Chapter 005
by @jeeddah3256
TAREEQ IMAM
Na
Jeeddah Aliyu
Arewabook@jeedddah3256
005.
Cikin sauri Nana ta kauda fuskarta jikinta na wani kalar rawa, kamar an mata dole haka ta sake waigawa ta kalli Tareeq
A karo na biyu idanuwansu suka sarƙewa karkaɗa mata yatsanshi ya yi tare da yi alamar da wuyanshi da ke nuna sai na yanka ki. Wani sabon tsoronsa ne ya ƙara kamata ana kammala assembly Kowanne ɗalibi ya nufi class saɓani Tareeq da ya nemi gefen doguwar baranda ajinsu ya zauna, duka abokan rashin jinsa ba su zo ba saboda kullum late suke zuwa shima sakamakon laifi da yai wa Ummi ya sanya shi yi sammako.
Nana tana hango shi jikinta ya shiga ɓari dole ta ja ta tsaya tana kallo ɗalibai ƴan uwanta suna shiga class da tayi yunkurin nufar class sai kuma ta ji bata da kwarin gwiwa yin hakan. Tsintar kanta tayi da zubda hawaye har ta shiga danasani faɗawa mamanta abin da Tareeq yake mata, da basu kai ƙarar shi gidansu wurin umminshi ba da yanzu bata cikin wannan halin.
Komawa tai ta jingina ga pillar da ke jikin baranda ɗin ta ɓoya ta yadda Tareeq ba zai ganta ba, inda ALLAH ya taimake ta, sai ta hango Uncle Joel zai shiga ajinsu, da gudun bala'i ta nufi class tana isowa dai-dai ƙofar shiga shima Tareeq yana shirin shiga duk iskancinsa yana tsoron Uncle Joel saboda ya kware da wulaƙanta mutum a gaban class shi kuma abin da ya tsana kenan.
Yadda ya nufi class da sauri kamar zai tashi sama ga kuma Nana da ta fallo da gudu idanuwanta sun rufe sam bata lura da Tareeq ba mummunan karo suka ci. Rai ɓace ya ɗago yaga wacece ko wanene ya siyawa kansa masifa da sanyi safiya, fusatattun idanuwanshi ya sauke akan fuskar Nana wacce saura ƙiriss ta saki fitsari a uniform skirt ɗin ta. Tareeq bai yi wata-wata ba ya ɗauke ta da mugun mari yana ƙoƙarin sake ɗauke ta da wani Uncle Joel ya ƙaraso yai karaf ya riƙe mai hannun.
"Why are you slapping her?"
Cewar Uncle Joel yana kallon Tareeq yayin da Nana ta tsuguna tare da sunne fuskarta tsakanin gwuiwayinta tana rera kuka.
Cikin fusata Tareeq ya fincike hannun shi dake cikin tafin hannun Uncle Joel, cikin ƙara ji yace.
"Ask her the reason Uncle!"
Ƙoƙarin sake magana Uncle Joel ya yi amma sai Tareeq ya bi ta gefenshi ya shiga class.
"Come back here Teeri I'm not finish with you yet Teeri i say come back am warning you."
Uncle Joel bai iya fadar Tareeq ba shi ne yake kiransa da Teeri
Banza yai da uncle Joel tamkar ba dashi yake magana ba, cike da takaici Uncle Joel ya kama hannun Nana ya miƙar da ita tsaye ya shiga rarrashin ta kafin ya umarce ta da ta shiga class.
Tareeq ya zauna a permanent sit ɗin shi sai wani cin magani yake yi, Uncle Joel ya shigo shima fuskarsa babu rahama ko kaɗan ya yi pointing ɗin shi da yatsa cike da bada umarni ya ce.
"You stand up and leave my class right now."
Basarwa Tareeq ya yi tamkar bai fahimce dashi yake magana ba, hakan kuma sai ya ƙara harzuƙa Uncle Joel cikin kakkausar murya ya sake furta.
"I'm talking to you Tareeq just get out of my class or else I'll report you to the principal.
Kasancewar yasan muddin maganar ta je kunnen principal, kashinsa ya bushe dan nan take yake rubuta maka suspension letter ya tura ka gida idan aka yi suspending ɗinsa a wannan karo shine na bakwai a wannan term ɗin kuma gashi ya yiwa Daddynshi alkawari, ba zai sake laifin da za a suspending dinshi dan haka baya fatar faruwar hakan. Shiyasa ya miƙe cikin tafiyar ƙasaita mai cike da zallar izza da taƙama ya fice har ya kai ƙofar fita ya waiga ya kalli side ɗin da Nana take ya karkaɗa mata ɗan yatsanshi tare da nuna ke kuma taki ta ƙare.
"Mtsss...useless boy.
Uncle Joel ya faɗa haɗe da tsaki kana ya bi Tareeq da harara.
Tareeq yana fita ya nemi gaba da class kaɗan ya zauna, sai cika yake yana batsewa.
Har Lil-prince ya iso kusa dashi bai sani ba sai da ya dafa ƙafadarshi,sannan ya ɗago idanuwanshi da suka kaɗa suka yi jajir.
