26
by @gureenjoh
KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
Zuhraa
Hamrah
Igiyar Rayuwa
Noor Iman
Ruwan Sama..
Lelewal
GAMON JINI paid
And Now
Kowa Ya ga zabuwa..
PAGE 26
FREE BOOK
Fisgota yayi da karfi kan ta ƙarasa kanta ya nuna ta da yatsa yace cikin harshen turanci
"karki kuskura ki fara abunda bazaki iya ba... Now! Get out of my house...!"
Idanunta gabaɗaya ta waro tace
"what do you mean?"
"I mean it's over between us.."
Kuka ta fashe dashi a zuciye ta wuce room da ta kwana ta janyo kayan ta ta fito ta sauka da gudu tana kuka.
Tsaki yaja yana ɗauke kai daga kallonta se suka Haɗa idanu wani irin numfashin tsoro take ta saukewa, kanta ta mayar kasa tare da cewa
"Seda safe"
Bata jira amsar shi ba ta wuce
Washegari shi ya sauke ta a makaranta Dukda dae ba wani hira suka yi ba bayan gaisuwa sede fuskanshi a sake ba kaman sadda yake fushi ba kuma sossai taji daaɗin hakan.
****
Roba me ɗauke da garin kunu kaɗan da kuma kullin tsamiya da gyaɗa ta dire mata.
"Tashi ki yi min kunu karki yarda tsamiya yayi yawa kuma ya nuna kar yayi ruwa"
Kallonta Surayya tayi zata yi magana suka Haɗa idanu da Umma ta girgiza mata kai alamun kar tayi.
Miƙewa Surayya tayi ta ɗauki robar kunun ta yi bakin murhu tana mitan..
"Kece matsiyaciya da kike shan kunu in ba da yanzu rayuwa ya chanza ba ai ko sunan kunu ba'a kira mana gida daga custard se oat"
Tak bata ce ba ta samu kujera ta zauna, a cike take da su dukkansu kuma kaɗan take jira kab ta saita musu zama, umma dake zaune cikin Asabar da Lahadi na kodaddiyar Atampha ta zabga tagumi tana Tunanin Abba
A lokacin da yayi mutuwar son tayi karatu ko don bayan ranshi tayi amfani da aikinta wurin kula dasu sede Sam ta ƙi tana ganin yana dashi ko ya mutu ba zasu yi rashi ba, ya sha gayamata dukiyar gado iska ce tsab se ta iya bin me shi cikin lokaci ƙankani, ya sha gayamata rayuwa ba tabbas sede duk tayi watsi da hakan.
Yau a yanzu wa gari ya waya? Da Kausar taƙi karatu ma ita ce ta bata goyon baya haka Abban ya hakura ita kuma fahiriyya a sadda zata auri mijinta da take aure ya shaida musu ba karatu a gidanshi Abba ya ƙi bada ita ba karamin bore suka yi ba haka ya hakura ya zuba musu idanu, ita Surayya da take ɗan karatun an kore ta saboda rashin kokari gatan da ta nuna mata na Hidayat take yi mata komai ciki har test da exams ya ja mata.
Yusuf bashi da maraba da mahaukaci, wanchan kuma bata ma san duniyar da yake ba..! Wata ashariya da hafsatu ta saki ne ya katsewa Umman tunani.
Mari ta gaure Surayya dashi tace
"don uwarki wanchan dake zaune haka na baki umarnin dama min kunu?"
Surayya tace
"Wallahi ba de uwata b..."
Kwashe ta da tayi ya hana maganan karasa fitowa, se ga Surayya a ƙasa wanwar dama gata kaman karan kaɗa miya, danne ta hafsatu tayi bata damu da zafin kunun ba ta fara ɗura mata tana cewa
"yau se nayi maganin bakin rashin kunyar nan..! Zaki san ni kika yi kokarin zagi"
Ga tsinkakken kunu, ga Shakura, ga tsami saboda tsamiyar da ta labta don mugunta ga rashin sugar da zafin kunun duka ya Haɗar mata shidewa take sede ko a jikin hafsatu, ba ta sake ta ba seda taga kunun na fitowa har ta hanci ga idanunta kaman garwashi ko da ta sake ta mikewa tayi ta fara kwara amai tana tari kaman zata mutu.
Idanu kawai umma ta zuba mata hawaye na gangaro mata a idanu tana tuna sadda suka yiwa hidayat ɗuren custard, lallai annabi yayi gaskiya da yace yadda kayi haka za'a yi maka.
Surayya bata gama tari da aman ba suka fara jin hayaniya a kofar gida, tsaye umma ta mike ganin an shigo da Yusuf ranga ranga jiki jina jina.
"Lafiya me ya faru?"
"Ki Ja wa wannan mahaukacin ɗan naki kunne ko kuma ku samu mari ku ɗaure shi yau duka kawai ya samu gobe kuma ina ga sede bindiga..."
