Chapter 006
by @jeeddah3256
TAREEQ IMAM
Na
Jeeddah Aliyu
Arewabook@jeeddah3256
006.
Yadda Tareeq ya dakawa Nana tsawa ya jawo hankali wasu tsirarun ɗalibai, sannu a hankali Nana ta shiga buɗe idanuwanta don ta zaci wani mari zai sake kifa mata. Da ta fahimci kallo ya dawo kansu tai sauri bari wuri, ta nufi class da mugun kallo Tareeq ya bi bayanta dashi, can ƙasan zuciyarshi yana cike da mamakin dalili zuwan nata wajenshi.
Har aka koma class su Tareeq suna zaune, da yake mathematics ne dasu kuma teacher ɗin mace ce, ko kaɗan basa tsoronta sai sukai zamansu har ta cinye first period ɗinta, ta shiga second da yake double period ne. Suna zaune abin su kuma basu da niyar komawa class ɗin. Fitsari ne ya matse Nana ta dau excuse, tana cikin gyara skirt ɗinta, sai kurum taji an turo kofa da ƙarfi sai da ta zabura Tareeq ta gani tsaye fuskarshi a murtuke kamar bai taɓa sani me ake nufi da dariya a rayuwarsa, nan take cikinta murɗa ya bada wani sauti mai ƙarfi kamar zatai gudawa sai zarar ido take, cikin kaduwa da sarkewar harshe ta haɗa haruffan sunansa "Ta.ta.ree...q!"
Mugun kallo ya watsa mata kafin ya maida kofa ya rufe har da murza key, wasu yawun tsoro Nana ta hadiya, ta shiga ja da baya fizga ɗaya yai mata ya kaita jikin wall tiles ya yi pinning ɗinta rikitattun idanunshi ya zuba mata, ai kuwa jikinta ya dau kakkarwa Nana tana ji tana gani Tareeq ya cire mata mini hijab ɗin jikinta, ga rigar uniform ɗinsu white ce tsautsayi yasa ta cire jacket saukar hannunshi ta ji akan ƙirjinta tai sauri runtse ido abun da yake mata ne ya haifar mata da daukewar numfashi na wancan gadi,tun sanda ya fara taɓa mata kirji bai taɓa yimata in a gentle way ba sai a wannan karo shiyasa ta rikice ta rasa wacce duniya take ciki. Nana tana da tsananin sha'awa wadda a karancin shekarunta bata gama fahimtar me hakan yake nufi ba amma sometimes idan tana kallon movies aka haska romantic scene saurayi da budurwa suna shafe-shafe sai ta dinga ji wani abu yana tsirga mata, har wani ruwa take ji yana fita a gabanta. Motsi taɓa kofa suka ji da sauri Tareeq ya janye daga jikinta, tare da yimata wani shu'umin kallo dakyar Nana ta iya jan kafafunta ta buɗe kofa ta fice, jikinta sai rawa yake.
Special breakfast food Ummi ta haɗawa Gifty duk abin da tasan tana so saida ta girka mata, sai wanda ranta keso za ta zaɓa. Ƙarfe bakwai dai-dai Fadila ta tashe Gifty ta haɗa mata ruwa tai wanka kana tayi sallah.
Bayan ta Kammala sallah Fadila ta jawo stool ta zaunar da ita gaban dressing mirror, tasan halin Gifty bataso gyaran gashi kusan kodayaushe sai an yi fama da ita kafin ta bari a taɓa gashinta musamman da yawaicin mutane suke tsokanar suman nata, kasancewar shi dark red hair gashi da matuƙar tsantsi gaske comb tasa a hankali ta taje mata ta yadda ba za ta ji zafi ba.
Ta raba mata shi gida biyu ta ɗaure mata da pink hairband mai hoton teddy bear a jiki, hairstyle ɗin ya ƙara ƙawa ta fuskarta tai matuƙar kyau, white colour Australia gown Fadila ta dauƙo mata mai watse Pink flowers a jiki ta mikar da ita tsaye tasa mata rigar ya tsaya iya guiwayoyinta kafin ta Kama hannunta suka fito main parlour kai tsaye dining room suka nufa inda suka hango Ummi da Baby na arranging table gani yadda Fadila ta shirya Gifty yai matuƙar faranta ran Ummi har ta kasa ɓoye farin cikinta tai sauri ajiye plate ɗin hannunta tana murmushi ta rungumo Gifty "ma-sha-ALLAH autar Ummi jiki ya warware zo maza ki ci abinci duk abin da ki ke so yau shi na girka miki."