"Wane mai ƙarar kwana ne ya taɓowa kanshi our highness?"
Lil-prince ya faɗa tare da zaunawa gafda ƙugun Tareeq, shiru Tareeq ya yi sai musu-musu yake da baki tare da jan iska daga ƙofufin hancinsa. Lil-prince ya kai dubansa ta window ɗin class ɗinsu ya hango Uncle Joel yana rubutu akan whiteboard, sai kuma ya dawo da ganinsa akan Tareeq, ya ce "Ga dukkan alama ka yi halin naka shine bald head ya cillo ka waje {Suna da suke kiran Uncle Joel dashi kenan sakamakon yana da irin mugun sanƙo nan na tsakiyar kai}
"Lil na rantse da Allah sai naci uwar Nana sai nai mata tabo da ba zai taɓa gogewa nan kusa ba. Shi ma bald head ɗin da take takama dashi in naga dama sai nai sanadin da za a kore shi a school ɗinan tun ba ta ubansa bace. Amma zan kyale shi sai ranar da na rubuta last final exam ɗina, wallahi sai na fasa masa sanƙonsa kuma daga rana ya bar makarantar nan shege mummunan."
Dariya Lil-prince ya shiga babbakawa tamkar wanda aka yiwa albishir mai daɗi, tun kafin Rooney ya ƙaraso kusa dasu cikin ɗaga murya ya fara jefawa Lil-prince tambaya.
"Kai ɗan iska dariya uba me ka ke yi haka kodai yau za ta fashe ne?"
"Kai dai ƙaraso mutumina yau bald head ya dauƙo dala ba gamo, don kutumar ubanshi da sanyi safiyar nan ya ɓatawa our highness rai."
Shima Rooney yana zuwa ya nemi hagun Tareeq ya zauna suka saka shi tsakiya.
"Wai me kuma ya koma haɗa ka dashi ne Slugger?"
Rooney ya faɗa yana kallon murtuƙaƙƙiyar fuskar Tareeq, zazzafan numfashi Tareeq ya sauke kafin cikin hasala ya shiga basu labari abin da ya wakana tsakaninsa da Nana.
Ronney ya dafa kafaɗar Tareeq cikin sanyi murya ya shiga faɗar
"Gaskiya slugger ka fita harkar yarinya nan kar ta sake zuwa gidanku ta haɗa ka da Ummi, banaso rashin jituwa yai ta shiga tsakaninka da mahaifiyarka."
Kafin Tareeq yai magana Roofy Sodangi ta fito daga cikin class, tun sanda Uncle Joel ya kora Tareeq waje hankalinta yake a tashe ga baki ɗaya ta rasa natsuwarta. Sai neman hanyar take da za ta fito tazo wajensa shine ta ɗauki excuse za tai fitsari. Tana fitowa dai-dai lokaci da Tareeq yake faɗar.
"Ni fa Rooney bana tsoro duk abin da Nana za ta faɗa a gidanmu, burina kawai na haɗu da ita kaɓaɓɓe wuri nai mata wulaƙanci da za ta adana shi a shafi na tarihin rayuwarta banasan Nana ta manta dani cikin rayuwarta."
Roofy Sodangi tana zuwa ta rufe Tareeq da faɗa idanuwanta sun rufe ruff wani irin masifaffen kishi ke nuƙurƙusar zuciyarta, don gani take yi, kamar Tareeq yana son Nana ne shiyasa kodayaushe yake ƙiƙƙirar faɗa a tsakaninsu, cikin kaushin murya ta shiga faɗar
"Nana... Nana! For God sake I'm sick and tired of hearing her name coming out in to your mouth Tareeq
miyasa ba za ka iya rabuwa da yarinyar nan ba, sai yunkuri jefa kanka matsala kake. Kana da labari idan har maganar nan bald head ya kai ta a kunnen PC zai iya gayawa Daddynka ka daina gani duk abun da kayi mahaifin ka baya gani laifin ka. Ka sani wannan karon laifinka zai iya taɓa ƙima da mutunci mahaifinka.
I swear to God na gaji da zance wannan banzar Nana ɗin, sai kace ita kaɗai ne mace a whole school ɗinan."
Maganganu Roofy Sodangi ba ƙaramin ƙara baƙatawa Tareeq rai suka yi, don ji yake yi kamar ya tashi ya rufe ta da bala'in duka.
Sauke fusatattun idanuwanshi yai akan fuskarta kafin yace.
"This is my first and last warning to you ki daina yi min shisshigi da kutse a cikin almurrana ke wacece da za ki faɗa min abin da ya dace nayi."
Gani yadda Tareeq ya harzuƙa yasa Lil-prince ya shiga bubbuga kafaɗarsa "calm down abokina kada ka dauki maganar Roofy da zafi saboda tana ƙaunarka ne shiyasa bataso ka sami matsala da mahaifinka."
"Dallah ya isa Lil! ka daina goyon bayan yarinya nan ta fiye shiga abin da bai shafe ta ba. Ni dan ALLAH Ku tashi ku shiga class kada mu taru duka mu yi hasarar darasin bald head.
