JIKAR BAUSHE

Page 19&20

by @meenatyandoma

J I K A R B A U S H E

©️®️ MEENAT A. YANDOMA

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

HARAMUN NE SARRAFAMIN LABARI TA KO WACE SIGA BA TARE DA IZININA BA. 'YAN YOUTUBE MA HAKA

GARABASA! GARABASA!! GARABASA!!!

Ina kuke ma'abota son gwangwaje yaransu da Kaya wadanda suka amsa sunan su kai har ma da na manya maza da mata? To ku matso kusa, ku matso ku sa na ce.

Kuna da labarin UMMU AYMAAN'S COLLOCATION? ku matso kusa domin jin garabasar data zo maku da ita na Bononzar da ta ke a halin yanzu. Ta shirya wannan Bononzar ne na tsawon kwana hudu rak! Sakamakon Children's Day da Ake.

Akwai Riga, wando, top, stark, plain T-shirt. Duk abubuwan nan da na lissafo na yara da manya ne. A 1500 kacal! Shin me kuke jira ku hanzarta domin samun wannan garabasa kafin ta kare.

Ga Number da zaku sameta ***. Unguwa uku layin maifata Zaria road.

LAST FREE PAGE

🅿️ 19&20

...Dariya Alhaji Biliya ya ke ce ta ita. Sai da ya gama mai isarsa kafin ya turbube fuska tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa.

"Kaf cikin matan da na yi na fi kaunarki, amma tunda kika nemi ki tona min asiri barin duniyarki shi ya fi komai sauki."

Sai dai duk iyakar kokarin shi na ganin ya dauki rayuwarta abu ya ci tura.

Guminn da ke tsattsafo masa ne ya saka hannu tare da sharce shi. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da jin gabansa na tsananta faduwa.

"Ko dai ita ma tana da wani mashahurin Boka ne, to in ma ta na da shi da bakinta ba zai rufe ba tunda har na kashe mata uwa da kaf yaran da ta haifa. " Kanshi ne ya sake ƙullewa domin ya san in har bai kashe ta ba wata rana zata iya dawowa hayyacinsa ta zama silar tonon asirin shi.

Da sauri ya baro gidan jami'an tsaron shi suka take mai baya tare da shigewa cikin motoci su.

...Kowa ya shirya in banda mutum biyu. Luba da Dada, juyin duniya anyi amma sam ta ki shirya wa ce wa ta yi babu inda zata je su je su kadai in sun dawo su bata labarin yadda ta kaya.

Luba ma lakafewa ta yi akan ba bu inda zata je tsoron samu ta ke. Dole Alhaji Hadi da Zinatu ne tare da marasa lafiyar guda biyu suka dauki hanya.

Momy da Samu su ne a bayan mota. In da Kawu Hadi da Asim ke a gaba. Tunda suka fara tafiyar gaban Momy ke tsananta faduwa.

Musamman da duk gefen da ta kalla sai ta ga wata mummunar tsohuwa ta na mata murmushi. Addu'a ta tsananta yi musamman da ta tuna abubuwan da ta gani safiyar yau.

Lura ta yi Samu kamar bacci ta ke ji.

"Kina jin bacci ne?"

Kanta ta daga alamun eh

A cinyar Momyn ta kwanta tare da rufe idonta. Karaf idanuwan Momy suka sauka akan tambarin da ke a wuyanta.

Hannu ta kai tare da shafarshi sai dai da sauri ta kira sunan Allah sakamakon zafin da ta ji tamkar ta kama rushin wuta.

Burkin da ta ji an taka ne ya sakata kallon Kawu Hadi.

Motar ce ta tsaya cak dubawar duniya sunyi ba su ga wata matsala ba.

"Ga faranku dai"

Suka tsinkayo Muryar dattijuwa na fada.

Juyowar da za su yi gaban Momy ne ya yanke ya fadi. Nuna ta tayi da yatsanta da ke faman kyarma

"Ke ce? Me ya kawoki nan?"

Dariya Tsohuwa ta yi

"Ya za ki tambayi mutum a gidan shi. Ai ni nan gidana ne, kamar kuna neman taimako ko?"

"Saurin girgiza kai Momy ta yi"

Dariya tsohuwa ta yi

"Haba diyata! Boye min za kiyi bayan nasan motarku ce ta samu matsala"

Jin abin da tsohuwa ta fada gaban Momy kara faduwa ya yi. Ita dai har ga Allah ba ta yarda da matar nan ba.