Cikin sigar shagwaɓa Gifty tace "Thank you umminmu."
Baby ta ja mata kujera ta zauna kana ta shiga bubbuɗa warmers tana nuna mata kaloli abincin.
"Ya Baby zan sha kunu gyaɗa da ƙosai kuma inasan na ci waina."
Gifty tai magana cikin shagwaɓaɓɓiyar muryarta.
Nan take Baby ta zuzzuba mata abubuwan da ta lissafa. Fadila ta karɓi mug ɗin kunu ta shiga bata a baki sai shagwaɓa take zubawa.
Aayya da fitowar ta kenan daga ɗakinta tai tsaye tana kallon yadda Ummi da ƴaƴanta suka taru akan Tahreem sai nuna mata kulawa da ƙaunar ta musamman suke. Hakan ba ƙaramin baƙanta mata rai ya yi ba, tsanar da tai wa mahaifiyar Tahreem har yanzu da bata duniya da raguwar ta a ƙasan zuciyarta, a fusace tasoma tattaki zuwa dining room ɗin tana tafe tana zazzaga masifa "Oh ni Aayya yau naga abin da yafi zare tsayi tsabar lalacewa Amina ku taru ayari guda ke da zugar ƴaƴanki duk akan cin abinci rai guda. Ni kuma tsabar ba ku damu da ni ba, ba ɗan bante uban da ya kira ni na zo na karya kumallo. To daɗin abin ɗa da na haifa ne ya kawo abinci ba Usmanu ba.
Aayya ta ƙarasa magana sa'ili da ta iso cikin dining room ɗin, cikin sanyi murya Ummi ta furta "ina kwana Aayya?"
"Ka ji wani rashin ɗa'a Amina sai yanzu za ki gaida ni halan ba ki san ɗakina ba?"
"Haba Aayya! ko kin manta da asuba ni ce na tashe ki?"
Cewar Ummi tana murmushi takaici.
"To tun da kinsan da haka miye na tambayana kwana, idan ma kwana kike so tambaya je ki ɗakina yana nan kan gado na baro shi."
Kafin Ummi tai magana Baby ta riga ta, ta hanyar ballawa Aayya harara tana faɗin
"To Bismillahi...Al-masifatu minal azabatu safiyarki ta waye kenan, za ki fara halinki in za kiyi breakfast ki zo ga kujera ki zauna, tun da sassafe za ki fara addabar mu da ruwan masifa...
Cikin tsawa Ummi ta takawa Baby birki.
"Ya isa Baby wallahi ki kiyayye ni banaso rashin kunya Aayya ba sa'arki bace ki san irin maganganun da za ki dinga furta mata."
"Allah ya ba ki haƙuri Ummi."
Baby ta faɗa tare da ajiye serving spoon rai ɓace ta nufi cikin parlour, kujera Ummi ta jawa Aayya tare da kwantar da murya ta ce "Dan Allah Aayya ki yi haƙuri wallahi ina da niyyar na je na kira ki sai gashi kin fito, amma In-sha-ALLAH daga yau hakan ba zai sake faruwa ba."
Taɓe baki Aayya tayi tare da zaunawa Ummi ta zuba mata kunu gyaɗa, da ƙosai ɗayan plate kuma ta zuba mata waina saboda tasan tana so waina sosai. Fuskar Aayya babu walwala alamun har yanzu bata gamawa hucewa ba, ta dubi Ummi a ɗage ta ce "ina fatar kafin Tareeq ya fita ya yi karin kumallo kinsan shi da son waina?"
Ita ma Ummi ɗaure fuskarta tayi cikin ɓacin rai ta shiga faɗin "kema Aayya kinsan halin Tareeq da rashin son cin abinci sau nawa za a yi waina a gidanan a ajiye masa ƙarshenta ya tsallake ya fi ce abinsa."
"Wannan kuma ai ba hujja bace Amina domin da kin yi niyar bashi yaci ki san hanyar da za ki bi kamar dai yadda ki ka saka shalelen ƴarki a gaba kina lallaba ta kamar kwai har da bata a baki sai kace kuturwa."
Da sauri Fadila ta ɗago ta kalli Aayya ta watsar wani shegen haushinta ya turnuƙe mata zuciya, ji take kamar ta taso ta rufe ta da shegen duka, sai dai ba halin yin hakan. Sau dama saboda halin masifar Aayya take fatar tayi aure ta bar mata gida.
Sai Ummi ta dube ta cikin danne ɓaci ranta ta ce "Haba Aayya Dan ALLAH ki dinga faɗar abin da zai yiwuwa yanzu fissibilillahi Tareeq da girmansa zan zauna ina rarrashinsa dan yaci abinci sai kace wani yaron goye."