Tareeq ya faɗa yana harara Roofy Sodangi da ke tsaye a gabanshi.
Sosai ta ji zafin abin da yai mata dama can ita ce ke binshi shiyasa kullum cikin wulaƙanta ta yake. Ba tare da tasake furta kalma ko ɗaya ba ta juya a fusace ta koma class, Rooney har ya yi niyar magana Tareeq ya dakatar dashi "Rooney please ku tafi kawai banaso damuwa."
Sani halinsa da suka yi da saurin hawa yanzu sai rashe ya juye da mujiya faɗa ya dawo kansu, shiyasa suka tashi salu-alu.
Saida period ɗin Uncle Joel ya ƙare bai wuce remain 11 minutes ya fita ba sannan ya kira Tareeq ya dawo class kuma don tsabar yana so ya ƙuntata masa yasa yace "Any question students?"
Suka ce "No Sir!
"Okay get ready for snap test."
Kuma all questions da ya tambaya daga cikin topic ɗin da ya kammala koyar dasu ne, cikin abin da bai fi ten minutes ba ya fara faɗar "everybody drop off your pens and and get ready to submit yours papers."
Dama Tareeq a front desk yake zama saboda haka da gangan Uncle Joel ya fara ta kanshi, da ƙarfi ya finciko takarda Tareeq ya ƙurawa haɗaɗɗen handwriting ɗinshi idanu yana karanta abin da ya rubuta, yayin da Tareeq ya kauda fuskarshi yana kallon window.
Girgiza kai Uncle Joel ya yi cike da takaici ya kammala karanta test ɗin ya rasa wane irin brain ne da Tareeq ga shi da rashin ji da ƙiriniya amma kuma shine best student a school ɗin, shiyasa yawancin schoolteachers suke ɗaga mai ƙafa. Duk da baya cikin class aka yi darasin amma shegen gari gaba ɗaya ya rubuta amsa tambayoyin dai-dai. Duk yadda kaso ka ƙure shi sai dai shi ya ƙure ka yaron yana da baiwa sosai.
Uncle Joel yaga test ɗin Tareeq ya duƙulƙuleta ya cilla a dustbin, ya nufi ƙofar fita yana faɗar "see you next time students!"
Gaba ɗaya class ɗin ya hartsine da ihu saboda sun fahimci ya yi cancelling test ɗin, haka kuma ba ƙaramin daɗi yai musu ba.
During breakfast period Kowanne students ya fito domin cika cikinsa, suna nufar students dining room da aka tanadar masu domin yi breakfast.
Ƙaton dining room ne mai dauke da ƙanana dining table masu four chairs, kowanne students da kalar breakfast food ɗin yake so shi zai ci saɓanin su Tareeq da tun lokaci da suka zama senior student suka daina taking breakfast a school, shiyasa ko kallo dining room ɗin bai ishe su ba.
Can bayan premises suka zauna har zuwa lokaci Tareeq yana cin kansa duk irin musu da ya kaure a tsakanin Rooney da Sasco bai furta uffan ba sai bin su kawai yake da ido.
Roofy Sodangi kasa jure shirun nasa tayi da kan har tayi fushi dashi sai kuma fushin nata ya kasa yin tasiri, ta taso daga wurin zamanta ta dawo kusa dashi. Hannunshi ta kama a hankali take massage ɗin palm ɗinsa idanuwanshi ya ɗago ya kalleta sau ɗaya ya ɗauke fuska.
"Are you still mad with me?"
"Who the hell think you're da zan yi fushi dake?"
"Haba slugger wai miyasa kake min haka ne, wallahi nakan shiga damuwa na rasa walwala ta a duk sanda ranka yake ɓace, ka yi haƙuri kadaina fushi nan ka saki ranka Please."
"Mtsss! ke dai ƙaramar ƙwaƙwalwa ce dake Roofy, duk zama na da ke kin kasa fahimtar wanene, ni. Nan da ki ka ganni ko mutane masu muhimmanci a rayuwata bana da lokaci ɓatawa nai fushi dasu balle ke, saboda haka karki nemi ki takura min."
Sosai Roofy Sodangi ta ji haushi maganganun shi, ranta ɓace ta miƙe gaba ɗaya ta bar wuri ta nemi can nesa da su ta zauna tana jira breakfast period ya ƙare ta koma class.
Kamar daga sama Tareeq ya ji ta bayansa an kira sunansa, kamar kuma muryar Nana, kamar wanda ya tsorata haka ya waigo idanuwanshi suka sarƙe cikin nata, tsoronshi ya hango shimfiɗe a cikin ƙwayar idanunta. Zubur ya miƙe tsaye.
"Ubanwa ya kawo ki wajena wa ya ce ki ambaci sunana?"
Tareeq ya ƙarashe magana yana wani dakawa Nana tsawa.
Tsananin tsorata da tayi yasa ta dafe kunnuwanta da hannuwanta biyu tare da runtse idanuwa.
#TareeqImam
#RoofySodangi
#NanaBashir
#***