Diddigar ƙaya...

5

by @gureenjoh

DIDDIGAR ƘAYA

   (Mai Wuyar Tsincewa)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            

         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:

Zuhraa

Hamrah

Igiyar Rayuwa

Noor Iman

Ruwan Sama..

Lelewal

GAMON JINI paid

Kowa Ya ga zabuwa..

And Now..

Diddigar ƙaya... Paid

                 Shafi Na Biyar

PAID BOOK

ƊANƊANO

WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI MRSJMOON GWANATA KUMA SHUGABATA🥰❤️

A hanya ta gamu da Fakiha don bata gaisheta ba ta mammake ta, bata koma sashensu ba sbd ta san da kuka Fakiha zata koma be gami Baba Alhj ba kuma ya daka ta in ta kaishi bango da daren nan, sashen Jaddah tayi ta same ta tana cin brabusko da miyar kayan ciki, zama tayi tace

"Wayyoooo yunwa Jaddah"

Murmushi tayi tace

"ai tunda na ga an turo da tuwo da miyar kuka daga gidanku na san se kin zo nan neman abinci, a yi mutum ne babu abunda ya tsana irin tuwo?"

Tura baki tayi tana me jan plate ta ɗibi brabuskon kaɗan ta saka miya dayawa da namomi don tana kaunar nama, haka ta ci, ta cinye naman ta bar sauran  gayan brabuskon, Jaddah da ta gama ci ta kalli plate ɗinta tace

"shiyasa kullum bakya karuwa cin abinci ne kaman ɗan jariri? dube ki fa kaman a hure ki faɗi"

Tana dariya tace

"dama Jaddah ni na ce miki ina son in yi kiba ne? Waiiii wa yaga Fauxa da ƙiba tayi tsokana ta kasa gudu" ta karashe da dariya

Jaddah na hararinta tace

"ashe ma kin san kina neman maganan"

Dariya suka yi a tare.

Hira suka cigaba da yi abunsu gwanin sha'awa, dama ita ce mutumiyar Jaddahn Dukda ita Jaddah kowa nata ne amma fa sun san Fauxa ta daban ce a wurinta, in har baka sameta gidansu ba to shiga wurin Jaddah.

Seda taga karfe sha ɗaya yayi kan ta mike tace

"Jaddah zan tafi, se da safe"

Jaddah ta buɗe baki tace

"Ina zaki? Kin kalli agogo kuwa? Na tabbatar yanzu sule ya rufe kofar shi, ba zaki shiga ɗakin ki na nan ki kwana ba?"

Girgiza kai tayi tace

"ni dae bana jin kwana anan Jaddah, ko ya rufe na san ta inda zan shiga, se da safe"

Bata jira amsar Jaddah ba ta fice abunta, girgiza kai kawai jadda tayi.

Kaman Jaddah ta sani tana isa taji barin Baba Alhj kofan da alamun yanzu ya rufe Seda ta ɗan bada mintuna zuwa ya shiga ɗaki kan ta cire hijab ɗinta dake jan kasa ta yarfa a matsakaicin ginin da ya zagaye gidan nasu, kusan ko wani sashi haka ne in ka cire sashen samarin da akayi kaman corridor a tsakiya se ɗakunan su huɗu na facing huɗu.

Sannan ginin na cikin gida bashi da back wire kaman asalin main building na gidan, ban gama shan mamaki ba seda na ga Fauxa ta kama ginin nan ta haye, dibbbb haka ta dirko daga kan ginin.

A tsorace Baba Alhj da ya gama dudduba tsakar gidan don tabbatar da tsaronsu ze shiga ɗaki kenan ya waigo, idanunshi suka faɗa kanta.

Itama tsayawa tayi tana Kallonshi se tayi saurin jan hijab ɗinta ta saka akan pencil trouser da karamar vest dake jikinta tana me cigaba da Kallonshi.