Abin da ya matukar ba shi mamaki shi ne kamar yadda ta ce ya shiga ya tayar da motar zata tashi haka kuwa ta faru.

Godiya ya hau jero mata tare da shigewa mota. Sai dai Momy na Gaf da shiga Mota ta ji an damki hannunta.

"Baki sanni ba. Amma ni nasan ke wace ce kai hatta tarihinki duk na sani. Wannan zoben da na saka mijii a tafin hanunki kada ki kuskura ki rabu da shi, domin ku duka rayuwarku na cikin hatsari. Ki tabbatar kin zauna tare da yaran nan su duka biyun a duk inda za su kasance. Barinsu su biyu kadai zai haifar da abin da ba zai ma kowa dadi ba."

Momy na shirin magana ta ji Kawu Hadi na kiranta ta shigo su tafi. Juyawar da zata yi har tsohuwa ta bace.

Jiki a sanyaye ta shiga motar hankali a tashe domin tasan wannan matar ba mutum ba ce.

Zoben ta ke karewa kallo zuciyarta na gargadinta da kada ta kuskura ta saka zoben a hannunta. Cikin aljihun rigarta ta jefa zoben tare da lulawa duniyar tunani.

Abin da ba su sani ba shi ne tun fitowarsu daga gida wata baƙar inuwa ke binsu a baya. Zoben da ke jikin Momy shi ya saka inuwata ta dan ja baya kadan amma duk da haka a biye ta ke da su.

Ba su tsaya ko ina ba sai a kauyen Yalwa. Kai tsaye gidan malamin suka nufa sai dai sub taras da mutane masu yawan gaske a kofar gidanshi don haka dole suka jira sai da ya sallame su kafin ya ce a shiga da su ciki.

Momy ce ta yi mai bayani daga farko har karshe. Amma bata faɗamai ce War Asim da Samu suna rikiɗa ba.

Wani daki ya shiga ya fi mintinan sha biyar kafin ya fito jikinshi jagaf da zufa.

Kallonsu ya yi tare da girgiza kai ya kalli kasa. An dauki lokaci kafin ya dago.

"Firgici da tashin hankali. Su ne abubuwan da ke Gaf da riskarku. Abin da kika fada har ma da wanda kika boye na ga komai, ki sani warakar su ta na a tare junansu."

Da mamaki Momy ke kallonshi don bata fahimci inda maganarsa ta dosa ba.

"Za ki iya bari a Daura masu aure a nan take" ba Momy kadai ba hatta Kawu Hadi sai da ya kadu da jin abin da Malamin ya faɗa.

"Aure kuma"

Momy ta fada a rikice.

"Kwarai kuwa. Domin ta hanyar aure ne kaɗai na hango mafitar matsaltsalonsu, akwai abubuwa da dama dake tafe a nan gaba. Amma ba za ki ji su a bakina ba, lokaci ne zai bayyana miki komai."

"Malam yarinyar nan da ba mu san wace ce ita ba, ga dukkan binciken da muka yi ita ba musulma ba ce ta ya zamu hada jininmu da jinin wanda ba mu san Asalinsu ba. Ka yi hakuri Malam wannan kuskuren da kake so mu aikata irinshi ne muka aikata a can shekarun baya. Ba za mu sake aikata irinshi ba Malam."

Kawu Hadi ya fada cikin matsananciyar damuwa.

Murmushi Malamin ya yi.

"Ba zan tilasta maku ku aikata abin da ba ku yi niyya ba. Amma ku sani muddun baku yarda da abin da na fada ba da matukar wahala ku duka ku koma gida a raye, domin abin da na ke gani ba ku ganin shi."

"Inna lillahi wa Inna lillahi rajiun!"

Ita ce kalmar da suke maimaita wa.

"Malaman ni ce na haifi Asim. Na yarda na amince a Daura auren nan, domin ce ton rayuka akwai bukatar sadaukarwa." Ta kara maganar tare da fashewa da kuka.

"Zinatu ki dai yi tunani. Kada idanunki su rufe ki sake sakamu a cikin wata matsalar bayan wadda muke a cikinta bata warware ba"

"Kawu ya zanyi. Na dauki ƙaddara kawu domin nasan Allah ba zai ɗorawa bawa abin da ba zai iya ba. Kawu ka taimake ni a Daura auren nan "

Tausayinta ne ya kullube Kawu Hadi ganin irin kukan da ta ke cizga tamkar ranta zai fita.