"Ita kuma wannan mai jan gashi ai yarinyar goye ce shiyasa ku ka taƙarƙare ku na bata a baki."
Gifty naji Aayya ta kira ta da sunan da ta tsana, nan take ta ji abinci ya fi ce mata arai domin har idanuwanta sun cicciko da hawaye duk tsangwama da hantararta da Aayya ke yi baya damunta amma da ta kira ta da mai jan gashi sai ranta ya sosu wani lokaci har kuka take yi, Fadila tana gani yanayi Gifty ya sauya tai sauri kama hannunta ta ja ta suka bar dining area ɗin. Duk da haka sai da Aayya ta bi su da zagi.
Ummi kan tsabar takaici kasa furta uffan tayi sai kawai ta tattara abinci Gifty ta bi ta dashi ɗakin Fadila, ai kuwa Aayya ta sake buɗe sabon shafin masifa sai da ta gaji don kanta, Sannan taci abincinta.
Ummi kuka ta tarar da Gifty tana yi Fadila tana rungume da ita sai faman rarrashinta take ran Ummi ya ƙara ɓaci ta tsani duk abin da zai ɓatawa Tahreem rai balle har ya kaita da zubda hawaye ita ɗin amana ce a gurin ta shiyasa take matuƙar kiyaye duk abin da zai iya saka ta damuwa ko ya ɓata mata rai.
Kusa da ita Ummi ta zauna ta ciro ta daga jikin Fadila ta mayar a nata jiki, ta rungume ta tsam...a hankali take shafar gadon bayanta.
"Bana so kukanki Tahreem yana saka ni cikin matsananciyar damuwa, har na kan ji na gaza maye miki gurbin uwa da kika rasa. Koda bana auren Daddyn Fadila Aayya tamkar uwa ce a gare ni ita da mahaifiyata uwa ɗaya uba ɗaya ne ya haife su, kuma lokaci da mahaifiyata ta bar duniya muna da ƙanana shekaru ni da mahaifinki kamar dai ke, ita ce ta rene mu cike da so da ƙauna tun tasowa ta har na kai muzalin aure bata taɓa nuna min bambancin da ƴaƴan da ta haifa ba. Asali ma zan iya ce miki tafi ƙaunata fiye dasu. Rashin jituwa tsakanin mu ta samo asali ne tun daga lokaci da na zaɓi mahaifin Yayanku Jabeer na ƙi ɗanta bayan mahaifin Jabeer ya rasu, suka aura min Daddyn Fadila batare da neman jin ra'ayina ba."
"To ita kuma Gifty miye laifinta anan Ummi da Aayya ke hantararta?"
Fadila ta tambaya da alamun akwai raguwar ɓacin rai a tare da ita.
Sai da Ummi ta gyara zamanta ta tattara natsuwarta wuri guda kana ta ce "Saboda Usman ya bijirewa auren yakumbo Ku Maimuna, ya aure mahaifyar Tahreem wacce ta kasance buzuwa."
Zaro idanuwa Fadila tayi tace "Cabdijam!... lallai tsangwamar da Aayya take wa Gifty ashe da walakin goro a miya."
Ajiyar zuciya Ummi tayi tare da kai dubanta ga Tahreem wacce taji jikinta ya saki alamun tayi barci, murmushi Ummi tasaki sakamakon gani yadda Tahreem ta jefa yatsan a baki tana tsotsa.
"Fadila bansan sai yaushe Tahreem za ta daina shan yatsa?"
Ummi ta faɗa tana jawo pillow ta ɗora kan Gifty akai kana ta gyara mata ƙafafuwanta ta yadda za ta ji daɗin kwanciya.
Dariya Fadila tayi tare da furta "Da yardar ALLAH zuwa gaba za ta daina Ummi. Ni kam ummi ina so wata rana ki ba mu tarihin rayuwarki da dukkan alama kin sha gwagwarmaya."
Murmushi ummi tayi kafin ta ce "Fadila babu komai a cikin tarihina face takaici da tausayi amma tun da kina buƙatar ji nai miki alƙawari watarana zan sanar dake tun daga farko har izuwa ƙarshensa.
Misali ƙarfe uku aka
tashe su Tareeq daga school tun kafin lokacin direbanshi yake zaune yana jiranshi, ƙa'idarsa ce kafin wa'adin tashin su ya yi dole direbanshi ya kasance a school ɗin a cewar shi ba zai iya jira ba sai dai shi a jira shi, tsabar iskanci irin na Tareeq ba zai wuce gida ba har sai ya jira an zo ɗaukar friends ɗinshi.