Ɓacin rai ya hana shi magana na seconds kan yace

"zo nan fauxiya"

Takawa tayi ta karasa ta tsaya ɗan nesa dashi.

"Daga ina kike?"

Tace

"gidan Jaddah"

Yace

"ba ɗaki ne a chan ko yau kika saba kwana a chan ɗin da bazaki kwana ba har se kin zo kin biyo ta gini kaman wata ɓarauniya? Dama kin saba haye hayen gini ko? Fauziyya kina mace kike hawan gini?"

Tura baki tayi tana me Kallonshi, ita fa bata shakkan saka idanunta cikin idanun ko ma waye, kufula yayi ya kai mata bugu tayi saurin ja da baya yace

"Ina magana kina kallon cikin idona? Tukuna ma wai ban hana ki saka irin kayakin nan ba?"

Cikin kunkuni tace

"ai Jaddah tace in zan ke saka dogon hijabs irin wannan ba damuwa"

Sbd yadda ranshi ya ɓaci be sake magana ba ya shige parlornshi, wato shi ya hana don na gaba dashi ta bata goyon baya komai ma ya faru ita kam ta saka. Allah ya kyauta ya faɗa yana zama.

Ammi dake ɗakin nashi a yau zata yi magana kenan suka ji ƙara me karfi, da sauri duk suka miƙe tunaninsu na basu Falaq ce sbd ta kan yi hakan wasu dararen wani lokacin ma har se baba prof ya shigo.

A tsakar gidan suka haɗu da Aunty Amarya se kawai suka yi ɗakin yaran, fa'iza suka gani tana tsaye tana zub da hawaye, Falaq na kwance idanunta kan Fauxa sede bata ce komai ba.

Fatima ma na kwance saman gadonta tana kallon fa'iza, shigowar Su Baba Alhj ne yasa duk suka maida hankali kansu banda Fauxa da ta hau kakkabe gadonta.

Ammi ce tace

"me haka fa'iza? Me ya faru?"

Tana share hawayenta tace

"ba komai Ammi"

Fatima tayi Charab tace

"wlh karya ne Ammi, Fauxa ce ta Ɗaka mata duka ita kuma ta firgita sbd baccin da ya ɗauke ta akan gadon Fauxan ta hauro muna hira shine dalilin ihun nata"

Baba Alhj da takaici ya sake kama shi ganin halin da Fauxa ta nuna kaman bata san shigowar su ba yasa yayi wurin chargers ɗin speakers ɗinsu ya zari ɗaya ya shiga dukanta cikin takaicin yarinyar, ihu kam Seda ta kusa cika gidan haka halinta in ana dukanta se kowa ya sani amma fa in ka zo ka bincika bazaka samu hawaye ko guda ɗaya a fuskanta ba, duk kuwa tsoron ta da bulala bazata mishi kuka ba tsabar taurin kai.

Falaq ce tace cikin sanyin murya

"Baba kayi haƙuri ihunta na damuna!"

Saketa yayi ya fice, Ammi da Aunty Amarya suka girgiza kai suka fice suma.

Harara ta zabgawa Fatima tace

"Duk munafurcin mutum ze yi ya gama Fauxa kam nan gani nan bari sadakin agalawa, a daɗe anayi se gaskiya..."

"Enough Fauxa"

Cewar Falaq

Itama harara ta zabga mata tana kunkuni ta haye gadonta ta kwanta, wlh se Fatima ta san ta Haɗata da baba Alhj, se ta rama.

Washegari bayan sallah asuba kowa ya fara hidiman gabanshi, masu aiki sun kama masu shirin makaranta nayi, Fauxa kam na chan kuryar Jaddah tana bacci, sarai ta san itace da shara ta ƙi komawa sashensu haka kawai mutum kullum Kaine bazaka huta kayi bacci son ranka ba.

A chan ɓangaren su kuwa Farhan ne ya shiga da sallama ɗakin na mahaifiyarsu, zaune ya sameta cikin kujerun parlorn tana jan chasbi, ya duka a ƙasa yace

"mun tashi lafiya Ammi?"

