aABI NA TARA
by @ummasghar
SAFEENATU
NA
UMM ASGHAR
Arewa books @UmmAsghar
BABI NA TARA
Cikin sati ɗaya muka yi wata irin shaƙuwa da Albi, soyayya yake gwada mini kamar babu gobe. Yadda yake tarairayata yana tattalina tamkar baya da wani abu mai muhimmanci bayan hidimata. Ko 'uhm' nace yanzun nan zai fara tambayar abinda nake so ko abinda yake damuna har sai ya tabbatar bani da wata damuwa kafin yake samun nutsuwa. Nayi wani irin sabo da shi ta yadda ko nan da can bana so ya matsa ya bar ni. Amarci muke yi mai daɗi abun mu. Kullum daga wajen Umma ake kawo mana abinci don haka ba wani aiki nake yi ba mai yawa sai gyaran gida kawai shima kuma tare muke yi, baya taɓa bari nayi aiki ni kaɗai sai yace to miye amfanin shi da zai zauna sai dai ni nayi ta aiki ba zai tayani ba.
Kullum tare muke shiga mu gaishe da Umma, kullum kuma irin karɓa ɗaya take yi mini. Babu wani sakin fuska, babu ja a jiki. Hatta ƙannen shi ƴammata Suhaila da Ummi ban wani samu fuska daga garesu ba. Kullum daga gaisuwa babu abinda yake ƙara haɗani dasu, basu taɓa shigowa wurina ba shi yasa abun yake damuna a ƙasan rai duk da ban taɓa fitowa nayi maganar da kowa ba.
Wani halina guda ɗaya da baku sani ba shine ina da zurfin ciki sosai, yana matuƙar wahala na iya fitowa na faɗi abu idan yana damuna sai dai yayi ta ci na a zuciya.
Ranar da muka yi sati ɗaya a ranar na fara girki, na shiga kitchen na fara fito da kayayyakin da zan yi amfani dasu ya shigo, sai ji nayi ya rungumoni ta baya. Luf nayi na kwanta a ƙirjin shi don zuwa yanzu nima na saba da yawan sakani a jikin shi da yake yi.
"Me zaki dafa mana ne?"
Kallon kayan dana fito dasu nayi nace "arabian rice zan yi da grilled chicken sai fried veggies."
"Hmm.. Delicious. Please ki saka girkin da Umma."
"To," nace na ƙara ɗebo kayayyakin girkin yadda zai isheni. Yana maƙale dani duk inda na ɗauke ƙafa nan yake ajiye tashi, a haka muka yi girkin muka gama. Na shirya namu akan table sai nasu Umma na ɗauko food warmers masu kyau na zuba a ciki. Shi ya ɗauka yace zai kai mata ni kuma na ƙarasa gyara wurin.
Ɗaki na tafi nayi wanka, kwalliya nayi cikin ƙananun kaya riga da skirt. Rigar body hug ce sai skirt ɗin three quarter daya bi jikina ya zauna. Sosai kayan suka yi mini kyau ni kaina sai ƙara kallon kaina nake yi a madubi ina yabawa bare kuma ace wanda aka yi kwalliyar domin shi ya gani, ai nasan babu zama lafiya. Hijab na saka wanda ya kai mini har ƙasa ya rufe mini ƙafafu, sallah nayi don lokacin ta yayi, ina ga Albi ma masallaci ya wuce shi yasa ya jima bai shigo ba.
Parlour na koma na zauna ina jiran shi yazo muci abinci don sosai nake jin yunwa kasancewar ba wani breakfast ɗin kirki muka yi ba. Wayata na ɗauka ina yin game kafin ya shigo.
Shiru-shiru Albi zai dawo bai shigo ba, abun ya bani mamaki don bai cika fita ya daɗe bai dawo ba ko zuwa cikin gidan su ne kuwa. Wayata na ɗauka na kira shi sai dai naji tana ringing a kusa dani. Kenan bai fita da wayar ba. Yunwa nake ji amma bazan iya cin abinci babu shi ba, a cikin ƴan kwanakin nan na riga nayi sabo da cin abinci tare dashi bana jin ko na zuba zan iya zama naci. Ajiye wayar nayi na zame na kwanta ina jiran shigowar shi. Ban san lokacin da bacci ya ɗaukeni ba sai dai ji nayi ana tashina.
Ina buɗe ido ya sauka a cikin nashi.
"Tashi kiyi sallah, la'asar tayi."
Tashi nayi zaune ina jin jikina duk babu daɗi, baccin da nayi sosai ya kashe mini jiki. Ban yi mishi magana ba na wuce ɗaki saboda ban cika son yin magana daga tashi na daga bacci ba tare da wanke bakina ba. Brushing nayi sannan na ɗauro alwala na fito, yana zaune a bakin gado na same shi. Duk inda nayi yana bina da ido, hijab na ɗauka nayi sallar, sai da na idar nayi dukkan addu'o'i na sannan na juya na kalle shi a shagwaɓe nace
"Daga zuwa kaiwa Umma abinci kaje kayi zamanka Albi bayan ina nan ina ta jiranka ka dawo muci abinci, a haka yunwa tasa ni baccin dole ban sani ba."