A wannan rana a daidai wannan lokaci aka daura auren Asim da Samu ba tare da sanin dayansu ba.

Asim sai gani yayi Momy ta fito ta na kuka.

Hannun shi ta kamo ta haɗa da na Samu da ke faman rarraba ido.

"Kaddara tamkar hawainiya ce a koda yaushe canza launi take. Sannan duk abin da Allah ya yi daidai ne, ban santa ba ban san wace ce ita ba ko an tambaye ni bansan su waye danginta ba. Amma a halin yanzu da karfin guiwa zance mune danginta domin maganar nan da na ke Samu ta zama matarka"

Tamkar rugugin aradu haka ya ji saukar maganar. Ja da baya yayi tare da nuna ta da yatsa

"Wannan halittar. Momy wannan halittar kika aura Mani, yarinyar da na tsana fiye da kowa ko inuwa daya ba mu haɗawa Momy ki farka daga mafarkin da ki ke yi domin da in aureta Kara in ƙarasa rayuwata ba aure. Shin kin manta duk wadda na aura mutuwa ta ke me ya sa za a aura min wata ba tare da sani na ba. In dai har ta tabbata auramin ita kuka yi a nan ba sai anje ko ina ba zan mata saki uku..."

Marin da Momy ta dauke shi da shi ne ya saka jin shi da ganin shi daukewa na wucin gadi.

"Karya ka ke Asim. Indai Har ƙaddara zata hada aurena da na ubanka to kuwa kai ma a yau ta haɗa na ka auren. Datse wannan aure daidai ya ke da datse duk wata alaƙa da ke a tsakaninmu domin kuwa zan sallama wa duniya kai"

"Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun! Zinatu wace irin magana ce wannan?"

Cikin kuka ta ci gaba da magana.

"Kawu in dai har zai bijiremin a yau ba sai gobe ba zan sallama wa duniya Asim"

Kafafunshi kasa daukarshi suka yi ba shiri yayi zaman 'yan bori, tare da dafe kanshi da ya ke jin maganganun Momy na masa amsa kuwwa.

Samu kuwa numfashinta ne ta ji ya na kokarin daukewa ba shiri ta fado a jikin Momy da ke kusa da ita.

Salatin suka fara ganin ta na kokarin suma da taimakon malamin ta dawo cikin hayyacinta lokaci daya hawaye suka balle mata.

Tausayinta ne ya ƙara kama Momy ita ma hawayen ta ke yi. Bayanin da Malamin ya yi masu shi ya ƙara tayar da hankalin Momy domin ya shaida mata su tsammaci zuwan bakon al'amari a kowane lokaci. Sannan karfin kiyayyar da ke tsakaninsu ta ragu amma kadan.

Tafiya suke a cikin motar kowa da abin da ya ke sakawa musamman Momy ta jima da lulawa a wata duniyar.

Ƙatuwar barewar da ta gifta masu ce ta saka kawo Hadi rikicewa ya taka birki. Sai dai wani baƙin duhu ne ya wanzu a cikin motar ko tafin hannunka baka iya gani.

Kalmar shahada Momy ta yi da karfi daga nan sautin kowa yayi tsit!

WAYE BAUSHE?

WAYE AINAHIN MAHAIFIN ASIM?

DA GASKE ASIM MUTUM NE KO KUMA ALJANI?

WACECE SAMU?

WACECE TSOHUWA? ME YE ALAKARTA DA BAUSHE?

INA LABARIN RAUHANIN DA BAUSHE YA TURO YA FARAUTO MA SHI TSOHUWA?

SU WAYE TAGWAYEN DA KOWA BAI SON AMBACI SUNANSU?

ME YE ALAKAR TSOHUWA DA DADA?

SU WAYE DANGIN MAHAIFIN ASIM?

AUREN ASIM DA SAMU ZAI HAIFAR DA ƊA MAI IDO?

WACE INUWA CE KE BIBIYAR SU MOMY A KAN HANYA?

ME YA FARU DA SU MOMY A KAN HANYARSU TA KOMOWA GIDA

ALHAJI BILIYA ZAI CIKA BURINSHI KO KUMA ASIRI SHI NE ZAI TO NU?

DUK WADANNAN TAMBAYOYIN AMSARSU NA GA WANDA YA BIYA 500

DOMIN SAMUN WADAN NAN AMSOSHIN ZAKU TURO DA 500 DINKU TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN

6051832238 KEYSTONE

AMINA ABUBAKAR

Meenat A. 'Yandoma

***

***