Tace

"lafiya ƙalau Farhan, ya gajiyan aiki? Ya ciwon kan hope yayi sauƙi?"

Don jiya ya shigo ya karbi paracetamol a wurinta yace kanshi na ciwo.

Cikin ladabi yace

"Alhamdulillah Ammi.."

Maganan shi ya katse ne a sadda ya ji Aunty Amarya na faɗan rashin fitowar Fauxa yin shara, Ammi ta zabga tagumi tace

"oh Allah na, ni kam yaushe ne zan huta da maganan fauxiya ne Allah nah!"

Hawaye ne ya biyo bayan zancen nata, cikin tausayinta yace

"Ammi ki dena zubarwa Fauxa hawaye kara dulmiyar da ita ze yi, Adu'a itace maganin komai in shaa Allah lokaci kaɗan ya saura da Allah ze sauya mata halaye"

Tace

"Allah ya sa hakan"

Mikewa yayi ya fice don duba ta sbd yana ji Fa'iza na cewa Aunty da ta aikata ta kirata ai tun bayan sallar asuba bata dawo sashen ba, ya tabbatar bazata wuce sashen Jaddah ba.

Kai tsaye nan yayi, be tsaya parlor ba ya wuce kuryar ɗakinta a cikin bargo ya sami Fauxa tana shan baccin ta, hannu ya ɗaga ya sauke mata mari.

A razane ta farka tana furta

"kan uba! Wani ɗan...."

Haɗa idanu da suka yi da ya Farhan yasa ta fasa karasa ashar ɗin da ta kwason se Haɗa rai da tayi tare da turo baki.

"Kin tashi kin wuce kin kama Sharan da kike dashi ko se na ɓallaki a wurin nan?"

Mikewa tayi ta ɗauki hijab ɗinta ta saka kan ta fito Sam bata san yana parlorn ba ta ɗauka ya wuce tace

"Wallahi Allah ya isa na haka kawai a firgi..."

Shiru tayi saboda idanun da suka Haɗa, rankwashi masu zafi da suka sakata sakin ihu ya sakar mata, ya ɗaga kafa ya kai mata harɓi.

Da sauri Jaddah dake kitchen ta fito tana kallon Farhan da ze kara kai mata duka tace

"Haba Farhan me haka? Ya zaka tasa yarinya da sanyin safiyar nan a gaba da duka?"

Yana huci yace

"Jaddah ba duka kaɗai ba idan ta tsaya na cigaba da ganinta anan se na karya ta wallahi, har Fauziyya tayi girman ja min Allah ya isa?"

Da sauri ta fice ta san sarai ze aikata, basu da mutunci yayyinta a kanta kam, bata san meyasa suka tsane ta ba, zata iya rantsewa bata taɓa ganin Ya Farhan ya duki su Fatima ba se ita, dake itace kullum me laifi a duniya.

Shara ta fara sauri sauri bata kwantar da tsintsiyar Sam, kan Farhan ya dawo har tayi rabi, korata yayi ta sake daga farko, tana ji yana cewa su Fa'iza suyi tafiyar su karsu jirata a dake su letti ita in ta gama ze kawo ta da kanshi kuma se ya damka ta hannun discipline master sbd karta kaucewa dukan letti.

Kunkuni take

'eh ai ni da ba'a ƙauna dole a damka ni hannun discipline master wato in ya ga dama yayi kuli kulin kubura dani.. To ta Allah ba ta mutum ba' ta karashe da murguda baki.

Haka ta gama Sharan ta shiga ta chanza zuwa uniform nasu na Elkenemy black trouser da white shirt da ya sauka zuwa gwiwa da tsagu gefe da gefe se farin hijab da shima ya sauka amma be kai rigar ba.