"Ban gane ba bawan Allah me yayi?"
Wani daga cikin waenda suka shigo da shin yace
"zaki gane ne a sadda aka shigo miki da gawarshi in ba mahaukaci ba daga ganin ɗan DPO rike da hannun Babanshi ya ruga ya chakwame yaro yana kiran sunan wani Usman, yaro ya firgice anyi anyi ya saki ɗan mutane ya ki ya kwankwame shi seda DPO yasa yaranshi suka lallasa shi kan ya saki yaron don azaba, to wlh gobe yayiwa soja haka harbe shi ze yi ba ruwanshi.."
Yusuf din umma ke kallo har suka fita, ba karamin duka ya sha ba se hawaye ke zuba a idanunshi.
Ta kalli Surayya da ta lallaɓa ta miƙe ta shige ɗaki, ta san matarshi na ji sede bazata fito ba ko in ta fiton ma sede ta kara mishi akan ciwon da nata tashin hankalin.
Murhun da Surayya bata kashe ba taje ta ɗaura ruwan zafi ta zauna ta zabga tagumi har yayi ta surka kaɗan ta zo tana matse mishi yana ihu tana share hawaye cike da Tunanin mafita.
*****
"ya hamza..!"
Zainab ta kirashi.
Firgigit ya dawo daga duniyar da ya shiga yace
"uhm baby hidayah"
Haɗe rai tayi ji wani salon iskanci, zata fara magana ya tuna barnar da yayi se yayi sauri cewa
"Don Allah kiyi haƙuri! Faɗamin menene?"
Harara ta zabga mishi ba don maganan da take son faɗa mai ba da ta bar wurin don yanzu zancen hidayat kaman ruwa yake a wurinshi, motsi kaɗan se ya ambace ta ta rasa wani kalar kyau hidayat ɗin ke dashi da ze susuce a kanta, ta rasa da wani irin Boka hidayat ke tsafi da zata kanainaye mata miji ta hanata zaman lafiya a gida, kab duniya in kace wa ta tsana to hidayat ce..
"Ina so in na haifi namiji a saka mishi sunan Abbana.. Idan kuma macece se ta ci sunan Hajiya ka yarda?"
Kallonta yayi na mintuna kan yace
"idan macece sunanta Hidayat.. zainab"
"mene? Sunan wanchan karu...."
Wani irin tsawa ya daka mata
"karki kuskura ki sa in nuna miki ɗayar kala ta, wallahi a duk sadda kika sake yin kuskuren danganta hidayat da mummunan kalma se na lahira ya fi ki jin daaɗi in kina Tunanin wasa ne kuma ki gwada... Sannan ina so ki rubuta ki ajiye in har nine uban abunda ke cikinki in har dae mace kika haifa babu fashi sunanta Hidayat..!"
Ya faɗa cikin zafin ran da hajiya ke sa mishi tension ɗin kuma sanadiyar zainab shiyasa take matukar bashi haushi, ya tsani mutum me kai ƙara anyhow zainab kuma tambarin ta kenan.
Be gama Tunanin ba Wayanshi ya fara kira dubawa yayi yaga hajiya, ya tabbatar zainab tayi aikin da ta saba, tsaki ya ja yana ƙara ji tana fitar mishi a rai, kaman ba ze ɗauka ba se kuma ya ɗaga
"Sannu isasshe..! Wato dayake hidayat ɗin itace uwarka shine zaka tada wa matarka jijiyan wuya akan ɗan cikin da ita ta ɗauki rainon kayan ta kuma zata sha wahalar nakuda ko? Wallahi hamza ka kiyayi ɓacin raina. Wai da wani irin Boka wannan hidayat ɗin take takama ne?"
Yace cikin muryar da ke nuna lallai ranshi a bace yake an taɓa hidayat.
"Hajiya hidayat baiwar Allah ce don Allah ki dena danganta ta da Boka, kiyi hakuri kuma amma na riga nayi rantsuwa in dae har mace zainab ta haifa sunanta Hidayat."
Kasa magana hajiya tayi daga karshe tace
"na yarda asiri gaskiyar me shi, wato ni kake sa'in sa da yau ko? To ba matsala zan ga uban da ze yarje maka auren ita hidayat ɗin take ko wa.. Sannan in har ni na haifeka ka tsallakeni ka sakawa ɗiyar ka sunan wata bazawara wallahi zaka gane baka da wayau, shashasha kawai"
Kit ta kashe wayan.
Takaici ya saka shi jin kaman ya sa hannu a kai yayi ta ihu, wallahi shi karan kanshi be san yaushe ya fara yiwa hidayat ɗin irin wannan son ba, gashi Allah ya ɗauki ran kakanshi wadda ya taɓa yi wa hidayat gyaran hannu da ya san kwarai ze shige mishi gaba wurin ganin ya mallake ta.
