25
by @gureenjoh
KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
Zuhraa
Hamrah
Igiyar Rayuwa
Noor Iman
Ruwan Sama..
Lelewal
GAMON JINI paid
And Now
Kowa Ya ga zabuwa..
PAGE 25
FREE BOOK
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Na gode matuka da adu'o'inku duk babu wadda ban gani ba... Allah ubangiji ya bar zumunci, baki yayi kaɗan ya furta irin godiya ta da kulawar ku... Wannan page ɗin naku ne masoyan Kowa yaga zabuwa🥰😍
"Sam ba zan iya baka gudummawa wurin saɓawa mahaifiyarka ba ya hamza, mu cigaba da Adu'a kaji? Sannan kayi hakuri komai ze zo ya wuce kaman ba'a yi ba"
Ta faɗa a tausashe sbd yadda hamza ya fara bata tausayi da gaske yake sonta yake sossai.
Ajiyar zuciya ya sauke ba wai don hankalinshi ya kwanta ba suka yi sallama, ta jima zaune a wurin cikin tunani kan ta miƙe ta fito wurin yaran, yau har suka yi magrib da isha be dawo ba saɓanin yadda ya saba yi a gida tare da yaran.
Suna zaune a dining suna cin abincin dare ita kuma tana tsaye a kansu tana Haɗawa Junior custard ya shigo, sannu da zuwa suka mishi da kai ya amsa kawai ya wuce room ɗinshi.
Ba'a yi awa da shigar shi ba se ga Kimorah ta shigo sanye da wasu irin kaya da daga ka gani ka san wannan a addininsun ma an wuce gona da iri, kallo ɗaya ta yiwa dining ɗin tace
"Norah, baby Farrah hey!"
Kan ta wuce ɗakin Raed ɗin, lumshe idanu Hidayat tayi tana me kau da kai..
Norah ma fuskanta be nuna ta ji daaɗin zuwan na buduruwar mahaifin nasu ba, se cin abincin ya zama wani iri haka suka gama suka tarkata suka wuce ɗakin hidayat ɗin, duk yadda yaran suka so su sanya ta cikin hiran su bata iya shiga ba haka suka kyale ta..
"Ma....ma u..wa"
Junior ya fadi cikin harshen yara waenda basu iya magana ba, Norah na assignment ne Aisha kam har tayi bacci yayinda Farrah take riƙe dashi hakan yasa hidayat ɗin miƙewa tace
"bari in kawo maka junior"
Ficewa tayi Sam bata kula dasu ba seda ta zo tsakiyar parlorn, zaune yake a karkace system ɗaure a kafanshi yana kallon Umar series yayinda kwance daga jikinshi Kimorah ce tana ta mishi magana cikin kanƙan da murya.
Da sauri hidayat ta kau da kai ganin sun Haɗa idanu a hankali ta musu sannu kan ta wuce kitchen, buɗe fridge tayi ta ɗauki ruwa me sanyi ta sha sossai tana jin ba daidai ba gabaɗaya a yanayinta, ta jima tsaye nan ba abunda take kan ta ɗauki ruwa marar sanyi ta fito, bata kalli inda suke ba ta wuce ɗaki..
"Why are u looking at her?"
Maganan Kimorah yasa ya ɗauke kai daga kallon bayanta ya mayar system ba tare da yace komai ba.
"Meyasa se in ta maka magana kana share ni ne? Tun fa kan na tafi na dena gane maka ɗan kulani da kake wadda shi kaɗai ma yake sawa inji na fi kowacce mace ɗin ma yanzu baka yi, yanzu ko kwanciya nayi jikinka ka dinga ture ni kenan idan ba na nace ba sede in hakura, please in wani abu nayi maka ka faɗamun"
Tayi magana da harshen turanci cikin Raurau da idanu.
Yace cikin gajiya da komai da ma kallon..