Tsau-tsayi yasa wata rana direban ya gwada yi mai complain rufe idanuwa ya yi yai masa rashin mutunci har da su zagi, daga lokaci Malam Musa bai sake kwantata yi mai korafi ba. Saidai ya yi zamansa cikin mota yana jiranshi.
Sai da abokan rashin jin nashi suka wuce kafin ya nufo mota da sauri Malam Musa ya fito ya buɗe mai ƙofa ya shiga.
Tareeq yana gudun haɗuwa da Ummi shiyasa bai bi ta ƙofar main parlour ba, bayan ya cire school uniform yai watsi dasu kan gado wanka ya yi ya fito ɗaure da brown towel a gaggauce ya shirya cikin black colour crazy jeans trouser riga mai gajeren hannu yasa ta matse mishi ƙirji da damtse hannuwanshi saida ya gabatar da sallar la'asar kafin ya dauƙo wayarshi ya fito daga ɗakin. Kai tsaye ɓangaren Hajiya Jamila ya nufa wacce ta kasance uwar gidan Alhaji Imam Wali, yana shiga babban parlour ya tarar da Baby da Zainab tare da Uncle Hamza su na fira, sai famar kyalkyalar dariya suke yadda ya turo ƙofa da ƙarfi yasa su katse dariya da suke yi kusan a tare su duka suka kalle ƙofa ɗin kowanne su da irin kallon da yake mai, shi ma kallonsu yai ya watsar cikin tanke fuska ya kalli Zainab ya ce "Ya Zainab Mommy na ciki?"
"Mommy bata nan Tareeq ta tafi koyon sallama."
Zainab ta furta tare da ƙare masa kallon banza.
"Mtsss! aikin banza!"
Baby ta faɗa tana gallawa Tareeq harara.
Murmushin reni wayau yai kafin ya ce "Ya Zainab ni ki ke wa baƙa ke kuma Ya Baby da wa ki ke?"
"Da kai ake ko za ka dake ni ne?"
Baby ta faɗa tana mai sake balla mai harara wacce tafi ta farko. Zainab kuma sai cewa tayi
"An maka ɗin ko akwai abin da za ka yi?"
Wani irin mugun kallo yake bin su dashi kafin ya yi ƙwafa ya ce "dukkan ku biyu kun yi marmarin kwanciya gado asibiti shiyasa bakunan ku basa tauna magana kafin su furta min. To amma ba komai dama can ni kwararre ne a karya ƙasusuwan mata."
Yadda yake magana cikin izza da taƙama dole ko waye kai ya ba ka haushi shiyasa yana dasa aya Uncle Hamza ya miƙe a fusace ya nuna shi ɗan yatsa "Kai wane irin marar ɗa'a ne Tareeq?Daga Zainab har Baby babu sa'arka amma kake faɗar za ka karya su to bara ka ji duk wacce tsau-tsayi ya aike ka taɓa koda ɗan yatsanta ne da sunan duka, na rantse ma da ALLAH sai nayi kusan kashe ka a gidanan ɗan iska kawai marar mutunci."
Kowacce kalma da ke fitowa daga bakin Uncle Hamza tana sauka a dodon kunne Tareeq tana daɗa tunzira shi, yayin da ranshi yai bala'in ɓaci cikin fusata ya ce "Ka ga ɗan wada{kasancewar Uncle Hamza ba shi da tsayi gajere ne shiyasa Tareeq yake kiransa da ɗan Wada😅} a shawarce ka daina shiga sabgar da ba taka ba, kamar yanda ka faɗa ba mutunci ne dani ba har kai ɗin zan iya kwantar wa a gadon asibiti."
"Iyeee Tareeq! Uncle Hamza ɗin?"
Kusan a tare Baby da Zainab suka haɗa baki wajen furta wa tare da zaro idanuwa haɗi da dafe ƙirji.
Tsaki Tareeq ya ja yana hararar su yake faɗin
"Mtsss! Uncle Hamza ɗin mana ko kuna kwankwato ne na gwada maku zahirin gaskiya."
A fusace Uncle Hamza ya taso ya nufi Tareeq ya ɗaga hannu da nufi wanke mai fuska da mari mommy tai sauri riƙe masa hannu wacce haniyarsu ce da taji tayi yawa yasa ta fitowa daga ƙaramin parlournta. "Subhanalillah! meke faru ne Hamza me Babana yai ma da za ka dake shi?"
