SAFEENATU

BABI NA GOMA

by @ummasghar

SAFEENATU

NA

UMM ASGHAR

Arewa books @UmmAsghar

BABI NA GOMA

Ranar da muka cika sati biyu da aure na samu baƙuncin Khadijah. It was an unexpected visit saboda a safiyar ranar ma mun yi waya da ita amma bata faɗa mini zata zo ba. A lokacin ina kwance akan doguwar kujera nayi pillow da cinyar Albi shi kuma yana ta jagwalgwala mini gashi wai kitso zai yi mini. Ƙarar door bell muka ji, shi ya tashi yaje ya buɗe. Ina ji suna gaisawa na miƙe zaune saboda muryarta da naji. Tana shigowa na tashi da sauri na tafi na rungumeta ina murna. Daga ni har ita murnar muke yi kamar waɗanda suka daɗe basu haɗu ba.

Zaunar da ita nayi akan kujera ina cewa "Khady irin wannan surprise haka, bafa ki faɗa mini zaki zo ba bayan ko ɗazu sai da muka yi magana a waya.

Dariya tayi tace " So nake nayi surprising ɗin ki ne shi yasa."

"Ai kam dai kin yi surprising ɗina kuma kin kyauta don kuwa nayi missing ɗin ki fiye da yadda ba kya zato."

Shigowa ciki Albi yayi suka gaisa har yana tambayarta ina ta baro Sadiq muka ganta ita kaɗai, tace shi ya ajiyeta sai ya dawo ɗaukarta zai shigo a gaisa.

Kallona yayi yace "yau baby ta samu abokiyar hira don haka bari nima naje wajen Faisal, dama yana tayi mini tsiya wai kin ɓoyeni kin hanani zumunci dasu."

Ɗaga hannayena nayi ina dariya nace "ni babu ruwana, ba kaga damar zuwa ba dai."

"Kina jin ta ko Khadijah, matar da ko masallaci sai nayi da gaske take bari na fita amma kin ji abinda take cewa."

Gaba ɗayanmu muka yi dariya. Tashi nayi na raka shi har bakin ƙofa kafin na bashi peck a kumatu, cikin narkakkiyar muryar dashi kaɗai nake yiwa magana nace "take care and please kada ka daɗe, kasan bana samun nutsuwa idan har kayi nesa dani."

Ɗan rungumoni yayi a jikin shi yace "In Sha Allah baby, sai na dawo."

Ina dawowa na zauna Khadija tace "ah dole Ya Hamza yace ke kike hana shi fita, irin wannan zuba love haka Feenah. Lallai bari muzo muyi course."

Harararta nayi nace "ko ba course ba ƴar rainin wayo, idan ba'a yi course a wurinki ba kuwa baza ki yi a wurina ba. Nasan yanzu haka Mallam Sadiq sai yadda kika yi dashi. Allah sarki bawan Allah ya gamu da gamon shi."

Duka ta kawo mini nayi saurin kaucewa ina dariya.

Tashi nayi na kawo mata kayan motsa baki kala-kala sai da na cika gabanta dasu.

Tana dariya tace "miye haka sai kace wata baƙuwa?" Ina zama nace "a yanzun dai ai na sannu da zuwa ne zuwa anjima sai dai ki tashi ki yiwa kanki komai ba ƙara yi miki zan yi ba."

Hira muka dasa kamar mun shekara bamu haɗu ba, sai zuwa can nace "tashi mu shiga kitchen mu ɗora girki."

kun dai san Khadijah da ƙin duk wata sabga data danganci kitchen don haka ƙyaleni tayi nayi aikina ita dai nata kawai ta tayani hira. Bayan na gama abinci na ɗibar mana namu sannan na zuba na Umma na shirya a basket.

Kallona tayi da alamar tambaya nace "na Umma ne."

"Kada dai kice kullum sai kin bata abinci?" Ɗaga kafaɗu nayi alamar 'eh'.

"Safeenah me ya kai ki ke kuwa? Kin san matsalar da hakan zai iya janyo miki kuwa a gaba?"

Juyar da kaina nayi nace "haka Albi yace na dinga yin girki da ita kullum ni kuma naga ba wani abu bane tunda ma ai ba daɗewa zamu yi a garin ba."