"Please kimorah let me be! Ki shiga spare room ɗin chan ki kwana ko kije one of the rooms down stairs am not in the mood"
Zata yi magana ya ɗaga mata hannu tare da mikewa ya shige dakinshi, haka ya karasa duk abunda ze yi ya kwanta cike da wasu tunannuka..
Washegari tayi ayyukan ta fiye ma da yadda ta saba tashi don kan ace bakwai ta gama komai da komai tayi wanka, bata jira tafiyar yaran ba ta fice don Allah ya gani kwanan ta da wannan buduruwar tashi inuwa ɗaya ba karamin baƙanta ranta yayi ba, haka ta isa makarantar ma ajin bata wani fahimta sossai ba.
Bayan ta gaji da kallon malamin kawai ta fito ta samu wani keɓantaccen wuri ta zauna, lokaci lokaci se ta share hawaye, rabon da tayi kuka tun daga ranar da aka bata labarinshi shima na tausayinshi ne amma kukan dake fita daga zuciyarta tun tana gidan Yusuf se gashi yau tana yi haiƙan.
Kafaɗanta taji an dafa, da sauri ta ɗago tana share hawayen idanunta se suka Haɗa idanu da Rashida..
"Hidayat! Lafiya kike kuka?"
Kai ta gyaɗa tace
"lafiya ƙalau Rashida, ba kuma kuka Nake ba"
"karƙi maida karuwa ƴar iska mana hidayat, ai ko makancewa nayi na shafa idanunkin nan na san kin sha kuka, ko de baki ɗauke ni yadda kika ɗauki ummi bane?"
A hankali tace
"Wallahi ba haka Bane, maganan ban san ta inda zan fara bane!"
"Fara ta ko ma ina ne zan baki listening ear"
Zata yi magana taji an ce
"Maama!"
Da sauri ta juya se taga, Norah da Farrah da Aisha tsaye amma Aishan ce tayi kiran.. Da sauri suka zo suka yi hugging nata..
Ɗago Aisha Rashida tayi tace
"Hidayat wannan ƙanwarki ce ko? Kinga yadda kuka yi kama?"
Dariya ne ya kama hidayat tace
"wani irin ƙanwa baki ji tace mama ba?"
Harara ta zabga mata tare da cewa Aisha da tace mata ina yini.
"Lafiya, gayamin gaskiya waye mamanki?"
Hannu ta ɗaga ta nuna hidayat tace
"itace mamanmu da ni da Ya Usman da kuma Junior, ko mama?"
Wara idanu Rashida tayi tace
"har ku uku?"
Kanta se ya kulle hidayat at her age har ta haifi yara uku? Sannan in ta haihu me yasa yanzu suke nema da hamza? Ya abun yake ne kam..
Maganan Norah ne ta katse ta.
"Miss hidayat! Daad is waiting in the car and he hates that."
Wara idanu tayi tace
"Meyasa baki faɗa min tuntuni ba? Mu Je"
Gaba suka yi se Rashida ta rike hannunta tace
"amma kin san ba zan bari ki tafi cikin damuwa ba ko? Ina so muyi magana tunda babu ummi ina so please kiyi shearing problems ɗinki dani wallahi aminiya na dauke ki"
Ajiyar zuciya ta Sauke tace
"yanzu kinga ana jira na ko zaki biyoni muje gidan se muyi magana?"
Kai Rashida ta gyaɗa suka fito a tare, ya ɗan sauke glass ɗin gefenshi fuskanshi a kame as usual.
Lekawa Rashida tayi ta gaishe shi se suka Haɗa idanu, gabaɗaya idanunta ta fiddo waje..
"OMG! Moh Raed??"
Wani ƙara ta saki tana sake Lekawa da kyau wallahi kuwa shine..
Murmushi ya saki ganinta da Hidayat ya san maybe ƙawarta ce, hidayat ce ta ja hannunta suka shiga motan tana sake kallon Raed, yau gata ga famous footballer da sede a kalla a TV ko a waya.
