TUNANIN ƘARSHE

Treaser

by @fateyzaahrah

 BOOK TEASER – TUNANIN ƘARSHE
A taste of the final thoughts before the storm begins…
“Read this book teaser from the upcoming novel TUNANIN ƘARSHE.”


Wasu labarai ba sa buƙatar fitowa da ƙarfe ko walkiya – sai dai shiru mai nauyi, zuciya mai yawo, da tunanin da ke dawowa daga inda aka fara ɓacewa.

Ta rayu cikin inuwa, tana ganin haske. Tana dariya a wajen da hawaye ke ambaliya. Tana gudu daga gaskiya tana mafarkin 'yanci.

Amma akwai rana, akwai rana da duk mai tunani zai tsaya ya tambayi kansa:
"Shin wannan ita ce ni?"
"Shin da gaske na gane me rayuwa take nufi?"
"Ko kuwa ni ce na ƙi ganewa?"


Tunanin Ƙarshe ba wai ƙarshe ne ba, sai dai mafari ne na gaskiya, da nadamar da ke daɗa ɗanɗano fiye da zuma.

“Wanda ya raina hanya, tafiya ta koya masa.”


     💦💦💦💦


 Kwana goma kenan tana mafarkin murya ɗaya, muryar wata da ba ta taɓa faɗar sunanta ba.

“Idan kika buɗe akwatin nan, komai zai sauya…” shine abinda ake faɗa mata a cikin mafarkin, zabga uban tagumi tayi, ta rasa meke mata daɗi a duniya, "akwatin bai ƙunshe da wasiƙa ba, sai amsar tambayoyin da bata taɓa shirya karɓa ba." Zuciyarta ta ƙara ayyana wa.

Tana jin zuciyarta na bugawa kamar wata ƙararrawa da aka manta da kashewa. A hankali ta miƙe tana ɗaga ƙarƙashin gadon mahaifiyarta, wanda ya zama nata a yanzu akwatin ƙarfe ta ɗauko, numfashinta ya yi nauyi. Tsohon akwati ne, ƙuraje sun rufe gefuna, ƙulli mai tsawo ya rufe makullin da ƙasa.

Ta san cewa akwai sirri a ciki. Sirrin da ya ke da nasaba da barin mahaifiyarta daga gidansu. Sirrin da ke hana ta barci tun barin Ummiee daga gidan.

“Idan kika buɗe akwatin nan, komai zai sauya…” wata zuciyar ta raya mata. Zama tayi a ƙasa tana buɗe wa:
Ba hotuna ne a ciki ba, sannan Ba zobe ba.
Sai wata takarda guda ɗaya…da aka yi rubutu, kuma aka sa hannu da jini.

Warware takarda tayi kalmomin farko da ta karanta sun wargaza komai da take tunani:
 “Ina fata idan kin karanta wannan, kin shirya jin gaskiyar da ta fi mutuwa zafi.”...... Hannunta ya ruɗe. Zuciyarta ta yi shiru. Duniya ta tsaya cak.


❤️🩸❤️🩸❤️


“Ki gaya min gaskiya, Aamanee. Ki gaya min komai kafin lokaci ya kure.”
Idonta ta lumshe, kamar tana ƙoƙarin rufe wani fim da zuciyarta ke haska mata. Cikin zuciyarta akwai kura da hadari, amma a fuskarta, sai nutsuwa mai ban tsoro.
“Idan na gaya maka gaskiya, za ka ci gaba da sona?” ta faɗa da muryarta mai sanyi
 Idanu ya zuba mata, ba tare da ya amsa ba. Baya buƙatar wata amsa, domin a lokacin da kalmarta ta fito, rayuwarsa ta canza.

"A ransa ya san haka, amma zuciyarsa ta ƙi yarda. Saboda Aamanee ce, Aamanee da kalmarta ba ya faɗuwa har sai ta noke numfashi. Aamanee da idan ta yi shiru, akwai wani abu da ke ƙuna a cikin ranta." Ya ayyyana a cikin ransa

"Yana so ta sanar masa da gaskiya amma ba duka ba. Yana jin akwai wani ɓangare da take ɓoye wani abu a rayuwar ta, ɓangare mai iya wargaza abin da suka gina da hawaye da jini. Amma ko da kuwa ta buɗe baki ta faɗi komai, shin zuciyarsa za ta iya ɗaukar gaskiyar?"

Ƙara kallonta yayi da narkakkun idanunsa "na fiso ki sanar da ni gaskiya duk ɗacin ta zan karɓa"
Da wani irin yanayi mai wahalar fassara ta ɗago dara-daran idanun ta tana sauke su akan sa tare da cewa.......


Shin Aamanee za ta iya fuskantar gaskiya?, ko kuwa za ta gudu daga abinda zata iya jurewa?
Wani lokacin ƙarshe na abu ne kawai farkon gaskiya.

🔍 Read between the words. The truth is never loud.

📘 TUNANIN ƘARSHE – A gripping emotional thriller.
 A novel by Fateyzahraah
🕯 Coming Soon
“Every silence has a story. Every goodbye hides a reason.”

07077791941
🖋️ Fateyzahraah