"Hu-um, amma Feenah ban san baki da wayo ba sai yau. Ina laifin ace idan kin yi ɗan wani abun marmari ki bata, amma girki kullum. Shikenan ko baki yi niyyar ɗora tukunya ba saboda ita sai kin ɗora tunda kin riga kin sabar mata."

"Babu wani abu Khadijah don nayi mata hidima ai ba faɗuwa nayi ba, ita ɗin uwa ce kuma in har da gaske ina son ɗanta to don na dafa abinci na bata banga wata matsala a ciki ba."

"Haka ne," kawai tace muka saki hirar muka kama wata.

Sai da muka yi sallah muka ci abinci sannan na ɗauki basket ɗin na cewa Khadijah tazo muje ta gaida Umma.

Irin karɓar da aka yi mata ko ni da nake surukurta bata taɓa yi mini irinta ba. Da fara'arta ta tare ta tana yi mata sannu da zuwa. Kafin kuce miye wannan an cika gabanta da kayan ciye-ciye abinda ni ba'a taɓa yi mini ba kenan don ni ko ruwan wurinta ban taɓa sha ba in ka ɗauke girkin kwana bakwai da aka yi mini.

Ina zaune a gefe ina kallon yadda suke ta nan-nan da Khadijah ita da ƴaƴanta, sai tambayarta Umma take yi suna dai zaune lafiya, tana fata bata da wata matsala ko. Kada taji nauyinta idan da akwai ta faɗa mata don ita da Mama basu da bambanci. A raina nace "haka ne kam," Tunda yadda take treating ɗina haka Mama take yi,har gara Mama wasu lokutan nakan ɗan ga fara'arta amma ita wannan ko kusa ban taɓa ganin dariyarta ba.

Suhaila ce tace "Aunty Khadijah ai muna nan zuwa miki yini."

"Allah ya kawo ku, Feenah tashi mu tafi." Tace haɗe da miƙewa tsaye.

Umma ca tace "tun yanzu zaki tafi Khadijah muna ƴar hirarmu, baza ki bari sai anjima ba."

Fir taƙi zama tace ta dawo wani lokacin yanzun dai shigiwa tayi ta gaisheta.

Haka muka tashi bayan ta cikowa Khadijah leda da kayayyaki tasa Ummi ta ɗaukar mata har part ɗina. Bayan ta ajiye mata ledar ta tafi ne Khadija tace "anya kuna zaune lafiya da wannan surukar taki kuwa Feenah?"

"Me kika gani?" Na tambayeta.

"Gani nayi tun daga amsa gaisuwar ki da tayi bata ƙara kula ki ba sai ni da na kasance baƙuwa, ko godiyar abincin da kika kai mata fa bata yi ba. Su kan su yaran fa babu wacce ta gaishe ki shine don neman wuri wai zasu je gidana su yini, to suje suyi mini me idan ba gulma ba."

"Umhm," kawai nace. To me ma zance. Kada fa ku manta Umman Albi aminiyar Mama ce, koda Khadijah take ƴar uwa ta akwai maganar da sam bana yi da ita. Duk abinda ya danganci Mama komai ƙanƙantar shi ina ƙoƙarin kiyayewa wajen ganin maganarshi bata haɗani da ita ba domin kuwa uwa uwa ce, duk yadda ta kai da so na a matsayina na ƴar uwarta to fa bazan canja kasancewar Mama mahaifiyarta ba.

Muna nan tare da Khadijah har dare sannan Sadiq yazo ya ɗauketa. Kafin ta tafi take faɗa mini ai jibi zasu tafi Abuja inda Sadiq yake aiki don hutun shi ya ƙare. Sai naji duk babu daɗi domin kuwa nasan zan yi kewarta don ma nima ɗin ba zaman zan yi ba banda haka da na sha kewa kam.

Har kuka sai da nayi don sai naji kamar yanzu ne ma auren ya raba mu. Lallashina Albi yayi tayi yana bani haƙuri, anan nema yake faɗa mini ai muma baza mu wuce next week ba zamu tafi Lagos don haka na daina kuka, ya kuma yi mini alƙawarin kai ni Abuja wurin Khadijah nayi mata kwana biyu.