Cikin irin mugun ɓaci rai nan Uncle Hamza ke magana
"Aunty wallahi-tallahi Tareeq ya fara kaini bango matuƙar ba ki yi mai iyaka dani ba na rantse da ALLAH sai na kassara mishi rayuwa."
"Waye kai Uncle Hamza me kake dashi ka manta a karkashin dukiyar ubana kake rayuwa, duk wata izza da jiji da kanka da bazar mahaifina kake taka rawa. Kuma wallahi idan ba ka yi a hankali ba sai nai maka korar ƙasƙanci a gidanan, kora irin wacce ake wa kare...
"Kai ya isa Tareeq banaso shirmen banza da rashin kunya Hamza tsarar wasanka ne da za ka dinga faɗa mai magana kamar kana yi da sa'anka?"
Mommy ce ta katse Tareeq cikin fushi.
Turo baki ya yi irin na sangartattun kuma tsageru yara yana wani ɗaure fuska.
"Babana ka natsu kasani kullum ƙara girman kake yi ka tuna kaine magajin wannan gidan, kai kaɗai ALLAH ya mallaka mana a matsayin ɗa namiji burinmu ka zame mana tamkar ɗa dubu ka zama abin alfaharin mu. Amma wannan halin naka na rashin girmama na gaba da kai yana faɗar min da gaba ka yiwa kanka karatun ta natsu."
Jikin Tareeq yai matuƙar sanyi shiyasa yake ƙaunar Hajiya Jamila saboda tasan yadda za tai mishi nasiha cikin ruwan sanyi saɓani umminshi da kullum cikin zagi da hantararshi take.
"Ki yi haƙuri Mommy In-sha-ALLAH ba zan sake ba."
Yadda Tareeq ya furta magana cikin tattausan lafazi da karya kai tamkar ba shi ba.
"Shi kenan yaron kirki maza ba Uncle Hamza haƙuri."
"Uhmm! mommy!."
Ya faɗa cikin muryar shagwaɓa har da bubbuga ƙafa a tiles alamar hakan fa da matuƙar wahala.
"What do you mean Babana ba za ka iya bada haƙuri bane?"
"No mommy ba haka nake nufi ba kawai dai ban yi laifi da zan bada haƙuri ba."
Kunne shi Mommy ta kama ta murɗe a hankali ta ce "Banaso gardama oya ka yi abin da nasa ka kafin na tuzge wannan kunne da ba ya jin magana, faɗi mana."
Mommy ta ƙarashe magana tana ƙara murɗe kunnen nashi da ɗan ƙarfi.
"Ouchhh!.... mommy zafi karki cire min zan faɗa i am sorry Uncle Hamza."
Wani irin mashahurin takaici ne ya kama Uncle Hamza, harara Mommy ta galla mai alamar kayi magana zuciyarsa tana masa tuƙuƙin ya furta "its okay. Daga haka ya sa kai ya fice daga parlour, yana mai jin haushi yadda kodayaushe yayarsa ke biyewa Tareeq su na ƙara sangarta shi yana yi wa mutane rashin kunya iri-iri.
"Saura Ya Zainab da Ya Baby suma kace su yi haƙuri."
Cewar mommy tana kallon Tareeq tana murmushi ɓata fuska ya yi tare da zubawa mommy manyan idanuwanshi masu kama da na mahaifin shi sakk.
"Su kuma Mommy miyasa?"
"Saboda su na gaba da kai kuma ka yi musu rashin kunya, a matsayinka na ƙaramin ƙaninsu dole ka bada haƙuri.
"Ku yi haƙuri."
Ya faɗa a takaice tare da kife kanshi a shoulder mommy ya runtse idanuwanshi duk duniya in da akwai abin da ke bashi haushi yake kuma yi masa matuƙar wahala furta wa shine kalmar ban haƙuri duk sanda ya aikata laifi, mommy da Daddy ne kaɗai mutane da suka isa su cilasta mai bada haƙuri.
Yana ɗagowa Zainab tai mai gwalo Baby kuma tai mai blowing kiss, sosai hakan ya ƙara harzuƙa shi kamar zai fashe da kuka ya ce "mommy kin gansu ko su na tsokanata wallahi ina karya ɗiya yanzu nan."
Dariya mommy tayi tare da watsa masu harara tana faɗin "Ku ɓace min da gani manyan Kwabo kawai shiyasa ya rena ku."
Ficewa suka yi suna ci-gaba da sheƙa dariya abinsu don kawai su ƙar
a tulawa mai haushi.
#Jeeddah Aliyu
#Tareeq
#Uncle Hamza
#Mommy
#Zainab
#Baby
#team TareeqImam.