbatar min cewa har yanzu akwai wanda zuciyarsa ke da laushi a duniyar nan.

*****

Ina zaune yanzu haka cikin ɗaki, nayi tagumi kai na lulluɓe da zullumi. Gajiyata ta zarce ta jiki har cikin ƙashi na nake jin nauyi. Na gama tuka tuwo da rana, na gyara falo, na wanke kayan girki, amma har yanzu babu wani abu da ya sanya zuciyata farin ciki. Na yi iya ƙoƙarina, amma kamar ruwa ne nake shanya a dutse.

Ba komai nake nema ba ɗan nishadi kaɗan ne kawai. Ko fim ɗin Korea da na saba kallo, wanda ke saka ni dariya, ya ɗan mantar da ni da damuwa. Amma yanzu, ko ₦100 da zan biya na kalla bani da shi.

Rayuwata ta dame ni. Gidan da nake ciki kamar gidan da aka kulle albarkacin zuciya. Ina aiki kamar baiwa, amma kamar ina hasken rana a idon makaho. Na rasa wani da zan bude masa zuciyata na faɗa masa haƙiƙanin abin da ke ci min rai, abin da ke rarrafe a cikin dare yana hana ni barci.

Na tuna da Fatima. Da na saurare ta, da na rungumi salon da ta bi Na kula samari don ɗan kuɗi. Watakila da yanzu ina da ɗan abu da zan biya matsalata da shi. Amma ban iya haka ba. Na tsaya da mutunci.

Yanzu ma wani kaikayi ke damuna, wani irin zafi kamar ana cizon wuta ne a gabana. Amma bana da kuɗin shaver, ko man cream, balle in iya zuwa asibiti. Na gwada shiga ɗakin Momy jiya na zaci zan ɗauki ɗan abu, amma gashi ita ke kallona kamar baiwa da aka aje a gaba marar daraja, marar murya.

Na miƙe a hankali daga inda nake zaune, na ɗauki laptop dina, sannan na fice zuwa harabar gidanmu. Iska mai laushi na busawa fuskata, tana ɗan shafa gajiyata da salama. Idona ya sauka a kan Musa, mai aikin gidanmu, yana share ƙasa a ƙasan bishiyar mangwaro. Na nufe shi da fara’a mai launin ɗaci.

“Ina wuni Musa,” na ce masa da ƙanƙanin murya, kamar wadda ke boye wani sirri a zuciya. “Don Allah, idan zaka iya, ka taimaka ka turomin wasu fina-finan Korea masu kyau. Amma dan Allah, kada kowa ya sani. Ni da kai ne kawai.”

Musa ya tsaya, ya ɗago da murmushi mai sanyi, ya ce, “Haba Hajiya Ramlah, ba matsala kwata-kwata. Abokina ne mai turawa, ai ni ma fina-finai kawai nake karɓa, ba sai kin bada ko sisi ba.”

Na ji wata ƙara mai sanyi ta zuba a zuciyata. Na miƙa masa laptop ɗin da hannayena biyu, cikin ladabi da godiya.

Na murmusa, zuciyata ta ɗan lafa. “Nagode sosai,” na faɗa a nutse, sannan na juya na koma cikin gida, kamar wata baiwar da aka samu nata ƙaramin nishaɗin da zai dan shafe gajiyar zuciya.

A yau ba zan ji kunya ba, na faɗa wa kaina. Ko 10,000 ce, zan tambayi Momy. Komai za ta ce, ko yaya za ta yi, in har ba zan mutu ba, zan fuskance ta.

Na ɗaura ɗankwali da hanzari, Na hau saman bene kamar wadda zuciyarta ke harbawa da fatan samun ƙanƙanin jin ƙai.

Tun kafin na karasa palon, idanuwanta ta zuba min. Tana zaune kan kujera kamar sarauniyar da aka gaji da mulkinta, tana kallon tashar da babu sauti.

Lafiya? Me kike nema da rana tsaka zaki hau min sama haka?

Na tsugunna a gabanta kamar wadda ake shirin yanke wa hukunci.

“Momy…” Na daɗe kafin na iya ci gaba. Muryata na rawa kamar tana kokarin fita ba tare da izini ba. “Dan Allah, ko 10k ce kibani. Akwai kayan gyara da nake so nasiya. Wallahi gaba ɗaya jikina wari nake ji. Ga gashi...”

Sai na ji saukar wani abu mai zafi. Hannunta ya buge min baki kamar ana yanka tunani a idanuwa. Na lumshe ido da sauri, hawaye suka taru amma suka tsaya gefe da gefe.

Ubanki ya bani kudi nace? Bazan bayar ba! Ina mazan da kike bi? Je ki su baki mana! Ni bana son damuwa fa Ramlah. Kada kiga ina yi wa Bilkisu komai, ita cikakkiyar ‘yata ce. Ke kuwa? Ke ‘yar kishiya ce. Kishiya dai dai da aƙalla? Ki tashi ki farka, kin ji? Wani sai kin bi hanya irin ta Fatima sai kuɗi da ake nema cikin sharri!”

Tana magana, zuciyata na fashewa a ciki kamar madubi mai tsufa da aka jefa a ƙasa. Kowace kalma kamar tabarya ce aka zuba min a rai.

Tashi ki bani guri! Wata shegiya! Sai kiba kikeyi kin sha ne har kin manta me kika zo nema? Ko maganin ƙarin kiba kika kara siya?

Zan iya jure yunwa, zan iya jure gajiya. Amma wannan kalmomi? Su ne suka fi komai fasani.

Na daure fuska cikin kwanciyar hankali da hawaye ke bijiro min daga zuciya ba daga ido ba. Na ce

“Mama… A’a..” Na sauka da ƙasa da murya, na durƙusa na juya kamar wadda ke ficewa daga duniyar da ba ta ƙara yi mata amfani ba.

Nana hadiza

***