Page 17&18
J I K A R B A U S H E
©️®️ MEENAT A. YANDOMA
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
HARAMUN NE SARRAFAMIN LABARI TA KO WACE SIGA BA TARE DA IZININA BA. 'YAN YOUTUBE MA HAKA
🅿️ 17&18
..."Kinyi mamakin gani na ko? Ko da ya ke babu mamaki domin Baushe ya zata in ya kashe ni bazan samu damar sake dawowa duniyar nan ba. Sai dai ya manya kashe Maciji ne bai sare kanshi ba."
Dada gwauron numfashi ta sauke cike da mabayyanin tashin hankali.
"Kina nufin har yanzu a matsayin fatalwa kike"
Dada ta jefa mata tambayar.
Murmushi da ke ƙara fito da ainahin muninta ta yi kafin ta ɗora da fadar.
"Mu aje wannan maganar a gefe. Ina labarin Asim?"
Shuru Dada ta yi
"Asim dai ya na nan lamuran sun sake cabewa fiye da lokacin baya. Idanuwanshi suna nan suna sake rikiɗa tamkar na gawurtaccen ma Maciji, ni yanzu babbar damuwata Zinatu ta tsinto wata yarinya wadda Indai suna a wuri ita da Asim to tamkar ruwa da wuta haka suke"
Abin da Dada ta fada shi ya saka annurin da ke kan fuskar Tsohuwa ya dauke.
"Akwai matsala! Ko mai kika ga zai faru kada kiyi gardama ko musu domin na hango gagarumar matsala ta tunkaro mu. Akwai yiyuwar in na tafi ba zaki sake gani na a nan kusa ba domin..."
Wani baƙin hayaƙi da ya fara cika ɗakin ne ya saka su biyun firgita musamman Tsohuwa domin ta san Rauhani ne zai bayyana.
Tsohuwa dariyar mugunta ta yi ganin ya bayyana cikin bakar suffar da ya saba bayyana tun a lokacin rayuwarta.
Dada tun bayan arba da shi ta sulale kasa ta suma.
"Barka da sake haduwarmu a karo na biyu, ya kai babban hadimin Baushe"
"Ki biyo bayana cikin salama ko kuma in tafi da ke ta karfin tsiya"
Dariya Tsohuwa ta ɓaɓɓake da ita.
"Yaro yaro ne. Kai a yanzu ka ga na maka kama da wadda zata bi umurnin ku? Daga kai har Baushen a yanzu na muku zarra"
Ganin tsohuwa na shirin bata mai lokaci da mugun nufi yayo. Ita ma din kanshi ta yi wata irin iska mai karfi ce ta kwashesu ta bace da su.
Mummunan mafarkin da Momy ta yi da su Asim ne ya sakata tashi a firgice bakinta dauke da sunan Allah. Ganin lokacin Asuba yayi alwallah ta yi tare da tayar da sallah.
Sai dai har ta gama Dada Bata farka daga barci ba. Buga kafarta ta ke a hankali tare da ambata sunanta.
A gigice ta bude ido tana fadar
"Ina ta ke. Ta na ina"
"Wace ce ki ke nema "
Ce War Momy.
Shuru Dada ta yi domin tafi tunanin abin da ya faru da ita a mafarki ne.
Ajiyar zuciya ta sauke ta na sake ƙarewa dakin kallo.
Da kyar Momy ta shawo kanta ta amince zata Shiga toilet ta yo alwallah Shi ma din CE wa ta yi ita fa sam ba zata kulle ba.
Tun bayan tashinta gabanta ke matsananciyar faduwa jikinta ya yi wani kala tamkar bata lafiya.
Kamar yadda ta saba dakin Asim ta shiga don ta tayar da shi ya yi sallah. Sai dai wayam! Babu kowa, a dan firgice ta dubi toilet nan dinma hakan take.
Ta na kokarin fita daga dakin ta jiyo motsi a bayanta. Da sauri ta juyo tare da yin tozali da Asim fuskar nan a murtuke. Jikinshi duk jar ƙasa.
"Daga ina kake, me ye a jikin ka haka faduwa kayi." Shuru ya yi ba tare da ya bata amsa ba sai na gani ta yi ya faɗa a gado yayi ruf da ciki.
"Da kai na ke magana kayi ma sallah kuwa. Ka tashi ina magana ka kwanta"
Ko alamar motsi bai yi ba bare ta saka ran zai bata amsa.
Da karfi ta finciko shi ya fuskance ta.
"Ki fita in na ji sauki zan fito" ya faɗa da karfi idanunshi na rikiɗa.
A dan firgice Momy ta ja da baya, domin wannan ne karo na farko da ta fara ganin haka a tattare da shi.
Kai tsaye dakin da Samu ta ke ta nufa duk da a zaman da suka yi da ita ta fahimci yarinyar ba musulma ba ce. Domin lokuta da dama in suna sallah zata kafesu da ido har sai sun gama. In an ce ta yi sai ta ce ita bata iya ba
Tura kofar dakin tayi a dan firgice ganin itama Samun jikinta duk jar kasa ita hada ciwo a wuyanta. Ga kuma dakin anyi fatali da kayayyaki.
