23
by @gureenjoh
KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
Zuhraa
Hamrah
Igiyar Rayuwa
Noor Iman
Ruwan Sama..
Lelewal
GAMON JINI paid
And Now
Kowa Ya ga zabuwa..
PAGE 23
FREE BOOK
"Na tabbatar ba se na nemi sani ba ina magana ne da Hidayat daga Paris kike ko ma ina ne... Ba na kira bane in ji muryanki ko maganan ki ba na kira ne in buga miki gargadi me karfi akan mijina... Wallahi wallahi in baki fita hanyar mijina ba se na zama ajalinki! In baki ji tausayina ba nima ba zan ji naki ba.. Kaman yadda ya tsallake ya bi ƙasa ƙasa ya tafi wurinki har wata uwa duniya be damu da ya barni da tsohon ciki ba haka nima zan tsallako in zo har inda kike in halakaki in baki kyalemin miji ba.. Daaɗin abun Kuma kema macece kaman yadda kika min Allah yasa a miki ninkin ba ninkin, bazawarar banza..!"
Tsit aka kashe wayan, tsamm hidayat ta tsaya a tsaye kaman an dasa ta tana kallon fuskan wayan da dama a hansfree ta saka, daga bayanta ya ɗan leko fuskanta don ya saka hannu kenan a kofan ya fara jin muryar yayi niyyar shigewa sede jin yadda ko ma waye magana take a harzuke da bala'i yasa ya dawo da baya.
Hannunshi ya saka yayi waving fuskanta se tayi firgigit ta dawo da sauri ta kalleshi tana fiki fiki da ido wadda ta saka shi dariya, duk yadda ya so ya danne seda sautin dariyar ya fito.
Yace
"Au wai dama bazawarin naki ma me mata ne?"
Raurau tayi da idanu ya sake sakin yalwataccen murmushi tare da ɗaga duka hannunshi yana shrugging kafaɗa yace
"I surrender! Ni ba ni na kar zomon ba"
Bata san ta Harare shi ba seda ya zaro Idanu duka waje yana kallonta da sauri ta shige zuwa room ɗinta tana ɗan murmushi, bayan ta shiga a fili ta furta
"nima na rama.."
Ajiyar zuciya ta sauke ta sake kallon fuskan wayanta, layin Nigeria ne kwarai kenan matar Hamza ce, baki ta taɓe ita bata san a gaske hakan na faruwa ba seda ya faru a kanta a yanzu, abunda ya daure mata kai shine yadda mata suke iya furta yin ajalin mace akan ɗa namiji, Hausawa suka ce maza ƴaƴan mamansu.. Lallai kam.
Aisha da su Noor da suka shigo ne yasa ta mance Tunanin wata matar Hamza da ta kirata, da shirin kwanciyar su suka ce yau a ɗakinta zasu kwana.
Gadon ta bar musu ta sauka kasa da blankets masu taushi, Seda ta tabbatar sun yi Adu'a kan suka kwanta.
Wayanta ne yayi ringing ta duba taga hamza se matarshi ta faɗo mata, baki ta ɗan taɓe kan ta ɗauka suka gaisa yace
"gobe kam in Allah ya kaimu zan ga hasken raina"
Tace
"uhmm hasken ranka kam na chan ka barota Nigeria.."
Yace
"ban gane ba!"
Tace
"manta kawai, ya Paris to?"
"Babu daaɗi tunda baki a kusa dani"
Tace
"hope kana ji daga wurin Aunty na?"
Dariya yayi sossai yace
"Zainab ɗin ce Auntynki?"
Tace
"eh mana, itace first wife ai Allah ya riga ya bata girman"
A ranta kuwa tace Ashe sunanta zainab!
Sama sama suka ɗan ƙara hiran kan suka yi sallama ta kwanta itama.
Washegari kaman yadda ta saba da wuri ta gama musu komai suka fice a tare shi kam har lokacin be baro ɗakin gym ɗinshi ba ma.