Har suka isa gidan bata dena mamaki ba, no wonder Norah suke kama sossai ai ita babbar fan ɗinshi ce.
Ko da suka isa gidan haka tayi ta kallon gidan kaman bata taɓa shiga gida irin shi ba kuma duk sbd dumbin mamakin yau gata a gidanshi har ciki ciki take yi.
Ko da suka isa ɗaki hidayat ta mata masauki tace bari ta samu simple abu ta yiwa yaran se suyi magana.
Norah ta turo ta kawo mata ruwa da snack, se ga Aisha da Junior sun shiga karɓan shi tayi tana mishi wasa.
Da Norah da ta fara shiga kitchen suna ayyuka tare tayi girkin ta gama ta zuzzuba musu lokacin da ta kai ɗaki rike da wani madaidaicin haɗaɗɗen tray ɗauke da warmers masu kyau da daga gani zaka san ya ja kuɗi ta samu tana sallah
Itama ruwa ta watsa tayi sallah, suka ci abinci kan hidayat ta fuskance ta.
A hankali ta fara bata labarin rayuwarta tun daga farko har kawo yau, se ga Rashida na kuka kashirban wallahi ita ko a labari bata taɓa gamo da irin na Hidayat ba..
Seda ta nitsa kan tace
"sannu hidayat lallai kinga rayuwa! Kuma daga hamza har Raed sun taka muhimmiyar rawa a rayuwar ki sede ko kama kafan na Raed hamza be yi ba.."
Kai ta gyaɗa tace
"na sani, Raed shi ya sama min rayuwar da nake cikin yanzu cikin sukuni da salama shiyasa nake iya yi na wurin ganin na taimakesu da yaranshi yadda zasu samu aljanna suma ta sanadiyata"
Rashida tace
"Amma Allah ya tsinewa Yusuf!"
Dariya maganan ya ba hidayat wadda se da ta dara ganin yadda Rashida tayi maganan kaman taga Yusuf a gabanta ta bindige.
"Hidayat maganan gaskiya ina Tunanin ke da Raed kuna son juna..!"
Gabaɗaya idanunta ta waro
"Ki rufamin asiri don Allah karki faɗa wani ya ji... Me Irin Raed ze yi dani? He is my boss for goodness sake in don damuwar da na shiga ne ba wai sbd wani abu bane ina baƙin cikin kasancewar shi cikin masu aikata laifin zina ne ba komai ba.."
Rashida dake sake da baki take kallonta tace
"ni bance ki kare kanki ba, sede fa na san Raed kuwa shi ke da abunda ze yi dake, wai kina kallon madubi kuwa? Wallahi idan ba don na kalli Aisha da Junior kuma naji labarin ki ba ba zan taɓa yarda kin haifesu ba.. U are really every man's dream kaman yadda Raed yake every woman dream kinga kenan se ku haɗu ku bada kala..."
Ajiyar zuciya ta sauke tace
"ni yanzu ba wannan ba Rashida taya kike Tunanin zan yi facing nashi da maganan haramcin zina? Yarinyar nan don bata da kunya kwance fa dare dare na sameta jikinshi jiya haka ma rannan.."
Dariya Rashida tayi kan tace
"uhmm, kawai ki fuskance shi ki mishi magana ta hankali da basira..amma ni de na san kuna son juna gwara kun dena kauce kauce ke kin mishi maganan wani ya ɗau fushi ke kuma ya kawo buduruwarshi kin hau koke koke!"
Duka take shirin daƙa mata ta ja baya tana dariya, ajiyar zuciya hidayat ta sauke tace
"amma ni kam hamza nake tunani! Shine ya furta mini kalamar so tun ban san kaina ba, bayan na fito ya sake tara ta da Kalmar so ba zan iya watsa mishi ƙasa a idanu ba zan yi Adu'a idan Hamza Allah yace in aura se kiga an yi Dukda yanzu auren baya gabana.. Don ban tsinci komai cikinshi da ze sani sake marmarin koma mai da garaje ba"
Ajiyar zuciya Rashida ta sauke itama tana duba hamza kam daga ganin yadda yake yiwa hidayat zaka san irin su ko kwanciya tace yayi tabi bayanshi ta wuce tsab ze kwanta.