Tambayar duniya tayi mata amma shuru sai ma wani nishi da take yi kadan-kadan.
Ganin halin da Samu ke ciki firgita Momy ta yi ta kira Luba sai dai lokacin da suka dawo wani irin bakin amai suka taras tana yi.
Zafi jikinta ya dauka ciwon da ke wuyanta ya bace bat.
Hannun Momy ta damƙa tare da fara wata irin kyarma idanunta suka kalli sama, ita dai Luba ganin abin da ke faruwa da gudu ta fita daga dakin.
Momy kuwa addu'a ta ke yi domin kaf tsoron da ke a ranta ya fita. Gashin da taga ya na fitowa a jikin Samu ne ya sakata daskarewa a inda take, a hankali suffarta ta cigaba da komawa ƙatuwar Mujiya.
Ja da baya Momy ta yi hawaye na wanke fuskarta tunawa da mafarkin da ta yi da dare.
"Da gaske ne abinda na gani. Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun! Kenan da gaske shi ma Asim Maciji ne."
Sulalewa ta yi a kasa tare da dafe kanta da ta ji ya na barazanar tarwatsewa.
Ji da tayi su Kawu sun nufo dakin ya sakata saurin mikewa tare da fita daga waje ta rufe dakin.
"Zinatu ko asibiti za mu wuce da ita"
Gabanta ne ya yanke ya fadi
"Kawu da hakuri muka yi. Domin ta samu bacci"
Ta karasa maganar muryarta na kyarma kamar wanda ya yi ma Sarki karya.
"Bacci kuma Zinatu! Shi kukan da kike yi na mene ne?"
"Kuka kuma kawu? Wani kwaro ne ya fadamin ido shi yasa ka ga hawaye na bin kumatuna.
Kallon tuhuma Luba ta yi mata domin kaf maganganunta babu kamshin gaskiya a tattare da su.
Sai sai babu yadda ta iya haka suka hakura dole kowa ya bar wurin tare da ce war in gari ya kara yin haske za su je wuriMalam.
Nannauyar ajiyar zuciya Zinatu ta sauke tare da share hawayen da ke fuskarta.
"Da yardar Ubangiji ba wanda zai san halin da ku ke ciki. Zan boye wannan Sirrin tare da nemar muku magani iyakar karfina."
Sai da ta tabbatar da ta kulle dakin kafin ta bar wurin...
...Su Alhaji Biliya kuwa sai bude idonsu suka yi suka tsinci kansu a asibiti.
Jikinshi ya ke kara dubawa domin tabbarwa shin da gaske hatsarin suka yi.
"Ba shakka in ban samo yarinyar nan ba duk wani sirri da tsarina sai sun wargaje"
"Ranka shi dade magana kake ne"
Likitan da ke gefen gadon shi ya faɗa.
Domin kowa ya san Alhaji Biliya dan takarar gwamna.
Saurin rufe bakinshi ya yi ganin maganar da yayi a boye ta fito fili.
Ganin ya daina jin komai ya saka shi tambayar likita zai sallame su.
Buguwar da jikinsu yayi ita ce abin damuwa. Ganin sun matsa ya saka shi yadda su tafi amma da sharadin duk rana zasu dawo ganin likita musamman Alhaji Biliya da kafarshi ta bugu har dingishi ya ke.
Ji da yayi gabanshi ya yi mummunar faduwa hakan ke tabbatar ma shi wani na gaf da shiga dakinshi na sirri.
A gaggauce suka tsaida abin hawa.
Kofar dakin Suwaiba ta yi tsaye zuciyarta na sake gargadi ta akan kashedin da Alhaji Biliya yayi mata game da kusantar dakin ba ma ta shiga ba.
Wata zuciyar ce ta hau zugata akan ta shiga ta gane ma idonsa abin da ya ke boyewa tsawon shekaru.
Da gudu ta karasa shigewa dakin ganin gawar Mahaifiyarta daskare a cikin wani glass. Da gudu ta karasa shigewa dakin
Gefen mahaifiyarta kuma tozali ta yi da yaranta da suka jima da mutuwa su biyu.
Ihu Suwaiba ta saki tare da durkushewa a wurin. Motsin da ta ji a bayanta ne ya sakata saurin mikewa.
A fusace ya kalleta.
"Yau ke ce a dakin da na yi miki iyaka da kusantar hanyar shi ma bare kuma ki shiga"
Wani ruwa da ke a gefenshi watsa mata lokaci daya ta daskare tamkar gunki..
SAURA KADAN FREE PAGES SU KARE. WASU HAR SUN FARA BIYA ZAKU TURO DA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER
6051832238 KEYSTONE
AMINA ABUBAKAR
Meenat A. 'Yandoma
***