Bayan sun gama lectures suka haɗu da Rash, hira suka sha seda taga call ɗin hamza kan ta kalleta tace
"kina da wani class ne?"
Tace
"A'a am done for today ya akwai outing ne?"
Tayi maganan tana dage gira, dariya hidayat tayi tace tana ɗaukan call ɗin
"ke yayana ne"
Daga bayansu suka ji an ce
"ta faɗi ba daidai ba husband to be dae"
Da sauri duk suka juya, dariya tayi tace
"ya aka yi ka gano mu?"
Yace yana me kallon irin fresh da tayi da wani kyaun da ta kara
"taya ba zan gano ki ba ke fa tauraruwa ce a cikin taurarin ma Zara kinga ko ko da zaki ɓuya cikin gajimare hasken ki baze dusashe ba"
Rash tace
"uhm bari na matsa kar in kurumce"
Dariya duk suka yi, Hidayat tayi musu introducing juna suka gaisa, fita suka yi daga school ɗin zuwa wani hadaddiyar wurin shakatawa, Seda suka ci abinci kan rash ta mike tace bari ta ɗan zagaya ta fice ta bar su tare.
"Tsakani Da Allah hidayat hankali na ya kasa kwanciya da aikin kin nan a gidan wannan ɗan kwallon, kin san ana cewa sunan musulmi kawai yake amsawa amma yayi Ridda tun yana matashi lokacin da kuɗi ya fara ratsa shi.."
Lumshe idanunta tayi tana jin ba daaɗi kan ta buɗe tace
"ka ce Astagfirullah Ya Hamza! Wallahi wallahi kaman yadda muke sallah haka shima yake yi, kaman yadda muke karatun Alqur'ani haka shima yake.. Zan iya cewa ya fi dayawa daga cikin musulmanmu da suka tashi cikin tsantsar musuluncin ma kyaun zuciya da na ɗabi'u karka yi Shedar Zurr saboda zaka tashi dashi a gaban Allah ayi muku hisabi"
Kallonta kawai yake, duk fara'ar dake fuskanta ya dusashe hakan ya nuna magananshi ya ɓata mata rai..
"Wait..! Hidayat me tsakanin ki dashi da har don na faɗi maganar da na ji a gari akan shi ranki ze ɓaci?"
Ya faɗa shima wani irin kishi da zafin zuciya na bijiro mishi.
"Raina be ɓaci ba ya hamza, kawai ina maka gyara ne sannan kai ji kayi ni kuma zaune nake dashi wuri guda"
"I will never let you stay in that house har zuwa sadda zamu yi aure, that won't be possible! Hidayat ba de son shi kika fara ba?"
Ya karashe da wani irin muryar da ya sakata saurin girgiza kai tace
"karka manta fa ya hamza hidayat ɗin nan ce dai marainiya, ni ɗin ce dai wacce bani da galihu da gata, hidayat ɗin nan ce bazawara wacce ɗa namiji ya yagalgalawa rayuwa, taya kake Tunanin zan kai kaina matsayin sanannen ɗan kwallon duk duniya? Ka san mata masu mutunci da ƙima! ƴan mata daga kasashe na Larabawa da na baƙin fata dake ma mutuwa a kanshi? Ko a mafarki Raed yafi karfina bare a zahiri... Don Allah karka yi min mummunar fahimta don kawai na gyara maka kuskuren ka a musulunce.."
Ajiyar zuciya ya sauke, se kuma yaji rashin daaɗin abubuwan da ta alakanta kanta dashi saboda maganan da shi ya kawo ta.
"Kiyi hakuri, wlh da Tunanin kasancewar ku inuwa ɗaya nake kwana nake tashi ba zan iya jurar wani abunda ze kuma raba ni dake ba kuma.. Don Allah ki amince mu yi auren mu kusa ko hankalina ze kwanta"
Tace
"ya wuce ya hamza! Sede aure har yanzu ban shirya ba, sannan karka manta matarka fa ko shekara baku rufa ba da aure taya zaka fara bijiro da wani maganan auren kuma?"