Tattaunawa suka sake yi kan, rashida ta mike da shirin tafiya.
Har ƙasa ta raka ta kan ta koma, tana jin hayaniyar su Norah a ɗakin Farrah sede bata leƙa ba ta nufi kitchen daidai lokacin shi kuma ya fito riƙe da coffee a hannu, saura kaɗan suyi karo yayi saurin janyewa har coffeen na fantsalar mishi a hannu, runtse idanu yayi a ɗan razane tace
"Subhanallah! Sannu don Allah ban san kana zuwa ba"
Kai ya gyaɗa mata ze wuce tace
"am..umm don Allah ina so ne muyi magana yallaɓai"
Kallonta yayi se ya kalli parlor, ta gane ba son Magana yake ba hakan yasa ya nuna mata da idanu akan suje parlor.
Seda ta bari ya je ya zauna kan ta zo ta zauna itama cikin lafazi me taushi ta fara magana na hankali.
Ayoyi da hadisai waenda ta sani da suka yi magana akan zina da haramcinsu ta fara ja mishi tana yi idanunta na cika da hawaye tana sharewa tana iya tuna a farkon aurenta da Yusuf a sadda ta fara fahimtar irin banzar ɗabi'ar shi ta zauna ta mishi wannan nasihan sede dukan da ya mata a yanzu da ta tuna Seda taji a jikinta kaman yanzu abun ke faruwa take duk wani tsika na jikinta ya tashi.
Tsam ya miƙe daga inda yake ya dawo kusa da ita yana shirin zama tayi saurin saka hannu tana kare fuskanta a razane tace
"Don Allah kayi hakuri ya yusuf...!"
Wani irin karyewa zuciyarshi tayi, after some months da ya kusa rufa shekara don yanzu wata ya saura ta cika one year da barin Nigeria, har yanzu akwai wannan taɓo ashe ƙasar zuciyarta? Tausayinta ne ya motsa a ƙasan ranshi wadda ya saka shi lumshe idanu a hankali yace
"calm down hidayat ban taɓa dukan ko kare bane bare mutum..! A jinsin ma ba namiji ba Mace.. I can't!"
Hawayen idanunta ne ya gangaro tayi saurin dawowa hayyacinta tace
"kayi haƙuri please"
Ya ɗan yi murmushi yace
"kalma me sauƙi kenan a bakinki na fahimta"
Gyara fuskanshi yayi yace
"Hidayat." Da sauri ta ɗago Seda suka Haɗa idanu yace
"ban taɓa aikata zina ba hidayat! Zina na daga cikin abunda na kyamata a duniya bayan shan kayan maye da tattoo... Ban sani bane ko Allah ya kare ni saboda watakila mahaifiyata ta taɓa yi min Adu'ar kariya daga sharrin su, ban sani bane ko Allah na so na da rahamar shi ne yasa ya kare ni all I know duk yadda mata suke rububin kawo kansu gareni a kyauta ma ban taɓa kallon wata da fuskan sha'awa ba."
Se kunyar maganan da tayi ya kama ta, Allah sarki ta mishi mummunan fahimta sede duk wadda ze ga yadda kimorah ke shishige mishi da yadda suke kwana ɗaki daya kaman yadda take ji bakin su Norah Dukda ta kan kwaɓesu kan maganan yaje ko ina har yanzu ma sun bari, tsab zaka ce sun yi ɗin ashe shiyasa Allah ya haramta shedar zina anyhow...
"Am sorry!"
Yana kallon fuskanta dake nuna kunyar da taji se yaji ta burge shi, be taɓa ganin wata na kunya a gabanshi ba se yau ko don rayuwar turawa ba ruwansu da wani kunya ne oho..
"U don't have to! Se menene kuma be da kyau?"