Jakanta ta rataya ta fito ko kitchen ɗinsu bata kalla ba balle tayi Tunanin breakfast ta fice, chan bakin gate ta hangi motar ya Farhan tsabar wulakanci a chan ze yi parking ya jirata ko duba tafiyar daga sashensu zuwa gate ɗin baya yi haka ta isa tana kunkuninta.

Kaman yadda ya faɗa Seda ya damkata hannun discipline master ɗinsu kan ya wuce, bulala biyar ta sha da tsallen kwaɗo zuwa class, tana isa wurin ajin su Fatima taga tana kallonta bata yi kasa a gwiwa ba ta zabga mata harara tare da tsirtar da miyau tace

"Munafuka kawai"

Tsohon Kurtun yace

"what are you saying?"

Tace

"I didn't say anything sir"

Kasa kasa tace

"banza ƙazami"

A class ɗin ma haka ta fitini kowa, malamai babu wadda ze shigo ba ze yi maganan Fauxa ba, malamin math nasu na shigowa ta fara tiƙar dariya wai suit ɗin da ya saka da yanayin jikinshi kaman an sakawa kwaɗo kaya ga keya kaman shantu, tana faɗawa seat mate ɗinta tana shan dariya.

Rai ɓace ya juyo yace cikin kufula

"Fauziyya Sulaiman kaka would you shut up! Are you insane? Ko kaɗaki ake yi da ruwan hanji ne ni kam?"

Baki ta murguɗa yana Juyawa yadda ya gyara tsayuwar da yadda yayi da keyar kan ya cigaba da rubutu ya sakata kwashewa da wani dariyan karshe koranta yayi a class ɗin.

Ko da ta dawo ma malamin English Seda ya nemo soletape ya manne mata a baki yana shedawa ƴan class ɗin she didn't suppose to be Fauxa ya kamata sunanta ya koma Zubaina, babu wadda yayi dariya Dukda dariyar da ke cin su sede sanin halinta kana dariya wlh ka shiga uku a wurinta yasa babu wadda ya dara.

Ko da aka tashi ma Seda ta gama ɓata musu lokaci a mota kan ta zo, ya farhu ya rarrankwasheta, bayan sun koma gida kowa ya fara shirin islamiyya cikin ɓacin rai take shiryawa ita fa ba son zuwa Islamiyyan nan take ba, mutum Kaine baka da hutu gashi baba prof da kanshi yayi Kane Kane a karantarwar islamiyyar.

Babu abunda ke bashi farin ciki irin koyar da yara ya kan musu nasiha da cewa babban sadakatul jariya da mutum ze yiwa kanshi shine ya koyarwa wani waye ne Allah, menene musulunci, har misali ya kan basu da wannan hadisi da yace "mafi alkhairin cikinku shine wadda ya koyi Alqur'ani kuma ya koyar da ita"

Hakan yasa ya kan ɓata time masu yawa wurin baiwa yara ilimin da ya kamata kuma Alhamdulillah bazaka shekara sha biyu a wurinshi baka sauke Alqur'ani ba.

Me hali baya fasa halinshi a Islamiyyan ma bata natsu ba seda ta fitarwa wata jini a baki sbd ya Faraj ya ce mata kaza kanki da motsi itama ta maimaita tana dariya case har wurin baba prof yasa aka zane ta.

Washegari ya kama Alhamis basu da islamiyya bayan sun dawo school ta chanza zuwa kayan gida ta wuce sashen Jaddah ko wurin Ammi bata shiga ba, a kan cinyarta ta kwantar da kanta tace

"Jaddah kan nan ya isheni a tsefe min"

Jaddah ta kira yarinya me yi mata aikace aikace tace ta dubo mata kifiya da cumb, cikin mintuna ta kawo nan Jaddah ta fara mata tsifan suna hiran su.

Saboda yawa da cikan gashi na Fauxa har aka yi la'asar suka je suka yi suka dawo ba'a gama tsifan ba, tana layin na biyun karshe suka ji sallama...

               🖤Gureenjoh🖤