A washegari na kira Anty bayan mun gaisa tambayata tayi "babu dai wata matsala ko Safeenah?" Wannan tambayar kullum ne sai Anty tayi mini ita, nace mata "babu matsalar komai."

"Har wajen surukarki duk lafiya?" Nan ma nace mata "lafiya ƙalau," don ban ji zan iya faɗa mata yadda har yau Umma bata sakar mini fuska ba. Hira muka yi kamar kullum kafin  na faɗa mata batun tafiyarmu Lagos wani satin saboda cewa da tayi idan tafiyar ta kusa na faɗa mata don zata saka ayi mini su garin tuwo, yaji, kuka dasu kuɓewa da dai duk wani abu data san zan buƙata idan mun je can. Bayan mun yi sallama gyarawa nayi na kwanta bacci kafin lokacin da zan shiga kitchen ɗora girki yayi don Albi yana cikin gida tunda muka shiga gaishe dasu Umma acan na baro shi.

Cike da nishaɗi suke hira da Umma, cikin hirar ne yake faɗa mata wani satin yake so ya koma Lagos don hutun shi ya kusa ƙarewa.

"Ikon Allah, abun ba wuya wai hutun naka har yazo ƙarshe. To Allah yayi taimako ya bada sa'a, ya kawar da idanun maƙiya daga kanka."

Sosai yake jin daɗin addu'o'in da Umma take yi mishi, gashi nan kuwa shi yasa kullum cigaba yake gani.

"Sai a haɗa mana kayayyakin da zamu buƙata ko Umma, kin san samun abubuwan mu na gargajiya acan yana wahala."

A mamakance ta kalle shi tace "wane irin kaya kenan kai da kake cewa baka son tafiya da shirgi."

Ɗan sosa kanshi yayi yana murmushi yace

"Komai ai kamawa yake yi Umma. Tunda da Safeenah zamu tafi ai dole a tanadi kayan girki."

A zabure ta ɗago ta kalle shi kamar wacce ya faɗawa wata mummunar kalma.

"Ina zaka je? Da wacce Safeenar kuma?"

Gaban shi ne ya faɗi da jin abinda Umma tace.

"Au auren zata bari ta bika Lagos don ta hanaka nutsuwa a wajen aikin ka?"

A rikice yace "Umma ban gane ba."

A fusace ta katse shi da "ina fa zaka gane, to wallahi ahir ɗinka ka kiyaye ni kana ji na. Kana nufin ka ɗauki mace ka tafi sai ranar dana ganka, kana kai kaɗai ma kake yin wata biyu baka zo gida ba bare ka ɗauki matarka ka tafi. To ban yarda ba ka barta anan ka dinga zuwa kana ganinmu kamar yadda kake yi a baya."

Kamar zai yi kuka yace "don Allah Umma kada kiyi mini haka, wallahi idan na tafi na barta anan hankali na ba zai kwanta ba."   

"Eh tunda zaka tafi ka barta da dodanni ba ai dole hankalinka ya ƙi kwanciya."

"Ba haka nake nufi ba Umma kema kin sani, amma ke baki ga kamar tafiya da ita taimako ne a gareni ba. Zan samu na nutsu a wuri ɗaya ga matsalar abinci da ba a ko ina nake iya sakewa naci ba, kasancewar mu wuri ɗaya kuwa zai yi maganin wannan matsalar."

"Ungo naka nan Hamza kana jina, ungo naka nan." Ta watsa mishi daƙuwa da hannayenta biyu.

"Ni ka zaunar kake faɗa mini taimakon da matarka zata yi maka idan ka tafi da ita ba. Ashe baka da kunya baka da mutinci ban sani ba, to na hana tafiyar da ita muga yadda zaka yi."

Umma mantawa tayi da Hamza ne shalelenta a cikin ƴaƴa ta rufe ido tayi mishi tas akan yace zai tafi dani.

Dafe kai yayi yana jin wani irin tashin hankali ya rufto mishi, me Umma take nufi da hana shi tafiya da matar shi saboda Allah. Yanzu ana nufin haka zai je ya cigaba da zaman gwaurontaka alhali ga matar shi nan a gida ance ba zai tafi da ita ba.

Shi babbar damuwar shi ma yadda yayi wani irin sabo da ita bai san ta yadda zai fara iya rayuwa babu ita ba......

UmmAsghar