Yayi maganan da iyakar gaskiyar shi.
A hankali ta ɗago ta kalleshi se suka Haɗa idanu sun ɗau seconds suna kallon juna kan ta kalli gashin kanshi da kana gani ka san ba kananun kuɗi ya ja a gyara da style ɗin ba, ta kuma kallon kunnenshi dake ɗauke da ɗan kunnen diamond ga dama ta samu sede tana tsoron kar ya ki amincewa saboda ta san yana mishi kyau ne ya saka.
"Uhyimm...!"
Ya faɗi kalamar daga ƙasan makoshi wadda seda ta ji har tsakiyar jininta.
Tattaro kuzarinta tayi ta fara magana.
"Akwai hadisin da annabi yayi magana akan maza masu shiga ta siffa irin ta mata sakamakon su wuta ne hakanan mata masu shiga ta sutura da kamanni irin ta maza su ma hakan ne"
A hankali ya sa hannu ya cire ɗan kunnen kunnenshi se ya wara mata fari Kal ɗin tafin hannun dauke da ɗan kunnen yace
"is it about this?"
Kai ta gyaɗa. Yace
"as from today an gama... Then?"
Kallonshi ta sake yi cikin kokonto yadda yake yin komai ba musu ko tantama shi ya fi tafiya da ita.
"See ina so na zama pure, a irin wa'azuzzukan da nake ji about jannah and hellfire I really want to be among alhul jannah... I badly want my relationship with my almighty to be good! U are an angel sent by him to us idan kika gani don't resitate kiyi mana gyara because maybe kan mu gani a Wa'azin ya jima.."
Ajiyar zuciya ta sauke tabbas kalamanshi masu tasiri ne, hakanan tsantsar gaskiya ce a ciki kwarai da dalilin haduwar rayuwarsu, komai dama Allah yayi shi cikin qadr.
"Wannan hairstyle.. Akwai hadisin da annabi yayi magana akai inda yayi hani da aske gashi rabi da rabi, wato a kwashe wani ya fi wani tsawo sede idan zaka aske ka aske gabaɗaya hakanan idan zaka tara ka tara gabaɗaya"
Kai ya gyaɗa yace
"I will change this hairstyle first thing in the morning... Thank you. Se me kuma?"
Tace bayan ta maida kanta ƙasa
"taɓa mace ko namijin da ba muharramarka ba ko da ba da sunan zina bane annabi yace da ka aikata hakan gwara an buga maka kusa inci tara a tsakiyar kanka"
Idanu ya lumshe yace
"Noted! Se mene?"
Ta ɗago ta narke fuska wadda ya saka shi ganin ta koma baby Farrah ko junior tace
"saboda nice sarauniyar kakale kakale ko? To ya kare"
Dariya ta bashi wadda seda ya murmusa har sautin ta fito.
"I thought akwai wani abu ne kuma and u don't want to say because of ur silly reansons da ban sani ba"
Kai ta ɗan karkata kan tace
"akwai na tuna"
Ya bata hankalin shi yace
"what's that?"
"Am sorry boss! Don Allah kayi hakuri"
Kallonta kawai yake irin kallon da ya sakata jin kaman ta narke, kaman ƙasa ya buɗe ta shige ko ta ɓace nan take su turawan nan basu san ruwan kunya ba.
Wannan kallon ma ya kamata ta mishi nashi karatun don ya fita musulunci.. Ze yi magana kenan kimorah da ta shigo tuntuni tace
"what the hell is going on here? So Raed that's the reason? This filthy nanny is the reason why you are giving me hard time?"
Yadda take magana da masifa ne yasa duk suka zuba mata idanu.
Da sauri tayi kanshi zata taɓa shi kaman wadda yaga wuta yayi sauri mikewa yana ja baya yace
"don't! Don't you ever lay ur finger on me"
Wani irin kukan kura tayi tayi kan Hidayat....
#Vote
#share
#comment
🖤Gureenjoh🖤