Gidan ya tafi don in ba Wurin Abban shi yaje ba baze samu natsuwar da yake buƙata ba, in ka ganshi kaman ba hamza ɗan gayu ba, ya tara kasumba wadda ya saka ramarshi fita, da Tunanin kasancewar hidayat inuwa ɗaya da Raed yake kwana yake tashi, ko ball yaga ake yi da PSG in har ya kyalla ido ya ga Raed ya ga irin kyaun sura da baiwa da Allah ya mishi se yaji kaman yayi hauka.
A gaban Abban ya zauna yana rike da hannun shi ya fara faɗa mishi abunda hajiya tace kaman Abban na ji.
Har ya gama yayi shiru, shi ba me yawan abokai bane Dukda yana da su ɗin sede be da maganan da ze sa ya iya baza musu duk wani sirrin shi, yana matukar kaunar Abban shi kaman yadda yake tuna sadda yake ƙarami Abban ke matukar ƙaunar shi ya san shi ze fahimce shi, Hajiya don tana mace ne ta kasa fahimtar shi.
Motsi Abban yayi wadda ya saka hamza waro dukkan idanunshi waje..
Kaman wadda aka Umarta a hankali yayi ta kokarin buɗe idanunshi wadda ya saka hamza Suman tsaye, wani irin sassanyar farin ciki ne ya lulluɓe shi yana mamaye dukkan ilahirin jikinshi.
Da gudu ya fito yana kiran hajiya.
"Wai menene? Ni kam na shiga uku na lalace hidayat ta haukata min ɗa. Me hakan?"
"Hajiya Abba ya buɗe idanu, Alhamdulillah Abba ya farka hajiya.."
Harara ta maka mishi tace
"mutumin da ƙasar waje ma cewa suka yi mu sa hannu a karasa shi saboda babu ranar waraka shine zaka ce ya buɗe ido?"
Hannunta kawai ya janyo don ba ze iya magana ba, suna shiga kuwa Abba da ya rufe idanun saboda haske da ya mishi yawa ya sake fara kokarin buɗewa ai murna a wurin su ba'a magana nan take suka fita dashi aka yi asibiti don ba zasu iya jiran doctor ba.
****
Zaune yake shiru a ɗaki yana jin wani irin tone tone da matan nashi ke yi suna baje iskan hammata, a razane ya miƙe tsaye da yaji sadda zarah ke cewa
"azzaluma me Haɗa husuma tsakanin uba da ɗa... Wato abunda kika yiwa Raed har yayi sanadiyar barin shi gidan nan nima shi kike kokarin yiwa ta wa ƴar to ahir ɗin ki me gida da mota dae se ta aura.. Ki ji da ƴan daba da karuwan yaran ki"
Wani irin shewa Badi'ah tayi tace
"ai gwara ni abunda nayi me sauƙi ne, ke fa? Tsabar tsanar da kika yiwa uwar Raed ina anan kika shiga kika sace kuɗin malam ya zo ya lakada mata duka wadda sanadin shi ta gamu da ajalin ta...? Gwara ni sau dubu muna da mashinshina Dukda ƴar daban ce, karuwancin na ki su samu mana"
Da wani irin gudun da be san akwai sauran karfin yinshi ba saboda cin rogo carbohydrate yayi yawa ya fito a hautsine yace
"maimaita abubuwan da kuke cewa ban ji da kyau ba...!"
Wiki wiki suka fara da idanu don tsabar masifa sun manta yana nan..
Da gudu yaje ya rufe kofar gidanshi ya dawo da arda da gora.
"Ko ku min filla filla ko in kashe ku in ya so nima se a kasheni...!"
****
"Rashida ba karamin mamaki yallaɓai ya bani ba...ban taɓa cin karo da namiji irin shi ba tabbas da a cikin musulunci tsantsa ya tashi da musulmai sun yi alfahari da samunshi"
Rashida tace
"kin zo se koɗa shi kike tuntuni ni baki gayamin ya kuka yi ba"
Dariya hidayat tayi tace
"Rashida Allah ya tseratar da bawan shi, ya min rantsuwar be taɓa aikata zina ba, abun mamaki shi da ƴan mata suke rububi a kanshi, ga kuɗi ga suna sede ya kiyaye jefawa zuri'ar shi bala'in zina saɓanin Yusuf da ko kafan takalmin Raed be kamo ba amma ya mai da zina ado a rayuwarshi"
Rashida tace
"hmm, ai shi Allah in ya so kare bawa ko tsirara mata zasu yi yawo gabanshi Allah ze kare shi, kuma kinga yayiwa kanshi babban kiyamul laili da baya shan komai"
"ban taɓa Tunanin Yallaɓai ze biyu ta sauki ba, yanzu damuwana tsakanin shi da Mahaifinshi"
"ke kin san wallahi ina Tunanin son ki da yake ne babban maƙamin da ya sa yake biyuwa ta sauƙi"
Harara Hidayat ta zabga mata tace
"ba so ba kin manta...!"