Yace
"in dae hajiyata ta fahimce ni in Shaa Allah bani kuma da sauran damuwa"
"mahaifinka fa?"
Yace
"ai Alhaji ya jima a kwance bashi da lafiya komai se an mishi"
Tace
"Allah sarki, Allah ya tashi kafadunshi" a lokaci ɗaya tana tuna Abbanta. Da Ameen ya amsa suka ɗan yi shiru kan tace
"ya kamata ka koma gida haka nan ko don Aunty na da ka bari da tsohon ciki"
Hmm kawai yace kan ya kara da
"zan tafi ne ba se kin Koran ba"
Dariya tayi tace
"ni na isa in koreka ni da ba a kaina kake ba?"
Dawowan rash ne ya katse musu hiran yace
"Rashida kinji ƙawarki na korata"
Rashida tace
"ba de Hidayat ce zata koreka ba sede in an yi kira dae daga gida"
Wara idanu yayi yace
"haɗe min kai Zaku yi?"
Se suka fashe da dariya, shima yana dariya yace
"to shikenan Allah na ze saka min"
Hiran se ya koma tare da Rash ita fa ba ruwan ta da wani kunya ko kauda kai...
Mikewan hidayat ne ya saka su duk kallonta tace
"my gurls are almost home bari naje na sama musu abunda zasu ci... Please ya hamza karka maida maganan mu wasa, kaga dae da tsohon ciki ka bar zainab baka mata adalci ba in ka cigaba da zama kwana da kwanaki, ya kamata ka koma.. Ko Rashida?"
Rashida tace
"kwarai kuwa, kar ya sa mana shakkun auren ma, muyi Tunanin anya kuwa ze yi adalci?"
Hidayat tace
"ko kuma mu ɗauka a sadda ze nemi ta uku muma hakan ze mana ba!"
Dage hannayenshi yayi yace
"don Allah karku kaini da nisa... In Shaa Allah zan nemi available flight to Nigeria in tafi"
Hidayat tace
"ko kai fa!"
Ya zabga mata harara wacce ta sakata dariya.
Sallama ya musu akwai inda za shi Dukda ya so sauketa a gida sede ana jiranshi..
Suna takowa zuwa inda zasu samu abun hawa tace
"kin san jiya matarshi ta kirani ta ci min mutunci?" Nan ta bata labarin duk abunda zainab ta faɗa mata.
Rash tace
"Kambuuu! Ke kuma me kika ce mata?"
Dariya tayi tace
"ni ko me zan ce mata? Ko 'a' ban ce ba har ta gama sauke min kwandunan masifan ta kashe wayan"
Wani kalar harara ta zabga mata
"Amma wallahi Hidayat baki haɗu ba, kan bala'i gaskiya zan kwana biyu da takaicin wannan rashin amsar da baki bata ba! Don Allah bani layinta, har ta isa ta kai ne mijinta ze kashe kuɗi ya baro ta a chan ya biyo ki har Paris? Waye ya tsaya mata kab Nigeria da zata furta Kalmar yin ajalinki?"
Ita dae hidayat kallonta kawai take tana tuna ummi ƙawarta, Allah sarki tun da ta samu waya take kiran layin ummi dake kanta sede baya shiga Allah kaɗai ya san halin da ta shiga na ɓacewarsu lokaci guda.
"Wai shiru kika yi kina ji na?".
Rash ta faɗa a harzuke
Dariya hidayat tayi tace
"Wallahi best friend ɗina kika tuna min da masifan nan taki"
Rash tace
"hala wani abu ne ya sameta?"