Tasowa yayi ya dawo inda nake, tsugunnawa yayi a gabana ya tallabo fuskata cikin hannun shi yace
"Ayya, sorry baby ban san kina jin yunwa ba da ban zauna ba. Hira na tsaya muka yi da Umma daga nan na tayata cin abincin, kin san in har ina gida to tare muke cin abinci tun ins yaro in dai ba tana tare da Baba ba shine nake ci ni kaɗai, yanzu kuma dana sameki sai nayi mata tawaye ko." Ya ƙarashe maganar yana mai ɗage mini gyara.
Shiru nayi ban tanka shi ba.
Cigaba yayi da cewa "tashi muje na tayaki ci, kin san duk da naci abinci wannan ba zai hanani ƙarawa ba in har tare dake ne."
Duk da magamar da yayi cike da lallashi ne sai da naji zuciyata ta ɗan sosu, kenan shi har zai iya cin abinci a wani wuri ba tare dani ba, ni ina nan duk da yunwar da nake ji na kasa cin ko kaɗan ne saboda sabon da yayi mini na cin abimci tare dashi. Kamo hannuna yayi ya ɗaga ni, ina maƙale a cikin jikin shi muka ƙarasa wajen cin abincin. Shi yayi serving ɗin mu yasa spoon yana feeding ɗina. Da gaske yaci abinci don kuwa ba wani ci yake yi ba alamun a ƙoshe yake.
Duk da yunwar da nake ji sai naji abincin ya isheni saboda kawai bana cikin daɗin zuciya. Kawar da fuskata nayi daga miƙo mini abincin da yake yi.
"Karɓa mana," yace yana ƙara nufar bakina da spoon ɗin
Girgiza kaina nayi nace "na ƙoshi."
Kallon plate ɗin yayi ya kalleni yace
"Har me kika ci da zaki ce kin ƙoshi."
"Allah da gaske nake yi, ya ishe ni."
Ajiye spoon ɗin yayi yana kallona sai kuma yace "ko dai fushi kika yi don ban dawo mun ci abincin ba."
Wai sai naji hawaye na neman cika mini ido, ƙoƙari nayi sosai wajen kawar da kukan dake neman taho mini.
Hannuna ya riƙo cikin nashi yace "kiyi haƙuri, ba zai yiwu Umma tace na zauna muci abinci nace mata a'a ba shi yasa naci abincin a wajenta duk da nasan kina nan kina jirana."
Kunya ce ta kamani jin yadda yake ta bani haƙuri.
Murya a sanyaye nace mishi "ni ba fushi nake yi ba kawai dai ji nayi cikina ya cushe shi yasa nace maka na ƙoshi."
Ajiyar zuciya ya sauke yace "to tashi mu mayar da kayan kitchen ma ƙara ci da dare ba sai kin yi wani girkin ba."
Tashi nayi na taya shi muka tattare kwanukan muka kai kitchen, sai da nayi wanke-wanken kayan da muka ɓata kafin muka koma parlour muka shiririce akan kujera muna zuba soyayya, tuni na manta da abinda ya faru ɗazu da har ya sosa mini zuciya.
Washegari ma lokacin dana shiga kitchen ɗora girkin rana Albi yace nayi da Umma. Kallon shi nayi kamar nace "yau ma?" Sai dai nayi shiru kada yayi tunanin wani abu, na dafa abincin da ɗan dama kamar jiya. Wasu warmers ɗin na ɗauko na zuba mata abincin duk da ba'a dawo mini da waɗanda na zuba mata a ciki jiya ba.
Yau bai fita kai mata abincin ba sai kiran ƙanwarshi Suhaila da yayi a waya yace tazo ta ɗauki abinci ta kaiwa Umma. Ina lura da yarinyar nan har tazo ta tafi ko kallona bata yi ba bare nasa rai da zata gaishe ni.
Muna zaune muna cin abinci sai ga Suhailar ta dawo. "Yaya wai kazo inji Umma."
Ko gama rufe bakinta bata yi ba ya ajiye spoon ɗin hannun shi ya miƙe tsaye, kallona yayi yace
"Ina zuwa baby, bari naje naji kiran da Umma take yi mini."
"Ok to," kawai nace na cigaba da cin abincin, da yake ma saura kaɗan mu ƙarasa cinyewa. Bayan na gama na tashi na tattare kwanukan na kai kitchen, sai naji bazan iya yin wanke-wanke ba a lokacin don haka na dawo parlour na zauna ina kallo.
.
Tunda ya fita amsa kiran Umma bai dawo ba sai bayan la'asar. Daga wannan ranar Albi ya sharɗanta mini yin girki da Umma, babu ja'inja na amsa mishi da to ganin ba wani zama zamu yi mai yawa ba zamu koma Lagos inda yake aiki shi yasa ma banji wata damuwa ba don yace na dinga yin girki da ita, a ganina na ɗan lokaci ne kuma kyautatawa ce idan nayi mata hakan. Abinda dai ya dameni shine yawan aikowa da take yi a kira shi idan ya tafi kuma sai ya daɗe bai shigo ba. Ban dai taɓa nuna mishi damuwata ba amma magana ta gaskiya abun nan ya dameni......
UmmAsghar