Dariya Rashida ta kwashe dashi tace "gashi daga magana kin fara blushing"
"Rashida tsakani da Allah tsoro nake ji"
"Tsoron me?"
Ta tambaye ta tana gyara zama.
"Rashida aure! Ina yin karfin halin maganan aure ne amma in na tuna da zancen auren wlh gabana faɗuwa yake, tsoro se ya shige ni. Ko kin san har yau bana samun cikakken baccin da ya kamata bawa ya samu?"
"Na sani Hidayat! Shiyasa nake so ki godewa Allah ki kuma godewa Raed, kina Tunanin ba don shi ba rayuwa zata miki saukin blending haka ne? Ko Kin san da a Nigeria kike da yanzu baki da maraba da mahaukaciya? Abunda yasa nace haka, a nan baki ganin violence hakan ya taimaka wurin baki cikakken natsuwa, da zaki ga ana faɗa se abunda baki yi tunani ba ya same ki, hakanan zama da yaran nan shima kwarai ya taimaka miki ai a likitance taɓon da Yusuf ya miki warkewarshi ba yanzu ba.."
Kai ta gyaɗa tace
"hakane, shiyasa bana iya kallon film Sam don yana sani tsorata.. Sau ɗaya na taɓa kallon Animation ɗin su Farrah, goigoi ne amma dayake ana duka da faɗa ciki seda na kwana ban runtsa ba haka jiya da buduruwarshi ta so tada husuma wlh baki ji yadda gabana yayi ta faɗuwa ba"
Rashida ta riƙe hannunta tace
"a hankali in shaa Allah komai ze daidaita, Raed ba irin Yusuf bane zaki rabauta da samunshi"
Zata yi magana wayanta ya fara ringing ta duba taga hamza tace
"Allah se na gayawa ya hamza karfi da yaji kike son danganta ni da abunda kin san ya fi karfina"
Tana kai nan ta ɗauki wayan, suka gaisa ya faɗa mata farkawar dad ɗinshi, sossai ta taya shi murna ta ba Rashida ma ta mishi murna, suka ɗan kara magana kadan kan suka yi sallama.
Yau ko da ta iso gida bata samu yaran ba, ko da ta tambayi miss Mary tace sun fita da babansu.
A natse tayi sallah ta hau girkin rana.
Seda ta gama ta fara jerawa suka shigo suna hayaniya ga ledoji a hannunsu.
Farrah ta zo da gudu ta kama hannun ta tace
"Miss hidayat! We are going for a trip yeeeeey"
Hidayat na ajiye tray ɗin hannunta tace
"easy Farrah, school ɗin fa?"
Norah tace
"we are on mid-term break, Dad na da wasa a Belgium and he want us to attend"
Aisha ta miko mata ledojin hannunta tace.
"Dad made this shopping for you saboda kina makaranta and we don't know what u like"
Ɗago idanu tayi se suka Haɗa idanu yana riƙe da Junior, murmushi ya sakar mata itama ta mayar mishi ba tare da ta san tayi hakan ba, ta karɓi Ledar Hannun Aisha tace
"thank you Daddy!"
Dariya ta bashi sede be yi ba ya ɗan murmusa.
Yace
"the trip is with u.. Hope bazaki samu matsala da karatunki ba"
Kallonshi tayi tace
"I don't think I can make it bcs ina da assessment this week"
Kwaɓe fuska duka su uku suka yi a tare suka ce
"oh no!"
Dariya sossai hidayat tayi tace
"ba wani abu ai u will enjoy the trip I trust Daddy"
Gira ɗaya ya dage yana zama a dining ɗin irin yeah ɗin nan, dukda be ji daaɗin rashin samun zuwan tan ba, ganin kuma yaran da gaske sun damu yasa ya chanza shawara yace
"hey gurls! Calm down and eat ur food.. "Mommy" is going in shaa Allah"
Ras haka gabanta ya doka a sadda ya ambaci mommy ɗin, sossai jikinta ya karɓi sakon nashi don da wani kalar murya yayi anfani, ya wani lakaba mata mommy ita sa yaranta ma mama suke cewa su Norah kuma miss hidayat, Yaran ina suka sani se murnan zata je suke yi.
A hankali ta kalleshi, ya dage mata gira ɗaya alamun what?
"Amma ma...."
"Shiii....!!" Ya ja I ɗin yana ɗora dogon yatsanshi bisa saman tausasan lips ɗinshi da yake tauna abinci a hankali, lumshe idanunta tayi kawai tana kauda kai...
#Vote
#share
#comment
🖤Gureenjoh🖤