Girgiza kai hidayat tayi tace
"na taho bamu yi sallama ba, tunda kuma na samu layin nan in na kirata bana samunta gashi ban riƙe numbern kowa ba kuma a gidansu da kai"
Rash tace
"Allah sarki amma fa tana fama dake wai dama haka kike?"
Dariya sossai hidayat tayi tace
"Rash kenan ai na fi haka, yanzu ne ma nake iya buɗan baki in yi magana ummi ce me karɓar min faɗa"
Rash tace
"lallai aiko wallahi Inde haka ne zaki cutu"
Hidayat ta ce
"cutuwa kuma na nawa? Ke de a dae yi sha'ani kawai sede fa an sha ni kuma na warke..!"
Dukda rash bata gane maganan ba sede bata sake cewa komai ba don sun zo inda zasu Rabu, sallama sukayi Rashida na ce mata idan matan hamza ta sake kira bata gaya mata shuwaka ba zasu haɗu wallahi.
Tana dariya ta ɗaga mata hannu.
"Masha Allah"
Shine Kalmar da ya fito bakinta a sadda ta hauro saman idanunta suka sauka bisa kansu a keɓantaccen wurin sallan su, yana gaba yana jan su su uku jere a bayanshi sun rufe jikinsu da kyau junior na ta up and down a kanshi.
Ba ƙaramin burgeta sukayi ba ta fidda wayanta ta musu hoto, a lokacin junior ya ganta ya taso da gudu gudu har yana faɗuwa yana mata oyoyo, da sauri ta ɗaga shi tana cilla shi tare da ɗan Juyawa se ya kyalkyale da dariya itama dariya take kan ta maida kanta garesu se taga duk sun sallame ita suke kallo ta ɗan yi murmushi tana kauda idanunta daga kanshi ta shige ɗaki.
Itama ta gabatar da Alwala tayi sallanta a ɗaki tana idarwa suna shigowa suka bata takeaway ta karɓa yau bata dawo da wuri ba ashe shine suka je suka yi takeaway da baban bayan sun idar da sallah.
Ajiyewa tayi don a ƙoshe take, bacci ma take ji hakan ya sa ta kishingiɗa bayan ta kora su, se la'asar Norah ta zo wai ta tashi suyi sallah in ji dad.
Mikewa tayi ta shiga bayi tayo alwala ta zo ta ɗauki wayanta ta fito, sallah suka gabatar a jam'i masha Allah, bayan sun idar duk Qur'anai suka ɗauka suka zagaye ta har Baban wadda hakan ya bata dariya.
Tana murmushi ta fara bawa yaran in ta ƙara maka se ka tashi ka koma gefe seda suka saura su biyu, kan su fara karatun ya kalleta murya chan ƙasa sbd yara yace
"anya kina tuna kina da buri kuwa a rayuwa?"
Kallon ban gane ba ta mishi.
Ya sake cewa
"na ɗauka da gaske kike da kika nuna zaki jajirce ki ɗaukar wa Usman fansa ta hanyar hukuma se gashi kuma wankin hula na shirin kai ki dare"
Kanta ta dukar tace
"kayi hakuri ba wai burina bane ya dusashe, kuma ba wai na manta bane da Usman har Abada ba ze bar kaina da zuciyata ba, kai tsaye ba zan iya cewa bana son hamza ba.."
Lumshe idanunshi yayi yana jin wani mitsini marar daaɗi a zuciyarshi.
"Saboda ya so ni tun ina kwaila ta, shine mutum na farko da ya fara nuna tausayi na da son taimaka na sede kaddara ta a rubuce take se na sha wahala a gidan Yusuf, ya hamza mutum ne me ƙima da ba zan iya wulakanta wa ba, na tabbatar shima yana Burin ganin an biwa Usman hakkinsa sannan na san ze taimakamin ko bayan na aurenshi wurin cikar burina.."
Team Raed! Wa ze iya hasko mana zuciyar ɗan kwallo a yanzu?*
#like
#share
#comment
🖤Gureenjoh🖤